Free chapter · Read without an account

Chapter 2

by Fatima Isa Manu · KARYAYYEN ALKAWARI


*KARYAYYEN ALƘAWARI*

   (THE BROKEN COVENANT) 


 

BY


Fatima Isa Manu

( Sahiba )




💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

(J.W.A) 



‎بسم الله الرحمن الرحيم 



PAGE 📄 2




“ Babu inda zanje wallahi, ban da ko sisi, gwara a jik’amin hararrabi na sha. Asabe yau kwanan gidan ubanki zakiyi, bazaku kasheni ba, wayyooo goshina”


Rabi ta isa gare shi tana fad’in, “ Haba Malam ka daina ihun nan mana kaman yaro ƙarami, muje a dinke maka goshin naka zan biya kuɗin”


“ Bani kuɗin ki barni da goshin nawa Allah na tare da bawa mai hakuri, gobe zan siya koko da safe “ Ya miƙa mata hannu yana jiran ta bashi kudi.


Asabe ta ce, “ Malam ina laifin a..”


Rarumo kofin da ke gefensa yayi yana wurga mata ya ce, “ Shegiya da baki kamar na jaɓa, Asabe ki ka sake yin magana a nan a bakin aurenki, ban manta ba saura igiya daya tsakaninmu”


Shuru Asabe tayi dan tasan idan ya saketa bata da gurin zuwa, Baba Ladi ta ja tsuki tana cewa, “ Jaɓa sako baki a bar miki zance ba, kin fasawa mijinmu goshin ban da asara irin naki da rashin hankali,”


“ Ladi ki fita ido”


Malam yayi karaf ya ce, “ Taki fita din, nace taki fita Asabe, karya ta miki ne ba ke ce kika fasamin goshin ba, rashin hankali irin naki da rashin godiya ga ubangiji”


Girgiza kai mutanen wajen sukayi suna fad’in, “ Allah ya kyauta” Sannan suka fice.


Malam ya dubi Rabi da ta yi shuru tana kallon su ya ce, “ Za ki bani ne ko kin fasa Rabi?”


Ciro kuɗinta tayi ta kirga dubu biyu ta miƙa masa ta juya ta koma wajen sana’arta.


Malam yayi dariya yana saka kuɗin a aljuhu ya dafe goshinsa yana cewa, “ Ai auren mace irin Rabi riba ce ba irinku da kuke asara ba, gobe ma ku fasa min goshin ina da wacce zata gyara min” Daga nan ya fita ya bar su tsaye.


Asabe ta ja tsuki tana faɗin, “ Mace sai warin baki”


“ Ahayye chass, gwara ni akan wacce gabanta ne ke wari dan cutan sanyi ta cinye ta sanadiyar da mijinta bai kwana ɗakinta”


“ Kutumar jar abun nan, Ladi da waye kike yi?”


“ Duk wacce ta tsargu da ita nakeyi wallahi, kuma ko mahaukaci ne ka zage shi yasan da shi kayi” 


Kanta Asabe tayi da niyar dambe Ladi taja hannun danta zuwa ɗaka, ƙwafa Asabe tayi tana faɗin, “ Bari Malam ya dawo sai ya gayamin dalilin da ya gayawa wannan tsinanniyar matar tasa sirrina”




*SCHOOL OF HEALTH SCIENCE*





Malam Hamisu da ya lura da tsayuwar Nameer ne yaja hannun Dr Mujaheed suka bi ta hanyar baya, Dr ransa a ba ce ya kalli Malam Hamisu yana cewa, “ Da ka barni da yaron nan na gyara masa zama”


“ Sai dai ya gyara maka amma ba ka gyara masa ba, kasan waye ubansa kuwa a garin nan? Wallahi ka fita harkar budurwarsa tun wuri, idan kuma baka yarda ba ka shiga”


Tsuki Dr yaja yana faɗin, “ Yana students ina lecturer shine zanji tsoran shi? Samira dai yanzu na fara sonta kuma ban ga ubanda zai rabani da ita ba”


“ Mujaheed kenan, ina ce maka ga maciji kana na barshi, indai Nameer Muhammad Sardauna ne bismillah je ka taɓo shi, wallahi ina da tabbacin ko kamanninka baza’a gane ba indai akan wancan aljanan budurwar tasa ce” Malam Hamisu ya faɗa yana shigewa office nasa.


Ƙwafa Dr Mujaheed yayi a fili ya furta, “ Naga kala ace bazan lasa ba, ai bazai yu ba”


A bangaren Nameer kuma jin shuru basu fito bane ya cusa kai ciki dan ganin me suka tsaya yi, da mamaki yaga wayam, ya dubi Mansoor da sauri tare da faɗin, “ Ina suka je?”


“ Tare muke da kai fa a waje Sardauna, bansan inda sukayi ba nikam” Mansor ya ce yana kallon dayan ƙofan.


Nameer yaja tsuki yana wucewa ya nufi hostel nasu.





***





Samira ta ɗaga ido tana kallon Nafisa da ke dariya tana faɗin, “ Ni fa guy ɗin burgeni yake yi, kin ga naushin da ya bawa Sadiq kuwa, omo ya nishadantar dani. Amma nifa sai nake ganin kamar yana crushing naki ne”


“ Uhm Nafisa, cireni daga wannan bayanin banso, ko kin manta daga gidan da na fito ne da har zan tsaya kula wani saurayi? karatu nazo yi bani da lokacin batawa, bazan wa uwata asarar kudi ba,” Ta fad’a tana jan bedsheet ta rufe har fuskarta.


Nafisa ta tabe baki tana kwanciya akan gadonta, sannan ta ce, “ Ai shikenan kuma, sai da safe”





*2 o’clock na dare*





Makarantar yayi shuru duk wasu dalibai sun shige ciki an kwanta, baka jin hayaniyar komai sai kukan tsuntsaye.


Tura k’ofan dakin nasu akayi a hankali cikin sand’a aka shigo, haska gadaje guda biyun yayi ya sauke akan Nafisa da ke shakar bacci, ya mayar da hasken wayan kan fuskarta. K’arasawa yayi ya zauna a gefenta, ya shiga shafa gashin kanta da suke watse saboda hulan da ta saka ya zame.


Ya gangaro da hannunsa zuwa fuskarta kan lips nata, matso kusa da bakinsa yayi da zummar ya sumbace ta ware ido da sauri, ya saka hannu yana jan rigar baccin daje jikinta ya barge zuwa cibiya, wani razananniyar k’ara ta sake wanda ya kusa rusa hostel nasu dan har bangaren hostel na maza sai da suka farka.


Danne mata baki yayi da sauri ya gaura mata mari, Nafisa da ta tashi a rikice ne ta saki ihu “ kwartooooo” Ta dauki morpha dake gefe ta buga masa akai.


A burkice ya fita da gudu, d’akunan sauran kowa ya fito da gudu, securitys da suke waje aka hawo sama da sauri, hostel na maza duk suka fito.


Mansoor ya kalli Nameer dake sanye da vest da gajeran wando ya nuna masa sama ya ce, “ Wancan ba room na su Samira ba” 


Da sauri ya dubi inda yake maganar dan ganewa idanunsa, a razane ya nufi hanyar da gudu zuciyarsa na harbawa a dari, yazo zai hau upstairs suka ci karo da wani zai fita.


Cak ya tsaya yana cikumo rigar wancan din, suka shiga kokawa Nameer yayi nasarar cire abunda ya rufe fuskarsa dashi yana kai masa naushi a ciki.

 

Mansoor da abokanan su da suka iso ne mamaki ya dauke su ganin wanda ya shigon, Mansoor ya furta, “ Dr Mujaheed!!!”


A d’imauce Nameer ya ce, “ Ku rike min shi ina zuwa” Ya nufi d’akin da mahaukacin gudu yana ture matan da suka tsaya a bakin k’ofan.


Idanunsa ya sauka akanta, ta rufe kirjinta da hannu tana kuka ta nanannade guri daya, ya bi fuskarta da kallo yanda shatin hannu biyar suka fito manya.


A wani irin slow motion ya durkusa a gabanta yana binta da ido, ya janyo hijabin da ke gefe da alama salla tayi ta barshi ya rufe mata jiki dashi, hannunsa na rawa ya janyota jikinsa ya lumshe ido hawaye na sauk’a.


Samira ta cigaba da kuka sosai ta kankame shi gam, mutanen da ke tsayen wasu daga ciki suka fara gulma, “ Dama sonta yake”


Nafisa ta harare su tare da cewa, “ Naga dai babu uban da zaku bamu ko? dan haka ko wacce shegiya ta bar nan” Duk suka juya suka bar bakin k’ofan.


A hankali ya janye ta daga jikinsa, sannan ya mik’e ba tare da yace komai ba ya nufi wajen su Mansoor kamar mayunwacin zaki, har filin makarantar ya je sannan ya same su tsaye a wajen security da wasu malamai.


Ya ratsa tsakiyarsu tare da cukumo Dr Mujaheed, kafin su ankara ya fara kai masa bugu ta ko ina huci, aka taru ana janye Mujaheed daga jikinsa amma yaki sakinsa sai ma abunda ya cigaba.


Sai da ya tabbatar ya sumar dashi sannan ya sakeshi yana faduwa, Sir Bashir ransa a bace ya ce, “ Baka da tarbiya ne ana maka magana ka barshi kaki, shi din ba malaminku bane, sai nayi suspending naka”


Nan sabon fad’a ta kaure tsakanin students da malamai, kamar za su kaiwa junansu bugu kowa ransa a kusa yake dan bacin rai, dama ba yau bane farko an saba musu irin iskancin nan, sai a fake da cewa barawo ne ya tsallako; to yau kuma an tabo wacce baza’ayi shuru bane.


Abokin su Nameer wato Nura kamar zai kaiwa Sir Bashir duka yana cewa, “ With due respect sir kai ma kwarton ne, idan baka yi suspending namu ba kaki Allah”


“ You will see, sai na koreku dukanku tunda dai tarbiya ce baku dashi”


Mansoor ya karbe zancen da cewa, “ Ku ma tarbiyan ne da ku? yaran cikinku kuke bi kamar bunsuraye, babu wanda ya isa ya mana abunda Allah bai mana ba, kuma ba makarantar nan kake takama dashi ba sai mun saka an kulle”


Malam Hamisu ya sassauta murya yana fad’in, “ Abun bai kai har haka ba, kuyi hakuri ansan an muku laifi sorry, abar zancen zuwa gobe da safe ku same mu a office”


Security suka kama Dr Mujaheed da ke kwance rai a hannun Allah da niyar kai shi ciki, Nameer ya ce, “ Ku ajiye shi fa, wallahi wallahi sai ya bayar da kudin magani dubu dari biyar, sannan kudin yaga mata riga naira dubu dari, da barin jikinta yasha iska shima 1m, idan kuwa bazai bayar ba sai na tura case din nan court yanzu a nan”


Da sauri Lecturers suka kalli juna zuciyarsu na harbawa, yayin da students kowa abun ya masa dadi duk sukayi bayan Nameer alamun dai suna goyan bayansa.


Sir Bashir ya hadiye yawu da kyar yana duban sauran ya mayar da kallonsa kan Mujaheed..



*Za su biya ko ko Aa?🤔*





*SAHIBA ✍🏻*

***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol