Free chapter · Read without an account

MATAR GIDA PAGE 84

by Maimuna Bala · MATAR GIDA

*MATAR GIDA BOOK* 2


*SHUUKRAN*/022



P84



Washe gari labarin rasuwar Unaisa da Anty Aisha ya karwaɗe garin Kaduna,safiyar wannan rana misalin ƙarfe sha ɗaya Hajiya Bilƙisu ce tare da tawagarta zaune saman tafurma farfajiyar gidan Mama fuskokinsu dauke da alhini da kuma jimamin rasuwa,gaba ki ɗaya Mama ta koma wata iri da kyar take iya amsa gaisuwa da ake mata,Hajiya Bilƙisu tare da Hajiya Zulfa'u zaune gefen Mama yadda Hajiya Bilƙisu ta riƙe hannu Mama cikin kwantar da murya tana ƙara kwantarwa Mama da hankali haɗe da nasiha,Mama jin dai Hajiya Bilƙisu kawai take hawaye na bin fuskarta,Hajiya Bilƙisu da sauran mata kungiya basu suka bar gidan ba sai misalin sha biyu da wasu mintina bayan sun yiwa Mama sallama ne Hajiya Zulfa'u ta bada umurnin a shigar da abin sadaka da suka kawo,katan katan ɗin lemoka ne da ruwa kusan guda talatin,Babah Rabi ta yi masu godiya da sa albarka,bayan fitowar su ne Hajiya Zulfa'u na daf da shiga motarta ta jiyu wata bakuwar murya tana mata sallama,a hankali Hajiya Zulfa'u ta waigo tare da mayar da dubanta ga wacce ke mata sallama ido hudu suka yi da Aina'u lokaci guda Hajiya Zulfa'u ta faɗaɗa fara'arta,kasancewar ta waye Aina'u ranar da Ɗalha ya sake Unaisa Hajiya Zulfa'u ta fara ganin Aina'u amma hakan bai sa ta manta fuskar Aina'u ba,kasancewar Hajiya Zulfa'u da Hajiya Bilƙisu sun yi ƙaurin sun garin Kaduna yasa da yawa yawan mutane sun waye su ciki harda Aina'u tun bata fara aiki gidan Ɗalha ba ta waye Hajiya Zulfa'u da Hajiya Bilƙisu,cike da girmamawa Aina'u ta gaida Hajiya Zulfa'u,bayan sun gama gaisawa suka yiwa juna jajen abinda ya faru numfasawa Aina'u ta yi tare da taɓe baki tana sauraron Hajiya Zulfa'u dake bata labarin yadda suka kai Unaisa asibiti ranar da Ɗalha ya sake ta,Aina'u ta yi shiru bata ce ba har Hajiya Zulfa'u ta idah zancen ta,a natse Aina'u ta buɗe baki tare da faɗin ''tabbas Unaisa bata ji dadin aure ba tabbas ta yi hakuri dan ba ƙaramin wulaƙanci da bakin ciki mijinta ya cusa mata ba''...Aina'u ta yi shiru na wasu ƴan mintina kafin ta daura da ''sama da watanni biyu bawan Allah nan ya daina cin abincinta baya mata magana tabbas Unaisa ta yi hakuri'' shiru Hajiya Zulfa'u ta yi tana sauraron Aina'u zuciyarta na tafasa tana jin zafi sosai cikin zuciyarta,tabbas duk wata rashin jituwa da tashin hankali da Unaisa ta tsinci kanta ciki Hajiya Bilƙisu ce sila da bata sa Mallam ya ɓata sihirin da aka yiwa Ɗalha ya aure Unaisa ba da ba haka ba,tabbas zata yi maganin Hajiya Bilƙisu da yarda Allah gobe zata je ta sami Alhaji Baba ta fada duk abubuwan da suka aikata ita da Hajiya Bilƙisu,sanin kanta ne har ita abin zai shafa amma is better a dakatar da abin tun yanzu zuwa gaba ba a san mata nawa zasu shiga kunci dalilin kungiyar matan gida ba,gyara tsayuwa Aina'u ta yi kafin ta ce ''ina da tabbacin har kaurace mata ya yi,amma duk ta danne ta yi hakuri to yanzu mai raba ya raba,harda Unaisa bata jin magana amma hukuncin da Ɗalha ya mata sai naga kamar ya yi tsauri'' ita dai Hajiya Zulfa'u shiru kawai ta yi tana sauraron Aina'u cike da mamaki,sun dauki sama da awa guda tsaye kofar gidan Mama,ganin ƴan zuwa gaisuwa maza da mata sun fara yawa yasa Hajiya Zulfa'u ta cewa Aina'u ta shiga motarta in ya so su ƙarasa zancen cikin mota,duk wani abinda Aina'u ta sani kan zamantakewar Unaisa da Ɗalha sai da ta faɗawa Hajiya Zulfa'u,bayan Aina'u ta gama bawa Hajiya Zulfa'u labari ne Hajiya Zulfa'u ta tambaye Aina'u unguwar da take,har kofar gida Hajiya Zulfa'u ta ajiye Aina'u,Aina'u ta yi godiya,a wannan rana Ammi da Husnah tare da wasu daga cikin relatives ɗin Ɗalha suka diro garin Kaduna,sai da suka biya gidan Ɗalha sun huta sun ci abinci kafin suka dauki hanyar gidan Mama tare da Amirah da Ɗalha suka je gidan Mama cikin motoci hudu tarɓa mai kyau suka samu daga Mama da Babah Rabi dukkaninsu fuskokinsu dauke da alhini musamman Ammi da Husnah,tun jiya da rana bayan Amirah ta sanarwa Ammi labarin rasuwar Unaisa hankalin Ammi ya tashi sosai ta yi ta nadamar abubuwan da ta yiwa Unaisa lokacin bikin Nailah, kusan kwanan zaune Ammi ta yi gaba ɗaya bacci ya yi kaura idanunta ta ji inama ta samu dama ta roke Unaisa gafarar abubuwan da ta riƙa mata,raba dare ta yi kallon hutonun twins da Amirah ta tura mata tun sanda suke one week da haihuwa,ina ma a ce yaran suna nan da ita zata riƙe su har girma Ammi ta yi kuka sosai,Ammi ta ji rasuwar Unaisa sosai kamar ƴar cikin ce ta rasu haka ta ji rasuwar,kamar yadda rasuwar ya daki kowa haka ma Husnah tun sanda Amirah ta sanar da ita rasuwar ta ƙasa cin abinci gaba ɗaya unin ranar ta yi sa ne wani iri,kamar yadda Ammi ta yi nadamar abubuwan da ta yiwa Unaisa haka zalika Husnah ta yi ta istigfari cikin zuciyarta,da dare kowa ta dauki sama da awa guda zaune ta yiwa Uniasa addu'o'i,su Ammi basu suka bar Kaduna ba sai da aka yi addu'a uku,a ranar da aka yiwa Unaisa da Anty Aisha addu'ar kwanaki uku da rasuwa Dady tare da Abba da wasu daga cikin ƴan uwan Amirah suka dira garin Kaduna suka yiwa Mama ta'aziyah sosai Amirah ta ji dadin ganin mahaifinta da ƴan uwanta har da basu kwana ba,a ranar da suka zo ranar suka koma Kano,can wajen Baffah kowa washe garin faruwar haɗarin ya shiga garin Kaduna da shi ake karɓa gaisuwa,Muhsin da Ɗalha kusan kullum gidan Mama suke uni dan karɓar gaisuwa,cikin wadannan kwanaki ba ƙaramin kokari Ɗalha ya yi ba wajen ɓoye damuwarsa can cikin zuciyarsa shi kadai yasan halin da yake ciki gaba ɗaya ya daina jin dadin komai abinci ma baya iya ci kamar yadda ya saba wanda hakan ya haifar masa da ƴar rama,kullum Amirah cikin kwantar masa da hankali take ta hanyar masa nasiha da karanto masa ayoyi da hadisai wanda zasu kwantar masa da hankali,har da itama wani sa'ilin ta kan ɓoye kanta ɗaki ta yi kuka iya son ranta hakan kuma bai hanata yiwa Unaisa addu'a duk dare ba









Bayan kwanaki bakwai da aukuwar haɗari Hajiya Zulfa'u ce zaune cikin wata babbar parlour na alfarma,parlour ne na masu hannun da shuni sosai an zuba kayan alatu cikin parlour,zaune take saman center carpet kanta ƙasa Alhaji Babba tare da mahaifiyarsu Hajiya Bilƙisu wanda suke kiranta da Hajiya zaune gefen Alhaji Babba,parlour ya yi shiru baka jin motsin komai sai ƙarar ceiling fan da A C dake aiki a hankali tun sanda Hajiya Zulfa'u ta fara magana Alhaji Babba da Hajiya suka kafeta da ido kowanensu fuskar da cike da mamaki musamman Alhaji Babba,shiru kawai ya yi yana sauraron ta har ta idah zancen ta,gyara zama ya yi tare da gyara zaman farar gilashi da ke idanunsa a natse ya buɗe baki ya fara magana kamar haka ''tsawon zaman ku a Kaduna ki da ƴar uwarki daman kashe auren ƴaƴa jama'a ku ke bani da labari? kasuwanci da ku ka ce kuna yi kenan kashe auren jama'a?"  Hajiya Zulfa'u kanta ƙasa bata ce komai ba Alhaji Babba ya daura da ''ina Bilƙisu?" sai a sannan Hajiya Zulfa'u ta ɗago ta kalle mahaifinta cikin kwantar da murya ta ce ''tana Kaduna bata san na taho ba,abin ya ishi ni ne Baba gaba ɗaya babu tausayi zuciyar yayah duk abinda yazo kanta yinsa take kai tsaye ba tare da tunani ba,yau kwanaki bakwai da rasuwar wata yarinyar mai suna Unaisa a kungiyar mu take'' nan dai Hajiya Zulfa'u ta dauki labarin Unaisa da yadda Hajiya Zulfa'u ta sa rayuwar Unaisa cikin tsaka mai wuya ya faɗawa Alhaji Babah,bayan Hajiya Zulfa'u ta gama fadawa Alhaji Babah komai shiru ne ya biyo baya a karo na biyu,Alhaji Babah ya yi nisa cikin tunani bayan wasu ƴan mintina ya mayar da dubansa ga Hajiya Zulfa'u ya ce ''tashi ki shiga ciki'' babu musu Hajiya Zulfa'u ta yunƙura tare da barin wajen ta nufi upstairs,bayan barin Hajiya Zulfa'u parlourn ne Hajiya mahaifiyar su Hajiya Bilƙisu ta mayar da dubanta ga Alhaji Babah ta ce ''me cece mafita Alhaji?" Alhaji Babah ya yi shiru bai ce komai ba can ya kai hannu stool dake gefe kujera da yake zaune a kai ya dauki wayarsa ya kira layin Hajiya Bilkisu bugu ɗaya ta amsa kiran,bayan ta amsa kiran ne ta gaishe Alhaji Babah cike da girmamawa,Alhaji Babah ya yi shiru bai amsa gaisuwar ba hakan yasa Hajiya Bilƙisu sake gaida mahaifin nata a karo na biyu numfasawa Alhaji Babah ya yi kafin ya buɗe baki ya mata magana a dake ya ce ''ina son ganin ki yau ba sai gobe ba ki zo kafin la'asar'' daga haka ya kashe wayarsa sosai Hajiya Bilƙisu ta shiga damuwa,daga yadda Alhaji Babah ya mata magana ta tabbata babu lafiya hakan yasa bayan ya kashe wayarsa ta kira layin Hajiya Zulfa'u ga mamakin ta layin a kashe ta kira layin ya fi a kirga amma wayar tana kashe,wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke daga haka ta fara shirin tafiya amsa kiran Alhaji Babah,a ranar Hajiya Bilƙisu ta bar garin Kaduna dan amsa kiran Alhaji Babah ana daf da kiran sallar magrib ta shigo garin,ganin motar Hajiya Zulfa'u a compound yasa zuciyar Hajiya Bilƙisu  bugawa da karfi,Allah ya sa ba abinda take tunani bane jiki a sanyaye ta fita daga mota hannuta riƙe da hand bag ɗinta,mai gadi ya yi saurin ƙaraso inda take, hannu ya kai ya karɓi karamin travelling bag ta fitar daga bayan mota










*SHUUKRAN*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol