Free chapter · Read without an account

45

by Anisa Muhammad Yahaya · NUFIN ALLAH



💕 NUFIN ALLAH 💕 
By
Anisa Muhammad yahaya 


 YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA

Page 4️⃣5️⃣


Abba,Baba, Daddy sai Abba Muneef da Baba munir dake nan Kano suke zaune a parlourn Daddy suna tattaunawa akan batun auren 

Dan shi Daddy so yake yi ayi bikin kafin su koma Egypt, aƙalla baza a dauki wata daya da ƴan kai ba kenan

Duk sun amince da hakan tunda duk yaran na gida ne ba bare, dan haka suka yanke wata daya 

Bayan su Abba sun tafi daddy ya kira Alhaji Muhammad mijin Momma yake faɗa mai dan daman akwai kyakkyawar fahimta da mu'amala tsakanin su

Itama Mommy Amma ta ƙira ta fara faɗa mawa,sai gashi ba jimawa ta zo gidan, part din ammi suka ƙule suna ta maida zancen da son sanin ta ina zasu ma fara, zasu aurar da yara huɗu 

Itama Anty Abba na dawowa ya sanar da ita, dan farin ciki har kwalla tayi

Koda zancen ya isa gurin su Mama da mamee ai bindiga ne kawai ba suyi ba, barin ma dai Mamee tunda tasan yanda zulaiha ke bala'in son Ahmad Kuma kowa ma yasani amma madadin a duba hakan a haɗa su shine za a nuna mata fifiko da wariyar launin fata 

Shine za'a nuna mata a family dan bata da kuɗi za amata yanda ake so, bayan sune silar rabuwar ta da mijinta mai kudi da daula, tunda tasan koda yana son Nabilan ai Zulaiha ta riga tunda kowa yasan ta daɗe tana son shi, maza nawa ta kora saboda shi za'a ce wai Nabila zai aura to wallahi bazai saɓu ba, da ace ai a gidan tsohon mijinta ne sun ma isa ƴar ta ta auri ɗansu, kuɗin da suke taƙama dashi ai be kai ko kamo rabin na tsohon mijinta ba, ai wallahi ba zeyu ba

Itama Zulaihan fitowa tayi jin abinda uwar ta ke faɗi, tun data ji ansa ranar auren Ahmad da Nabila taji wani kuka mai karfi ya taho mata ta rungume mahaifiyarta tana ta kukan 

"Ke banza kawai dalla can ɗaga ni mara hankali, me makon ki nemi mafita zaki wani saka kuka, ubanki kuka ze miki magani, ni bansan irin wannan banzan cin naki ba wallahi"
"Ai wallahi Mamee sai naci uban yarinyar nan idan na ganta"
Ta tashi tayi ɗaki fuuuuu kamar zata tashi sama 

Mama kam kusan dama ba son wannan soyayyar da Amra kewa Umar take ba dan ta tsani duk wani abu da ya shafi Ammi da muƙarraban ta, tana biyewa Amra ne dan kawai farin cikin ta, bata son abinda zai ɓata wa yaran ta rai ko kaɗan 

Amma abun ya ɓata mata rai ai da suna da zumuncin kamar yarda suke iƙrari maisa ba'a haɗa da Amra ba aka haɗa da Anisa idan ba son zuciya ba tunda tasan dai bayanda za'ayi ma ace Umar yaso Anisa a yanda yake saidai idan su suka haɗa kayan su dan sun ga ƴarsu naso, suna gudun kar ace za'a haɗa da Amra shiyasa sukayi saurin tusa nasu yarinyar 

Amma dan tsabar son zuciya har uwar shi ai tasan Amra na sonshi tunda saboda shi lokacin ma ta bisu Egypt Kuma tana sane da hakan amma ta take taƙi dayake sune ƴanuwanta data fi so

Koda aka faɗa wa amra zancen suma tayi seda aka sheka mata ruwan sanyi ta farfaɗo tana ta balai, tasan yanzu kam da ƙar kuma ya aure ta daman tun can be san tana haukar ta ba ita kaɗai ke wahalar ta

Mamee ce ta ƙira Mama dan balai ke cinta tace gidan Abba zata rakata, daman itama Maman abun ya dame ta duk da bawai so take ba amma wannan cin fuska ne ai sun san ƴaran su na son su amma dayake suna son su haɗa da nasu suka take hakan

 gidan Abba suka yiwa tsinke bayan Mama tazo ita da Amra 

Suna zuwa suka samu Anty a parlourn tana serving Amma da bata daɗe sosai da zuwa ba, bayan ta baro gidan Ammi

"Salama alaikum''
Dagowa sukayi suna kallon su da mamaki akan fuskokinsu dan anty bata ma yi tunanin su bane 

"Anty ashe kune bismillah"
''mune, ina mijin naki" faɗin Mamee 
"Yana sama"
'' to kira shi wajen shi muka zo dan naga alama kamar shine daman wanda ya haɗa komai"

Kan Anty ne ya daure haɗi da fatan dai Allah sa ba abinda ke ranta bane ya kawo su dan tasan ƴanuwan nata abun kunya gaba suka bashi ba baya ba

Ita kam Amma abincin ta ta cigaba da ci dan ba wanda ya bi ta kanta itama ko ƙala bata ce da su ba ta cigaba da abinda yafi mata

Suko tsagerun yaran duk suna tsaye kusa da iyayensu babu wanda yayi hankali ko yasan ya gaida anty ko Ammah da ke gurin acikin su, dan tsabar tarbiyya irin Wanda aka basu, se wani jijjiga suke kamar zasu daki wani

Da baza ta kira Abban ba amma sai taga gwara ta ƙira shi zai fi akan ta barsu dan yanda ta gansu tasan ba alkhairi ya kawo su ba


Follow me on arewapen danAllah ba dan halina ba se dan kawo muku sabbin Updates 🥰 🙏🙏🙏🙏🙏 


______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺 
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol