Free chapter · Read without an account

64

by Anisa Muhammad Yahaya · NUFIN ALLAH



💕 NUFIN ALLAH 💕
       By 
Anisa Muhammad Yahaya

Young Talented Writers Association YOTA

Page 6️⃣4️⃣

Shirye-shiryen bikin nata ƙara nisa dan bai fi five days ba gaba ɗaya, kowa yana cikin farin ciki da hidimar bikin ba kama hannun yaro, barin ma su Jalila ƙawayen amare, itama Leema har ta zo jiya da yamma, ita kanta amarya Anisa har yanzu tana jin farin cikin hakan amman bata nunawa tana iya bakin kokarin ta kar a gane halin da take ciki, duk kokarin ta wani lokacin kunya take ji idan aka ambaci ranar da za ta zama matar Faruq a hukumance.
Ita kam Nabila ba'a ma magana, Allah ne kaɗai ya san irin tsantsar farin cikin da take yi 

Suna zaune duk tare da Momma suna zaɓar kaya a wayar Momman wayar ta ta yi ƙara. Ganin sunan Ya Faruq a fuskar wayar ya sa ta ɗan yi murmushi kafin ta ɗaga wayar ta kalla su Momma. Kasa ɗaukar wayar tayi ta kalla Momma da tayi saurin kauda kanta tana ɗan murmushi, kunya ce ta rufe ta tayi saurin tashi tayi ɗaki, tana jin su Fareedah na mata tsiya 

“Assalamu alaikum,” ta faɗa cikin sanyin murya.

“Wa alaikum mussalam, amarya ta ruhin Faruq, mon Cherie, ya shirye-shiryen mu suke tafiya?”

Dan sunkuyar da kanta tayi, duk da cewa ba ya ganinta. “Alhamdulillah, komai yana tafiya lafiya.”

“Alhamdulillah. Ina fatan ba ki gaji da hidimar ba?”

“Ɗan kaɗan,” ta amsa, tana ƙoƙarin ɓoye murmushin ta.

“Da ace ina kusa da ke, da na taimaka miki.”

“Ka taimaka min ta yaya kuma?” ta tambaya cikin wasa.

Ya yi dariya a hankali. “Ko da ba zan iya ɗaukar dukkan nauyin shirye-shiryen ba, aƙalla zan riƙa sa ki murmushi.”

Shiru tayi na ɗan lokaci. Maganarsa ta taɓa wani wuri a zuciyar ta da ba ta san yadda za ta bayyana ba.

“cherie?”

“Na'am?”

“Kin yi shiru. Ko na faɗi abin da bai dace ba?”

“A'a,” ta amsa da sauri. “Ina sauraron ka ne kawai.”

Ya yi murmushi a ɗayan ɓangaren wayar. “To, ki ci gaba da sauraro na. Ina da sauran abubuwa da yawa da nake son ki sani game da ni.”

Ya kara cewa ''zan iya tambayar ki wani abu Amor''

A hankali muryar ta ta fito tace '' ina ji Yah Allah yasa na sani'' tun bata iya amsawa da sunayen da yake kiran ta har ta saba 

“Love, idan da za ki sami damar zaɓar mijin ki a yau, bayan duk abin da kika sani game da ni… har yanzu za ki zaɓe ni?”

Shiru tayi tana juya maganar a zuciyar ta, a yanzu ko sau miliyan za'a bata zaɓi shi zata ƙara zaɓa, a da ne dai ko ana ha maza ha mata baza ta dosa inda yake ba, amma ba yanzu ba, sunkuyar da kanta tayi kamar tana ganin sa, sannan ta amsa da

“Ai an riga an zaɓa min, Ya Faruq.”

Ya Faruq ya yi murmushi kaɗan, amma murmushin ya ɓace lokacin da ya sake tambayar ta

“Dan kina son hakan ko dai kawai kina yin biyayya ne ga Ammi?” 


-------


Ahmad yana zaune tare da Faruq suna tattauna wasu shirye-shirye na bikin ya kalli Faruq

“Amma kai, Man, ka tuna cewa hutun watanni huɗu da aka ba ka ba zai dawwama ba dai koh,” ya faɗa, yana kallon sa.

Faruq ya gyara zamansa. “Na sani. A halin yanzu ina aiki a portharcourt kuma idan na koma bakin aiki, akwai yiwu war a mayar da ni Abuja kamar yadda aka tsara, tunda kaga yanda a ka tsara transfer ɗina daga Lagos zan tafi portharcourt inyi 2 years Kuma kaga na cinye years ɗin an bada hutu so posting letter na na Abuja zan zauna jiran ya fito.”

“To, ka riga ka shirya yadda rayuwar auren za ta kasance?”

Faruq ya ɗan yi shiru kafin ya amsa, “Abin da nake so shi ne Anisa ta saba da ni kafin in koma bakin aiki, ina da gida a maitama sai ta fara saba wa dani ne zan maida ita can but for now a nan Kano za ta zauna, bana son ta ji kamar an bar ta ita kaɗai, musamman yanzu da muke ƙoƙarin gina sabuwar rayuwa”

Ahmad ya kalle shi da murmushi. “Kai dai ka tabbatar ka ba ta kulawar da ta dace, amma ka sani, ba kowace mace ce take iya bayyana abin da ke zuciyar ta da sauri ba, a hankali a hankali.”

Faruq ya sauke ajiyar zuciya.

“Shi ne abin da nake tsoro, Ahmad. Har yanzu ban san ko Anisa ta fara sona ne, ko kuma tana ƙoƙarin yin abin da iyayen mu suke so ba.”

“Ka ba ta lokaci. Wani lokaci zuciya tana buƙatar lokaci kafin ta yarda da abin da take ji.”

Faruq ya gyada kai, amma a cikin zuciyarsa akwai tambayar da har yanzu ba ta da amsa.

Shin Anisa za ta taɓa son shi kamar yadda yake sonta ko kuwa?

---

Da dare, Anisa tana kwance tana tunanin hirar da ta yi da Faruq. Ta tuna yadda yake yawan tambayar lafiyar ta, yadda yake ƙoƙarin ganin ta yi farin ciki, da yadda yake guje wa duk wani abu da zai ƙara mata tsoro.

Ta juya a kan gadon ta rungume pillown hannun ta

“Me ya sa nake jin daɗin kulawarsa haka?” ta tambayi kanta a hankali.

Ta tuna shawarar Leema cewa kada ta bayyana komai da wuri. Amma yanzu ta fara fahimtar cewa abin da take ji ba wai kawai godiya ga kulawar Faruq ba ne.

A hankali, murmushi ya bayyana a fuskarta.

“Allah ka sa wannan auren ya zama alheri a gare mu,” ta furta cikin ƙaramin murya kamar whispers.

Ba ta san cewa nan gaba kaɗan, za ta fahimci zurfin abin da zuciyar ta ta fara ji ba.

-----

Mamee da Mama

Zaune suke gaban wani tsamurmurin malami yasa wani uban gammo a kansa, ga wani uban carbi irin me dubu ɗinnan a hannun sa, fuskar sa ɗauke da wani munafukin gemu kamar na matashin bunsuru 

Kallon su yayi yace '' ya sunan yaran kuka ce''

Da sauri Mamee tace
'' Anisa da Nabila, su kuma mazajen Umar da Ahmad '' ta faɗa cike da yaƙi ni



Hhhh masu karatu gwarama, toh!! Shin abinda su Mamee ke shirin aikatawa ze cimma haƙa ko yaya,ma ji ma gani wai an birne tsohuwa da ranta


Follow me on arewapen for more 🥹 🥰 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏


______________________
By
Anisa Muhammad Yahaya 🌺 
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol