Free chapter · Read without an account
6
by Asmy b Aliyu · OMRI HAYATII
OMRI HAYATII
by
Asmy b Aliyu
6....
"Yaushe zan mallake ka dan Allah?"
ta fada da wani irin yanayi cikin muryarta
hannunta ya cire a kirjinsa.ya juya
Yana kallonta abubuwan da take hangowa acikin idanunsa a wannan lokacin ba masu saukin fadi bane.kallon da yake mata
Yana tabbatar mata da Shima namiji ne Mai cikakkiyyar lafia mai son kasancewa da macce a ko wane lokaci,
"malaak je falo ki jirani na saka kaya.
wani irin mamakinsa ya daskarar daita
a wurin,juyawa yayi a hankali ya daga kafa tasa hannunta tana rike dayan
hannunsa da yasa ya juya Yana kallonta
da idanunsa da har lokacin basu koma daidai ba.
batareda ta furta komai ba dan irin wannan yanayin da ya nuna mata tasan shiru yake bukata,sai ta zabi da tayi shirun
shigewa tayi cikin jikinsa tana yimasa wata irin runguma.haka tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa, a hankali ta dago tana kama fuskarsa da hannayenta biyu,tana ganin yadda fuskar tasa tayi wani irin ja,
harshenta ta fidda tana lasar dogon hancinsa.wani irin kallo yake binta
dashi gangaro harshen nata tayi adaidai kan jajjayen lips dinsa da Suka bushe lokaci daya, saboda yadda malaak din
ta kunnasa.wani irin numfashi yake sauke mata akan fuska mai zafi
batasha wahalar samun bakinsa ba,
wani irin nutsassen kiss ta rika yimasa
a hankali take tsotsar harshensa tana shafa kirjinsa ,babu sautin da kakeji a dakin Sai sautin numfashinsu .
wani zazzafan kiss suke aikawa junansu tamkar xasu cinye bakin junansu
wani irin kiss mai zurfi yake mata Wanda bai taba yimata kalarsa ba ,jin tayi kafafunta na kasa daukarta. dan yau al'amarin yafi na ko yaushe Karfi
Kara manneta yayi da jikinsa Yana jin wani abu na sauka cikin jikinsa jin
yayi duniyarsa na canjawa a hankali,
itama malaak din lokaci daya ta fara fita hankalinta. dan bai taba birkitata haka ba,
sunyi nisa da abunda suke wayarsa ta katsesu da sauri ya saketa Yana jin ya fara dawowa hankalinsa numfashi yake fitarwa
Yana saukewa ,har Kuma lokacin wayarsa bata daina ring ba kan bed ya karasa ya dauki wayar ganin Mami ce ke kira Sai da zuciyarsa ta tsaya da bugawa na Yan sakanni........halin da yake ciki baya jin zai iya daukar wayar mamin dan idan taji muryarsa a wannan lokacin yasan Mami
Zata iya gano abunda ya faru tsakaninsa da malaak musamman Mami yadda ta iya kula da duk wani motsi na ya'yanta....
ya kalli malaak din da har lokacin
take kallonsa ganin yaki daukar wayar,
"Mami ce ke kira pls ki tafi bangaren Mami
idan nagama zanzo."
bai jira mai zatace ba ya nufi bathroom Yana jin wani mugun ciwon mara na saukar masa,da wani irin mayen kallo ta bisa tana kissima abubuwa dayawa
akansa juyawa tayi tabar room din
nasa ,koda ta fita a parking lot ta tsaya
tana jin kamar turaren jikinsa cikin nata jikin.
gashi tabar Jakarta a falon Mami carkey dinta na ciki da bude motarta kawai xatayi
ta kara fesa turare.cigaba da tsayuwa wurin tayi na dan wani lokaci kafin ta koma bangaren Mamin......tunda ta shigo
falon mami ke kallonta ko kiftawa batayi
jin tayi tana neman rasa natsuwarta da irin kallon da Mami din keyi mata,
dakyar ta xauna gefen fadeela tana kirkirar murmushi.
tunda ta shigo falon Mami taji kamar malaak din na kamshin turaren Mu'azzam din.tamkar Yana wurin zuciyar Mami Sam takasa natsuwa.miqawa tayi ta nufi kofa batareda ta furta komai ba .Sai da ta fita
malaak din ta rika Jan numfashi tana saukewa.dabi'un mami basu yiwa malaak din ba ko kadan mamin ta cika takura da sakawa ya'yanta ido,Sam babu wani freedom acikin Rayuwarsu.har mu'azzam din dake matsayin namiji.mama's boy ne na qarshe.
gajeren sako ta turawa mu'azzam din tana fadin idan yagama tana jiransa .gida takeso ta wuce....... knocking kofar dakinsa akayi da mamaki yake kallon kofar.
isa bakin kofar yayi ya bude kofar,idonsa
cikin na Mami da take binsa da kallo tun daga sama har kasa jin yayi zuciyarsa ta buga haka nan take kafafunsa suka fara rawa jin yayi Suna neman kasa daukarsa,
"Mami!!!"ya fada da sanyi a muryarsa,
na kira baka dauka ba har sau biyu ?"
meyasa?"ta fada tana tsaresa da idanunta masu kaifi,koda kika kira ina toilet
yanzu nakeson zuwa na sameki.
ka sameni a daki yanxun nan
Mami tana fadin haka ta juya ta nufi kofa tana ficewa daga dakin,zama yayi a bakin bed dinsa hannu yasa ya dafe kansa
har lokacin zuciyarsa bata daina bugawa ba,wani irin tsoro yaji Yana shigarsa
yafi minti goma zaune cikin wannan
yanayin.kafin ya tashi ya wuce bangaren Mami,koda ya shiga har lokacin malaak da Fadeela na a falon baice komai ba ya nufi up stairs da ido malaak ta bisa
tana karantar yanayinsa.itama jin tayi zuciyarta ta kasa natsuwa yadda taga Mamin tana behaving...
a bakin kofar mamin Ya tsaya yayi knocking kofa,kusan minti biyu aka basa umurnin shiga.da sallama ya shiga dakin Mamin da Sai kamshin turaren wuta ke tashi acikinsa,Mami na zaune akan soofa
tana danna waya batareda ta daga Kai ta kallesa ba sallamarsa kawai ta amsa,
haka yasa jikinsa ya qara yin mugun sanyi
da wani irin tsoro da farargaba hadi
da sanyi jiki ya qarasa wurin Mami,
ya sauke kafafunsa kasa ya xauna akan carpet,samun kansa yayi da saukar da kansa kasa.da wata irin taushin murya yake fadin"Mami gani...............sunfi minti biyar a haka kafin Mami ta bude baki da wani yanayi mai zafi cikin muryarta take fadin
"Ibrahim?"""daga Kai yayi Yana kallon Mamin Yana jin zuciyarsa na wani irin bugawa,ba sosai Mami ta fiye Kiransa da wannan sunan ba saboda sunan mahaifinsa yaci shi yasa suka mayar dashi mu'azzam,tun Yana karami idan har Mami ta kirasa da wannan sunan yasan akwai
magana mai muhimmanci a bakinta
akwai hukuncin da Zata zartar akansa Kai
tsaye Wanda bai isa ya tsallake umurninta ba,tun kafin Mami ta bude baki ta fadi abunda ke ranta yaji iskar dakin nayi masa wata irin kadan,nan take ya soma hada gumi duk sanyi AC.dake cikin dakin na Mami jin yayi sanyi yayi masa wani irin kasa.
"Meye ainahin matsalarka da baxaka fidda mata kayi aure ba kamar kowa??"tunanin da yake daban akan Mamin Sai gaya tambayar Mamin ta Sha baban da tunaninsa,
kasan shekarunka nawa??"shiru kawai yayi Yana kallon mamin Yana jin wani sassauci a zuciyarsa dama jikinsa da yayi masa nauyi lokaci daya.sumar kansa ya shiga shafawa a hankali,
Banda nazarinsa babu abunda Mamin keyi.
Banda ita....... Banda malaak Rano Mu'azzam!!!" ba itace maccen da nake mafarkin ta zama surukata ba duk da nasan babu soyayya a tsakaninku!!!"
kalaman Mami yasa wuta ta dauke masa
da wani irin shock ya daga kai Yana kallon Mami,irin kallon da ya kafeta dashi
ya tabbatar mata da akwai wani abu tsakaninsa da malaak.jin yayi yawun bakinsa Sun kafe masa lokaci daya,
harshensa yaji ya masa wani irin nauyi
wani irin juyawa yaji kansa nayi.
haka yaji duniyarsa na kokarin tsayawa guri daya,Mami bata barsa ya dawo hayacinsa ba ta kallesa ido cikin ido
take fadin"zan baka dama kafin na yanke maka hukunci watanni shidda mu'azzam ka zabo matar da zatayi daidai da raayina
ka gabatarmun daita a matsayin matar aurenka idan tayi daidai da raayina
bani da matsala ,idan watanni shiddan nan Sun cika baka motsa ba zan yanke hukuncin zaba maka matar auren da Zata dace da rayuwarka.zaka iya tafia na sallameka.""duk yadda yaso ya fahimtar da Mami a wannan lokacin kalaman bakinsa bacewa sukayi ya kasa furta kalma ko daya akan Mamin ya miqe da sanyi jiki
ya nufi kofa har ya fice daga dakin
Mami tana kallonsa.
wani irin abu mai nauyi ya danne mata zuciya ko mu'azzam zai mutu bazata bari ya auri ya'r zainaba ba.ashirye take da fada da kowa akan hakan,tun daga kan stairs malaak ke kallon yanayinsa
wani irin mummunan yanayi take hangowa cikin fuskarsa.ga mamakinta bai tsaya falon ba ya nufi kofa .Fadeela ma nayi masa magana bai kulata ba ,bai san Yana son malaak ba Sai yanxu da Mami take kokarin rabasa da malaak din .bai San Yana yiwa malaak so na hakika ba da soyayyar Aure Sai yanxu tafia yake bai San inda yake jefa kafafunsa ba shi dai ya gansa kawai a kofar shiga falonsa. da wani irin nauyin kafafu ya karasa cikin falon
hannu yasa Yana murxawa kofar key
anan bakin kofar ya zube Yana furta kalmar innalillahi wainnah ilaihir rajiun!!!
malaak da duk a firgice take ta kalli Fadeela tana fadin"besty zan wuce
gida bana son mum ta fara kira bari naje nayiwa Mami sallama,cike da kulawa Fadeela ta miqe tsaye ta raka malaak din har bedroom din Mami.Cike da kulawa da sakewa Mamin ta tarbeta nan ta fadawa Mamin Zata wuce ,Mamin tayi mata fatan sauka lafia haka tace ta gaisheda mum dinta.malaak ta dan samu natsuwar zuciya da taga Mamin yadda ta karbeta ,
Amman acan kasan ranta tunani ne sosai cikin zuciyar malaak din.,me ya canja mu'zzaam?"har bakin mota Fadeela ta rakata tun kafin ta shiga motar take Kiran lambar mu'azzam har tagama ring bai dauka ba kira 3 tana jera masa bai daga ba,jin tayi hankalinta na Kara tashi
dakyar taja mota tabar gidan......
#OMRI HAYATII
#LOVE/ROMANCE
#MALAAK FAROOK RANO
#MU'ZZAM MARAFA
#ASMY B ALIYU
#***