Free chapter · Read without an account

46

by Anisa Muhammad Yahaya · NUFIN ALLAH


💕 NUFIN ALLAH 💕 
  By
Anisa Muhammad yahaya 


 YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA


Page4️⃣6️⃣


Tare suka sakko da Abba yana gaba tana biye dashi a baya

"Yauwa Allah ya sakko dakai, yanzu kai Hafeez ace dan mu ba ƴanuwan ka bane ko ince dan son kai ai kasan Zulaiha sarai nason Ahmad zaka hada shi da ƴarka, saboda son zuciya"

Mamee ce ke wannan zancen tun basu gama sakkowa daga stairs ɗin ba

Sai yanzu ya gane bakin zaren daman yayi mamakin da Anty tace gasu suna neman shi, shi da yasan ba wai shiri suke ba dan shima ba son shi suke ba a cewar su ɗanuwan su Ammi ne shima duk bakin su ɗaya, har ita Antyn da ta shige cikin su, kuma sun san daga baya seta zo tayi nadamar barin su ta koma wajen su Ammah suka haɗe musu kai

"Abida ki barsu son zuciya ne fah ai shiyasa za'a turawa yaro Anisa dan nasan dai ƙarya ne ace suna son juna ne saidai a haɗa su, dukda cewa har uwarsa tasan da Amra na son shi amma dan mugunta da baƙin hali shine zaku cusa mai ƴarku dan son cutar da namu yaran, ai koda haɗin za'ayi sai ayi da Amra tunda dai ai ta girmi Anisan kuma ita tana son Umar ɗin, amma ba kuyi duba da hakan ba, dan ku kawai naku kuka sani"

Mamee ce ta ƙara amshewa da
"Anty ai indai abu ya shafe su kansu suka sani, ahaka kuma suke iƙrarin wai suna son gyara zumunci dam, yoo ina gyara anan? Ai daman can munafurci ne kawai da kisisi na, ai da suna so ɗin kamata yayi su haɗa da namu yaran waanda su suna son su ba su cusa nasu yaran a gurin da ba'a buƙatar su ba, su bar waɗanda ake buƙata su kasance tare da juna ba su ringa kokarin se sun tura nasu ta ƙarfi da yaji ba"

Kai Amra da Zulaiha suka jinjina kamar da su ake magana suna harara Abba a fakaice, barin ma Zulaiha da take jin kamar ta haɗe tsohon da jikin bango, tunda shike kokarin cusa ƴarsa a wajen masoyin ta

Abba yana jin abinda suke cewa amma ko ƙala be ce musu ba sai zama da yayi kan kujera yana kallon su kamar ya samu waɗansu ƴan dramar hausa 

Ita dai Anty gefen shi ta tsaya hankalin ta atashe dan ita bata son fitina barin ma irin waɗannan rigingimu da ya shafi family, bata son abinda zai ringa taɓa zumuncin ta da ƴanuwanta, bare ma yanzu suna ganin kamar ta juya musu baya ta zaɓi ƴanuba fiye da su

"Kun gama ko akwai sauran ƙorafin"
Faɗin Abba hankali kwance, ya ƙara cewa
"Munifah haɗa mun coffee, se ki dauko mun laptop dina in ƙarasa anan tare da glasses please tunda naga basu da niyyar gamawa nikuma ina da abubuwa da yawa a gabana"

Kai ta jinjina tayi kitchen jiki a sanyaye, itama dai Ammah dan ɗagowa tayi daga danna wayar da take da tayi kamar bata san da wani halitta bayan ita a parlourn ba ta ɗan kalli Abba jin abinda yace 

Dan murmushin gefen baki tayi ta maida kanta kan abinda take

Shock ne ya kama su Mamee dan ba amsar da suka yi expecting ba kenan, so suka yi ayi bala'i yau dan bama zai yiwu bane dole wannan haɗin a ruguje shi, Mama ce tace
"Yanzu kai Hafeez bama kaji kunyar abinda ka faɗa ba, dan tsabar son kuɗi ba dan kunsan yaran nada kuɗi yasa kuka cusa yaran ku duk da bason su suke ba, ga waɗanda suke son su tsakani da Allah amma dan son zuciya kuka haɗa da naku"

Sai a yanzu Abba ya magantu
"Kuɗi" ƴar dariya yayi irin tasu ta manya ya ƙara cewa 

"Aje a hakan, su yaran namu ba ƴaƴan ku bane, da ace Ahmad nason Zulaiha ai ba tun yau ba zai kawo mana ita gaban mu yace Ita yake so ba wai Nabila ba, da kika ce Jannat ma ta san Amra na son Umar Anty kinga ai da tana son haɗin ko shi Umar din na son hakan ai da shima sanda yake ta mun sintiri akan Anisa madadin ta sai ya mun akan Amra, amma duk ba suyi hakan ba, dan haka kinga maganar na tura musu yarana ta ƙarfin tsiya be taso ba, gwara dai kusan abincewa ba wannan ba"

"Ai koma ace hakan ne ai da sai kuyi adalci, ƴaran nan suma fa ƴan uwansu ne, ai kamata yayi koda zaku haɗa sai ku haɗa da su tunda dai kowa ya sani sune suke son su, kuma dai Amra ai ta girmi Anisa ta fita hankalin da ya dace ace ita aka aura ma Umar" faɗin Mama tana riƙo hannun ƴarta

"Bare ma Zulaiha da harshi Ahmad yasan da irin son da take mai, amma da yake uwarsa makirace daman ba son mu take ba yasa ta toshe kafar yin hakan" Mamee ta cafe zancen da faɗin haka tana hararar Ammah dake gefe har lokacin bata nuna alamar ta san dasu a wajen ba

Dan tasan idan ta yarda ta biye musu za suyi abinda be dace ba, tunda Abba na gurin gwara ta bassu dashi 

"Koda ace tursasa musu mukayi ai mun isa da su ne, kuma aure nan da wata daya in Sha Allahu ba fashi da nufin Allah saidai ko wani ikon Allah" 

Yana gama fadin haka ya tashi ya bar musu wajen dan yasan ya cigaba da zama zai iya faɗa musu abinda bai dace ba dan yaga su basu kama mutuncin su, kawata kawata basu san ta ido da kara ko wani abu sanin mutuncin kai ba, ina tarbiyya zasu tiso yara a gaba su zo a gaban su suna muhawara, wai kuma a haka suke son a haɗa su da yaran su, yoo koda ace Umar da Ahmad basu da waɗanda suke so wallahi Bama za'a fara wannan haɗin ba yana nan duniya sedai wani ikon rabbi

Wani uwar harara Mamee ta buga wa Ammah da bama tasan tana yi ba, suka fice, banda ɓaci da ransu ya ƙara ba abinda suka amfana da zuwa 

A waje suka haɗu da Anisa Wanda Anty ta aike su iskanci suke mata yasa tayo gaba ta kyale su

Gaishe su tayi ba Wanda ya amsa ta cikin su Mamee, ko ajikin ta tayi gaba zata wuce Amra ta riko hannunta, sukuma su Mama ginin haka suka fita suka barsu

Juyowa tayi ta kalle ta tace
"Lapiya" ta kwace hannunta 

Da wani mugun kallo Amra ta bi ta tace
"Wai ke daɗi kike ji za a cusa wa Ya Umar ke dan to wallahi ki sani yafi ƙarfin ki ba class din ki bane shi, ba abinda zaiyi da ke, waɗanda suka fi ki ma bai kula ba bare ke da za'a cusa mawa, Ya Faruq ba irin ki yake so ba in gaya miki, na je na zauna da shi na san wani kalan mata yake so dan haka kar kiyi murna da wannan abun dan wahala zaki sha, gwara ki matsa gefe kibar mu mu irin mu Ya Faruq yake so ba ke ba, fara ƴar dumaduma, keko kalle ki fah duk a bushe, baƙa dake a wajen kamar gawayi"

Baki ta taɓe ta kalle ta sama da ƙasa tayi wani shuumin dariya tace

"Haba da gaske, ina harda ke a cikin irin matan da suka fini, a haka ya gani yace yana so, da ba kalana yake so ba ba yanda zeyi ya zo da bakin sa ya ce yaji ya gani, da kalan ki yake so me shan sha ka mutu dan wannan yafi sha kafashe, da ya dade da zuwa gare ki ba waje na ba, Malama kije kiji dawarin bleaching din dake damun ki tunda baki gode wa Allah da ya barki baƙa ba sai kin koma zabiya se kije ki ɗaɗe ki haɗu da daidai ke zabiya ba Ya Faruq dina ba a canja wani kafar, kuma Bbara in gaya Miki, daman kin yi gaskiya da kika ce ba kowace kucaka yake kulawa ba kamar dai ke, da ace kina da class din Amra da an daɗe da haɗa kun kamar yanda kika ce haɗa mu akayi, ashe ma nida aka cusa mai, anga dacewar mune aka cusa mai ni din, ke kuma fa, da kun dace din da tun kafin yanzu da kika nace kika zama chewing gum girl da an cusa mai ke, tunda ke kike so ba shi yake so ba, ni kuwa kinga yana so ne ana son shi, a haka da rashin class din nawa nafiki samun shiga, kuma ni karewa kusan a gidan mu yake daba dan aiki ba, ba binshi nayi wani garin ba dan ina samu shiga, har inda nake yake zaune kuma yaji ya gani" ta kaɗa kanta tayi gaba

San darewa Amra tayi agurin, ita wannan yarinyar zata gaya wa magana, itace kucakar mara class, yanzu wai wannan figigiyar yarinyar ce da bata fi ta mata ɗauka ɗaya ba ko ta buge ta ta sume ta faɗa mata magana amma ta kasa mata komai 

Zulaiha ce ta ja hannun ta wadda itama ba karamin mamaki Anisan ta bata ba sukayi waje daidai su Jalila na sawo kai

Da harara suka bisu suka fice, suko ko ta kansu ba su bi ba



Kuyi following Dina a arewapen for more updates 🥹🙏🙏🙏


______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺 
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol