Free chapter 路 Read without an account

59

by Anisa Muhammad Yahaya 路 NUFIN ALLAH



馃挄 NUFIN ALLAH 馃挄 
By
Anisa Muhammad yahaya 


 YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA

Page 5锔忊儯9锔忊儯

Zancen Abida tayi ciki ya zagaye unguwar su, daman wa蓷anda suke shiri da Umma suna gasa mata magana akan ta samu fitsarariyar yarinya bata jin maganar ta, wa蓷ansu kuwa kafin su bar gidan se sun yada mata magana kan cewa abinda tawa su Rukayya ne ta fara girba, kuma bata ga komai ba ma tukuna, 

Kuma duk masu yada mata wa蓷annan maganganun 茩awayen ta ne na unguwa da bata iya 蓳oye musu komai na cikin gidan ta, dan kwata kwata umma bata da sirri, 

Hatta Hajiya Kursum din da take aminiyar ta itama ta juya mata baya dan duk asire asiren da take wa mijinta ya karye, mahaifiyar sa ta sa ya 茩ara aure yanzu waccan ke cin karen ta ba babbaka, yace a yanzu baze rabu da ita ba amma ta cigaba da abinda take kuwa red card dinta zata amsa a hannu kuma ya mata iyaka da sahura, shiyasa ko numbern ta ma tayi blocking, ranar da ta taka taje gidan ta kuwa, kwalli tawa idonta ta ci mata mutunci ta mata korar kare

Abubuwa ne suka taru suka mata yawa, kullum tana cikin damuwa ga jinin ta da kullum a sama yake dan 茩ananan maganganun mutane akan cikin da Abida tayi ga ita kanta Abidan da ke gasa mata magana son ranta

Ana haka ta kawo wani wai ta samu mijin Aure kuma yasan da ta zubar da ciki amman ya amince ze aure ta, kuma mai ku蓷i ne, yayi aure kusan so uku yana rabuwa da matan, a cewar sa wai duk dan kudin sa suke son shi ba tsakani da Allah ba, amma ita yaga tsakani da Allah take son shi shiyasa yake son ya aure ta duk da abun kunyar da ta aikata 

Ita dai Umma ba baka se kunne dan a jikinta tana jin kamar akwai wani makarkashiya a auren, haka kawai take jin 茩arya yake, da ta zaunar da Abida ta mata wa'azi, ta tambaye ta ko an bincika an san waye shi se tace

'' haba Umma, wai me yasa kike mun haka ne eyye, na lura fa tun na samu wannan mai ku蓷in kike mun ba茩in ciki da hassada, ni nayi bincike karki wani kawo mun 茩abali da baadi, ko nima irin ta Rukayyan zaki min, ina fa tuna lokacin da kika sa saida Abba ya aura mata driver, bayan ta kawo wanda take so dan yana da ku蓷i kika hana ta auren sa dan hassada, nima kenan abinda kike son yi mun kenan yanzu, to wallahi baki isa ba'' 

Kasa magana Umma tayi jin yanda wai Abida ke gasa mata wannan maganganun haka, duk wannan abubuwan dan su tayi, kar yaran Harira su fi su da komai amma wai yau ita take fa蓷awa wannan maganar, wani kwallar takaici ne ya cika mata kurmin idanun ta, da kallo kawai take bin Abida dake ta sur fa ruwan masifa, ji tayi ta fara dana sani akan abubuwan da tayi wasu Juwaira 

Abida da kanta ta kira Abba Munir ta sanar mai dan ta fa蓷a wasu Mama Safiya amman ko wacce tace ita ba ruwan ta da sha'anin ta, dan a lokacin Umma sauke duk wani abu da take ji da shi tayi taje wajen Mama Maimuna ta fa蓷a mata halin da suke ciki ita da Abida, aikam ta kira Mama Safiya ta fa蓷a mata ta zo gidan, Mama Safiya ce tace wa Ummah ta 茩ira Abidan tazo 

Duk wani fa蓷a da nasiha da suka mata ta kunnen dama ya shiga ya fice ta hagu, suma bata kalli girman su da darajar su na zama 茩annen mahaifinta ba ta tsige su, aikam Mama Maimuna da yake ita tana da zafi ta zane ta kuma itama ta mata tass dan ba daga nan ba,

Ko a baya abinda yasa bata shiga sha'anin su Rukayya saboda yanda Papi ya musu shiyasa ta zare hannunta ta zuba wa sarautar Allah ido, dan tasan Allahn da ya jarabce su shine zai fitar da su, duk abinda ke faruwa dasu da nufin sa da 茩udurar sa, jarabawar su kenan kuma zasu tsallake da izinin sa, tasan ba abinda ze faru a duniyar nan seda NUFIN ALLAH shi ke jarabtar bawan sa

Lefe na gani na fa蓷a Alhaji Mamman yawa Abida gidan ta kuwa ba'a magana, itama da dukiyar gadon su taso da amata kayan 蓷aki na alfarma amma su Ammi suka ce za su ha蓷u ayi mata,ganin ta samu bulus yasa tace suyi amma idan baza su mata masu kyau ba su bar shi bata so

Jin haka har Amma zata fara bala'i amman Ammi ta taushe ta, ta danne zuciyar ta, anyi biki an watse lapiya aka kaita gidanta a nan malali kaduna

Sun fara zama zaman lafiya da jin da蓷i a satin farko, satin su biyu da aure kuwa yace mata zasu yi tafiya, zasu je taga 拼anuwan sa a Kano, suka je suka yi sati biyu a wani 茩untataccen gida me 蓷akuna uku da parlour sai kitchen, girman parlourn bai fi na wani 蓷aki guda 蓷aya ba, su kuwa 蓷akunan ba'a magana dan baifi shima 蓷aki 蓷aya aka raba gida uku ba, kitchen din kuwa ba wasu kayan kirki da za'a iya zubawa a cikin su ba, dan gas ma dai saidai idan 茩arami, kuma mutum 蓷aya ma a 茩untace zai yi aiki a ciki

Dan ganin dangi kuwa sun ga dangi har sun gaji, amma kusan wata 蓷aya kenan basu koma ba suna zaune a gidan, tama yi tunanin ita idan sun zo a wani babban hotel zasu sauka yanda zata ji da蓷in yiwa su Ammi fiffi茩a da 蓷agawa amma saidai me

Da tayi 茩o茩arin 蓷aga mai hankali su koma ne ya fito mata a mutum ya nuna mata ainihin kalar sa,  

Lefen da aka kawo mata daman yace karta 蓷inka ta bari yana da mai 蓷inki da zai mata 蓷inkin kece raini, ta amince har tana tunanin zata dawo ta cigaba da fantama wa irin yanda take yi da, shi yasa ta amince 

Ashe lefen hayan su yayi na wata 蓷aya, gidan ma na haya ne, shi yasa ya ce mata zasu zo ziyara, da yake a Kano yake kuma ba shida gida ma a Kanon a gidan 茩anin mahaifin sa yake da zama yasa ya siyar da kujerun ta ya siya wanan gidan da suke ciki a yanzu, kuma lefe da gida masu shi sun amsa abin su tun a washe garin ranar da suka ta ho Kano 

Tsabagen gigita saida ta sume mai a wajen, jin wannan tashin hankalin, lefen nata da kayan 蓷akin ta, wani irin ha蓷a蓷蓷en luxury bed ne da ita a wannan 蓷akin na ta da yayi mugun ha蓷uwa, yanzu duk wannan master bedroom 蓷in da take tunanin zata kwanta a ciki na har illa mashallah shine za'a ce wai ba nata bane 

Tayi Three zero kenan, ba kayan 蓷aki ba, lefe ba gida, sai wannan akurkin kajin, tuna wani gagarumin abu tayi tace

'' ku蓷i na ku蓷in gado na da na ba ka fa???'' 



Follow me on arewapen for more 馃ス 馃グ 馃檹 馃檹 馃檹 馃檹 馃檹 馃檹
______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 馃尯 
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol