Free chapter · Read without an account
Page 23
SAWU BIYU
Khadijah Sulaiman
Young Talented Writers Association (YOTA)
Book 1
Page 23
Da taimakon sojojin suka isa wurin motar tare da yaran,mutumin sai huci yake amma babu damar gudu.
Sadauki ya cire wayar dake jikinsa aka daure hannun.
Bayan kowa ya gama shiga ya koma can gefe ya kira Brigadier,bugu ɗaya ya ɗauka.
“Sir, Lieutenant Sadauki reporting.”
“Go ahead, Lieutenant.”
“Sir, we've located the missing children,all of them are alive and have been secured,one suspect is in custody. We're preparing to evacuate the children back to the temporary camp.”
Cike da jin daɗi ya ce“Any casualties?”
Sadauki ya ce“None among the children, Sir. Our team is also safe.”
“Good work, Lieutenant,bring the children back and secure the suspect. I'll expect your full report in the morning.”
“Yes, Sir.”
General ya ce“Carry on.”
Sadauki ya ce“Yes, Sir. Out.”
Ƙarfe biyu na dare suka koma tent,nan take medical personnel ɗin ciki suka hau basu taimakon gaggawa,cikin daren ya fita da Bilal suka karbo musu abinci.
Gabaɗaya a firgice yaran suke,zuwa safiya ya sake kiran Brigadier General,yana ɗauka ya ce"Sir, Lieutenant Sadauki reporting.”
Ya ce“Go ahead.”
"Yaran na ƙarƙashin kulawar mu cikin ƙoshin lafiya tare da wadda ake zargi Sir,muna jiran umurnin ka akan mataki na gaba".
Ya ce"ku cigaba da kare yaran har zuwa lokacin da zan aiko hukumomin da suka dace su zo su karɓe su,you are to return to headquarters with the suspect and your investigation team."
"Understood Sir".
Ƙarfe goma ya koma makarantar,bayan sun gaisa da Principal ya ce a kira mishi Mallam Labaran.
Jiki na rawa ya iso wurin,Sadauki ya kalle shi cikin ido ya ce"Mallam Labaran,zamu tafi tare da kai bisa zargin akwai sa hannun ka cikin sace ɗaliban wannan makarantar".
Ya zube a ƙasa jiki na karkarwa ya ce"ku min rai ranka shi daɗe,ban san komai ba,ku tausaya min".
Sadauki bai saurare shi ba ya yi musu alamar su kama shi,sauran malaman sai zare ido kawai suke a tsorace.
Suna isa tent ƴan child protection suka iso wurin tare da ƴan jarida,aka yi musu hotuna da ƙananan videos tare da yaran.
Duk yadda ya so kaucewa ƴan jaridar amma hakan ya faskara,sun dabaibaye shi sai tura mishi microphone suke.
Ɗaya daga cikin su ta ce"za ka iya faɗa mana yadda aka ceto yaran?”
"Tawagar mu tayi aiki dare da rana don bincike akan lamarin,Alhamdulilah mun yi nasarar ceto su kuma suna cikin ƙoshin lafiya".
“Shin masu garkuwar suna ɗauke da makamai?”
Tayi tambayar tana sake cusa mishi microphone.
Ya ce"Ba zan iya bayyana cikakken bayani akan lamarin ba saboda har yanzu ana kan bincike".
“Shin kun kama wani daga cikin waɗanda ake zargi?”
"Eh,mun yi nasarar kama waɗanda ake zargi".
Wani daban ya ce"wani saƙo kuke da shi ga iyayen yaran?”
"Saƙona ga iyayen yaran shine su kwantar da hankalin su,mun yi nasarar ceto yaran kuma cikin ƙoshin lafiya,wannan shi ne babban abin da muka sa a gaba tun farkon binciken mu”
Da ƙyar ya samu ya sulale ya bar wurin,bayan an tafi da yaran suka tattara kayayyakin su dake wurin suna zubawa a mota.
**********
The Dark Network
Rai ɓace Chief ke kai komo a makeken ɗakin,ya buga sandar shi da ƙarfi ya ce"this is absolutely bull shit,me yasa tun farko baka sanar da ni da wannan hatsabibin yaron aka tafi ba?"
"Ka yi haƙuri Chief,ni kaina ban san shi zai jagoranci case ɗin ba sai daga baya,a gafarce ni".
Ya koma ya zauna yana sauke numfashi,Bracket ya ce"yanzu dole mu samo mafita, wannan banzan yaron da ya mana shirmen dole ne mu hukunta shi kafin lokaci ya ƙure mana".
"Ai ba shi kaɗai ba,har wancan wawan daya gayyato dole a haɗa dashi saboda rufuwar asirin mu,ku bar komai a hannuna, wannan ba wani babban aiki bane".
Chief ya ce"make sure you achieve a very neat job,good luck".
**********
Suna zaune a dining gabaɗaya aka sako news na abinda ke faruwa,Mami tayi hamdala cike da farin ciki ta ce"Allah Sarki Faruq,Allah ubangiji ya cigaba da dafa maka".
Gabaɗaya aka amsa da Amin,Zarah ta zubawa fuskar shi ido ganin kamar ya rame akan yadda suka dawo daga Bauchi,sosai ya mata kyau har bata san ana magana da ita ba,sai da Firdausi ta ɗaka mata duka sannan ta dawo hayyacinta.
Ta ɓata fuska ta kalli Mami ta ce"Mami kin ganta ko?"
Mami ta ce"ina hankalin ki ya tafi ana magana kin yiwa mutane banza?"
Tayi shiru don bata san abin faɗa ba.
"Dauko min wayata a parlour".
Ta mike ta dauko wayar ta dawo, Mami tayi dailing number Sadauki amma a kashe.
Ta ajiye wayar tana cewa"ga wayar tashi a kashe,ya kamata a mishi girki Zeenah,da kaina zan shiga kitchen in dafa mishi abinci,da gani ba wani abincin kirki ya ke samu ba duk ya fige ya rame".
Zeenah ta ce"to me zaki girki masa Mami?"
Mami ta ce "shine abinda nake tunani Zeenah"
Zarah tayi caraf ta ce"ki yi masa dambu Mami".
Duk aka juya ana kallonta,ta kama bakinta da sauri jin katoɓarar da tayi.
Mami ta ce"haka ya ce miki dambu yake so?"
Ta karya wuya ta ce"a can Bauchi naji Umma ke maganar yana son dambu sosai".
Mami ta ce"to ai shikenan,ki gama cin abincin ki zaga baya ki samo zogale sai a fara aikin da wuri".
Ta amsa da toh ta cigaba da cin abinci.
Zuwa azahar Mami ta sauke tukunyar dambunta da ya sha haɗi sosai,kamshi kawai ke tashi a part ɗin.
Ta dauko kula ta cika abincin a ciki ta haɗa da zobo mai sanyin
gaske,tayi arranging komai a basket.
Sai da ta sake dailing numbern shi amma har lokacin a kashe,ta juya ta kalli Zarah ta ce"mu je ki rakani in kai masa abincin nan Zarah,har yanzu wayar tashi a kashe".
A bakin gate ta ajiye motar suka shiga ciki,bayan tayi knocking ƙofar parlour Bilal dake kwance a ƙasa ya taso ya buɗe,yana ganin Mami ya durƙusa da sauri ya ce"ina kwana Mami".
"Lafiya ƙalau Bilal,kun dawo lafiya?"
"Lafiya Alhamdulilah Mami,bismillah shigo".
Dai dai nan Sadauki ya fito daga ɗaki,yana ganin Mami ya karaso da sauri ya ce"Mami, shine ba ki kira ni ba?"
Ta zauna kan kujera ta ce"nayi ta kiran wayar ka a kashe Faruq,naga anyi nasarar ceto yaran,Allah Ubangiji ya cigaba da dafa muku ya tsare ku ya kare ku a duk inda ku ke".
"Amin Mami".
Mami ta ce"na san ba wani abincin kirki ku ke ci ba,ga abinci nan na kawo,bari mu tafi ku samu ku huta".
Ya miƙe tsaye ya ce"bari in ajiye ki Mami".
Ta girgiza kai ta ce"a'a na yafe Faruq,zauna ka ci abinci dan Allah ka kwanta ka huta".
Sai lokacin suka haɗa ido da Zarah,ta ɗauke kai ta ce"ina wuni Yaya Faruq".
Ya ɗan kalle ta ya ce"Lafiya Alhamdulilah".
Har waje ya raka su sannan ya dawo ciki,ya zauna kan carpet ya janyo basket ɗin,yana ganin dambu bai san sanda yayi murmushi ba.
Bilal ya zauna kusa da shi yana leƙa cikin kulan ya ce"what do we have here?"
"Oh I see,shi yasa kake wannan murmushin ashe?"
Jin ringing ɗin wayarsa ya sa yayi shiru, ya miƙe tsaye ya ɗauki wayar,sai da ya ɗan saci kallon Sadauki sannan ya fita waje.
Sadauki ya bishi da kallo ƙasa ƙasa,a nutse ya ajiye spoon ɗin hannun shi ya dafe kai ya ce"Ya Allah,not Bilal please".
Ya kai kusan minti biyar sannan ya dawo,ya ajiye wayar ya ce"shine babu jira?"
A taƙaice ya ce"ban ga zan iya ba".
Ya gyaɗa kai ya ce"ka kyauta".
Ya ja plate ya zuba abincin ya fara ci,babu wanda ya sake cewa komai a cikin su har suka gama.
Bilal ya miƙe ya kai kayan kitchen,ya dawo riƙe da ruwa ya ajiye kusa da ƙafafuwan shi ya ce"zan shiga in watsa ruwa".
Bai ce mishi komai ba har ya tafi.
Ya sa hannu ya ɗauki wayar dake kan kujera,ganin akwai lock yasa ya ɗan ja tsaki ya maida ya ajiye ya koma ya kwanta.
Bayan kusan minti biyar ya sake daukar wayar yayi ƴan danne danne sai ga wayar ta buɗu.
A nutse ya dinga bincika wayar tun daga kan call logs har messages amma babu abinda ya gani,ya shiga contacts,nan ma bai ga komai ba.
Bilal ya shigo parlourn sanye da singlet da gajeren wando don fitowar shi daga wanka kenan ya tuna wayar shi na parlour,ɗan still yayi ganin wayar a hannun Sadauki.
Ya miƙe tsaye ya jefa wayar kan kujera ya wuce shi ya shiga ɗaki ya bishi da kallo.
Hutun sati ɗaya aka basu don haka throughout basu shiga Headquarter a satin ba.
Sosai suka sami isasshen baccin da basu samu damar yi an ƴan kwanakin ba.
Cikin baccin da ya ɗauke shi ya ji ringing,ɗan tsaki ya ja don har ga Allah bai yi niyyar farkawa a wannan lokacin ba,da kyar ya sa hannu ya janyo wayar,ganin sunan General ya sa shi tashi zaune da sauri.
“ Lieutenant Sadauki, Brigadier General speaking. I want you in my office immediately. No delay. Is that understood?”
“Yes, sir. I’ll report immediately, sir.”
Wanka kawai yayi ya shirya ya fita ko Bilal bai nima ba,yana isa Headquarter ya san ba lafiya ba,a babban office ɗin Brigadier ya tarar da dandazon officers,yayi saluting Brigadier ya ce“Reporting as ordered, sir.”
"Lieutenant Sadauki,kana da labarin mutuwar duka suspect ɗinmu?they were found dead in their various cells this morning by hanging".
Da wani irin ƙarfi kirjinsa ya buga,yayi wani irin still hankali tashe.
Da ƙyar ya iya buɗe baki ya ce"How, Sir?"
Brigadier ya sauke numfashi ya ce"abinda mu kan mu bamu sani ba kenan,Colonel Bagudu zai jagoranci case ɗin tare da Colonel Hafiz,dole ne a kawo min cikakken bayanai akan hakan".
Da sanyin jiki ya fita waje,ya sami gefe ɗaya ya zauna don sosai al'amarin ya taɓa shi,ya ciro waya yayi dailing number Bilal.
Yana ɗauka ya ce"Bilal !"
"Ina ka je ne haka,yanzu na fito ban ganka ba?"
"Ina Headquarter,an kashe duka suspects dake Custody".
Da ƙarfi ya ce"what ! Da gaske ka ke?"
"Ta ya zan yi wasa da magana irin haka Bilal,Ya Allah zasu haukata ni".
Da sauri Bilal ya ce"ina zuwa".
Yana zaune a wurin Bilal ya iso,bai ma san da isowar sa ba sai da ya dafa kafaɗarsa.
Ya ɗan yi tapping bayan shi ya ce"kwantar da hankalin ka bro,it shall be well".
"Yanzu suna ina?"
A hankali ya ce"ban sani ba Bilal,ban sani ba".
"Ka nutsu Falcon abi komai a hankali dan Allah".
Dole ya koma gida saboda wani zazzabi da ya rufe shi,ya kai kusan sati a kwance don har drip sai da Doctor ya zo gida ya sa masa.
Ranar Monday jin jikin da dama yasa ya hau shirin tafiya office,yana cikin fesa turare Bilal ya tura ƙofar bedroom ɗin ya shigo.
Ganin shi sanye da uniform ya sa shi cewa"are you sure you're okay?"
Ya ɗan kalle shi ya ce"yeah,thank you".
Tare suka isa Headquarter,suna shiga ya ga sai congratulations ake masa,bai kawo komai a ransa ba har ya isa office.
Bai wani daɗe da zama ba Bilal ya shigo fuskar sa ɗauke da murmushi ya ce"congratulations my friend".
Ya ɗan kalle shi ya ɗauke kai, Bilal ya riƙe hannun shi ya ce"mu je Brigadier na neman ka".
"Lafiya kuwa?"
Bilal ya ce"idan mun isa za ka gani".
Bai ce komai ba ya miƙe suka bar office ɗin,office ɗin cike yake da manyan Officers tun daga kan Brigadier har zuwa kan Captains.
Captain Musa ya mishi alamar jinjina daga inda yake zaune.
Brigadier ya miƙe tsaye ya ce"come forward Lieutenant Sadauki".
Ya tako a nutse ya isa inda yake tsaye,ya ɗan bubbuga kafaɗarsa ya ɗauki rank insignia ya ɗora masa saman uniform,wani irin still Sadauki yayi cike da mamaki.
“Effective today, you are no longer a Lieutenant. You have been promoted to the rank of Captain.”
Bilal ya ƙaraso ya rungume shi cike da farin ciki,shi kam bin kowa kawai yake da kallo don bai kawo hakan a ransa nan kusa ba.
Bayan ya koma office Emmanuel da su Adebayo suka shigo, kowannen su fuskar sa ɗauke da farin ciki kamar su aka yi promoting.
Emmanuel ya ce"we must celebrate this bro".
Sadauki ya haɗe rai ya ce"You and who?"
Bilal ya ƙyalƙyale da dariya ya ce"ji wani tambayar banza,Mallam idan za ka saki rai ka saki rai dole mu gwangwaje".
Bai sake bi ta kan su ba ya cigaba da harkar gabansa.
Daga office gidan Mami ya tafi,sosai tayi farin ciki tayi mishi addu'a,yana gidan har magrib bayan Daddy ya dawo sun gaisa shima ya taya shi murna sannan ya dawo gida.
Da mamaki yake kallon gate ɗin gidan dake wangale,ganin motoci a waje yasa ya ƙarasa shiga yana bin wurin da kallo.
Ashe da gaske suke,anyi decorating compound ɗin gidan da balloons, everything was navy green.
Ga ƙaton cake da wine jere saman table,bai san lokacin da murmushi ya suɓuce mishi ba.
Hotuna da videos aka fara ɗaukar shi from different angles, Idayat ta nufo inda yake riƙe da flower,ta ci kwalliya kamar ba ita ba ,yana ganin ta ya haɗe rai ya ɗauke kai.
Da sauri Bilal ya matso kusa da shi ya ɗan dafa kafaɗarsa ya ce"kar kayi disgracing ɗinta don Allah, we're not alone please Falcon."
Babu yadda ya iya ganin yadda aka mishi caa da ido dole ya ƙarba ba don ya so ba.
Daga nan ya sulale ya shiga ciki ya shiga wanka,a kan gado ya tarar da sababbin suit, takalmi da jaka,yayi guntun murmushi don ya san ba aikin kowa ba ne sai na Bilal.
Yana cikin shiryawa message ya shigo wayarsa,ya dakata ya sa hannu ya ɗauko,ganin unknown number yasa ya buɗe.
“Congratulations, Captain Sadauki.
Muna taya ka murnar zama Captain,tabbas ka cancanta,amma duk wani sabon matsayi yana zuwa da sabbin nauye nauye
"Amma bamu labari Captain... yaya ka ji lokacin da ka ji labarin cewa waɗanda ake tsare da su sun mutu?Ka yi mamaki?ya kamata ka yi.
Ka ɗauki wannan a matsayin gargaɗinka na farko. Abin da ya faru a Rafi,wasan yara ne kawai ko mu ce sharar fage.
Ka sani duk wani motsin ka akan idanuwan mu ka ke yin sa,domin nan ba da daɗewa ba,asalin wasan zai fara.
Mun barka lafiya,a sha party cikin aminci".
Book 1 ya kusa ƙarewa which is free,Book 2 na kuɗi ne.
***