Free chapter · Read without an account

BOOK ONE CHAPTER 19

by Hindatu Auwal · ƘYAURE KARIYAR GIDA

*ALIYA*

Misalin ƙarfe 4:10pm.


Zaune take afalo tana jin Ustaz a kicin yana sauko ruwan shayin da ta dafa mai kafin yaje masallaci yadawo.



Sallama akayi ta amsa. Ammar ya shigo da fara'ansa ya zauna suka gaisa.



Ledan hannun shi ya miƙa mata yana cewa:


"Aunty Aliya don Allah taimaka min zakiyi. Ƙanwarki ce zakima ɗinkin ankon abokina Mumtaz ai kin sanshi ko?"




"Eh. Ba wanda kukai islamiyya tare ba, na gidan doctor."



"Yes exactly shi pha. Tom zaiyi aure gashi Love batai anko ba. Kinga ai ba lafiya."




"Aikam insha Allah nan da gobe zan kammala. Inada measurement ɗinta ai kota ƙara girma ne?"



"No tananan ayanda take."



"To shikenan."



Baki Ammar ya bude zeyi magana. Fitowan Ustaz daga kicin zuwa inda suke yasanya Ammar gaidasa cikin ladabi.



Wuri yanima ya zauna akusa da ita. Kusa sosai, har kafadarshi na gugan nata.


Aliya ta kallesa tana waro mai idanu, mai fassara bamu kaɗai bane.



Kafaɗa yaɗaga mata cikin salon I don't care. Ya ɗaga ƙafansa yaɗora akan cinyarta. 


Ta turesa tana murguɗa mai baki cikin yanayin daya ƙara mata kyau.


Hannu ya kai zai jawo ta.


Ammar ya miƙe dasauri yana cewa"Yaya sai anjima. Aunty Aliya nagode sosai."



Kunya ne duk yabi yakama Aliya. Kai aƙasa ta amsa masa. 


Shikam gogan ko ajikinsa. Ammar na fita yaƙara matsowa kusa da ita sosai. 


Ta zabura zata miƙe ya jawota dasauri tafado jikinsa. 


Ɗayan hannunsa dake riƙeda cup ya girgiza, yaɗan zuba a fatan hannunsa.


Ƴar ƙara ya saki daya sanya Aliya tsorata ta riƙo hannun dasauri ta zare cup din ahannunshi ta ajiye akan coffee table.



Batare da wani tinani ba ta ɗora harshenta awurin da ruwan zafin ya zuba. 


Bilhaƙƙi take lashe masa saboda sanin da tayi idan mutum yaƙone aka lashe anan take baya tashi.



Seda ta gama tass, ta ɗago ta kallesa tana furta sorry.


Idanunsa ya lumshe ya matso da fuskarsa kusada nata ya hura mata iska, ta ɗan runtsesu akansa. Before she knew it, he had captured her lips in a deep, passionate kiss.



Ƙyallen kujeran ta cakume da hannayenta duka biyu tana karkatar da kanta garesa sosai.



Hayyaci ke bama hankalin ɗan adam sanin lokaci na tafiya.


Aliya da Ustaz sun rasa duk wannan a tiƙin da ake kai yanzu. Infact ma duniyarsu ta tsaya cak da abinda ke wakana atsakanin su.



Kamar saukan aradu sukaji vibrating din wayarsa a tsakiyar kansu.


Sukai tsam har lokacin bakinsu na cikin na juna. 



Seda kiran ya katse wani ya kuma shigowa sannan tai jarumtar zare harshenta dake sarƙe da nashi. Tai ƙasa da kanta tana gyara gashin kanta daya sauka gefen fuskarta saboda ɗan kwalinta daya zame.


Daga inda take tana jin muryan Ustaz Zaid yana magana batareda Ustaz Rayyan ya amsa ba.



"Hey! Lafiyanka ƙalau kuwa?...meke damunka?! Kana jina kuwa?!!...kai magana please Ni ina jinka.



Magana yake ajejjere cikin kulawa da tashin hankalin rashin jin maganar Ustaz Rayyan.


Iska yake shaƙa yana fesarwa ta bakinsa kamar me koyon hakan.

Seda ya tabbatar yasami natsuwan da ze iya magana sannan ya bude bakinshi ya amsa shi.



"I'm okay ina jinka pha."



Duk yanda Ustaz Rayyan ya kaiga ƙoƙarin danne abinda ke yawo ajikinsa seda Zaid ya gane akaron farko.


Yai tsaki yana cewa"ɗan iska mai yakai ka wai! Jipha yanda magana ya gagareka. So kakeyi ka kashe kanka ko me?!"



Sanin bazai amsa shiba ya sanya shi cigaba da magana rai aɓace:


"Matarkace zata iya ɗaukan nauyin ka. Kamanta da komai ka rungumi matarka awuce wurin in ku..."


"Dama abinda yasa ka kirani kenan ko akwai saura?."



Yai maganar adake da muryansa da babu ƙwari kamar yanda jikinshi yake yasa Zaid yin shiru yana fadin abinda ya sanyashi kira tun farko.



"Kafara duba time kagani inzaka iya fitowa da natsuwar ka."


Be sauke wayanba se kanshi daya ɗago ya kalli agogo yaga ƙarfe 4:45pm.


"Ganinan zuwa." Yafaɗi yana miƙewa.


Aliya dake kusa dashi kanta aƙasa ya jama kumatu cikin tsokana.



Kanta ta ƙara sunkuyarwa tana murmushi.



Shima murmushin yayi mata. Ya wuce dakinshi ya ƙara kimtsa wa, ya fito har lokacin tananan azaune a'inda yabarta.



Inda sabo tarigada tasaba a ƴan kwanakinnan. Seda yai kissing fore head dinta yai mata sallama ya fita.



Se alokacin nema taga ruwan teanshi daya bari ta ɗauka ta zuƙa ahankali tana sakin wani ƙayataccen murmushi.


Bayan tagama sha tamiƙe. Cup din ta soma kaiwa kicin ta wanke ta saka shi acikin basket.



Taje bedroom din ta acikin wadrope ta dauko trolly din kayan dinkinta. Dukkan wani abu data san zata buƙata seda taɗauko shi. Inda akai sa'a kuma seta sami komai da zatai amfani dashi. Hatta zare akwai kalan atamfar.



Dama batada sanya ita. Shiyasa mutane ke son ɗinkinta tun tana gida. Atake ta yanka kayan acikin dakin da kekenta yake.


Bayan sallahn magrib Ustaz Rayyan yadawo.


Yanda ta saba tarban shi haka ta kai mai ruwan wanka, itama tai wankan, sukaci abinci atare.


Amma pha tana kai kayan da sukai amfani dashi kicin ta dawo ta shiga ɗakin kekenta ta soma aiki. Don adaren nan take so taci ƙarfin ɗinkin gobe idan Allah yakaimu ta ƙarika, ta goge mai, sai yakai mata tunda yace jibi ne bikin.



*


Ahankali ya rufe alqur'anin dake hannun sa. Ya ɗan waiga ya kalli agogo ƙarfe 10:00pm.


No wonder yaji idanuwansa na lumshewa. Miƙewa yayi yaje ɗakinsa ya ajiye qur'anin a'inda ya dace. 


Ya shiga bathroom ya kimtsa. Ya fito ya sauya kayansa har lokacin yana jiyo sautin keken Aliya dake ɗinki.


Ƙofar ɗakin ya tura da sallamar sa. Rashin amsawanta yasan yashi sanin bata jishi ba. Ɗinkinta kawai take yi hankali kwance.



Kujeran da take kai ya jawo baya. Tai ƴar ƙarar tsokana, ta runtse idanu tareda bude su akanshi.



Hannayen shi biyu ya sanya ya ɗauketa daga kujerar yana soma takawa da ita duk da zillon da take yi, tana mai magiya akan yasauketa ta tafi da kanta.



"Don Allah kai ko kayahakuri. Kabarni na ƙarika, kalmasa na keyi.. wallahi gobe suke buƙatar kayan, gashi banyi guga ba, kaga ya..."


Maganar da take yi ya katse sanda yabuɗe bedroom ɗin sa suka shiga.


Fuskar sa ta kalla tana narke tata fuskar"to ka sauke Ni na tafi ɗakina."


Amemakon ya bata amsa sai ya miƙa hannunsa kan switch ya kashe light, ya haye gadon da ita.



Baki ta ƙara budewa za tai magana ya ɗora ya tsanshi akan lips ɗinta yana kwanciya arigingine, Aliya na saman ruwan cikinsa, yana kallon ƙwayannin idanunta dake aware tana kallon sa itama.



Fatan laɓɓanta yaɗan sumbata yana zagayo da hannunsa ta ƙugunta da kyau. Abinda ya fiso wato tudun ƙirjinta na sauka anashi ƙirjin daya sanya shi lumshe idanunshi. Maganar Aliya ya sanya shi ware idanunshi akanta.



"Banda nauyi?!."


Amemakon ye magana seya gyara mata kwanciya yanda zatai balance da kyau.


"Ƴan hanjinka zasu sami matsala idan na cigaba da kwanciya ahaka."


Wani ɗan ƙaramin kiss ye trailing agefen wuyanta. Ta sadaƙar bazai yi magana ba, taji amon muryansa akasalance.



"Kece ginshikin mahadin Rayyan. Wani sashi na jikina ba zai cutuba saboda kin kasance ataredashi."



Idanunta ta lumshe na ƴan seconds maganarsa na mata yawo. Ta buɗe su akanshi tana kallonsa babu ƙimtawa. Numfashin sa na hawa da sauka ahankali, alamar yarigada yayi bacci.



Taƙura masa idanu zuciyar ta na sauya bugu akansa ta fannin data kasa fahimtar ma'anar da yake nufi.


Sai kawai ta kwantarda kanta ahankali tana sauraron bugun zuciyoyinsu tare da juna. Ƙamshin tirarukansu na sanya wani irin natsuwa na daban na saukar mata.





Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol