Free chapter · Read without an account
67
💕 NUFIN ALLAH 💕
By
Anisa Muhammad yahaya
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA
Page 6️⃣7️⃣
Shire shire su Mamee suka fara kain da nain ba kama hannun yaro, dan tun suka ba malam makudan kudaden da saida Mama ta siyar da wani ajjiyayyen gold din ta sannan suka cika, ya tabbatar musu su kwantar da hankulansu anyi an gama se dai kawai su jira ran ɗaurin aure
Har invitation cards sun buga suna ta rabawa ƴanuwa da abokan arziki, koda invitation yazo wajen zu Mommy rigama suka so su tayar ita da Amma amman Ammi ta ringa tausar su ita da Anty, har Momma ma da suka ƙira suka faɗa mata,
Taso ta kira su Abidan taji wani shirme ne haka suke aikatawa amman Ammi tace abarsu aga gudun ruwan su tukuna, tunda dai waliyai sun san waɗanda zasu bada auren su ai shikenan,
Ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta
-----------
Sunyi events har sun gaji, kuma duk sun tafi akan tsari, duk abubuwan da suka yi iya mata ne Quran day ne kawai harda maza, sunyi ladies party, Fulani day, Arabian night kowa yaci abaya aikan suka koma kamar larabawa barin ma Nabila da yake fara ce, duk sun yi kyau sosai har ka rasa waye yafi wani kyau, sunyi girls night iya su da ƙawayen su aka kwana aka yini ana tun da, sai suka yi cocktail, su kenan events ɗin da suka yi kuma ya haɗu ya ƙawatar, har suma angwayen sun halarci Quran day ɗin inda ko wanne a cikin amare da angwayen suka karanta abinda ya sauwaka daga Alqur'ani mai girma, sannan aka ƙira wata babbar malama da malami suka musu nasiha wanda ba iya su da suke maauratan ba har kafatanin jama'ar wajen saida ya ratsa zukatan su
---------------
AKACE RANAR WANKA SAIDAI UWAR DIYA TAJI KUNYA, ALLAH YA KAWO MU,
RANAR DA TA ZAMA SANADIN SAUYA KOMAI…
Tun da sassafe gidan Ammi ya cika da hayaniya da murna. Mata na ta zirga-zirga, wasu suna gyaran kayan amarya, wasu kuma suna shirya abin da za a kai wajen ɗaurin aure dan a Kano za'a yi ɗaurin auren
Angwaye kam ba'a magana baki kam kamar zai yage tsabar yanda baya rufu wa tun ba'a tafi masallaci ba sai haɗa hada suke suna shiri
--------
A bangaren su Momma
Anisa tana zaune a ɗaki, sanye da kaya masu kyau, yayin da Nabila ke can kan gado suna soyewa da sweet din ta ta ma ƙi tsayawa a gama kwalliyar, ita kuma Jalila na gyara mata kwalliyar ta ɗan tunda yau ɗaurin aure ba sai anyi wani heavy makeup ba daman ba so take ba ko na ranar Ladies party da cocktail da kyar ta bari aka mata, tana cewa wai ita ji take kamar ana ɗaura mata duniya a fuskar gwara su barta dai da iya gazar da lipgloss ko powder Kar a shafa mata
Seda suka yi da gaske sannan ta amince amman tace iya events biyun nan baza ta sake yi a kowanne ba
“Anisa, yau fa za ki zama matar Ya Faruq!” Leema dake ta mata video ta faɗa tana murmushi.
Anisa ta sauke idanuwan ta ƙasa. “Don Allah, ki daina faɗa min haka. Kina sa ni jin kunya.”
Dariya Nabila dake jin hirar tasu tayi, ta kammala wayar ta da Ya Ahmad tace. “Ai wannan gaskiya ce, kin kusa zama mallakin Ya Faruq, na kusa zama mallakin Ahmadun sweet din shi.”
Fareedah ce tace
'' Allah dai ya kyauta miki Nabila gaba ɗaya kin fitsare wannan idan kika shiga daga ciki kuma bamu san yanda zaki koma ba'' kallon Anisa Fareedah tayi ta ɗan yi shiru, sannan ta tambaye ta cikin tausa sa wa, “Kina jin tsoro ne?”
Shiru ta ɗan yi kafin ta amsa.
“Ɗan kaɗan, amma ba kamar da ba. Yanzu idan na tuna da shi, ba tsoro kaɗai nake ji ba… akwai wani abu dabam.”
Jalila ce tayi murmushi da sauri tace “Wani abu dabam kamar me?” ta tsaya da gyara mata kwalliyar tana kallon ta
Ture hannun ta da ta riƙe fuskar ta da shi tayi a hankali tace. “Ke dai ki bar ni! Ki cigaba da abinda kike yi”
Dukansu suka yi dariya, amma a zuciyar Anisa akwai wani irin abu dake mata yawo da ta rasa tsakanin farin ciki ko fargaba da ta kasa bayyanawa
Ta tuna yadda Faruq yake kula da ita, yadda yake tambayar lafiyarta, da yadda yake ƙoƙarin ganin ta samu kwanciyar hankali. Ba ta san lokacin da waɗannan ƙananan abubuwa suka fara zama masu muhimmanci a gare ta ba.
Amma yau, za ta zama matarsa.
---
A wajen ɗaurin aure, Faruq yana zaune tare da Ahmad. Duk da murmushin da yake yi, Ahmad ya lura cewa yana ɗan cikin damuwa.
“Lafiya kuwa, ango? Tun da muka zo kake ta shiru, kamar dai akwai abu a ranka.”
Gyara zaman sa yayi ya na kallon Ahmad din. “Ina tunanin Anisa ne.”
“Me kuma? Ka kusa samun abin da ka daɗe kana so.”
Faruq ya yi murmushi kaɗan. “Shi ne. Ina son ta samu farin ciki a wannan aure. Bana son ta taɓa jin cewa an tilasta mata zama da ni.”
Ahmad ya dafa kafadar sa. “Ka ci gaba da nuna mata gaskiyar zuciyar ka. Sauran kuma ka bar wa lokaci, maganar tilasta wa tun a baya ya kamata kayi shi ba yau ɗaurin aure ba so keep that aside”
Gyada kai yayi yana jin kwarin guiwa, yana jin addu'ar abokinsa tana ba shi kwanciyar hankali.
Abba ne ya ma Umar Faruq wakilci shi kuma Abba Muneef yama Ahmad wakilci, su kuma matan dukan su Daddy ne ya musu wakilci
Sanarwar ɗaurin auren ne ya doƙi kunnen su Mamee da tun suka zo gidan suke wa kowa kallon ɗaɗɗaya dan a cewar su gwara su bar nasu hidimar su zo su ga fuskar su Ammi a yayin da ake sanar da ɗaurin auren harda nasu yaran.
A zabure Amra dake gefen Mama ta tashi tace '' Mama kina ji ko kunne na ne ni kaɗai har aka gama ana maimaita wa ban ji sunan mu ba, karo na uku da ake maimaita wa kenan''
Suma su Mamee da sauri suka mike suna jiran su ji an ƙara maimaita wa amma ina sai kunnen su da yake ji ye musu
'' A YAU JUMA'A KOWA YA SHAIDA MUMA MUN SHAIDA, AN DAURA AUREN (UMAR FARUQ ADAM BAFFAYO
DA
ANISA ALIYU MUHAMMAD) DA KUMA
(AHMAD YUSUF ABDULLAHI BAFFAYO
DA
NABILA HAFEEZ MAITAMA)
AKAN SADAKI DUBU DARI UKU LAKADAN BA AJALAN BA
Da jin labarin, gidan ya cika da murna da addu'o'i da guɗa. Ammi ta share hawayen farin ciki, tana gode wa Allah da ya kai 'yarta wannan rana. Amma ta rungume a tare suka fashe da kuka Anty da Mommy na rarrashin su, Ammi ke ta tunanin ashe hakuri na cimma nasara da bata yi juriya da hakuri ba abaya sun amshi kaddarar da ta zo musu hannu biyu ba da ba wannan zancen ake yi ba yanzu
ALHAMDULILLAH ALA KULLI HALIN ta faɗa a sarari, wani abu da ya daɗe da tokare mata maƙoshi ya wuce a duk sanda ta tuna rayuwar ta ta baya, amma a yanzu tana jin babu sauran sa kuma
----------
Faruq
Tun bayan gama daura auren yake jin zumuɗin ya fara kiran ta ya kasance shine na farko da zai sanar da ita wannan albishir, amma ya kasa motsa koda yatsa, ji yake kamar mafarki yake, yarinyar da ya daɗe yana jiran girman ta har akai ga wannan lokacin yau gashi lokacin yayi har an ɗaura ma ƙarewa, baisan sanda wani kwalla ya zubo mai ba ya kai goshin sa ƙasa a wajen yayi kusan minti biyar kafin ya iya ɗagowa su Ahmad dasu Usman kuwa sai dariya suke mai harda su Abba dan ba wanda zai ce ya taɓa ganin hawayen sa sai a yau, duk yanda yake haɗe rai kam yau ba wannan haɗe ran ba ma alamar wai ya taɓa haɗa hanya da ita ma
Dan duk wanda yasan Umar kuma ya gashi a yau sai ya rantse ba shi bane, tun ya tafi ƙasa Ahmad ya fara mai video har ya ɗago fuskar sa shaɓa shaɓa da hawaye, bakin sa kam kamar zai yage dan murna Finally Finally Anisa ta zama mallakar faruq ruhi ya samu salama ga sweet din Ahmadu ma a gefe, ƴanzu an samu peace of mind
----------
Anisa
Da aka tabbatar mata da ɗaurin auren, ta yi shiru na ɗan lokaci, ta ji wani sabon nauyi a zuciyar ta, amma tare da shi akwai farin cikin da ba ta taɓa tsammanin za ta ji ba.
“Alhamdulillah,” ta furta a hankali.
A yau, ba ta zama amarya kawai ba. Ta fara wata sabuwar rayuwa tare da mutumin da zuciyar ta ke fara fahimta a hankali.
Ita kam Nabila ba'a magana ƙasa tayi dan murna tayi sujudur shukur, tana ɗagowa sai kuka, duk yinin ranar jikin ta a sanyaye, ko ince dukan su, ko ƴar iskancin da ta saba musu akan auren kasa wa tayi ko zolayar ta akayi kuwa
Ita kam Anisa tun ta kwanta ta rufe ido, ta rasa me ke mata daɗi a zuciyar ta, farin ciki ne ya fi yawa ko kuwa fargaba, ta rasa yanda zata yi, ita gaba ɗaya ma muryar sa kawai take fata da burin ji a yanzu
-----------
Da yamma, wayar ta ta yi ƙara. Faruq ne yake kira.
Ta ɗaga wayar cikin kunya da sanyin jiki,
“Assalamu alaikum, ranka ya daɗe,” ta faɗa, tana zolayar sa.
Dariya yayi mai sauti sosai dan farin cikin sa kasa ɓoyuwa yayi, ko ɗazu bayan sun fito daga masallaci gaba ɗaya kuɗaɗen aljihun sa saida yayi sadaka dasu, da ba su ishe shi ba ma sai da ya ciro wasu yayi sadakan har liman ya ba.
“Wa alaikumus salam, matata ruhin Umar Faruqu, wannan girma mawar duk dan kina farin cikin zama mallaki abar kauna ruhin Faruq ne?”
“Ni dai na ga ya dace ne.”
“Allah ya sa wannan girmama war ta kasance tare da ƙauna,” ya faɗa cikin sanyin murya. “Anisa, na san komai yana faruwa da sauri, kuma bana tsammanin za ki fara jin komai kamar yadda nake ji nan take, amma ina so ki sani cewa zan ba ki lokaci. Ina so ki ji daɗin zama da ni.”
Runtse idanuwan ta yayi . Maganar sa na taɓa zuciyar ta.
“Na gode, Ya Faruq.”
“Ba sai kin gode ba. Abin da nake so shi ne ki kasance cikin kwanciyar hankali. Kuma ki sani, duk abin da ya faru, zan yi ƙoƙarin zama mijin da kika cancanta, ban taɓa ma komai kuka ba da wayo na sai ke, yau saboda ke naje har kasa na godewa Allah da ya bani ke a rayuwarta, yau nayi hawayen farin ciki saboda ke abar kaunar Faruq, a kullum zuciyar Umaru zata kasance mai mura di da ƙaunar ki, ina son ki fiye da yadda zan iya faɗa miki matata abar alfahari na”
Ji tayi kwakwalwar ta da zuciyar ta kamar sun fita su bar gangan jikinta, wani irin abu ne taji tun daga jijiyar kanta har kafar ta, ji tayi kamar itama ta furta tana son shi amman ta kasa, bata tunanin zata iya
“Allah ya taimake mu,” ta amsa a takaice dan ta ma rasa abin faɗa gaba ɗaya jin zance da Leema tama ta ya tabbata, yau Ya Faruq da kanshi ke ce mata ya zubar da hawaye akan ta.
“Amin, matata ruhin Faruq.”
Bayan sun gama wayar, ta riƙe wayar ƙam a ƙirjin ta, tana murmushi ita kaɗai.
Wata zuciya ce ta fara buɗe ƙofa a hankali.
Ba ta shirya furta soyayya ba tukuna, amma a yau ta fara jin cewa wata kila rayuwa da Ya Faruq ba za ta zama abin tsoro ba kamar yadda ta taɓa zato.
Amma shin za ta iya fahimtar girman gurbin da Faruq zai samu a zuciyar ta
Lokaci ne kaɗai zai ba da amsa.
Follow me on arewapen for more updates 🥹🥰🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏
______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺
***