Free chapter · Read without an account

MATAR GIDA PAGE 83

by Maimuna Bala · MATAR GIDA

*MATAR GIDA BOOK* 2



*SHUUKRAN*/022



P83


Jin Ɗalha ya yi shiru bai ce komai ba yasa Amirah kashe wayarta tana kuka sosai yanzu shikenan Unaisa innalillahi wa 'inna ilaihi raji'un'' a can wajen Ɗalha kuwa bayan Amirah ta kashe wayarta,daukar wayarsa ya yi hannunsa na rawa ya buɗe sakon da Baffah ya tura masa,da wani irin sauri ya rintsa idanunsa sanda ya gama karanta sakon har da a zaune yake amma sai ya ji gaba ɗaya duniyar tana juya masa lokaci guda wani irin ciwon kai ya ziyarce sa, jijiyoyin kansa sun fito raɗa raɗa idanunsa sun yi ja sosai tashin hankali kwance ƙarara fuskarsa,yana cikin wannan yanayi Muhsin ya shiga ya same sa ga dukkan alamu ya samu labarin hadarin da ya auko,a natse ya tako inda Ɗalha ke zaune ya ja kujera da aka tanadar wa baƙi ya zauna yana ƙarewa Ɗalha kallo,har sannan wayar Ɗalha na ajiye kan tebur,a hankali Muhsin ya kai hannu ya dauki wayar cikin sa'a wayar bata shiga password ba hakan ya bawa Muhsin damar karanta sakon da Baffah ya turawa Ɗalha,wata doguwar ajiyar zuciya Muhsin ya sauke yana son yiwa Ɗalha magana amma bai san ta inda zai fara ba,har da Ɗalha ya rabu da Unaisa sanin kansa ne rasuwarta dole ta ɗagawa Ɗalha hankali musamman da ba ita kaɗai ba har yara da ta haifa,a natse Muhsin ya buɗe baki da niyyar magana amma magana ta maƙale a makoshin sa ganin yadda Ɗalha ya mike da sauri ya nufi kofar fita daga office,ba tare da ɓata lokaci ba Muhsin ya bi bayan Ɗalha da sauri bayan ya dauki wayar Ɗalha tare da wallet ɗinsa da sauran tarkace,bayan fitarsu ne Muhsin ya ja kofar office ɗin Ɗalha ya rufe,daga haka ya yiwa sectary ɗinsa alama da ta rufe masa nasa ofishin sosai Ɗalha ke sauri kamar zai tashi sama duk wanda ya kallesa sai ya kuma kallonsa,bayan fitowarsu harabar kamfani Ɗalha ya buɗe mota ya shiga sai a sannan ya tuna bai dauki car key ɗinsa ba yana shirin fita daga motar Muhsin ya buɗe front seat door ya shiga motar ya zauna Ɗalha bai ce masa komai ba sai binsa yake da ido shima Muhsin shiru ya yi bai ce komai ba,can ya ce ''let me drive,ina ka ke son zuwa?" har sannan idanun Ɗalha kan Muhsin bai ce komai ya dauki a kalle sakanni uku zaune cikin mota yana kallon Muhsin kamar yau ya fara ganin sa gaba ɗaya Ɗalha baya cikin nitsuwa,ganin haka yasa Muhsin sake tambayarsa inda yake son zuwa,da ƙyar Ɗalha ya iya furta ''gidansu'' jin haka yasa Muhsin fahintar gidan su Unaisa Ɗalha ke nufi,fita ya yi daga motar zuwa wajen zaman driver shi dai Ɗalha banda kallo babu abinda yake, alama Muhsin ya masa da ya fita babu musu Ɗalha ya fita daga driver seat ya zaga ta ɗaya ɓangaren ya buɗe murfin mota tare da shigar front seat ya zauna,bayan Ɗalha ya zauna Muhsin bai tsaya ɓata lokaci ba ya shiga mota ya tayar, kamar yadda Ɗalha ya faɗa kai tsaye Muhsin ya kama hanyar gidan Mama,daidai lokacin da motarsu ta isa juction ɗin gidan Mama suka tarar da mutane tare da alama har yanzu ba a gama watsewa ba ga motar kashe gobara gefe cikin taimakon Ubangiji motar ta yi nasara kashe wutar da motar da aka yi haɗari, zuciyar Ɗalha ne  ya yi wani irin mammunar bugu sanda ya yi ido biyu da motar ga mutane kewaye da motar suna kokarin fitar da ƙonannun gawawwaki tare da wasu kaya,sosai wuta ta ci kayayyakin da su Unaisa suka shiga mota da shi haka zalika gawawwaki biyu ba ƙaramin tashin hankali mutane da ke waje suka shiga ba yara da mata sai ihu suke suna kuka masu karfin hali daga cikinsu suna ambatar sunan Allah wani irin zufa ne ya fitsowa Dalha yana zaune daga cikin mota shi dai Muhsin yana anƙare da Ɗalha,sosai ya mayar da hankali kan Ɗalha duk motsi da Ɗalha zai yi kan idonsa yake,a natse Ɗalha ya fita daga mota tare da nufar inda motar take, Muhsin bai tsaya ɓata lokaci ba ya bi bayansa a kan idonsu aka fitar da gawawwaki mata biyu tare da wasu ƙonannun kaya,wasu daga cikin jama'a dake tare wajen suka bada mayafai biyu masu kwari sosai,a kan mayafan aka daura gawawwakin aka kai su gidan Mama,da taimakon Muhsin Ɗalha ya shiga mota Muhsin sai faman kwantarwa Ɗalha da hankali yake,sanda aka shigar da ƙonannun gawawwaki sumewa Mama ta yi duk yadda Babah Rabi ta kai ga jureya ita ma sai da ta suma,Mama dai ta suma ya fi a kirga da farfarɗo zata sake yanke jiki ta faɗi ba iya Mama da Babah Rabi ba kusan gaba ɗaya mutanen unguwa hankalin su ya yi mugun tashi,matan makwabta ne suka yiwa gawawwakin wanka aka suturtasu, ana shirin fitar da gawawwakin zuwa gidan na gaskiya Amirah tare da Rumaisa da Fadeelah suka shigo gidan, sosai gidan ya cika da jama'a ko wajen zama babu da kyar dai su Amirah suka samu waje suka zauna babu wanda ya san da zuwansu,har aka fitar da gawa Mama bata cikin hayyacin ta Babah Rabi da yaranta na tare da Mama,kowacce tana kuka sosai,sanda za a fitar da gawawwakin Amirah ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya Rumaisa ta yi ta rarrashinta,Amirah da Rumaisa tare da Fadeelah basu suka bar gidan Mama ba sai da aka yi sallar la'asar tun bayan da aka dawo daga maƙabarta Ɗalha ya shiga tare da Muhsin suka yiwa Mama da Babah Rabi ta'aziya Babah Rabi ce ke amsa gaisuwar ita dai Mama sai bin mutane take da ido sam bata magana,Amirah da Rumaisa tare da Fadeelah suma sun yiwa Mama ta'aziyah Rumaisa ce ta gabatar da Amirah wajen Babah Rabi,Babah Rabi ta ce ta shida Amirah,bayan komawar Amirah gida sosai ta yi ƙokari ta danna damuwarta saboda yara,da dare misalin karfe takwas Amirah ta dauki wayarta ta shiga whatsapp chat ɗinta da Nailah ta shiga ta rubutawa Nailah sakon rasuwar Unaisa,tun da rana ta sanarwa Ammi da Husnah kasancewar Nailah bata ƙasar Maroco sun tafi hutu da mijinta kasar Cairo wannan dalilin yasa Amirah tura mata saƙo a tunaninta ba lallai Anty Nazaaha mahaifiyar Nailah ta fadawa Nailah rasuwar ba,bayan ta gama rubutawa Nailah sakon ta tura mata, family group ɗin dangin Ɗalha ya shiga kasancewar tana cikin group ɗin ita da duk wacce aka aura family duk suna cikin group,sakon farka da fara cin karo da shi  shine sakon rasuwar Unaisa wanda Husnah ta tura tare da huton Unaisa,kusan duka family Ɗalha rasuwar Unaisa ya dake su  sosai musamman wa'inda suka wulakanta Unaisa sanda ta tafi Kano bikin Nailah duk suna tura saƙon gaisuwarsu ta group sun kuma tsayar da magana zuwa jibi za su shiga Kaduna su yiwa Mama ta'aziyah tun da a gidan Mama ake karɓar gaisuwa,Amirah na riƙe da waya shiru tana bin sakonni da ido,can dai ta tashi ta shiga bathroom ta yi wanka ta shirya kanta cikin wata riga da wando Pakistan bata shafa komai jikinta ba,rabonta da abinci tun rana,har yanzu kuma bata jin yunwa,kwanciya ta yi shiru kan gado ta ƙurawa Fauziyya ido can ta janyu Fauziyya jikinta ta rungumeta,har yanzu ta ƙasa yarda Unaisa ta rasu tausayin Unaisa ya cika mata zuciya fam gani take gaba ɗaya Unaisa bata ji dadin rayuwar aure ba,tun bayan auren ta da Ɗalha ta riƙa fuskantar ƙalubale iri daban daban wanda da yawa laifin ita Unaisar ne amma harda haka in ta yi la'akari da karantar shekarun Unaisa sai ta yi mata Uzuri,ba ƙaramin kuka ta yi ba yau idanunta sun kumbura ga wani ciwo da kanta ke mata sama sama,tana nan kwance har karfe goma da wasu mintina na dare ko kaɗan bata jin bacci gaba ɗaya bacci ya yi kaura a idanunta,sai juyi take kan gado tana cikin wannan hali tunanin Ɗalha ya faɗo zuciyarta,wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke tare da rintsa idanunta daga haka ta raba Fauziyya da jikinta ta shimfiɗa ta kan gado,ta karanta addu'a bacci ta tofa mata tare rufe mata jiki da bargo daga haka ta yunkura ta sauka daga kan gado,gaba ɗaya mantawa ta yi daƊalha yau tsabar tashin hankali da ta shiga,jiki babu kwari ta zura hijab ɗinta har ƙasa,kitchen ta shiga ta haɗawa Ɗalha tea daga haka ta jira masa abinci saman try sanin kanta ne ba lallai ya ci ba,bayan ta gama shirya komai ta dauki tray tare da nufar ɗakin Ɗalha sallama dauke a bakinta ta shiga ɗakin shiru ta ji ba'a amsa sallamar ba a hankali ta kai hannu handle ɗin kofar ta buɗe kofar tare da tura kofar ciki daga haka ta cusa kai cikin ɗakin tana sake sallama a karo na babu adadi wutar ɗakin na kunne wanda haka ya bata damar ganinsa kwance saman gado












Bayan shigarta ɗakin ganinsa ta yi kwance kan bed bai ko canza kayan jikinsa ba,ga dukkan alamu ko wanka bai yi ba,try ɗin abinci da take riƙe da shi ta samu waje ta ajiye daga haka ta nufi bed ɗinda yake kwance kafesa ta yi da idanunta tana ƙare masa kallo,ta dauki a ƙallah mintina uku tsaya tana ƙare masa kallo bacci yake amma kallo ɗaya zaka masa ka fahimci ko kaɗan baya jin dadin baccin har wani rama ya yi,a hankali Amirah ta sauke ajiyar zuciya a karo na biyu can ta samu waje gefe gado ta zauna,a hankali ta kai hannu fuskarsa tana kiran sunan sa tare da shafa fuskarsa,a hankali ya buɗe idanunsa da suka masa nauyi sosai ya sauke su fuskar Amirah a hankali Amirah ta buɗe baki ta yi magana kamar raɗa ta ce ''barka da yamma'' Ɗalha ya mata shiru bai ce komai ba yana kallon ta jin ya yi shiru yasa Amirah gyara zama tare da faɗin ''ban san ka shigo ba ina can wajen su Sudais'' daga haka ta yi shiru,shi dai Ɗalha yana kwance sai binta yake da ido ''ka daure ka ci abinci ko kaɗan ne,in kuma ba ka son abinci akwai tea na haɗa maka'' Amirah ta faɗa tare da niyyar barin wajen, muryar Ɗalha ne ya dakatar da ita yadda ya ce ''idanunki sun kumbura sosai addu'a take bukata ba kuka ba''..shiru ya yi na wasu ƴan mintina kafin ya daura da ''please ki daina yi mata kuka all she need is our prayer's'' lokaci guda Amirah ta ji wasu hawaye masu zafi sosai sun ciciko idanunta,ita da ta zo rarrashin sa,zai sa ta kuka cike da jureya ta hana kanta kuka ta kirkiri murmushin da yafi kuka ciwo fuskar ta dauke da murmushi ta kallesa murya can ƙasa  ta ce ''insha Allah'' hannu Ɗalha ya miƙo mata alamar ta zo babu musu Amirah ta yi taku biyu zuwa uku ta je kusa da gadon da Dalha ke kwance a kai a hankali ta sa hannunta cikin nasa daga haka ta cire easy foot wear dake kafafunta tare da hijab da take sanye da shi,a hankali ta hau gado ta kwanta gefensa, rungumeta ya yi sosai kamar za a ƙwace masa ita,Amirah ta buɗe baki da niyyar magana Ɗalha ya yi saurin daura yatsar sa ɗaya saman lips ɗinta tare da mata alamar ta yi shiru,babu musu Amirah ta yi shiru bata ce komai ba a hankali ta daura kanta saman kirginsa hawaye da take ta kokarin ɓoyewa ya jangaro fuskarta,Ɗalha ya yi shiru yana jin yadda hawayenta ke zuba a kirginsa shiru ya yi bai ce komai ba ya kafe fanka dake aiki a hankali da ido,can ya manna mata kiss samar hular dake kanta,gyara mata kwanciya ya yi daga haka ya kai bakinsa daidai kunnenta ya shiga mata nasiha tare da nuna mata illar dake cikin yiwa mamaci kuka,Ɗalha ya dauki sama da mintina talatin yana yiwa Amirah nasiha,Amirah ta zo dakin Ɗalha da niyyar rarrashinsa da kwantar masa da hankali kan rasuwar Unaisa da ƴaƴanta, karshe ita Ɗalha ya koma rarrashinta







 *SHUUKRAN*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol