Free chapter · Read without an account

5

by Asmy b Aliyu · OMRI HAYATII

OMRI HAYATII 
by...
Asmy b Aliyu

5....
daidai get din gidansu mu'azzam ta tsayarda motar.ahankali take yiwa mai gadi horn.....baa jimaba ya bude get din,
inda aka tanada dan parking motoci can 
tayi parking motarta ganin motar Fadeela
wurin ya tabbatar mata da tazo gidan,
Yana zaune cikin motar yanata kallonta da idanunsa wanda suka tara wata irin gajiya still yanajin ciwon kan nasa sama-sama
hannu yasa zai bude murfin motar ta rigansa bude masa kofar ,daga Kai yayi Yana kallonta ko kiftawa bayayi 
langabe Kai tayi tana kallonsa gamida ware masa idanunta, murmushi yayi 
Yana shafa sumar kansa a natse ya fito daga motar hannunsa ya daura akan marfin motar batareda ta Jaye hannunta ba,kusan tare suka rufe motar.

juyawa sukayi ahankali suka nufi entrance din shiga gidan ,samun kanta tayi da riko 
hannunsa ta rike cikin nata hannun,wata irin ajiyar zuciya take saukewa lokaci daya Mai cike da natsuwa.suna gafda shiga kofar falo ya cire hannunsa cikin nata,
binsa tayi da ido ,tana jin yadda bakinsa ke furta sunan mami a hankali batareda sautin ya fita ba daga Kai tayi alamar ta fahimta ,
babu kowa a falon farko Sai karar AC haka falon ya dauki wani irin sanyi tareda kamshin roomfrehner,mai dadin gaske
falo na biyu suka nufa dan can Suka fara jin hayaniya,Fadeela ce kanwarsa da yaranta guda biyu sai Kuma Fareeda da AYUSHERH,da sauri Fadeela ta wara ido 
tana kallon malaak din da mamakin ganinta,
qarasowa itama malaak din tayi da murmushi a fuskarta ta zauna tana baiwa Fadeela side hug tana furta bestyyyna."

"Yaa malaak Ina wuni sannu da zuwa
fareeda ta fada cike da sakewa a muryarta .cike da fara'a malaak din ke fadin"Ya'mmatan Mami ya kike ya school ??"Alhmdullahi fareeda ta furta 
tana tsaye a gefen kujera har lokacin,
da wata irin murya ta kalli malaak din 
tana gaisheta,batareda malaak din 
ta baiwa gaisuwarta muhimmanci ba ko ta kalli inda take take fadin."kina lafia,
da haka malaak din bata qara furta komai ba ta tattara hankalinta akan Fadeela,
Kai tsaye Ayusherh ta nufi kitchen dan kawowa malaak din ruwan sha.

"Yaayanmu Ina wuni."
Fadeela ta fada tana kallonsa,hararata yayi Yana fadin"Auh ashe kin San da zamana a falon?"murmushi Fadeela tayi tana fadin"bazaka amsa mun ba Sai ka yimun bakar magana ,,dariya malaak tayi
ta juya tana kallonsa tana fadin"kodai kana kishi ne??"
kai tsaye up stairs ya nufa Yana jefawa malaak din wani kallo mai ratsa zuciya da ruhi.

Ayusherh ta aje madaidaicin tray agaban malaak din mai dauke da snacks da lemu,
cigaba da danna wayarta malaak tayi 
batareda ta kalli tray ba,batasan meyasa 
duk taga Yarinyyar nan agabanta ba take jin wani irin mugun faduwar gaba,
gaba daya yanayin malaak din canjawa 
yayi.itakam Ayusherh na aje tray taja hannun ya'yan Fadeela zuwa dakin kaaka
itama ba wani sakewa take ba,muddin Xata ga  malaak din a gabanta.wani irin shakka da tsoro ke mamayar zuciyarta.
baa jimaba mu'azzam ya fito tareda Mami 
cike da fara'a Mami ke kallon malaak din 
da ta taso Cike da natsuwa da wayewa 
tayi hugging din Mami.

"Mami Ina wuni......"ta fada sounding so very respect a muryarta itama mamin cikin kulawa da tattali take fadin."lafia kalau 
my baby ya kike ya mum?"lafia lau Mami,
mum tana gida tace a gaisheki,
mu'azzam juyawa yayi 
ya nufi kofar fita da alamar bangarensa
zai tafi,Yana barin falon malaak din ta tura masa gajeren sako....

"Ina Kuma xaka tafi??"
Ina bangarena wanka nakeso nayi.
Shima ya tura mata reply,
kalmar ok.......kawai ta turamasa ta cigaba da hira da Mami ,da Fadeela daman Kuma Mami kawar mahaifiyar malaak din CE
sanadiyar mazajensu suka kulla zumunci,
duk da akwai banbanci halayya sosai 
a tsakanin mahaifiyar mu'azzam din 
da malaak,Mami macce ce Mai sanyi 
hali mai girmama jama'a bata da izza da nuna ita watace saboda Mijinta yana da tarin dukiya sabanin hajiya zainab mahaifiyar malaak din macce mai isa 
da wulakanta dan Adam da wani irin girman Kai,Yadda take juya mahaifin su malaak tamkar itace mai dukiyar Yan uwansa babu Wanda ya isa ya rabesa daga ita sai ya'yanta ,hakama bai isa yayiwa Yan uwansa wani Alkhairi ba Sai ta basa umurni shiyasa ya'n uwansa da mutanen gari ke mata kallon ta riga tagama da mahaifinsu malaak din ta shanyesa Sai abunda tace Wanda hatta Kara idan ta axa idan bata bada umurnin ya tsallaka bai isa ya tsallaka ba.kusan rayuwarsu 
itada ya'yanta da mijin a US suke gudanar daita dan kasuwancinsa yafi karfi acan
haka kamfanoninsa sunfi yawa acan,
kusan ya'yanta acan ta haifesu acan suke girma acan sukayi karatu.....Sai da girma 
ya fara kama masa yake zaman Nigeria akai akai Kuma hakama ya'yan nasu Allah ta dora masu son zaman Nigeria musamman malaak din,
ya'yansu biyu a duniya duka mata
maleeka itace yarsu ta farko Sai malaak din daga nan Suka dakatar da haihuwar
dan daga shi har hajiyar bama su raayin Tara Yaya bane,
fara zamansu a Nigeria zumunci ya hadu 
tsakanin mahaifiyar malaak din da mami Mu'azzam yawan zuwa gidan da suke
nan take mu'azzam din ya shiga ran malaak sosai akai akai take yawan zuwa gidan saboda shi,duka fakewa take a wurin Fadeela take zuwa Wanda suke kusan sa'annin juna da malaak din,
Dan ma ita Fadeela tana cikin karatu
jami'a tana samu miji akayi aurenta 
a dakin Mijinta tagama karatunta,
haka malaak din tayi ta mita lokacin 
Auren akan meyasa Zata yadda tayi aure da kananun shekarunta ,duk da lokacin bazata wuce 18years ba dan kusan shekara biyar ta baiwa fareeda shi Kuma mu'azzam shekara goma ya baiwa Fadeela
akwai tazarar shekaru a tsakaninsu,
tun Mami batason mu'amalar mu'azzam da malaak din har ta hakura ,dan ganin yanayin rayuwarsu ba iri daya bace 
tsoron allah tsoron Mami Kar a juya mata kan yaronta kamar yadda aka juyawa 
uban malaak din.

duk da har yanxu Mamin batason mu'amalar tasu. inda hankalinta ya kwanta har yanxu mu'azzam baiyi maganar Auren malaak din ba,Shima mu'azzam din kafin ya sakewa malaak din Sai da tasha wuya da naci kafin ta samesa ,farkon fara mu'amularsu yadda take rungumarsa 
take masa yawan abubuwan da babu tsari
ya fara binta da nasiha,haka Yana nuna mata bacin ransa akan haka.tafia tayi tafia
haka ya kula bazai iya canja malaak din ba,saboda rayuwar turai tayi.duk yadda yake kauce mata Sai da tasa ya biye mata
duk tsananin kamun kansa da tarbiyar da Mami ta shafe shekaru talatin da shidda tana azasa akai Sai da malaak tasan yadda tayi ta ruguzasa,ta riga tayi ammana da babu namijin da ya isa ya kita a wannan bangaren komai kamewarsa.tun tana yimasa kiss Yana kaucewa hakan,
har ya saba idan batayi masa ba shi 
zaiyi mata.duk iya kiss da hugging kawai suke tsayawa bai taba wuce iyakarsa ba,
kullum Yana hango idan wani yayiwa 
fareeda ko Ayusherh haka??"ai Ranar yasan konewa zuciyarsa xatayi duk yadda 
yakeson ya daina taba malaak din
ita Sai tasan yadda ta sakasa ya dawo hanya ya kula abun ajininta yake.......

######
kusan awa daya tanata danna wayar hannunta hirar da Fadeela ke mata bama ganewa take ba gaba daya hankalinta da tunaninta na kan mu'azzam tana ta tunanin ko ciwon kan da yake ya hanasa dawowa .ta rasa ta yadda Zata Kai bangarensa batareda Mami tayi tunanin wani abu ba, dan sosai Mamin ke mata wani irin kwarjini.....da sauri ta turawa
yayarta maleeka test akan ta kira wayarta,
cikin minti biyu Sai ga maleeka din ta kira.
da sauri malaak din ta miqe tsaye da murmushi a fuskarta ta kalli Fadeela 
tana fadin bari ta amsa waya ,da haka ta nufi kofa wayar na cigaba da ring kafin ta daga kiran.

"malaak lafia?"
maleeka ta tambaya .zan kiraki zuwa anjima bye....da haka ta katse Kiran batareda ta baiwa maleeka damar maganaba da sauri ta nufi bangarensa,
hannu tasa ta tura kofar Sai tajita a bude wani irin cool kamshi ke fita cikin falon,
da wani irin sanyi mai saka nutsuwar zuciya...babu kowa a falon Kai tsaye bedroom dinsa ta nufa harta saka hannu tayi knocking Sai Kuma ta fasa
tura kofar tayi Kai tsaye hangosa
tayi tsaye agaban dressing mirror 
da dryer a hannunsa Yana busar da sumar kansa,babban towel ne a kugunsa kalar brown.ta cikin mirror yake hangota tsaye a bakin kofa ta wani kafe bayansa da ido,
Wanda ya nuna alamar karfaffa namiji Mai wata irin maxantaka dan koina jikinsa a murde yake,Zata iya kirga sau nawa ta gansa da towel a jikinsa wani irin abu ta rikaji Yana bin jinin jikinta,
hatta numfashinta jin tayi Yana neman tsayawa,takawa take a hankali tana nufar inda yake .haka wani irin yanayin son kasancewa tareda shi na saukar mata,
rabonta da shiga irin wannan yanayin 
tun tana soyayya da wani baturen tsohon saurayinta,kusan shekara biyar a baya.
a hankali ta saukar da hannunta akan kirjinsa haka tana hade fatar bayansa da jikinta.......lokaci daya komai nasa
ya tsaya jin hannayenta akan kirjinsa wani irin numfashi mai dumi take sauke masa cikin bayansa.
Runtse ido yayi yanayinsa na canjawa lokaci daya.....

"malaaaak!!!!!!!!ya fisgi sunanta da wani irin qarfi haka lokaci daya yake kokarin kaucewa abunda takeson yi......

#OMRI HAYATII
#HOT LOVE/ROMANCE 
#MALAAK FAROOK RANO 
#MU'AZZAM MARAFA
#ASMY B ALIYU 
#***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol