Free chapter · Read without an account
60
💕 NUFIN ALLAH 💕
By
Anisa Muhammad Yahaya
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA
Page 6️⃣0️⃣
Kame kame ya fara dan kuɗaɗen dasu aka yi duk shagalin bikin su, ido ta ƙara zaro wa jin abinda yace, ita dake son kama wani babban sana'a da zata kece raini a wajen su Amma, so take ta fara order daga ƙasar waje tana siyar da manyan abubuwa amma zai ce mata haka
Kuka ta saka tana fashewa da wani ihu ta fara iƙrarin sai ya sake ta, shi kuwa yace ko zata yi mai baze sake ta ba suna nan zama na har abada, daman ƙarya yake bai taɓa aure ba so yake ta tausaya mai shiyasa, kuma ita da tayi abin kunya a gari shine take son ya sake ta
Yaji tayi ta gudu zuwa gidan Shaheeda dake fama itama da kanta, dan itama ba wani daɗin auren take ji ba kawai dan ta ajje yara a gidan ne bata san halin da zasu shiga ba idan ta rabu da su ta koma gidan su, tasan irin yanda yara ke shan wahala a hannun matar uba dan ita shaidar hakan ce kuma akwai sa hannunta shiyasa take fargaba kuma take son tayi haƙuri ta jure ta zauna
Koda labari ya isa kunnen Ummah, baƙin ciki yasa ta yanke jiki ta faɗi a toilet, wata kawar ta dake yawan shigar mata ce ta shigo ta ganta a bakin toilet a kwance suka kaita asibiti, da farko tana ɗan iya magana amma ba wai yana fita sosai ba, ga wannan rikicin har yanzu ba'a gama ba
Abida kam matsawa tayi a maida ta wajen mahaifiyar ta zata kula da ita amma a raba ta da shi, shi kuwa Alhaji Mamman yace bazai rabu da ita ba
Bayan ta dawo wurin Ummah kuwa taga ba zata iya ɗawai niya da ita ba wani lokacin haka zata ɓata wajen amman Abida na gani ba zata gyara ba sai ta ga dama dan ita kyankyamin taɓa mahaifiyar tata take yi,
Wani ziyara ne da Muneefa da su Ammi suka kawo dan duba ta suka zo suka same ta duk ba kyan gani har gidan ma, a nan Anty ta tada hankalinta kawai zata tafi da ita Kano, amma Momma Zuhura wadda gidanta suka fara tafiya suka zo gidan tare tace A'a itace babba ita zata tafi da ita
Saida Abba Munir ya ma Abida tass kafin ta koma gidan mijin nata da yake itama masifaffiya ce yasa suka zauna lafiya
Kafin bakin Umma kam ya gama rufe wa seda tayi ta rokon su Amma da su yafe mata musamman ma dai Ammi dan tasan ta azabtar da su kuma yanzu abinda ta shuka ne take girba, gashi har Papi ya mutu bata roƙi yafiyar sa ba, tasan ta cutar dashi da yawa shiyasa yanzu Allah ke hukunta ta akan san zuciyar da tayi
Tayi tunanin zata ci karen ta ba babbaka, kuma Allah ya barta ashe ta yaudari kanta, Allah ba azzalumin bawan sa bane, daman kome ze faru a duniya seda NUFIN ALLAH, lokacine Allah ya ƙiyasce mata da zata yi yanda take so ba tare da ta yi tunanin makomar ta ba, ta manta akwai Allah ta manta ko wani bawa a duniya Allah ne ya halicce sa kuma yana son dukkanin halittar sa
Bayan Anisa ta koma daki nazarin maganganun su da Leema take yi, kusan kwana uku kenan da suka yi maganar, gashi Ya Umar yanzu ya linka kulawar da yake bata har su Momma da su Nabila ma sun fara lura ya fara canja mata, wanda ba ƙaramin kunya da sa zuciyar ta a wasi wasi take ba,
Ganin hakan yasa ta ƙara wa Leema Magana, ita ko Leema ta ce
“Anisa, ni dai shawara nake ba ki. Kada ki bari ya ga kin fara sakin jikin ki da shi da wuri. Shi fa ya daɗe yana sonki, har ya je ya sanar da iyayen ku kafin ke da kanki ki amince, yanzu da ya ga saura wata ɗaya bikin, sai ya fara nuna miki kulawa, ki yi hankali, kada ki amince da shi da wuri har ya ɗauka ya same ki a arha ba tare da ya sha wahala ba.”
Anisa kam shiru tayi tana nazarin maganar ƙawarta ta
“To, me kike so in yi kenan Leema?”
“Ki riƙa mu'amala da shi cikin mutunci, amma kada ki nuna masa cewa kin fara jin wani abu a ranki wanda nasan zaki Musa mun haka kuma nasan dai kin fara son shi. Ki bar shi ya ƙara nuna miki ko da gaske ne abin da yake ji,ya tarairaye ki fiye da haka.”
gyada kai tayi kamar tana ganin ta, amma a cikin zuciyar ta ta san cewa ba zai yi mata sauƙi ba. Domin duk lokacin da yake nuna mata kulawa, sai ta ji wani irin daɗi da ba ta saba ji ba, zuciyar ta na wani irin motsawa, kuma ta rasa dalilin da yasa take jin hakan dan ita tasan ba wani son shi da Leema da su Jalila ke iƙrarin tana yi.
Washegari, Ya Umar ya kira ta da yamma. Dan jiya ya koma Kano Daddy ne ya ƙira shi yace ya dawo ai by now ya gama abinda yake yi ɗin
“Anisa!!, ya kika yini?”
“Lafiya lau.”
“Alhamdulillah. Kin ci abinci kuwa?”
“Eh.”
Ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya tambaye ta, “Anisa, akwai wani abu da nake yi ne da ba kya so? Ina jin kamar kina jin tsoro na har yanzu, ban san yanda zan cire miki wannan tsoron nawa da kike yi ba”
Ta yi saurin amsawa da, “A'a, babu komai Yah ni me zaka mun”
“Shikenan. Ni dai abin da nake so shi ne ki saba da ni. Ba na son ki riƙa kallona a matsayin dodo mutum a idon ki, musamman da yake saura kwanaki kaɗan ki zama mallaki na, bana son ki riƙa tsoro na ni ba dodo bane”
magana ta kasa yi na ɗan lokaci.
Sai ya ƙara da cewa, “Kina da muhimmanci a gare ni, Anisa. Kuma ina so ki ji cewa kina da wanda za ki iya dogara da shi.”
Ji tayi zuciyar ta ta yi wani irin motsawa, ta so ta tambaye shi me ya sa yake faɗin waɗannan kalmomi masu daɗi, amma sai ta tuna shawarar Leema.
A taƙaice tace “Nagode.”
Ya yi dariya a hankali. Dariyar ta tsaya saurara, a ƴan kwanakin nan yana yawan mata murmushi amman be cika dariya ba,wanda ada ko alfarmar ma sakin fuska ba samu suke ba amman yanzu wai Ya Faruq ita yake wa dariya ba iya murmushi ba
“Ke kam, sai an sha wahala kafin a ji muryar ki mai daɗi, kina wahalar da zuciyar bawan Allah amma ba komai ”
Ita ma murmushi tayi ba tare da ta sani ba.
Bayan sun kashe wayar, sai ta zauna tana tunanin maganarsa.
Yau a karo na farko, ta fara tambayar kanta ko za ta iya jin daɗin zama da shi bayan auren su.
Follow me on arewapen for more 🥹 🥰 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏
______________________
By
Anisa Muhammad Yahaya 🌺
***