Free chapter · Read without an account

LOKACI CHAPTER 5

by Rabi'atu kabiru Fulani · LOKACI

***

⏳🕛 LOKACI 🕛⏳ 

RABI'ATU KABIR ACHADU FULANI 

YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA 

Under Team Yota's Amazing Pen's.

SADAUKARWA GARE KI KARYMAT BASHEER (An karime karime na)

      FULANI ❣️ 
***

 
       ⏳🕛 LOKACI 🕛⏳

     PAGE 5️⃣

Juyawa ta yi ta fara tafiya duk da ta ji ƙarar buɗe get ɗin hakan bai saka ta juyawa ba, ci gaba ta yi da tafiyarta, "Aunty Zahra" ta kira sunanta daga ciki ba ta juyo ba ta cigaba da tafiya, ba ta ɗaukar wulaƙanci bare kuma a ce daga ƙanwar bayan ta, jin wayarta na ringing ya sa ta duba wake kiranta, ganin ki Mahmah ce ya sa ta furzar da iska daga bakinta, ba ta iya ɗaga wa ba sai juyawa da tayi ta koma gidan, bata mata magana ba ta zagaye ta ta shige, ita ma ganin fuskar ta sai ta sha jinin jikin ta ba ta iya mata tsiwa ba, dan tasan zata iya shan mari a hannun ta ba komai bane.

Flat house ne gidanta mai kyau, idan ka shiga za ka samu parking space wanda zai iya ɗaukar mota ɗaya da machine, sai ɗaki guda ɗaya da toilet a cikin sa, sannan wani extra toilet ɗin guda ɗaya a wajen, sai ƙaramin kitchen idan ka wuce nan kuma sai ƙaton parlow mai ɗauke da 2 bedroom's sai ɗaki guda ɗaya, da toilet da kitchen, sannan ventilation, tun da ta saka ƙafar ta a parlown ran ta taji ya yi mummunan ɓaci, gaba ɗaya parlourn tamkar na mahaukata bazaka taɓa ɗaukar akwai mutum dake rayuwa a cikin parlown.

Ƙuƙunta ta riƙe tana ƙara ƙarewa wajen kallo, kitchen ɗin dake parlown ta shiga babu shiri ta dawo bata gama shiga ba dan wani irin wari da tsami ne suka buso mata a lokaci ɗaya, toilet ɗin ta wuce da niyyar dubawa saidai bata ƙarasa ba ta dawo dan zarnin daya ke tashi tun daga waje ya tabbatar mata da nan ɗin ma babu gyara, bata bawa kanta wahala ba wajen duba sauran ɗakun tasan suma a haka suke, zama tayi akan kujera ta dafe kanta tana tunanin ta inda zata fara, yaushe Sadiya ta zama ƙazama shine abinda take tunani dan kaf ɗin su babu wanda bai horu da aiki ba bare tace daman can a haka take.

"Zonan" ta kira ta cike da tsare gida dan ma kar ta kawo mata raini, daga nesa da ita ta tsaya tana gunguni, duk iskancin ta bata isa tayi mata ba da dai Mahmah tananan ne tasan zata shigar mata. Hannun ta miƙa mata ta ce "bani wayar ki" baya tayi wayar alamun bazata bata ba. Yunƙurawa tayi kamar zata ta shi, miƙa mata tayi tana hararar gefe, bata bi ta kan ta ba ta kashe wayar ta saka a cikin jakar ta. "Ki shiga cikin kitchen ɗin ki duk wani abu da kika san mai datti ne ki fito da shi waje minti biyar na baki wallahi kika yi min shirmen Sadiya daga ni sai ke a gidan jikin ki sai ya faɗa miki" tana gama faɗa mata haka ta tashi ta ɗauki belt ɗin mijin ta da ta gani akan kujera ta riƙe a hannun ta.

Babu yanda zata yi haka ta shiga ta fara fito da abubuwan da suke da datti kusan kaf kayan kitchen ɗin saida ta fito da shi, bayan ta gama ta dawo ta tsaya a gaban ta, saka ta tayi a gaba ta wanke su tana kuka da komai, bayan ta gama shima bata bar ta ba ta saka ta wanke toilet, sannan ta saka ta shara da mooping duk da aikin nata ba wani burgeta yayi ba amman haka ta saka ta tayi, saida ta gama ta zauna tana maida numfashi, hararar ta tayi sannan ta shiga kitchen ɗin, sosai ta gyara kitchen bayan ta fito ta ƙara da mooping, sannan ta wanke toilet ɗin ta gyara mata ɗakunan ta ta shimfiɗa sabon bedsheet, waje ta fita ta wanke tsakar gidan da toilet ɗin wajen.

Tana gamawa ta koma kitchen ɗin bata tambaye ta me zata dafa mata ba kawai tayi gaban kanta, fried rice tayi mata sai ta haɗa da farfesun kaza, sannan ta haɗa goslow, tana gama wa da su ta haɗa mata ginger jus da lemon na'a na'a, tana gamawa ta wanke abubuwan da ta ɓata, ta ƙara gyara kitchen ɗin, tana fitowa tayi wa ta jona burner tayi turaren wuta take gidan ya ɗauki ƙamshi kamar bashi ba, toilet ɗin waje ta shiga ta wanke jikin ta sannan ta dawo inda take ta zauna.

"Sadiya" ta kira sunan ta a hankali. "Na'am" ta amsa tana kallon gefe, dan sosai taji haushin aikin da ta saka ta. "Meyake damun ki menene ya canza wannan ba rainon da Mahmah tayi miki bane, ƙazanta fa Sadiya haba kinga gidan ki yanzu ke ba'a bin kunya bane wani yazo ya ga gidan nan a haka, Bama wannan ba yanzu idan mijin ki ya dawo unexpected me zaki ce masa da zaki kare kan ki? Ina aikin yake a gidan nan har da zaki bari ya dinga wannan dattin gaskiya kin bani kunya faɗa min menene matsalar da har kika koma haka?" 

Shiru tayi kamar bazata yi magana ba sai kuma cike da izgili ta ce "kome zan ce miki akan aikin gida bafa zaki gane ba aunty Zahra" kallon rashin fahimta tayi mata "meyasa bazan fahimta ba?" Kallon ta tayi suka haɗa ido sai ta ce "Saboda ke baki auren ba shiyasa bazaki fahimta, da kinyi aure zaki gane aikin gida dana gidan miji yana da bambanci, amman tunda ke baki ba ba fahimta zaki ba aunty Zahra" Murmushi tayi mata kawai ba tare da tace mata komai ba ta tashi tayi mata sallama ta tafi. Tana fita ta kunna wayar ta ta kira Mahmah ta fashe mata da kuka ba tace komai ba ta kashe wayar bayan jerin tambayoyin da ta jera mata akan kukan me take haka.

Tunda ta tafi take tunanin maganar Ƙanwar ta ta, dagaske aikin gida ba irin na gidan aure bane da har hakan zai saka ka koma ƙazami ko kuma kawai ta faɗa mata ne dan taci mata mutunci, ko kaɗan bata ji haushin ta ba, dan ba a ranar suka fara mata gorin rashin aure ba, itama tana fata da burin Allah ya nuna mata ranar da zatayi nata auren, dan bata cire rai da zatayi ba kawai tasan *LOKACI* ne dan haka tasan idan nata yazo itama zatayi insha Allah, batasan meyasa ba amman tana zuwa gidan gaban ta ya yanke ya faɗi.....


 ★★★★

Har akayi kiran sallar asubah ta kasa miƙewa dan sosai ƙuƙun nata ya bugu, ga wani irin zazzaɓi da ya rufe ta ruff, gashi shi sallah ba wani damun shi tayi ba idan ya tashi ya taimaka mata tayi, gajiya tayi da kwanciyar da raɗaɗin da yake ratsa ta ga sanyi dake shiga har cikin ƙashin ta, hakan yasa ta fara jan ciki har ta ɗora hannun ta akan shi, bubbuga shi take tare da kiran sunan shi har ta sare taji ya motsa hakan yasa taci gaba bata dena "ke baki da hankali ne baki ga bacci nake ba?" Yayi maganar cike da Muryar bacci yana tashi zaune.

"Bayana Auwal zai cire" yanda tayi maganar cike da ciwo da kuka ne ya hana shi balbaleta da masifa duk da kukan nata ba wani damun shi ya ke ba. "Meyasa meki?" Ya tambaye ta yana sakkowa daga kan gadon. Ji tayi wani irin abu yazo ya tsaya mata a ƙahon zuciya, kenan ma bai san abinda yayi mata ba "jiya ba kai ka turo ni daga kan gado ba?" Ta mayar mishi da tambayar.

"Malama bana son sharri yaushe na turo ki ni?" Banza tayi mishi ta koma ta kwanta, ganin haka ne yasa shi tasowa zuwa inda take yana taɓa fuskar ya yaji wani irin zafi da hanzari ya cire hannun shi yana ɗago ta zaune, wata iriyar azaba ce ta ratsata hakan yasa ta ƙanƙame shi tana fashewa da kuka, ƙara riƙe ta yayi yana jera mata sannu "ni ka taimaka min na tsarkake jikina nayi sallah" yanda tayi maganar ne yasa shi sakin baki yana kallon ta "ke baki da lafiya ma maganar sallah ki ke?"

"Hmmm Auwal kenan dan kai kana wasa da sallah sai ka ɗauka kowa ma haka yake? Nasan banda lafiya amman ai ina motsa jiki na kuma a cikin hayyacina nake, kai fa? Kana da lafiya kuma kana cikin hayyacin ka amman hakan yana iya hanaka wasa da sallah ne? Wai kasan hukuncin wanda yake wasa da sallah da gangan kuwa? Wallahi yana cikin babban haɗari Auwal, domin sallah ibada ce mai girma a cikin addini, saboda girman tane akace idan har sallar ka ta gyaru a ranar lahira toh ayyukan ka ma sun gyaru, ba zan gaji da faɗa maka ba koda zaka min dukan mutuwa yin sakaci da kake da sallah da gangan ba abin wasa bane, ya kamata kaji tsoron Allah ka kiyaye sallolin ka, ka kuma ji tsoron Allah tun kafin lokaci ya ƙure maka"

Shiru tayi tana jiran jin saukar duka dan duk sanda tayi mishi magana akan wani abu sai ya dake ta ko ya mare ta. "Mtsssss" yaja wani irin dogon tsaki, ji yake kamar ya rufe ta duka tsabar raini shi za ta saka a gaba tana wa wa'azi saboda ta maida shi shashasha taci Sa'a bata da lafiya wallahi da sai jikin ta ya faɗa mata. "Dan Allah ka taimaka min kaji Auwal lokaci yana ƙurewa"

Riƙe ta yayi ya kaita toilet ya fito ya tsaya, wanka tayi ta tsarkake jikin ta tare da alwalah, buɗe ƙofar tayi ta miƙa mishi hannun ta ya riƙe ta suka koma ɗakin, daga zaune ta samu tayi sallah ganin ya koma zai kwanta ne yasa tace dan Allah ya bata wayar ta, miƙa mata yayi ya ƙara kwanciya, kanta kawai ta girgiza sallar ce dai bazai ba Allah ya shirya ta faɗa ƙasa ƙasa tana kara waya a kunne, jin an ɗaga ne yasa tayi sallama tare da miƙa gaisuwa shiru tayi alamun ana amsa mata "Ummu bani da lafiya Ummu ƙuguna zai cire dan Allah kizo Ummu na" wani irin kuka ne ya ƙwace mata tun kafin ta bata amsa, kashe wayar tayi ba ta jira cewar ta ba.

Daman ita tasan abu ne mai matuƙar wahala tazo dan ta kawo mata ɗauki, kwanciya tayi a wajen tana jin yanda zazzaɓi yake nuƙurƙusar ta, bacci ne ya fara ɗaukar ta babu bata lokaci kuwa yayi gaba da ita dan daman bata samu tayi na dare ba, kamar a mafarki taji ana bugun ƙofar gidan can kuma taji ringing ɗin wayar ta idon ta a rufe ta ɗaga kiran jin Muryar yayar ta a take baccin nata ya wartsake da kuma tsakin Auwal da taji.

"Ko wane ɗan wahalan ne yake damun mutane da farar safiya" ganin ya miƙe zai nufi ƙofar yana bala'i ne ta kira sunan shi, amman ko juyo wa baiyi ba, tasan har ya buɗe ƙofar yana zage zagen da ya ke amman babu yanda zatayi haka ta zuba wa ƙofar ido babu jimawa kuwa taji sallamar babbar yayar su da ƙanwar ta "ku shiga tana ciki" inji Auwal da ya nufi ɗayan ɗakin.

Da sallama suka shiga, tana ganin su taji wani irin sanyi a cikin ran ta, sai kuma hawaye suka zoba mata hannun ta ta miƙa musu da sauri kuwa suka riƙe a tare "Subhanallahi meyasa meki haka khairiyya?" Duk yanda taso buɗe bakin ta kasa sai kuka da take har da sheshsheƙa, duk da autar su bata san meya saka yayar ta ta kuka ba hakan bai hana ta itama fashe wa da kuka. "Innallilahi Khairiyya kiyi min magana mana meyasa meki Ummu tayi min waya tace nazo baki da lafiya yanda tayi min maganar daga ji hankalin ta a matuƙar tashe yake, nazo kuma kin ƙi magana sai kuka menene ya faru?"

"Aunty ki tafi dani idan ba haka ba wata rana zaku zo ku ɗauki gawa ta, ƙugu na kamar zai cire tsabar ciwo ga zazzaɓi da ciwon kai dan Allah ki kaini a gyara min" kuka ne ya ci ƙarfin ta hakan yasa ta yi shiru tana maida numfashi. "Bani hijabin ta auta" ɗakko mata tayi ta saka suka riƙe ta suka miƙe a hankali suke tafiya sun gab da fita daga gidan ya fito ya sha gaban su "ban gane ba ina zaki tafi min da mata????


FULANI
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol