Free chapter 路 Read without an account

56

by Anisa Muhammad Yahaya 路 NUFIN ALLAH


馃挄 NUFIN ALLAH 馃挄 
By
Anisa Muhammad Yahaya 


 YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA 

Page 5锔忊儯6锔忊儯

''Kun dawo, har ina cewa ku tafi dasu yanmatan nawa suma suga gari, ashe ku har kun tafi abun ku'' 

Kanta ta 蓷ago ta kalli Momma dake zancen se ta kalli Ya Umar din, ashe ma Momma tasan da fitar su amman shine ya mata shiru ya kyale ta tana ta fargaba 

'' Ai Momma muma Ya Usman ze Kai mu yawo kuma ba inda zata bi mu tunda mu ko fa蓷a mana ba tayi ba ta saci jiki ta gudu ta bar mu'' 

Ya Usman ne ya juyo ya kalli Jalila jin tana cewa ze fita dasu, ai ko ze fita dasu shegen surutun ta ma baze bar shi ba, shi be fiya son hayaniya ba amma ya lura ita dai Jalila surutun ta yawa ne da shi, kai ya kawar yana ta蓳e baki bece dasu komai ba, duk surutan da suke yana zaune ne a parlourn kawai dan shi be fiye son zaman 蓷aki ba a cewar sa shi ba daddawa bane da zai ta zaman 蓷aka ba gwara ya fito ya zauna cikin mutan 拼anuwan sa, shi in ba dai hayaniya ce ta fiye yawa ze bar muku gurin, se ya zauna kuma manta yana gurin

Sum sum kamar wata mara gaskiya tayi hanyar dakin su, da kallo ya bita shi kuma ya zauna kusa da Usman ya mi茩a wa Nabila dake kusa da shi ledan hannun shi guda 蓷aya yace ta bata, sannan ya mika wa Hamza biyu yace ya sa 蓷aya a plate ya kawo Momma, 蓷ayan kuma nasu ne, suma tashi suka yi suka bita, suna shiga Jalila tace 

'' uhmm wannnan zagaye wa haka, to ina kuka je, shine ko a fa蓷a mana, aka munafurce mu ko sister''
Ita dai bata ce komai ba se murmushi da ta mata, 
'' Kee har wani blushing take awwwwn'' murmushi sosai ta 茩ara yi jin yanda Fareedah ke mata abu, haka kawai yau taji ta kasa jin haushin tsokanar tasu se dariya da suke bata

'' sister ga ledan ki, masoyin ki yace a baki'' 
'' wallahi Allah ya kyauta muku'' ta fa蓷a ta shige toilet dan yin alwala dan suna shigowa ana magriba

Bayan sun idar da Sallahn suka baje ledan tsiren a tsakiyar dakin suna ci suna hira da zolayar juna,
'' Allah sarki tsire na, wallahi nayi missing parrot 蓷innan bare ma idan naga na Momma se inyi ta kewar shi, ko ya Ahmad na duba mun shi ma oho, Allah sarki kar ni dai ya mutu ma ''

'' da yake ajje shi kika yi da ze zauna zaman miki kiwo, shima bu茩atar a duba shi yake so ayi ba ya zauna kiwon wannan akun naki me banzan suna ba'' 

'' iyeee to ai se ki je ki duba shin, kuma akuna sunan shi ba banza bane, kishi kike ji sunan shi yafi naki da蓷i ''

'' ai kema kin san da ina kusa da na duba shi amma tazarar da yawa''
'' wallahi Nabila kinyi nisa ba kya jin 茩ira, mudai ayi ayi mu sha biki''
'' ai Reedah bikin ban kawai hango mu nake ni dake a stage, lailaha illalla, se mun ci uwar sa bada''
'' kedai bari pickles zagewa zanyi in danse inyi wa idona kwalli bani ganin kowa bare kunyar su Amma ta hanani rawar gaban hantsi''

'' ku bafa wani event din rawa da za'ayi''
Dukkanin su har Nabila juyowa suka yi suka kalli Anisa jin abinda tace aiko suka kwashe da dariya har da tafa hannu suna shewa 

'' ustazan cin ne yau ya motsa, ai idan ke ba zaki yi ba nikam se an girgije''
'' ba wani ustazan ci fah Kuma kun san ba tun yau ba ina yawan fa蓷a muku idan dai biki na za'ayi ba dinner ba duk wani taro da ze ha蓷a maza da mata waje 蓷aya ana wannan haukan, gwara dai imu imu mata wannan ko me za'ayi ba lefe''

'' baki da hankali wallahi, aiko wallahi baki isa ba kinga za mu yi dinner, zamu yi ladies party, bridal shower, henna day, Fulani day, kamu na iyaye ne, Arabian night, girls night, ke se mun yi event fun goma''

'' Allah ya kyauta miki Reedah, to ko za'ayi duk Wannan ko Qur'ani day ban ji kin lissafa ba''
'' Kee sha'afa tayi mana, amma for serious ko bamu yi event goma ba gaskiya se mun danse''

''Pickles waye ze hana ku rawa indai iya mata ne ai ba wani abu bane, amma duk dinner 蓷innan mata da maza suyi ta ba蓷ala ana hauka wai rawa ana sa wasu 蓷amammun kaya duk su ke kwashe albarkan auren, har gwara ku zauna ku sauke ma ma'auratan Alqur'ani, ku musu addu'a Allah ya albarka ci auren, amma ina!!!, yanzu gani akeyi kai ya waye duk wannan old fashion ne sedai ayi she蓷anci a watse, koda za kuyi rawa da raye raye, indai iya ku maza iya ku mata falillahil hamd, amma duk wannan maza da mata su cunkushe guri guda ana hauka kwashe albarkan auren ku kuke yi baku sani ba''

'' wallahi haka ne kuma sister kina da gaskiya, to za muyi events imu imu banda mazs se mu girgije abun mu hakan ya miki'' 
Kai ta gya蓷a wa Jalila jin abinda tace

'' awwwn sister ashe dai kina da hankali, su Anisa an girma, ko da yake an kusa zama married woman karewar girma saura zuwa mu amso babies dinmu''
'' wallahi Reedah Allah ya kyauta miki, tun ma ba a riga da anyi ba har kina maganar wasu babies, Allah ya miki me kyau''

Duka dariya suka kwashe da shi Nabila tace '' ameen dai, Allah ya kyauta miki, gaskiya zancen ki haka yake Allah ya dai bamu ikon gyarawa''

Da ameen suka amsa, Anisa ta na蓷e ledan da suka gama cin tsiren ta fitar waje, suna nan shida Ya Usman a parlourn, ita kuma Momma na da茩in da umma take taje gyara mata jiki, dan kafin tayi bacci take zuwa ta mata duk gyare gyaran da ya dace




'' jama'a shin wace umman ake gyarawa? Kuma me ya same ta?


Let's keep going, ance dai in zaka gina ramin mugunta ka gina shi gajere ba ka sani ba ko kai zaka fa蓷a



Follow me on arewapen for more updates 馃ス 馃檹 馃檹 



______________________
By 
Anisa Muhammad yahaya 馃尯 
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol