Free chapter · Read without an account

71

by Anisa Muhammad Yahaya · NUFIN ALLAH



💕 NUFIN ALLAH 💕 
      By
Anisa Muhammad Yahaya 

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA

Wannan page ɗin sadaukar wane ga KHADIJA HASSAN BELLO (deejamerh tah) autar Mama, my lovely sister, you helped and encouraged me tun daga farko har zuwa yanzu thank you so much love 😘 (saranghea🥰❤️‍🩹)



Page 7️⃣1️⃣

Da ƙyar suma aka raba su, ɗauka mutanen da ke parlourn saida zukatan su ya karye, kafin su fita Anisa tayi saurin cewa 

'' ina zuwa Amma abu zan ɗauko in dawo'' da sauri tayi hanyar ɗakin ta, wani order ne nata tun suna Kaduna ya iso, tun da taga da gaske zasu rabu lokacin ta yi musu ordern saboda su ringa tuna wa da juna a duk inda suka kasance 

Daukowa tayi ta dawo ta buɗe ta ba kowaccen su biyu, buɗewa suka yi, sarƙa ne iri ɗaya da zobe, duk sawa suka yi suna kara rungume ta suka sake fashewa da sabon kuka, amma na yanzu beyi tsayi ba aka janye su Anisa na riƙe da hannun Jalila, ita ma Nabila ta riƙe na Fareedah suka fito 

Daddy ne ya kai Anisa, ita kuma Nabila Baba ne ya kai ta,

Kuntau aka kai su duk su biyun, ko ince gida ɗaya, tare Umar da Ahmad suka yi ginan gidan, da so sukayi suyi shi suna makwabtaka da juna, daga baya suka katange shi ya zama ƙofa ɗaya kowa da part ɗin shi, same and exact building suka yi ba wani bambanci 

A maza daga Ya Usman, Ya Jamal,Hamza, abokin Ya Umar wato Haydar da kuma abokin Ya Ahmad Muazzam, su suka musu rakiya 

------

Ahmad 

Bayan su Baba sun tafi Ya Jamal da Hamza da abokin sa muazzam (daya tuƙa su da zasu je sword crossing) suka mai rakiya 

Suna zaune a parlour yaya Saudat da Fareedah zaune a kusa da ita, suma zama suka yi, adduo'i da nasiha muazzam ya musu sannan shima Jamal ya amsa, suka saka musu albarka sannan su yaya Saudat suka maida ta ɗaki suka fito a daidai yan part ɗin su Ya Umar sun fito wai Ango ya koro su 

-----

Bayan ya dawo daga raka su da zumuɗin sa ya shiga ɗakin, tana zaune bakin gadon ta na ta uban kuka, a hankali yaye mayafin idonta jage jage da hawaye ya ɗago fuskar tata suna kallon juna yace

'' kukan me kike yi, ko ba kya son zama mallakin Ahmadun naki ne yanzu sweet?''

A hankali ta girgiza mai kai wani hawayen na bin fuskar ta ya ƙara cewa
'' to daina kukan kinji sweet ɗina, ko ba sweet ɗina bace''

Ɗan murmushi tayi ta sunkuyar da kanta ƙasa yace
'' tashi muje muyi alwala mu zo muyi sallah ''

Tashi tayi jiki ba kwari suka yi alwala suka yi sallah, bayan sun idar ya riƙe kanta ya mata addu'a kamar yanda musulunci ya tanadar, sannan ya janyo musu ledar kazar da ya shigo da ita

A daren ranar dai Ahmad ya tabbatar wa da Nabila ta zama halal ɗin sa mallakin sa sweet ɗin Ahmadu, sun raya daren cike da so da ƙauna mai tafiya da zuciyar masu karatu 

----

Umar Faruq

Duk da yanda ya so ace shi kaɗai zai zo wajen matar sa amma saida Haydar da Usman suka tuso shi a gaba har Usman na cewa 

'' ai ko fashewa zaka yi yau sai mun raka ka in yaso in mun zo shiga ka datso kofar karshen zumuɗi ''

'' koma ya rufe muna ciki, tun da mu zai ringa nuna wa rashin ta ido dan rainin wayo'' Haydar ya faɗi yana ɗan bugar bayan Ya Umar 

Aikam ransa a mugun haɗe suka shigo, tun suka shigo ya kafe ta da idanu har suka zauna, duk surutan da adduo'i n da su Ya Usman ke yi ba jin su yake ba, ya kafe ta da idanuwa, Allah Allah yake yi kawai yaga face ɗin ta dake ƙasan veil ɗin, ji yake yi kamar bai taɓa ganin kyakkyawar fuskar ta ba yau ne farkon da zai buɗe ya gan ta

Cike da neman magana Ya Umar yace da Jalila dake kusa da ita '' a buɗe mana face ɗin amarya mu gane'' 

Ai kafin ma ya mayar da yawu Ya Umar ya tashi a zabure kamar wadda Jalilar tayi ƙoƙarin buɗe wa ɗin yace
'' ai kuma wannan ba ku isa ba, tunda dai kun ce sai kun shigo gashi nan kun shigo to yanzu ku tashi ku tafi mun gode'' 

Dariya ya basu duka, hatta ita kanta Anisan dake kuka sai da ta saki wani murmushin da bata san sanda ya kuɓ ce mata ba, Leema da Jalila kuwa da kyar suka iya ƙunshe tasu ganin zai zabure musu a wajen sai muzurai yake yi

Ganin basu da niyyar tafiya, ba kunya ya tako har inda take ya ɗauka kayar sa yayi ɗaki da ita ya juyo ya kalle su yace 
'' idan kun gama ku rufe kofar idan kun fita sai da safen ku''

Dukkan su da kallon mamaki suka bi shi, yana ƙulewa kuwa Leema da Jalila suka kashe hannu suna dariya 

'' to ai se mu tafi tunda an mana kora da hali''. Faɗin Ya Usman yana kallon Jalila, kai ta sunkuyar tana ɗan murmushi suka fita 


------

Tun ya ɗaga ta sama ta ji numfashin ta ya tsaya cak, kasa jan numfashi tayi har sai da ya dire ta akan gadon, duk da ba ganin ta yake ba amma taji wani irin kunya ta mamaye ta da sauri ta kai hannu ta danne veil ɗin ta da yake ƙoƙarin cire wa 

'' baza a barni naga wannan beautiful face ɗin ba'' kai ta girgiza tana ƙara danne veil ɗin 
'' to shikenan, tunda haka ne, zan kwana ina kallon fuskar taki ta ƙasan mayafin tunda baza ki buɗe in ganki ba'' 

Baki ta cuno gaba kamar yana ganinta tace
'' ni ya ban yi isha ba'' 
'' To muje in raka ki''
'' nidai a'a ina ne hanyar toilet ɗin''
'' oh baza ki yaye veil ɗin ba kenan'' 

Kafin ta an kara yayi saurin jan mayafin gaba ɗaya yana tsare ta da idanu, baki ta tura gaba ta juyar da kanta tsugunna wa yayi yana facing ɗin ita, ganin yanda ta wani juyar da kai tana cuno baki ya kalle ta ya kalli lips ɗin nata yana wani murmushi 

Hannu ya saka ya juyo da fuskar ta a hankali, ido suka haɗa ta ƙara cuno baƙi, magana tayi niyyar yi amman kafin ma ta iya cewa komai ya haɗe bakin su waje ɗaya 

Ido ta zaro a mugun firgice ta wani irin ja numfashin ta, gudun zuciyar ta kam ba'a magana, idon ta ya ke kallo cike da tsantsar so da shauƙi yana kissing ɗin ta kamar ya samu lollipop 

Ita kuwa cike da tsantsar tsoron da firgice take kallon sa, ya daɗe yana tsotsar lips ɗin nata kafin ganin zai iya wuce makaɗi da rawa ya sake ta a hankali idanun sa kuwa har sun canja kala, gaba ɗaya ko yatsar ta takasa motsawa, a hankali cikin wani irin murya da da kyar take fita yace 

'' ki tashi kije kiyi alwala, ga toilet can'' ya tashi ya fice daga ɗakin, ta kusan minti 10 kafin ta iya miƙe wa jikin ta a mugun mace wani irin tsoron shi da dana sanin auren na shigar ta

Gaskiya baza ta yarda ba a kaita wajen ammin ta

------

Toilet ya shiga saida yayi wanka sannan yayi alwala ya fito ya saka dogon wando ya ɗaura jallabiya akai, wardrobe ɗin shi ya buɗe ya ɗauko darduman da hijab ya nufo ɗakin, a lokacin itama bata daɗe da fitowa daga wanka ba ta nemi kaya a wardrobe ɗin ta saka bata ga hijab ba, suma kamar wannan kayan an fara shiryawa ne aka barsu, ta mayar da veil ɗin ta ta nannaɗe jikin ta dashi

Ganin yanda ta wani kanannaɗe jikin ta yasa dariya neman zuwan mai amma ya kauda kai ya miƙa mata hijjab ɗin, a sanyaya ta kai hannu ta amsa, shimfida musu darduman yayi, saida tayi isha sannan ya ja su suka yi raka'a biyu ya juyo ya riƙe kanta ya mata addu'a 

Itama yana gama wa ta riƙe nashi kan ta mai addu'ar, da tsantsar farin ciki yake kallon ta, tana sauke hannun ta ya janyo ta jikinsa ya raɗa a kunnen ta

'' ina alfahari da kasancewar ki mata ta, ruhin Umar Faruq” 
Ƙasa tayi da kanta ta lafe a jikin nashi tana ɗan murmushi, a hankali ya sake ta ya tashi ya ɗauko plate da cup ya zuba musu drink ya janyo kazar gaban su,

Hana ta sa hannu yayi gaba ɗaya, saidai ya gutsura ya bata sai ya kai mata cup baki gaba ɗaya kunya ta rufe ta, tun tana ci da kyar ganin ko a jikinsa yasa ta ware suka ci har ta ƙoshi 

Yace ta tashi ta wanke hannu shi kuma ya tattara kayan ya kai kitchen, yana shigowa ita kuma lokacin tana naɗe dadduma ya jingina da bango ya zuba mata ido, ajje wa tayi ta shiga toilet ta wanke hannunta still yana wajen, da ɗan mamaki da tsoro take kallon shi ganin ya tsaya kallon ta, kafin ta ma iya wani tunanin ya kashe wutar ya tako har inda take ya ɗage ta sama sai kan gaɗon 

Mutsu mutsu da cicilla ƙafafuwa ta ringa yayi amman saida ya kaita kan gadon sannan ya kwantar da ita, kwanciya yayi ya saka ta a jikin sa amman har lokacin bata daina kokarin kuɓucewa ba yace

'' shhhh, ki daina bacci za muyi kawai,muyi bacci kinji Mie Amor''
A hankali ta daina ƙoƙarin kwatar kan nata tana maida numfashi, dan rikon da ya mata duk da ba wai ƙarfi ya saka mata ba gaba ɗaya kasa kwacewa tayi

Saida ya tabbatar ta nutsu har ta ɗan fara bacci sannan kuma ya canja salo, itama jin haka yasa ta fara ƙoƙarin ta kwace amma a banza,

ranar da ita taga haza haza ya ganta, dan ya Faruq mancewa yayi da kowa da komai sai ita kaɗai a duniyar sa, ya nuna mata irin tsantsar son da yake mata 



Follow me on arewapen for more updates 🥹 🥰 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏



______________________
By
Anisa Muhammad Yahaya 🌺 
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol