Free chapter · Read without an account
63
💕 NUFIN ALLAH 💕
By
Anisa Muhammad Yahaya
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA)
Page 6️⃣3️⃣
Ahmad ne ya shigo ɗakin Faruq ya tarar da shi yana duba wasu kaya da ya kawo musu jiya da daddare
“Subhanallah! Ango, har yanzu kana nan kana duba kaya? Kai kuwa ka san cewa saura kwanaki kaɗan ne?”
Faruq ya ɗago kansa ya kalle sa.
“Me kuma kake so in yi? Wai kai wannan angon bazai fita daga bakin ka ba, ai kaima angon ne, ba iya ni ba”
“Ka fara koyon yadda ake murmushi a ranar aure mana. Kada a ce ango ya fito kamar an tilasta masa auren! Bayan kafi kowa zumuɗi da rawar ƙafa”
Faruq ya harare shi yace
“Ahmad, wallahi wata rana sai ka sa na manta cewa kai abokina ne, kai ka fara koya kafin ni in koya.”
zama yayi a gefensa yana dariya.
“To ai kasan ni ba sai na koya ba a kwai ni da fara'a, ni dai ina ƙoƙarin ganin ka yi farin ciki ne. Amma gaskiya akwai wata matsala da nake son ka warware mun ya zaka yi dashi kafin ranar aure.”
Faruq ya kalle shi da yanayin rashin fahimta a fuskar sa yace
“Wace matsala kuma?”
Ahmad ya gyara zama, ya ɗan yi shiru kamar zai faɗi wani babban sirri.
“Amaryar ka fa! Ya za ka yi idan har bayan aure ma tana ci gaba da amsa maka da ‘na gode’ da ‘to’ kawai?”
Faruq ya jefa masa wani ƙaramin pillow dake kusa da shi yace
“Ahmad! Kai ka fi kowa damuna a wannan rayuwar! Nayi tunanin wani abu ne babba wallah, tashi ka fita nagode”
Ahmad ya kauce yana dariya.
“Ni dai na faɗa maka tun wuri. Ka shirya zuciyar ka!”
Duk da zolayar, Ahmad ya lura cewa Faruq yana cikin damuwa fiye da yadda yake nunawa.
Dan shiru Ahmad ya yi sannan ya ce, “Faruq, da gaske nake faɗa maka. Kada ka bari tsoron cewa ba ta sonka ya hana ka jin daɗin abin da kake da shi yanzu. Ka yi ƙoƙarin zama mijin da za ta ji daɗin kasancewa tare da shi.”
Faruq ya sunkuyar da kansa.
“Abin da nake so kenan, Ahmad. Ba na son ta ji kamar an tilasta mata zama da ni. Ina so wata rana ta kalle ni da kanta, ta yi murmushi saboda tana farin cikin kasancewa tare da ni.”
Ahmad ya ɗan yi murmushi.
“In sha Allah, Allah zai sauƙaƙa.”
Sai ya tashi ya nufi ƙofa, amma kafin ya fita sai ya juyo yace.
“Amma dai idan ta fara sonka, kar ka manta da wanda ya riƙa sauraron kukan ka tun kafin ka zama ango!”
Faruq ya ɗauki wani pillown ya sake jefa masa.
“Ka fita daga ɗakin nan dan rainin wayo!”
fita yayi yana dariya.
---
Nabila tana ta magana kan kayan da take son a tanada, yayin da Anisa take sauraron ta cikin natsuwa.
“Anisa, ke kam me kike so a ranar bikin? Tun da muka fara tambayarki, sai ki ce duk abin da aka zaɓa ya yi.”
Anisa ta yi murmushi.
“Ni dai ina son komai ya tafi lafiya, hakan ma ya ishe ni, duk abinda kuka yi nasan nima ze mun”
Jalila ce dake kwance a kan gadon suna sauraren su ta ɗaga gira tace
“Wannan na sani duk me muka tsara za kiyi, amma ba wannan ba, ke ma ya kamata ki yi wa kanki wani abu''
Anisa ta yi dariya tace,
“To, me kike son in ce pickles?”
Nabila dake zaune kusa da ita a ƙasa ta matso kusa da ita tace,
“Ki faɗa min gaskiya. Kina jin daɗin tunanin cewa nan ba da daɗewa ba za ki zama matar Ya Faruq koh?”
Murmushin da ke fuskar Anisa ya ɗan tsaya.
Ta yi shiru, tana nazarin tambayar.
“Ban sani ba, Peebles.”
Duk kallon ta suka yi cikin kulawa Fareedah da bata saka musu baki ba sai yanzu tace.
“Ba sai kin san komai yanzu ba, amma ki ba kanki damar jin abin da kike ji, ba tare da kin tsorata da shi ba.”
Anisa ta sauke ajiyar zuciya, ta kalli ta, kwana biyu sai tayi ta mata magana ba tare da ta bayyana abinda take nufi ba kai tsaye amma indai tayi hakan se ya je har zuciyar ta, a hankali ta sunkuyar da kanta tace
“Wani lokaci idan na tuna da yadda yake kula da ni, sai in ji kamar ina son in ƙara kusantar sa. Amma da zarar na tuna cewa har yanzu ban taɓa gaya masa cewa ina son shi ba, sai in ji kunya.”
Jalila da Fareedah suka kalli juna cike da farin ciki, murmushin fahimta Nabila ta mata tace
“Ba lallai sai kin furta komai yanzu ba, Anisa. Wani lokaci zuciya tana fara magana kafin baki ya samu ƙarfin faɗin abin da ke cikinta.”
Anisa ta kalle ta, sannan ta yi murmushi a hankali.
Wayarta ce tayi ƙara. Saƙo ne daga Ya Faruq.
“Amor(love da spanish), ina fatan shirye-shiryen suna tafiya lafiya. Kada ki wahalar da kanki da yawa kin ji ruhi na. Ina fatan ranar da za ki shigo gidana, za ki ji kwanciyar hankali kamar kina gidan Ammi”
Ta karanta kusan sau nawa, wani irin daɗi ya mamaye zuciyarta, har
ji take kamar idanun sa na kallon ta, kamar yana gabanta, suna kallonta cikin kulawar da ta fara sabo da shi.
Reply ta masa da
“In sha Allah, Allah ya sa komai ya tafi lafiya.”
Dan jimmm tayi na ɗan lokaci sannan , sannan ta ƙara da
“Na gode da kulawar ka.”
Da ta aika saƙon, sai ta ji wani irin farin ciki da ba ta iya ɓoye shi ba, tayi saurin yin ƙasa da kanta saboda gulmar su Jalila dan tun ɗazu suke zuba mata ido
Nabila ce ta leƙa fuskarta tace,
“Me ya faru kuma?”
“Babu komai!”
Dariya suka yi dukkansu, Fareedah tace
“To, munji, amma dai idan ranar auren ku ta zo, zan sa ido sosai a kanku!”
Hannu tasa ta rufe fuska bata iya cewa komai ba, suka fashe da dariya.
Amma bayan dariyar ta lafa, Anisa ta sake kallon wayarta.
Ta fara fahimtar cewa ba wai kawai tana son Ya Faruq ya kula da ita ba ne. Tana son shi da kansa ya kasance cikin rayuwar ta.
Sai dai har yanzu ba ta shirya gaya wa kowa wannan gaskiyar ba.
Ranar aure tana ƙara matsowa kusa, kuma ba da daɗewa ba, za su shiga wani sabon babi na rayuwar su
babin da ba ta san irin abubuwan da ke jiranta a cikinsa ba.
Follow me on arewapen for more 🥹🥰🙏🙏🙏🙏🙏🙏
______________________
By
Anisa Muhammad Yahaya 🌺
***