Free chapter · Read without an account

THE JOURNEY BACK

by Nihaal Maalik · KIRAN KADDARA


Dare ya fara yin nisa, amma Maryam ba ta iya yin baccee ba 

Tana zaune a gefen gado, hannunta ɗaya a kan cikinta, ɗayan kuma tana riƙe da wayarta. Saƙon da aka aiko mata take ta karantawa

“FILE 17. Ba a taɓa lalata ainihin yarjejeniyar da ke ciki ba. Idan kina son sanin abin da ya faru da mahaifinki, ki daina neman wasu abu daban. Amsar tana Abuja.”

Ta sake karanta saƙon, sannan ta kalli Zaid da ke zaune yana kallonta

“Rouhi?”

“Yes, Haya?”

“Me zai faru idan abin da muke nema ya fi ƙarfinmu?”

Ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya kamo hannayenta ya riqe

“Then we face it together.”

Maryam ta ɗaga idanunta ta kalle shi.

“In shaa Allah.”

Maryam ta sauke numfashi.

“Har yanzu ina tunanin Baba, yadda ya rasu yana cikin zargi, yadda muka rasa Aisha bayan haka… Shekaru sun wuce, amma har yanzu ban san ainihin abin da ya faru ba.”

“Ba zan yi miki alkawarin cewa abin da za mu gano zai zama mai daadin ji ba, amma in shaa Allah khair”

Maryam ta ɗan yi murmushi tana maimaita in shaa Allah

Ya yi murmushi shi ma yana rungume ta

“Zo ki bani abnci” ya fadi yana kashe mata ido daya

Ta ɗan buga masa kafaɗa tana turo baki

Yayi dariya me dan sauti, Ya ja ta a hankali zuwa jikinshi

Washegari da safe, Zaid ya raka Maryam zuwa asibiti domin tattaunawa da dr game da tafiyar da suke shirin yi.

Dr ta duba sakamakon tests din da aka yimata, ta tambaye ta game da tashin zuciya, gajiya da sauran alamomin da ke damunta

“Your pregnancy is still in its early stages,” dr ta fara magana “Based on your current assessment, flying may be possible, but I want you to understand that your condition and symptoms matter, keep taking your prescribed supplements, drink enough water, move around during the flight when appropriate, and alert the crew if you feel anything”

Maryam ta saurare ta da kyau, sannan ta tambayeta

“Doctor, is there anything specific I should avoid during the journey?”

Dr ta yi mata bayani kan yadda za ta kula da kanta, irin alamomin da ya kamata ta ɗauka da muhimmanci, da kuma lokacin da ya kamata ta nemi taimakon crew su nemo mata dr in case of emergency.

Zaid ma yana saurare ba tare da katsewa ba, Har ya rubuta wasu abubuwa a wayarsa.

Daga nan dr tache zatayi mata first ultrasound scan, kwantar da ita tayi akan gadon da ke office din, sannan ta zuba mata acoustic coupling gel daga nan ta fara ultrasound din, akan screen din da ke gabansu suke kallon abunda dr take nuna musu me kamar girman lemu, zaid se tasbihi yakeyi a zuciyar shi, shuru ya qura ido yana kallo, ita kuma maryam se kallonshi take, Dr ta lura da wani irin daadi da zayd keji don haka tayi amfani da handheld fetal Doppler device ta kunna musu heartbeat din babyn, zayd seda ya miqe tsaye ya sake zaunawa, maryam da dr se dariya suke mishi, shi besan ma sunayi ba se tambayar da yayima dr wai yaji heartbeat na bugawa da sauri, tayi murmushi tache mishi hakanan yake, suna qara girma yana rage sauri, se da yaji bayanin sannan hnkalin shi ya kwanta

Da suka fito daga office din dr, Maryam ta lura da yadda yake duba bayanan da ya rubuta a waya

“Rouhi”

Ya ɗago ya kalleta 

“Naam are you okay?”

“Se rubutu kake, ka rubuta kusan duk abin da dr ta faɗa!”

Ya kalleta da fuskar da bai ga abin mamaki a cikin hakan ba.

“Of course. I need to know how to take care of you.”

Maryam ta girgiza kai tana murmushi.

“I’m the husband of the woman carrying my child. So technically, I’m the most involved”

Ta fashe da dariya.

“Technically? kana neman hujja ne kawai!”

Ya buɗe mata ƙofar mota

“Get in, Haya. Before you start”

Ta shiga motar tana dariya, shi kuma ya zagaya ya shiga ta ɗaya gefen.

A hanyarsu ta komawa gida, Maryam ta dube shi.

“Yaushe za mu tafi?”

Zaid ya yi tunani na ɗan lokaci.

“Da zarar mun shirya komai. Zan tabbatar mun tanadi duk abin da za ki buƙata, sannan mu sanar da Mammi cewa muna shirin dawowa.”

“Kar ka gaya musu komai ta waya, ka bari se munje please”

Zaid ya gyada kai

Maryam ta jingina da kujerar

A wannan karon, za ta nemi gaskiyar da kanta.

Tun daga wannan lokacin Zayd ya fara shirin komawarsu nigeria duk wani abu daze iya yi ynxu zeyi kokari yayi dan besan lokacin da ze dauka a cen ba, be san me Nigeria ta tanadar musu ba. 

Wata ranar sunday da safe bayan maryam ta gama rigimar ita bata son chips se roasted yam, irin gashin qarwashi dinnan da qyar zayd ya lallabata ta yadda taci fried yam dinda ya soya mata sannan suka shirya zuwa sayen kayan baby, duk da cikin qarami ne ynzu yake 14 weeks basu san gender ba amma yana son su siya komi kafin su wuce Nigeria, Baby dump Amsterdam suka shiga, babban mall ne da babu abunda babu na kayan babies da maternity care, nan suka siya komae da komae bathset, baby cosmetics, baby bed, baby bag, sleep suits, onesies, blankets, shawls da duk wani abu da baby ze buqata da wanda maryam zatayi using itama, su nursing pillow, breast pads, pads da sauran abubuwan buqata duka kayan baby din sun zabi neutral colors yadda zasu yima ko wane gender, bayan sun gama sunkayi payment hadda shipping zuwa Abuja Nigeria.


BALARABE MANSION, ABUJA

Mammi tana zaune a falon gidan tana duba wasu tsofaffin takardu lokacin da Hajiya Raliya ta shigo, dama duk kwanakin nan aikinsu kenan

Tun bayan tattaunawarsu da Malam Nuhu Garba, hankalinsu bai kwanta ba.

“Mammi, akwai abin da nake son mu sake tattaunawa a kai,” Raliya ta faɗa tana zaunawa kusa da ita.

Mammi ta ajiye takardar da ke hannunta.

“Me kuma ya faru?”

“Na sake nazarin abin da Nuhu ya faɗa mana. Ina ganin bai kamata mu tsaya ga binciken takardun kawai ba. Akwai buƙatar mu gano mutanen da suka yi aiki da Bashir a sashen kuɗi a wancan lokacin, saboda mu gano dawa dawa aka kulla mishi sharri”

Mammi ta yi shiru.

“Amma Raliya, idan muka fara tambayar waɗannan mutanen, ba za a ɗauki labarin ya bazu ba?”

“Se mun yi hankali. Ba kowa ne za mu iya yarda da shi ba”

Mammi ta runtse idanunta.

Raliya ta kama hannunta ta riqe don tasan abnda take tunani

“Mammi, har yanzu ba mu da cikakkiyar hujjar da za mu zargi Fahad, amma abin da kika ji da kunnuwanki game da mabuɗin ƙofar garden ɗin ba ƙaramin abu ba ne da zamuyi ignoring”

Mammi ta kalli keys din da ke ajiye, kamar zataje ta bude dakin amma ta kasa

“Idan da gaske Fahad ne ya cire mabuɗin, me ya sa bai ɗauki takardar ba tun shekaru biyar da suka wuce? Besan Wace irin takarda bache ko kuma be ganta bane?”

Raliya ta yi tunani kafin ta amsa.

“Wataƙila bai san takardar da yake nema ba. Wataƙila ya san akwai wani abu a ɗakin amma bai iya gane shi ba. Ko kuma akwai wani abu da bai fahimta ba game da takardun.”

Mammi ta kalli Raliya.

“To, me za mu yi?”

“Za mu jira Maryam da Zaid. Amma kafin su iso, ina son mu tabbatar cewa ba wanda zai qara shiga ɗakin”

Mammi ta gyada kai tare da yima hajia Raliya sallama, koda ta koma dakinta kasa yin komai tayi, babban tashin hankalin ta be wuce ace fahad nada sa hannu cikin wannan abun ba, me zesa yayi musu haka a hankali ta furta “Rahman ko munyi kuskure a wani wurin ne?” A hankali ta zauna gefen gadonta, kwakwalwarta ta shiga tuna mata baya…

WAIWAYE

Gidan marayun yana a wata suruƙiyar unguwa a gefen Abuja, kewaye da ƙaramar katanga da farfajiyar da yara suke wasa a ƙarƙashin hasken rana.

Alhaji Rahman Balarabe ya kasance me yawan ziyartar gidajen marayu kuma watarana har yakan tafi da mammi, watarana Allah ya kaishi ya ziyarci wannan gidan 

An san shi da bayar da sadaka, amma taimakonsa bai tsaya ga kuɗi kawai ba, yana kai musu abubuwan buqata sosai, a chan yaga Fahd ranar da yaje da mammi, yaro me cike da rauni, gashi qarami sosai a lokacin ko magana be iya ba, kuma ga alama beda isassar lfya, mammi ma kallo daya taji Fahd ya shiga ranta sosai, ta matsa ma mijinta hadda hawaye ita dai tanaso suyi adopting Fahd, lokacin zayd yanada shekaru uku a duniya, ya girmi Fahd da kamar shekara daya da wani abu, kuma a wurin haihuwar zayd aka tabbatar musu mahaifar mammi ta samu matsala bazata iya sake daukar ciki ba

Tana tuna ranar da ta fara ganin Fahd 

Kwanche a wani daki a kan yaloluwar katifa yana numfasshi a hnkali, a take sukayi magana da masu kula da gidan marayun suka nemi a basu Fahd wanda a take suka amince aka ciccike takardu aka basu

“Mun gode da kuka sake karɓar mu kuma har kuka yadda damu kuka bamu yaro” in ji Rahman

“Kullum muna maraba dakai Alhaji Allah dai ya biyaka da gidan aljanna,” matar ta amsa. “Ai yaran nan har Allah Allah suke suga zuwanku.”

Rahman ya yi murmushi.

“In shaa Allah zan yita zuwa akai akai, dole ne in tabbatar ban ba su kunya ba.”

Bayan ya raba kyaututtuka ga yaran, kuma ya yiyi hira da wasa da yaran, kamar yadda ya saba suka dauki Fahd suka tafi

Haka Mammi tayita Renon Fahd tareda zayd, sun sha yawon asibiti da Fahd har qasashen waje kafin su samu pheneumonia da tayi mishi mugun kamu ta sake shi

Mammi na tuna lokacin da ya fara magana ya kirata da “umma” ranar hadda hawayen murna tayi, sun taso tareda zaid a cikin su babu wanda yasan chewa Fahad ba mammi ta haifeshi ba

A haka Fahad ya girma tare da Zaid.

Sunyi makarantu daya masu kyau da tsada, kuma Rahman da Mammi sun ba su kulawa iri ɗaya, Idan Zaid ya yi nasara a karatu, ana ƙarfafa Fahad ya yi ƙoƙari ya chimma zayd, haka Idan Fahad ya samu tashi nasara, iyalan suna murna sosai

Rahman bai taɓa barin kowa ya nuna ma Fahad shi ba cikakken ɗan gidan bane

“Jini yana iya haɗa mutane,” ya taɓa gaya wa wani ɗan uwanshi da ya nuna shakku game da soyayyar da suke nuna ma Fahd, “amma kulawa, ƙauna, da halin kirki su ne suke gina iyali.”

Mammi bata mantawa da waɗannan kalmomi saboda tabbas yadda takejin Fahd a ranta ba kadan bane

Yayin da shekaru suke wucewa, Fahad ya zama mutum mai kwarin gwiwa da hazaqa, yana da basira, kuma yana saurin fahimtar harkokin kasuwanci, kuma yana son yayi aiki tareda Babanshi, Rahman ya ƙarfafa shi ya koyi yadda ake tafiyar da company, yayin da Zaid shi ma ya fara bin nasa burin na ganin yayi nashi company daban.

A wajen mutane, iyalin Balarabe iyali ne mai cike da natsuwa da kwanciyar hnkali, A cikin gidansu kuwa, ana ɗaukar Fahad a matsayin ɗa na Gaskiya da babu wanda yasan ba dan gida bane

Amma akwai wata gaskiya guda ɗaya da Rahman bai taɓa tattaunawa da shi ba.

Gaskiyar da yake fatan ba za ta taɓa zama sanadin ciwo a zuciyar dansa ba, ha kada suka rayuwa har shekaru biyar zuwa shidda da suka wuche, lokacin Rahman ya kamu da rashin lafiya, wasa wasa abun nata qara tsanani, anyi yawo qasashe amma sedai abun ya kwanta ya taso, ciwon leukemia ciwone da idan mutum ya kamu sedai wani ikon Allah, qarshe rahman ya zauna a gida be sake fita kowace qasa ba, yache idan mutuwa zata sameshi yanason ta dauke shi cikin gidan shi, tareda ahalin shi, lokacin zaid barin Amsterdam yayi gabadaya ya dawo gida, ahalin sun shiga tashin hnkali mara misaltuwa, haka dai suketa jinyar Alhaji Rahman kuma suna qarfafa rayuwar su domin daukar duk abnda zeje yadawo

Ƙarfinsa ya fara raguwa, kuma iyalin suka fara fahimtar cewa mutumin da ya riƙe duniyarsu tare yana iya kasancewa a kwanakin qarshe taredasu.


NORTHERN CREST HOLDINGS ABUJA

Fahad yana tsaye kusa da babban windown office dinshi lokacin da wayarsa ta yi ƙara.

Ya kalli wayar kafin ya ɗaga.

“Talk.”

Muryar Ali da ke ɗaya gefen ta fito a hankali.

“Sir, akwai wani sabon abu.”

Fahad ya juya daga window

“Inaji”

“Anata binciken tsofaffin ma’aikatan Northern Crest Holdings. Wasu suna neman bayanan abubuwan kamfanin na shekarun baya.”

Fuskar Fahad ba ta sauya ba, amma yatsunsa suka matse wayar da ƙarfi.

“Waye?”

“Ba mu da tabbaci tukuna, amma zamu bincika”

A hankali Fahad ya rufe idanunsa.

Bashir Maisalati, wani suna da ko bayan shekaru, sunan mutumin kawai yana tayar masa da hankali fiye da yadda yake son nunawa.

“Saurareni dakyau,” ya faɗa cikin murya mai sanyi. “Inaso insan wa ke bincike. I want names, not rumours, kuma ina son a samo bayanan kafin a samu damar kai qarshen binciken, a binciko dawa dawa aka gano cikin tsofaffin ma’aikatan”

“Yes, sir.”

Ya katse wayar.

Ya tsaya a wurin na ɗan lokaci, yana kallon kansa a cikin glass din widow 

Shekaru biyar kenan da ya cire mabuɗin ƙofar garden ɗinnan yana bincike, shekaru biyar yana shiga ɗakin a ɓoye, yana binciken tsofaffin files, yana neman takardar da za ta iya rusa duk abin da ya gina, amma har yanzu bai same ta ba.

A yanzu kuma, kamar dai wani ya fara kusantar gaskiyar.

Ya ɗauki wayarsa ya buɗe wani tsohon saƙo da bai taɓa gogewa ba, ya karanta shi, sannan ya kulle wayar.

“Not this time,” ya faɗa a hankali.

Idan takardar nan ta bayyana, abubuwan da ya yi a baya ba za su sake kasancewa a ɓoye ba.

Kuma ba zai bari hakan ta faru ba, nan  tunanin baya ya fara dawo masa, silar komae da yadda wannan burin nashi ya fara.

Wata Ranar friday che da yamma, Daddy ya kira Fahad ya zo ɗakinsa shi kaɗai, Fahad ya shiga ya zauna kusa da gadon da yake kwache

“Daddy, ka kira ni, ya karfin jikin ka?”

Rahman ya gyada kai.

“Alhamdulillah Fahad, naji saukee, Akwai abin da dole ne in gaya maka shi kafin me dauka ta daukeni”

Fahad ya matso kusa yana kama hannun babansu ya riqe yanajin zuciyar shi na karyewa,

Rahman ya yi ƙoƙarin tashi zaune, Nan take Fahad ya taimaka masa ya daidaita zaman 

Sai ya kalli Fahad kai tsaye.

“Fahad, ina so ka fahimci wani abu a rayuwa”

Fahad ya mai da hankali sosae dan jin abun da Daddy zece.

“Ka san ina ƙaunarka.”

“Na sani, daddy”

“Kuma ka san cewa babu abinda ya banbanta ka zayd a wurina”

“Me ya sa kake faɗin haka daddy? Me ya kawo wannan maganar?” Ya tambaya sanin babu wani banbanci tsakanin shi da zayd 

“Saboda ban san tsawon lokacin da ya rage mini ba, kuma ba na son ka fahimci abin da zan gaya maka ta hanyar da ba daidai ba.”

Rahman ya yi shiru na ɗan lokaci.

“Fahad, ni ba mahaifinka na cikinka ba ne.”

Ɗakin ya yi shiru.

Fahad ya zuba masa ido.

Na wasu daƙiƙu, kamar bai fahimci kalmomin ba.

“Naam daddy?”

Rahman ya ci gaba cikin karaya

“Ba mu bane mahaifan ka, lokacin da muka haɗu da kai, kanada shekara daya da yan watanni a duniya, ni da mammin ku muka zaɓi mu dauko ka wannan gida.”

Fahad ya miƙe a hankali.

“To, duk waɗannan shekarun…”

“Duk waɗannan shekarun, kai ɗana ne a duk ma’anar da ta dace, bn taba jin ko da second daya chewa bani na haife ka ba”

“Amma daddy kana nufin ba ni da jininka a jinina?” Ya tambaya a raunane

Alh Rahman ya kasa magana

Fahad ya juya baya.

Rahman ya kalle shi cike da dachin rai

“Ya kamata mu gaya maka tun ba ynzu ba, amma mammin ku tana jin tsoron yadda zaka dauki maganar, amma yanzu dole ne in tabbatar cewa ka sani”

Ya nuna mishi wani ƙaramin safe da ke gefen gadon.

“Buɗe” ya karanto mishi password “Akwai envelop mai launin ruwan kasa a ciki.”

Fahad bai motsa ba.

“Fahad kayi abnda nache”

A karye Fahad ya buɗe safe din ya fito da envelope din

A ciki akwai takardu masu ɗauke da sunansa.

Takardun gidaje, Takardun filaye, Takardun zuba jari da wasu kadarori da Rahman ya saya masa a ɓoye cikin shekaru.

Fahad ya dube su cikin mamaki.

Rahman ya chigaba da magana “Na fara saya maka su tun tuni bisa ga shawarar mammin ku, saboda ko bayan babu mu zaka kasance kanada abun dogaro

Fahad yayi shuru

Rahman ya yi numfashi a hankali.

“Waɗannan kadarorin naka ne bisa tsarin da na yi, duk abnda ke ciki mallakinka ne”

Fahad ya sunkuyar da kai yana duba takardun.

Ya ji kalmomin sun shiga kan shi amma a take tunaninsa ya fara komawa wani wuri jin zanchen daddy na gaba

“Akwai kuma wani abu game da Northern Crest Holdings, zuwa gaba zaka iya cin karo da takardu da za su rikita ka. An kafa kamfanin ne ta hanyar haɗin gwiwa tsakanina da Alhaji Bashir Misalati. Wasu daga cikin tsoffin yarjejeniyoyinmu suna nan ajiye, inada nawa copy shima yanada nashi, asalin kampanin ba nawa bane ni kadai, wannan wani sirri ne da ko mamminku bata sani ba, saboda Bashir ya nemi da in boye wannan maganar bayason kowa ya sani, yafi son kawai idan an assasa kampanin a daukeshi aiki a matsayin ma’aikaci, amma a cikin yarjejeniyar da mukayi a rubuche, akwai tsarin da za’a raba northern crest zuwa ga magada idan daya daga cikin mu ya rasu, don haka inaso ka sani northern crest ba nawa bane ni kadai, rabin abnda ke ciki na Bashir ne, na zabi in sanar dakai saboda nasan dakai za’a tsara komi idan na rasu, nasan dan uwanka be damu ba ko kadan da harakar northern crest.

Fahad ya ɗaga kai a hankali.

“Bashir Misalati?”

“Eh. Ni da Bashir muka gina northern crest tare. Duk abin da zai faru da kadarorina na kaina, dole ne a mutunta yarjejeniyar mallakar company dinnan. Dashi da Iyalinsa suna da haƙƙin da ya kamata a kiyaye.”

Yatsun Fahad suka matse takardun da ke hannun shi

“A qiyasi nawa ne rabonsa a company”

Rahman ya dan nazarce shi.

“Babban rabo ne, mun amince da rabon daidai lokacin da muka kafa haɗin gwiwar, duk da kudin da ya bayar lokacin da za’a assasa company din sunfi nawa yawa”

Fahad ya ji kamar ɗakin ya juya a kansa, wannan maganar ta dake shi fiyeda jin chewa alh rahman da mammi ba iyayenshi bane

Daidai? Rabin Northern Crest Holdings?

Shi da ya ɗauki northern crest a matsayin ginshiƙin dukiyar iyalinsu, tushen da zai gina makomarsa a kai, yayi imanin cewa idan ya yi aiki tuƙuru kuma ya tabbatar da ƙwarewarsa, wata rana kamfanin zai kasance a ƙarƙashin ikonsa.

Amma yanzu ana gaya masa cewa wani ɓangare mai girma na kamfanin na wani ne? Kuma shi gabadaya ma bema da gado a ciki? Waton shi yana nan yana aiki amma kampanin idan ma aka raba zayd kawai da mammi keda kaso a ciki, ina baze yiwu ba

Yana cikin tunanin yaji hannun Alh Rahman yakama nashi

“Fahad, ka dube ni.”

Da kyar Fahad ya iya hada ido dashi, alh Rahman ya lura da yadda maganar ta girgiza shi

“Kada ka bari kuɗi su gurɓata kyakkyawar zuciyarka, na yarda dakai yarona nasan irin tarbiyyar da na baka, kuma na tanadar maka da makoma, baza’a watsar da kai bayan na rasu ba, mamminku tana nan, kuma nasan kai zata bari ka chigaba da jagorantar kason mu na northern crest”

Fahad ya gyada kai a hankali.

“In shaa Allah daddy” 

Rahman ya matse hannunsa.

Fahad ya kalli fuskar mutumin da ya kira mahaifinsa tsawon shekaru.

Sai ya kalli takardun da ke hannunsa.

Rahman ya rufe idanunsa, yana jin sauƙi a qirjinshi, ya samu ya fitar da maganar da ke ciki tsawon shekaru

Kuma ya gaskata ɗansa.

Bai san cewa a wannan lokacin ne Fahad ya fara ganin haƙƙin Bashir a matsayin wani shinge da yake tsakanin sa da dukiyar da yake so ba.

Bayan ya fita daga ɗakin Rahman, kai tsaye ɗakinsa ya koma ya shimfiɗa takardun kadarorinsa da daddy ya bashi a kan table.

Ya duba kowace takarda da kyau.

Kadarorin suna da yawa. Rahman bai yi masa ƙarya ba. Ya tanadar masa da makoma daban da dukiyar company 

Wa’innan kadarorin ya kamata su wadatar da shi.

Amma Fahad ya kasa dena tunanin Northern Crest Holdings

Wa yake riƙe da ainihin yarjejeniyar haɗin gwiwar?

Ina aka adana tsofaffin bayanan company?

Su waye suka san ainihin sharuɗɗan yarjejeniyar?

Me zai faru idan Bashir ya nemi rabon shi na gaskiya idan daddy ya rasu?

Ynzu shi da ya kwashe shekaru yana aiki tuquru a kampanin shikenan beda kaso a ciki? Ina baze yiwu ba, dole ya fara chire wani kaso na dukiyar a hnkali ta yadda baza’a fahimta ba, har ya debi iya adadin kudin da yake ganin zasu fanshe aikin da yayi a company din, kuma ze nemi ainahin takardun yarjejeniyar nan don ya batar dasu,

Idan ainihin takardun suka ɓace, dole ne kamfanin ya dogara da sababbin bayanan da ze fitar, kuma idan ana iya canja waɗannan bayanan, wataƙila ze iya sa ƙarya ta bayyana a matsayin gaskiya 

Fahad ya jingina da kujerarsa.

Dazu ya shiga ɗakin Rahman a matsayin ɗa mai tsoron rasa mahaifinsa.

Amma ya fito daga ɗakin a matsayin mutumin da ya fara lissafin abin da zai iya ƙwacewa da ba nashi ba

Dole ne ya nemo ainahin yarjejeniyar nan, bai san irin nisan da zai kai ba tukuna kafin ya samu biyan buqata

Don haka ynzu ze fara diverting funds din kampanin daga boye, haka kuwa akayi, ya fara diverting kuddi daga kampanin a sache, bai san cewa Alh Bashir ya fara lura ba har ya fara tambayoyi game da kuɗaɗen kamfanin da suke ɓacewa ba, kuma hakan ya janyo attention na finance da audit aka fara bincike

Hankalin shi ya tashi sosai da yaga an fara bincike, tareda wasu gurbatattun ma’aikata ya biyasu kuddi masu yawan gaske sukayi forging documents da zasu nuna chewa ai Bashir shine ya sachi kuddin, a take kuwa Bashir ya shiga zargi, aka fara binciken shi, duk wani abu da aka buqata ya kawo don ayi bincike yana kawowa, a nan ne wani ya gayama Fahad ai cikin file din da Bashir yazo dashi office yau yaga wata takardar yarjejeniya da yake kyautata zaton Itache copy din Bashir, a take suka tsara yadda zaayi, zasuyi temparing da burkin Motar Bashir yadda ze samu accident, idan ze wuche gida zasu bishi daga baya su gani idan plan dinsu ya tafi dd, zasuyi kidnapping dinshi lokacin da ze samu accident din sannan su dauki wannan yarjejeniyar, daga nan kuma zasu azabtar dashi har se ya karbi lefin chewa shi ya sache kuddin company, shikenan se a dena binciken da akeyi a hukunta shi kawai

Sun aiwatar da nufin su, amma da yake abu yazo da qarin kwana a inda Bashir yayi accident a nan ya rasu, koda suka fito daga motarsu suka nufi tashi rai ya riga yayi halinsa, kawai se suka dauki takardar yarjejeniyar suka gudu, wannan kenan.


SOKOTO

Rana ta fara faɗuwa lokacin da Imran ya tsaya da motarsa a gaban gidansu Hauwa Koulou.

Hauwa ta gama shirya littattafanta, amma kafin ta buɗe ƙofar motar, ta juya ta kalle shi.

“Yaya, in tambayeka??”

Ya kalleta cikin kulawa.

“Eh, inajinki.”

Ta ɗan yi shiru kamar tana neman yadda za ta tsara tambayar.

“Me ya sa kake ƙoƙarin taimaka min sosai? I mean, duk yadda kayi busy da aiki you still make time to check on my studies.”

Imran ya yi murmushi.

“Saboda burinki yana da matuƙar muhimmanci a gare ki, kuma idan ina son in kasance cikin rayuwarki, ya kamata in girmama abubuwan da suke da muhimmanci a gare ki.”

Hauwa ta sunkuyar da kai tana murmushi.

“Ba ka jin tsoron cewa wata rana zan fi son karatu da aikina fiye da kasancewa da kai?”

Ya ɗan yi dariya.

“Hauwa, I don’t want you to choose between your future and me. Ina son ki ci gaba da karatu, ki cimma burinki. Idan Allah Ya ƙaddara mu zama tare, za mu samu hanyar gina rayuwarmu ba tare da na hana ki zama wadda kike son zama ba.”

Hauwa ta ɗago kai ta kalle shi.

Wannan halin nashi suna ɗaya daga cikin abubuwan da suka fara sa ta amince da shi.

Ba ya ƙoƙarin mallakar lokacinta gaba ɗaya. Bayasa taji kamar burinta zai bi iska idan ta shiga rayuwarsa.

“Thank you,” ta faɗa a hankali.

Imran ya gyada kai.

“You don’t have to thank me for respecting you.”

Ta buɗe ƙofar motar, amma kafin ta fita sai ta sake juyowa.

“Yaya?”

“Yes?”

“Thank you so much” ta sake maimaitawa

Murmushi ya bayyana a fuskar Imran ya nuna farin cikinsa.

Hauwa ta fita daga motar ta shiga gida, yayin da Imran ya jira har sai ya ga ta shiga lafiya kafin ya juya

A cikin zuciyarsa, yana addu’ar Allah ya sanya wannan dangantaka ta zama alheri a gare su.


AMSTERDAM

Maryam tana zaune a ɗaki tana tunanin kayan da za ta ɗauka, yayin da Zaid ke tabbatar da cewa an shirya duk abin da za su buƙata a tafiyarsu, se waya yaketa yi 

A ranta take raya chewa bazata dauki komai ba se supplements dinta da fit to fly din da aka bata daga asibiti

Zaid ya miqo mata wata ƙaramar jaka.

“Here. I’ve put your medical documents and supplements together.”

Maryam ta leqa ta duba ciki.

“Ka riga ka shirya komai?”

“Almost everything.”

Ta ɗago kai.

“Su kenan abnda zan dauka, bazanje da kamai ba”

Ya yi murmushi.

Sunyi shirin baccee da niyyar tafiya washegari

Amma tambayar da ta fi damun Maryam a zuciyarta itache 

Idan Fahad yana neman wannan paper din tun shekaru biyar da suka wuce, me ya sa bai samu ba? Ko be ganta bane?

Ta kalli Zaid, shi ma kallonta yake

Babu wanda ya furta abin da ke zuciyarsa, amma dukansu sun san cewa wannan tafiyar za ta zama farkon wani sabon babi.

Ba wai kawai dawowa gida ba ne.

Tafiya ce zuwa ga gaskiyar da ta ɓoye tsawon shekaru.

Kuma a wani wuri an Abuja, bayan wata ƙofa da ba a buɗe ba tun da dadewa, FILE 17 yana nan yana jiran wanda zai gano shi.


join our WhatsApp group 

***


764EEC4A-1D67-43EC-AD23-457229273A4F.png

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol