Free chapter · Read without an account
The Price Of Pride
CHAPTER FIVE
THE PRICE OF PRIDE
by Rabi Muhammad Shariff
Ramsha Tales
Rayuwar da Hibba ta yi a kamfanin Latif ta bar wani babban gibi a rayuwarsa. Duk da irin yadda yake nuna cewa bai damu da tafiyarta ba, a zahiri ya fara jin kamar ya rasa wani abu mai muhimmanci. Hibba ba kawai ma'aikaciya ba ce; tana da ƙwazo, basira da jajircewa wajen aiki. Duk wani aiki da aka ba ta, tana ƙoƙarin ganin ta yi shi yadda ya kamata.
Wata safiya, Latif ya tashi daga barci, ya yi wanka, sannan ya sanya kaya masu sauƙi na zaman gida. Ranar Juma'a ce, kuma ba ya zuwa ofis a irin wannan ranar. Yakan zauna a gida domin ya kasance tare da mahaifiyarsa da ƙanwarsa.
Hajiya Aisha da Layal suna zaune a falo suna cin karin kumallo cikin raha da farin ciki. A lokacin ne Hajiya Aisha ta fara magana kan batun auren Latif, domin wannan ce maganar da ta fi yawan yi masa.
"Latif, yaushe za ka yi aure ne? Ka san fa ba zan gaji da tambayarka ba. Ina so in ga ka yi aure tun ina da rai," Hajiya Aisha ta faɗa tana kallonsa.
Latif ya yi murmushi kawai, bai ce komai ba.
Suna cikin wannan hirar ne aka ji an shigo gidan. Da suka juya, sai ga Jaddah, kakar Latif, wadda ta fito daga ƙauyensu.
Duk da cewa Hajiya Aisha ta daɗe tana son Jaddah ta dawo ta zauna a birni tare da su, Jaddah ta ƙi amincewa. Ta fi son zaman ƙauyensu saboda yadda ta saba da rayuwar wurin da kuma mutanen da ke zaune a ciki. A ƙarshe, sai suka haƙura suka bar ta, amma suka ɗauki wata ma'aikaciya da za ta riƙa kula da ita, tana mata wanki, girki da sauran ayyukan gida.
Duk da haka, Jaddah ba ta cika son a yi mata komai ba. Wani lokaci ma sai ta ce ana son a mayar da ita mai san jiki, ta tashi ta yi ayyukanta da kanta.
Abin da ya fi haka kuwa shi ne, Jaddah mace ce mai son magana, musamman idan ta kama mutum da wata magana. Idan ta taso mutum gaba, sai ya ji kamar ya gudu ya bar wurin.
Yanzu ga ta nan ta shigo gidan, ɗauke da wani babban buhu da kuma tarin kaya. Babu wanda ya san abin da ya kawo ta birni a wannan karon.
Da suka gan ta, kowa ya yi farin cikin zuwanta. Layal ce ta fara tashi tana zuwa wajenta.
"Jaddah, sannu da zuwa! Jaddah uwar rigima!" Layal ta faɗa cikin fara'a.
Maimakon Jaddah ta amsa mata da fara'a, sai ta murɗe fuska.
"Ku 'yan birnin nan kun zama kamar ba ku san yadda ake gaishe da mutum ba. Duk sai ku shake masa wuya wai kuna nuna ƙauna!"
Layal ta yi murmushi.
"Haba Jaddah, na yi missing ɗinki ne fa!"
Jaddah ta ƙara murɗe fuska.
"To, na ji. Mu je."
Hajiya Aisha ta durƙusa ta gaishe da ita, ta yi mata barka da zuwa. Jaddah ta amsa cikin fara'a, sannan ta sa mata albarka.
Sai ta fara leƙen ko'ina.
"Amma ban ga wannan ja'irin tuzurun ba. Shi ba zai fito ya tarbe ni ba ne?"
Hajiya Aisha da Layal suka yi dariya.
A lokacin ne Latif ya ƙaraso da ɗan murmushi a fuskarsa.
"Haba Jaddah, ai dole in zo in gaishe da ke."
Ya yi ƙoƙarin rungumar ta, amma Jaddah ta yi saurin ja da baya.
"Kai, matsa! Ni mace ce, amma ban yarda kowa ya rungume ni ba. Ballantana kai, baligin tuzuru!"
Layal ta ɗan haɗe rai.
"Haba Jaddah, tuzuru kuma?"
Jaddah ta dube ta.
"Eh mana! Ka yi aure. Idan ba ka so, in gaya maka haka? Kai wuce ka ɗebo kayana!"
Ta juya ga Layal.
"Ke kuma, mu je."
Latif ya ɗauki jakunkunan Jaddah da buhunan kayanta, ya kai su inda ya kamata. Bayan ya gama, sai ya dawo ya zauna kusa da ita.
Ya kalle ta da murmushi.
"Jaddah, ko dai kin canza shawara ne yanzu? Za ki zauna a nan ne?"
Jaddah ta harare shi.
"A dole na dawo, ko? Ai tun da na ga Indo ta kasa sa ka aure, sai na ga ya dace in zo da kaina."
Latif ya ɗan ɓata rai.
"Wace Indo kuma, Jaddah? Haba mana!"
Jaddah ta taɓe baki.
"Uwar ka mana! Akwai wata Indo da ka sani ban da ita? Duk kun zama irin ɗaya. Ka zama baligi, ka ƙi aure!"
Ta ɗan gyara zamanta sannan ta ci gaba.
"To, ni yanzu na zo da niyyar sa ka aure. Wallahi sai ka yi aure kafin in koma ƙauye. Yanzu dai ka gaya mini, wace mace kake so?"
Latif ya haɗe rai.
"Ni fa ba ni da budurwa."
Jaddah ta yi saurin miƙewa tsaye, ta zaro ido.
"Ba ka da budurwa? Kai, baligi da kai! Ga ka da kyau, ga ka da kuɗi, amma ba ka da mace? To, ko dai ba lafiyayye ba ne kai?"
Latif ya tashi tsaye.
"Haba Jaddah!"
Jaddah ta nuna shi da yatsa.
"To, idan ba rashin lafiya ba ne, me ya hana ka samun mace ka yi aure? A can ƙauyensu ma, yanzu namiji ɗan shekara goma sha biyar yana burin yin aure!"
Latif ya girgiza kai.
"Ba su da future ne shi ya sa."
Ya miƙe yana tashi.
"Ni fa barci nake ji. Tsohuwar nan, za ki zo ki sa mutum ciwon kai!"
Ya wuce ya bar su a wurin.
Jaddah ta girgiza kai.
"Kaji ja'irin yaro!"
Layal kuwa tana gefe tana dariya. Jaddah ta juyo gare ta.
"Ke kuma, me kike dariya? Ke da kika mai da zaman gida da saka gajerun riguna sana'a, kin ƙi neman miji!"
Layal ta buɗe baki cikin mamaki.
"Haba Jaddah! Ni fa yarinya ce!"
Jaddah ta ja da baya tana kallonta daga sama har ƙasa.
"Cibbb! Ke ce yarinyar? Wallahi ai da ya kamata kina da yara biyu ko uku yanzu!"
Dariya ta ƙare a fuskar Layal. Ta tashi a hankali ta bar wurin, ta koma ɗakinta.
Jaddah ta zauna tare da Hajiya Aisha, sannan ta fara yi mata magana cikin damuwa.
"Haba Indo, wallahi kin lalace. Ke, kina son ki ci gaba da ganin su dirka-dirka da su a gabanki haka? To, wallahi sai wannan tuzurun ya yi aure kafin in koma ƙauye!"
Hajiya Aisha ta yi murmushi cikin jin kunya.
"To, Jaddah, ai yadda kika ce haka za a yi."
Shi kuwa Latif, da ya koma ɗakinsa, ya ɗauki laptop ɗinsa sannan ya kira Alisa ta hanyar video call.
Alisa ta amsa kiran.
"Good morning, sir."
Latif ya amsa mata, sannan ta fara magana.
"Sir, waɗannan mutanen sun ce suna son Hibba ta jagoranci wannan aikin gaba ɗaya. Sun ce saboda yadda ta tsara design ɗin, ita ce ya kamata ta kula da sauran aikin."
Latif ya ɗan ɓata rai.
"Amma Hibba ba ta aiki da mu yanzu. Ki gaya musu haka."
Alisa ta ɗan yi shiru, sannan ta ce, "But, sir, don't you think if they find out that the person who designed the project won't be leading it, they might reject the whole thing? Honestly, sir, we've never had a design as good as Hibba's."
Latif ya ƙara haɗa rai.
"Don't talk nonsense, Alisa. What do you mean? With or without Hibba, my company will keep moving."
Alisa ta sauke numfashi.
"I'm sorry, sir, but this time, I think we might lose the contract."
Maganar ta ƙara harzuƙa Latif. Ba tare da ya ce komai ba, sai ya katse kiran.
Ya tashi daga inda yake zaune, ya buga ƙafarsa a gefen gado.
"So what if she resigned? I can do my work!"
Ya furta hakan cikin fushi, yana ƙoƙarin shawo kan kansa cewa kamfaninsa ba zai tsaya saboda tafiyar Hibba ba.
Yana cikin ɗakin ne ya ji muryar Jaddah tana kiransa.
"Ahmadu! Ahmadudu!"
Latif ya runtse ido.
"Kash! Wai Ahmadudu? Dan Allah, tsohuwar nan za ta sa mini ciwon kai!"
Ya shiga toilet, yana ƙoƙarin guje mata.
Jaddah ta shigo ɗakin ta zauna a gefen gado.
"Ahmadudu, kana ina ne?"
A lokacin ne ta ji alamun ruwa yana zuba daga toilet.
Ta ɗan yi shiru, sannan ta ce, "Kai, Ahmadu, haka ake yin wanka? Ko dai bayan gida kake yi ne? Ka san fa idan mutum yana yin bayan gida, wani lokaci ma ba ya iya magana, musamman idan abin ya yi tauri!"
Latif ya yi shiru, yana jin haushin maganganunta.
Bayan ɗan lokaci, ya fito daga toilet ɗin fuskarsa a haɗe.
"Haba Jaddah! Wai ni tsaya, me kika zo yi a ɗakina?"
Jaddah ta ɗan haɗe rai.
"Uwar ka na zo yi mana!"
Latif ya girgiza kai ya zauna kusa da ita.
Jaddah ta kalle shi da gaske.
"Ka saurare ni, Ahmadu. Gobe wasu mata za su zo nan. A cikinsu za ka zaɓi wadda za ka aura."
Latif ya zaro ido.
"Jaddah! Mata kuma? Kamar wani abu ake zaɓa? Ai yanzu ba haka ake yi ba. Ni fa ba ni da shirin yin aure."
Jaddah ta miƙe tsaye, ta daura hannu a kai.
"Innalillahi! To, Ahmadu, ko dai ba lafiyayye ba ne kai?"
Latif ya haɗe rai.
"Kin ga kamannina kamar na mara lafiya?"
Nan take Jaddah ta fara kuka irin na tsofaffi masu son yin rigima.
"Wayyo ni, Mariya matar Ilu! Jikana ya lalace! Wayyo ni!"
Latif ya dube ta cikin rashin haƙuri.
"Wai Jaddah, me ya faru kuma?"
Jaddah ta share hawaye.
"Ahmadu, idan ba iskanci ba ne, kai baligi ne, lafiyayye, amma ka ce ba ka da mace. To, me kake yi kenan?"
Latif ya ɗauki kansa da hannunsa.
"Kash! Ni fa ba zan iya da ke ba!"
Ya miƙe ya fita daga ɗakin, ya bar Jaddah tana girgiza kai.
Da Rana, Latif ya fita yin jogging. Yana kan hanyarsa ne wayarsa ta yi ƙara. Da ya duba, sai ya ga Alisa ce ke kiransa.
Ya ɗaga wayar.
"Me ya faru?"
Alisa ta yi saurin magana.
"Sir, waɗannan mutanen sun ce dole Hibba suke so. Sun ce ba za su amince da wani ba."
Latif ya ji ransa ya ɓaci sosai. Amma a wannan karon, ya fahimci cewa idan ya ƙi yin wani abu, akwai yiwuwar kamfaninsa ya rasa wannan babban kwangilar.
Ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ce, "Ki kira ta. Ki gaya mata ta dawo."
Alisa ta amsa, "Sir, na riga na kira ta, amma ta ce ba za ta dawo ba. I think you should talk to her yourself."
"What?" Latif ya faɗa cikin mamaki.
Alisa ta ci gaba da magana.
"Sir, please. This is the only way."
Latif ya katse kiran.
Ya tsaya a gefen hanya yana tunani.
"Ina son wannan contract ɗin, amma gaskiya ba zan iya kiranta ba!"
Ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya tuna cewa idan ya rasa wannan kwangilar, kamfaninsa zai iya yin asarar miliyoyin kuɗi.
Ya riƙe kansa.
"If she doesn't come back, my company could lose millions!"
Bayan ɗan lokaci, ya sake kiran Alisa. Da ta ɗaga wayar, bai yi magana ba, sai kawai ya ce, "Send me her number."
Ya katse kiran.
Latif yana tsaye a wurin ne lambobin Hibba suka shigo wayarsa. Ya dube su na ɗan lokaci, sannan ya kira ta.
Da Hibba ta ɗaga wayar, ta yi magana.
"Hello? Hello? Wane ne?"
Latif ya kasa magana.
Hibba ta sake cewa, "Hello? Waye ne wannan? Idan ba za ka yi magana ba, zan kashe wayar."
A ƙarshe, Latif ya tattara ƙarfin hali.
"Hibba, ki dawo aiki."
Hibba ta yi shiru na ɗan lokaci, kamar ba ta yarda da abin da ta ji ba.
"Na dawo aiki? Why? Kawai ka kira ni ne don ka ce in dawo aiki? Haka ake magana da mutum?"
Ta ɗan dakata, sannan ta ci gaba.
"Gaskiya ba zan iya sake yin aiki da kai ba. Ka ba ni wahala sosai!"
Kafin Latif ya samu damar cewa komai, sai Hibba ta katse kiran.
Latif ya tsaya yana kallon wayarsa cikin mamaki.
"Dama na san haka halinta zai kasance. Yanzu ma mutuncina ya zube kenan!"
Ya ajiye wayar, ya ci gaba da jogging ɗinsa, yana ƙoƙarin nuna wa kansa cewa bai damu ba.
Amma a zuciyarsa, ya san cewa wannan karon abubuwa sun fi ƙarfinsa.
Bayan Hibba ta yi masa wannan magana, Latif ya yi alwashin cewa ba zai sake kiranta ba. Amma matsin lambar da yake samu kan wannan aikin ya sa ya fahimci cewa ba shi da wani zaɓi.
Ya kira Alisa ya nemi ta tura masa adireshin gidan Hibba. Alisa ba ta yi musu ba; nan take ta tura masa.
Bayan ya shirya, Latif ya shiga motarsa ya nufi gidan Hibba.
A gidan Hibba kuwa, tana zaune a tsakar gida lokacin da suka ji an yi sallama.
Wani saurayi ne ya shigo da saƙo.
"Ana sallama da Hibba."
Hibba ta yi mamaki.
"Ana sallama da ni?"
Saurayin ya amsa, "Eh."
Hibba ta miƙe tsaye.
"Ina zuwa."
Ta fito daga cikin gidan, amma abin da ta gani ya sa ta tsaya cak.
Latif ne a tsaye a bakin ƙofar gidan, yana jingine da motarsa.
Ta tsaya tana kallonsa cikin mamaki. Shi ma ya juyo ya kalle ta.
Na ɗan lokaci, babu wanda ya ce komai.
Hibba ta tsaya tana jiran jin abin da ya kawo shi har gidansu.
Latif kuwa, duk da irin girman kai da yake nunawa a wajen aiki, ya fahimci cewa wannan karon ba zai iya yin magana da Hibba yadda ya saba ba.
To be continued...