Free chapter · Read without an account
LOKACI CHAPTER 11
***
⏳🕛 LOKACI 🕛 ⏳
RABI'ATU KABIR ACHADU FULANI
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA
Under Team Yota's Amazing Pen's.
SADAUKARWA GARE KI KARYMAT BASHEER ❣️
FULANI ❣️
***
⏳🕛 LOKACI🕛⏳
PAGE 1️⃣1️⃣
Wani irin azababben ciwon marar, da ya murɗa mata ne, ya farkar da ita daga suman wahalar da tayi.
Ƙoƙari take ta ɗago hannunta, amma ta kasa. kanta kawai take juyawa saboda tsananin azabar da take ratsata, gaba ɗaya ta daina gane komai, a hankali ta fara fita daga cikin hayyacinta, zuwa wani lokaci gaba ɗaya numfashinta ya ɗauke daga gangar jikinta, babu wani alamu da yake nuni da akwai rai a tare da ita.
Sai wajen ƙarfe ɗaya na dare mayen ya fara sakin Auwal, ƙoƙarin tashi yake, sai ya ji sa kamar a cikin ruwa, dake akwai hasken nepa a ɗakin, take ya ganshi a cikin jini, gaba ɗaya farar singlet ɗin jikinsa ta koma ja.
A firgice yake kallon jikinsa, yana neman inda jinin yake fita, kamar kuma ance ya kalli inda Khairiyya take sai ya ganta kwance cikin jini.
"Khairiyya"
Ya kira sunanta cikin tsoro da tashin hankali.
Ganin lokaci ɗaya, tayi wani irin haske, kuma bata motsi. A take yaji wani irin tsoro ya ƙara dira a cikin zuciyarsa. Matsawa yayi hannunsa na rawa ya ɗagota. "Khairiyya" ya ƙara kiran sunanta.
Zanin jikinta dake yashe a ƙasa ya ɗauka ya ɗaura mata, wayarsa ya ɗauka zaiyi kira akan a taimaka masa, ya kaita asibiti, sai kuma ya dakata. "Auwal me zaka ce idan aka tambaye ka meyasa meta?" Daka ta wa yayi da kiran wayar, tashin hankalinsa na ƙaruwa akan wanda yake ciki.
Wandonsa ya saka ya fita waje neman napep, dan haka yake ganin zai fi masa, yana fita babu jimawa saiga wani napep ya zo wuce wa shan gabansa yayi. Dasauri mai napep ɗin ya taka burki.
"Dan Allah ka taimaka min matata bata da lafiya, mu kaita asibiti"
Ganin yanayin da yake ciki ne, yasa baiyi masa wata tambaya ba, ya ce ya ɗakkota suje. Shiga yayi suka koma baya, ya shiga ya ɗakko ta, asibitin dake kusa da su ya kaisu nan kunya hospital.
Suna zuwa babu ɓata lokaci, likitoci suka karɓe ta, suka shigar da ita emergency.
Tsayawa yayi a ƙofar ɗakin da aka shigar da ita, kallon ƙofar yake jikinsa na rawa a bayyane.
Bayan wani lokaci likita ya fito.
"Waye mijinta?"
Matsowa Auwal ya yi ya ce "Ni ne"
Wani irin kallo likitan yake masa, dan shi dai da ɗan shaye_shaye yayi masa kama, bama zaice kama ba, yana kallonsa ya ga yanda shaye_shayen ya huda shi, can ya kuma kallonsa ya ce "ka kwantar da hankalinka, zata samu lafiya in sha Allah, mun fara bata kulawar da take buƙata, tayi ɓarin ciki ne ɗan kimanin wata ɗaya, sannan tana buƙatar jini, dan ta zubar da jini sosai"
Auwal ya haɗiye wani irin yawu, dan sosai kallon da likitan yake masa yake saka shi faɗuwar gaba, da ƙyar ya daure ya ce "zata samu lafiya likita?".
"Insha Allah. Amman muna buƙatar ƴan uwanta a kusa, sannan da buƙatar a bata kulawa sosai dan tasha wahala, amman dai alhamdullah tunda munyi nasarar dawowar numfashinta"
Kai kawai Auwal ya ɗaga yana jin yanda hantar cikinsa ta kaɗa. Ganin likitan ya juya ne yasa shi kiran sunansa a hankali.
"Likita"
Juyowa yayi yana mishi kallon ina jinka.
"Dan Allah basai an kira ƴan uwanta, yanzu ba"
Sosai likitan ya ɗaure fuska dan haka kawai yaji bai yarda shi ba.
"Meyasa"
Sai da ya haɗi miyau sannan ya ce "ƴan uwanta ba'a kusa suke ba, zan sanar da su da safe".
Likitan baice komai ba, ya koma cikin ɗakin. ganin haka sai ya koma shima ya zauna. kansa ya jingina da bango.
A karon farko tun da ya auri Khairiyya, yaji tsoro ya mamaye zuciyarsa, da kuma mamakin wai ɓarin ciki tayi, ko yaushe yayi mata cikin ma oho. Idan ya ce zuciyarsa bata cikin tsoro ya yi ƙarya, shi kansa yasan mahaifin Khairiyya ba kanwar lasa bane, dan yana da tabbacin wannan case ɗin sai yaje har gabansa, haka kawai sai ya ji yana jin tsoron abin da zai faru a washe garin ranar.
Har washe gari da safe Khairiyya na cikin emergency, tana karɓar kulawar likitoci, Auwal ya kasa tafiya, duk da yanda yake son zuwa ya canza kayan jikinsa, saboda duk wanda zai huce sai ya kallesa. Ya kasa zama safa da marwa kawai yake a wajen.
Tamkar wanda yayiwa sarki ƙarya, yana jiran hukunci.
Yana a wannan halin aka fito da ita akan gadon marasa lafiya, da rigar asibitin a jikinta, hannunta ɗauke da drip, ganin sun nufi wani ɗaki da ita, sai ya bi bayan su, bayan sun kwantar da ita sun gama mata duk abinda take buƙata, sai suka bashi list na abubuwan da zai siyo, da kuma kuɗin da zai biya, suna bashi suka fice.
Matsawa yayi gaban gadon da take yana kallon fuskarta, wani iri yake ji a cikin ransa, kamar mai danasani da nadama, ga kuma wata mahaukaciyar soyayyarta da tausayinta da suka dirar mi shi a lokaci ɗa ya, ya jima a haka kafin ya juya ya fita ya ja mata ƙofar, fita yayi daga asibitin, ya nufi gidan dan bai fito da komai ba a jikinsa.
Yana zuwa gidan yana shirin buɗe wa, yaji tsayuwar motoci a bayansa, juyawa yayi a take gabansa ya yanke ya faɗi ganin motocin gidan su Khairiyya har guda uku a ƙofar gidan.
Buɗe ta farkon a kayi, mahaifin Khairiyya ne a farko, sai mahaifiyar ta, sannan Aunty Maryam, sauran ma duk fitowa suka yi, yayyanta ne maza, su 5 sai mai bin aunty Maryam.
"Khairiyya ta kirani jiya da daddare wajen 8, banga kiran ba sai wajen ƙarfe 9, tun lokacin kuma nake kiran wayarta ba'a ɗagawa, kaima na kira taka baka ɗaga ba, har yau da safe, Auwal me ya faru? Ya na ga gidan a rufe, ga kuma jini a jikinka, ina Khairiyya? Meyasa mi ƴar ta Auwal?"
Ummu ta jera mishi tambayoyin cike da tashin hankali.
Tun jiyan ta kira Aunty Maryam ta faɗa mata, dan haka kawai hankalinta ya kasa kwanciya, ga maganganun da Maryam ɗin ta faɗa mata, tana jin tsoron su tabbata, dan daman tunda ta dawo da ita gidan Maryam ɗin ta ce zatayi danasani, gashi tun ba'a je ko ina ba hakan na shirin faruwa. batasan me ya faru ba, wajen ƙarfe shida mahaifin Khairiyya ya kira meeting cikin gaggawa, ciki kuwa har da Maryam, tambayar farko da yayi akan me yake faruwa da Khairiyya a gidan aurenta, wace kalar rayuwa take, ta kusa sakin fitsari saboda tsoro, tana jin yanda Maryam ta faɗa mishi komai da komai, amman ta kasa cewa komai ma.
"Wallahi duk abin da ya samu ƴarta da ke da mijinta sai nayi shari'a daku, kuma zanje a yau na dawo da ita gidan nan, idan na dawo da ita ki mayar da ita kinji Ummu"
wannan shine furucinsa, haka kuma ya sakota a gaba suka tawo gidan, da yayyanta da suma suka ɗauki zafi da lamarin, sai kuma tazo taga Auwal cikin wannan yanayin da yake shirin tarwatsa mata zuciya, dan soyayyar Khairiyya daban take a cikin zuciyarta.
Auwal kasa magana yayi ganin yanda zaratan samarin suka zuba mishi ido, cike da fusata.
"Kai ina ƴarta take?" Alhaji ya jefa masa tambayar babu wasa a fuskarsa.
Wani irin kwarjini yayi masa har baisan san da ya ce "tana asibiti bata da lafiya"
Baya Ummu tayi zata faɗi, Aunty Maryam ta riƙe ta.
"Wuce muje asibitin" cewar Alhaji. Babu musu ya shiga ɗaya daga cikin motocin, faɗa musu sunan asibitin ya yi, suka nufi can, suna zuwa da hannu ya nuna musu ɗakin da take. Suna shirin shiga sai ga wata ma'aikaciyar asibitin ta dakatar da su.
"Kuyi haƙuri ba za ku iya shiga yanzu ba"
Da sauri mahaifiyarta ta kama kanta, dan ji take kamar zai cire, gani take kawai Auwal ya kashe Khairiyya.
"Me ya faru da ƴata" ta tambayesa cike da sanyin murya.
Auwal ya sunkuyar da kansa kamar na Allah.
Ganin ransu ya fara ɓaci ne ya ce "ta samu matsala ne jiya da daddare"
"Wace iriyar matsala" inji Alhaji.
Shiru Auwal yayi.
Matsawa yayi kusa da shi. Cikin ɓacin ran da ya fara rasa control ɗinsa ya ƙara ce wa "Auwal ina tambayar ka me ya faru da ƴata"
Ɗago ido yayi ya kalle shi, "Ɓari ta samu, cikin tane ya zube"
Kamar an jefawa Ummu dutse a ƙirji haka maganar ta dake ta.
"Ciki"
Ta maimaita kalmar cikin rauni. "Wane irin ciki? Ciki dai na haihuwa?" Ta tambayesa a haɗe.
Shiru babu wanda ya amsa mata, gaba ɗaya ta manta Alhaji fushi ya ke da ita ta nufe sa, jikinta har yana rawa. "Alhaji kaji wai Khairiyya ta, ta samu ciki, kuma wai ya zube, burin Khairiyya ta samu ciki ta haihu kaji wai yanzu babu cikin"
Babu wanda maganarta bata karyawa zuciya a wajen ba, har shi kansa Auwal ɗin.
Kai tsaye Alhaji ya nemi office ɗin likita sukayi magana, tare da shi, har zuwa ƙofar ɗakin, zai shiga Ummu ta biyo bayansa, bai hanata ba suka shiga tare, tana kwance samɓal idonta a rufe, tayi wata iriyar rama, tamkar wadda ta ɗauki kwanaki a kwance, sai wani irin haske da tayi, wanda duk wanda ya gani yasan bana lafiya bane.
Kuka Ummu ta fashe da shi, ta riƙe Alhaji shi kansa sosai zuciyarsa tayi mishi rauni, ya ji kuma kome zai faru a yau auren nan zai zo ƙarshe, dan yana son rayuwar ƴarsa.
Nurses ne suka shigo su biyo da ledar jini a hannun ɗaya, daman ana faɗawa Alhaji ana buƙatar jini, yayi wa Ahmad magana yaje aka ɗauki nasa. Saka mata akayi suka fita, shi kuma kujera ya samu ya zauna, yaja hannun Ummu suka zauna tare, babu mai magana a cikinsu.
Wajen 12 ta fara buɗe idonta a hankali, bata iya buɗe su duka ba, saboda kumburin da suka yi mata, mayar da idon tayi ta lumshe, tana jin jikinta kamar ba nata ba, ƙara motsa wa tayi hakan ya janyo hankalin su Alhaji.
Har suna rigegen zuwa wajenta.
Jin maganar su akanta saita buɗe idonta, a hankali ganinta ya sauka a kan Ummu.
Juyar da kan nata gefe tayi cikin muryarta da bata fita ta ce.
"Ummu kin zo ganin ko na mutu ne ki tafi da gawata???...."
FULANI
***