Free chapter · Read without an account
65
💕 NUFIN ALLAH 💕
By
Anisa Muhammad Yahaya
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA
Page 6️⃣5️⃣
Anisa tana zaune tare da Leema wadda take ta mata hira, amma duk hankalin ta yana kan wayar ta.
Leema ta lura da hakan, sai ta yi murmushi.
“Amaryar mu, ko dai kina jiran wani ne?”
Anisa ta ɗago kai da sauri tace “Wani kuma?”
“Ke kika sani, amma tun da kika fara yawan kallon waya, na fara zargin akwai wanda yake satar miki hankali.”
“Leema!!!!!! ” ta ja sunan tana ɗan dariya.
Matso wa tayi kusa da ita ce,
“To, ki gaya min gaskiya, Kina jin daɗin kulawar Ya Faruq ko kuwa har yanzu kina tsoron sa baki san halin da zuciyar ki take ciki ba kamar yadda kike ce min?”
Shiru tayi na ɗan lokaci sannan ta kalle ta
“Ban san yadda zan bayyana miki ba,” ta amsa a hankali. “Amma yanzu idan ya kira ni, ina jin daɗi. Idan kuma bai kira ba, wani lokaci na kan duba waya ina tunanin ko lafiya.”
Nabila da ta shigo ɗakin ta buɗe baki cikin mamaki, sannan ta fashe da dariya.
“Anisa! Ke fa kin fara shiga ruwa!”
“Ba haka ba ne!” Anisa ta yi saurin kare kanta, ta juya tana kallon Nabila da ta shigo, duk da murmushin da ya ƙi barin fuskarta.
“To, ba zan ce komai ba, amma ki ba zuciyar ki damar fahimtar abin da take ji, ba sai kin tilasta wa kanki komai ba.”
Maganar Nabila ta sa Anisa yin shiru. A karon farko, ta fara tunanin cewa watakila zuciyar ta tana karɓar Faruq a hankali fiye da yadda take tsammani.
Leema ce tace '' ki bashi chance yanzu Neesat ai mun wahalar da shi haka''
'' ohh kece kika sa ta wahal mun da brother no wonder duk yabi ya rame kamar ba Ya Faruq ɗinnan ba'' Jalila ta faɗa suna kashe hannu ita da Fareedah da suka shigo ɗakin suka tarar da zancen
---
wayar ta ta ce tayi ƙara,aikan da sauri ta dauka ganin Ya Faruq ne,daman tayi tunanin shine, sai ta kalle su sannan ta ɗanyi murmushi ta ɗauka wayar tana sunne kai
“Assalamu alaikum, Ruhh.”
“Waalaikum mussalam.”
“Na kira ne domin in ji ko kina lafiya. Na san kina cikin hidimar aure, kuma bana son ki gaji sosai.”
“Ina lafiya. Kai fa?”
“Alhamdulillah. Ina ƙidayar kwanakin nan ne kawai.”
Murmushi tayi a hankali tace. “Kwanaki fa ba za su ƙare da sauri saboda ka ƙidaya su ba.”
Faruq ya yi dariya. “Na sani, amma kin san dalilin da ya sa nake ƙidayar su?”
Shiru tayi bata ce komai ba sai kallon su Jalila da suka zuba mata na mujiya, kunya ne ya ƙara rufe ta ta sunkuyar da kanta
“Saboda ina jiran ranar da zan kira ki mata ta ba tare da na damu da ko na dame ki ba, ranar da Anisa zata zama ruhin Umar Faruq”
Zuciyar tace ta wani irin bugawa da sauri. Ta kasa samun amsar da za ta bayar, sai sunkuyar da kanta da ta ƙara yi kamar yana gaban ta,ji take yi kamar su Reedah na jin zancen da suke yi yanda suka ki ɗauke idon su a kanta
Faruq ya lura da shirun nata, sai ya ƙara da cewa, “Ki yi haƙuri idan na sa ki jin kunya, ba na son ki ji wani nauyi saboda ni.”
“A'a,” ta faɗa cikin sanyin murya. “Ba ka dame ni ba.”
Ya yi shiru na ɗan lokaci, kamar yana ƙoƙarin fahimtar abin da ke bayan kalamar ta.
“Na ji daɗin jin haka,” ya amsa. “Allah ya sa ranar ta zo mana da alheri.”
“Amin,” Anisa ta faɗa a hankali.
Bayan sun kashe wayar, ta daɗe tana kallon fuskar wayar ta. Kalmar mata ta, ruhin Umar Faruq ta ci gaba da maimaituwa a zuciyar ta.
A da, tunanin zama matar Faruq kawai na hautsina ta, yana sa ta jin tsoro, amma yanzu, a cikin wannan tsoron, akwai wani irin farin ciki da ta kasa misaltawa.
---
Gidan Amma
Yana zaune yana tunanin ta bayan ya kashe wayar da murmushi akan fuskar sa na yanda yanzu take sakewa dashi sosai Ahmad ya shigo, da alamu duk ya gaji yace
“Yanzu dai ka shirya, an kusa ɗaura maka aure,” Ahmad ya faɗa cikin zolaya.
Faruq ya ɗago kai. “Ka san dai tun da daɗewa nake jiran wannan ranar, kai banda kai za'a ɗaura auren ne halan”
“Na sani, amma ina fatan ka shirya da abin da zai biyo baya, ai mu nida sweet mutane ne basu shaida ba tukuna amman an daɗe da ɗaura wa.”
Faruq ya gyada kai. “Allah dai ya kyauta maka wallahi Ahmad, Allah sarki Mie Amor” ya faɗi tuna har yanzu bata amsa soyayyar sa ba
“Allah ya sa ku fahimci juna.”
“Amin,” Faruq ya amsa.
A zuciyar sa, yana da buri guda ɗaya a yanzu, ya ga Anisa ta yi farin ciki da auren su, ba don ta bi umarnin iyayen su ba, sai don ta zaɓe shi da kanta, duk da yasan ba shine zaɓin ta ba.
Amma abin da bai sani ba shi ne, a hankali Anisa ta fara kusantar wannan zaɓin.
Kuma saura kwanaki kaɗan, za a ɗaura auren da zai sauya rayuwarsu gaba ɗaya.
-------
''To yanzu me kuke so ayi'' malamin ya faɗa yana taunar goro ga hakwaran nan nasa dafaffu a wajen, baki sai tsami yake yi, jikin sa duk hamami
Duk da yanda gurin da jikin malamin ke tashi amman saboda yanda suka sa buri kuɗi ya makarantar musu da idanu da zuciya da kuma son kai da abin duniya
Mama ce tayi saurin yin magana dan tasan halin Mamee ba imani ta cika ba ita ba wani abu da yawa take bukata ba
'' mu ba wani abu muke son a wa yaran ba, kawai so muke yi a haɗa da namu yaran ranar auren a ɗaura tare suma su more wannan damar''
'' haba Adda ya zaki ce haka, so muke a lalata auren a fasa yi da nasu yaran su ji yanda muka ji ayi da namu yaran, yaran su kuwa saidai hange daga nesa ''
Follow me on arewapen for more updates 🥹 🥰🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏
______________________
By
Anisa Muhammad Yahaya 🌺
***