Free chapter · Read without an account

73

by Anisa Muhammad Yahaya · NUFIN ALLAH



💕 NUFIN ALLAH 💕 
      By
Anisa Muhammad Yahaya 

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA


Wannan page ɗin sadaukar wace ga ƴan gidan mu( Fatee, Khadija,Anas,Hassan, Ikhram, Wasila, Mama da Baba) da kuma sahibah wato (Amina Ado Garba 🥰❤️‍🩹)da (Adda karymat 🌺🥰 Adda Mai kwai 🥰🌺) da Fans din 💕 NUFIN ALLAH 💕🥰🥰😘❤️‍🩹, ina godiya da kasancewar ku tare dani har zuwa yanzu Nagode sosai masoyan nufin Allah ina alfahari da ku🥰🥰❤️‍🩹❤️‍🩹🙏🙏



Page 7️⃣3️⃣

(Last page In Sha Allah)


A haka dai suka gama cin abincin yana bata a baki tana amsa da ƙyar har dai ta fara sakin jiki, kallon shi tayi tace

'' Yah to ai kai baka ci''
'' sai kin ƙoshi tukuna''. Ido ta zaro tace '' A'a gaskiya kaima ka ci yanzu na ƙoshi''
'' saidai ki bani a baki''. Kai ta kawar tana murmushi, gaskiya his not even serious 

'' Yah ƙato dakai ne zan baka abinci a baki''
''ai ni small boy ne indai ina gaban ki'' 
'' Tabb ni asuwa'' ta faɗa tana dariya 

'' ke a princessa, ke kike da raƙumi da a kala sai inda kika jani''. Ya faɗa yana jan hancin ta haɗi da kara rungume ta a jikin sa, dariya take yi kawai ta ɓoye fuskar ta a ƙirjin sa da kunya, ganin yanda yake bin ta da kallon da ta kasa fassara wa

'' to yanzu kenan baza ki bani ba koh'' ya faɗa yana wani marairaice fuska cike da shagwaba, kallon sa tayi tana mamakin wai daman ya iya shagwaba
'' ki ka kafe ni da waɗannan kwala kwalan idanuwan naki kamar baki taɓa gani na ba'' baki ta cuno cike da shagwaba tace 
'' ni ido na ba kwala kwala bane normal ne'' ta faɗa tana wani juya su, ze yi magana tace

'' wai Yah a ina ka samu abinci, dan nasan dai ba kai ka dafa ba'' 
'' hmmm ke kika tashi ina jin kika dafa mun tunda bani na dafa ba'' 
'' to wai daman ka iya girki? Ai na sha ko ruwan zafi baka iya dafawa ba bare ka iya yin sauce'' ta faɗa tana riƙe dariyar ta

Shima cike da dariya yace
'' lallai yarinyar nan, ni ne ban ma iya dafa ruwan zafi ba, to a Barak wake mun girki kenan?"
'' na sani ko siyowa kake yi'' 

'' lallai ma, wai daman haka kika iya surutu, shine idan na kira ki a waya sai dai ki ringa amsa mun da short short magana kamar ba ki iya surutu ba'' ya faɗa yana shafa lips ɗin ta kai ta kawar tana dariya 

'' ni ina zuwa'' ta faɗa tana ƙoƙarin gudu wa dan daren jiya ne kawai ya faɗo mata da ya shafa lips ɗin ta, wani kunyar sa ce ta rufe ta shiyasa take son tashi ta bar wajen

'' ba inda zaki je har sai kin yi feeding ɗina''. Marairaice fuska tayi zata mai kuka dan gaba ɗaya kunyar sa take ji, gashi yana wani cewa sai ta bashi abinci a baki ita ina zata iya bashi wani abinci 

--------

4 months later 


Zaune suke gaba ɗaya su huɗu sai hira suke suna raha Nabila tace

'' wai nikam Anisa me kike Sha haka kwanakin nan sai wani ƙiba kike kamar ana hura ki'' 

'' uban hura ni,ai da yake kin san breadi ce ni ake bulbula mun yeast, yar rainin wayo'' 

'' dan Allah Fareedah baku ga shegen kiban da tayi ba'' 

Jalila ce tace
'' yo ina ruwan ki kin bi kin sawa pixie na ido ke baki ga naki ƙibar ba har wani fresh kika yi amman kina wa wani tsiya'' 

'' yauwa dai pickles faɗa mata, ta takura mun sai shiga mun hanci da ƙudundune kike yi, ni banso ma gidan mu ɗaya da wannan fitinaniyar ba, duk kin bi kin fitine ni'' 

Ta faɗi tana hararar Nabila, taɓe baki Nabila tayi tace
'' ni kuma naji daɗi ko dan inyi ta addabar ki'
Fareedah ta kalla wacce kamar bata san dasu a wajen ba tace 

'' ke wai pookie uban me kike yi a wayar nan da kika share mu hankalin ki na kan screen ɗin waya tun ɗazu'' 

'' ina ruwanki kiyi harkar ki''. Ta faɗi tana sakin murmushi, Jalila ce tayi saurin shammatar ta ta fuzge wayar ta duba 

'' awwwn ai dole baza ta tanka ku ba, ita da Romeo ne sarkin soyayya''.
''Jalila bana son iskanci wallahi meye haka'' ta fuzge wayar tana turo baki, ta haɗe rai

'' waye kuma Romeo Jalila''
'' hmmm Ya Haydar ne fa''
'' wani Ya Haydar ɗin wai'' Nabila ta tambaya 

'' wani Ya Haydar kika sani, abokin dai ya Faruq'' faɗin Jalila 
'' wan da ya mai best man da bikin mu '' Anisa ta faɗi tana kallon Fareedah da tayi kicinkicin da fuska 

'' ah abunku ɗagetion kuna cin lokaci keda Leema, itama sun jone ita da muazzam abokin hubby''. Nabila ta faɗi 

'' wai da gaske, ashe duk dahir kuka kama'' Jalila ta faɗa tana sheƙewa da dariya 

Anisa ce ta kalle ta tace '' to banda ke''. '' nii!! Ai ni saliha ce'' ta faɗa tana kunshe dariyar ta

'' kiji sai kace ba soyewa suke yi ita da Ya Usman ba munfuka''

'' ke kuma Anisa a bakin wa kika ji zancen nan'' 
'' kenan dai gaskiya ne kike mun tsiya'' Fareedah ta faɗa tana gyara zama jin ba ita kaɗai bace 
'' sister bamu mu sha'' faɗin Nabila 

'' nima ban daɗe da sani ba in faɗa muku, yaya Saudat ce fa da tazo ina jin ma kamar last week ne, sai ya Jamal ya zo ɗaukar ta, ina gaya muku ashe suma love suke sha, amma su iyaye sun sani mune dai bamu sani ba, take fadin wai Yah Jamal yace mata soyayya Ya Usman da Jalila suke, niko da son jin gulma na tambaye shi''

'' shi wa ɗin'' Jalila ta katse mata hanzari. '' to bashi mijin naki ba, nawa mijin'' ta faɗa tana sheƙewa da dariya 

'' banza kawai'' Jalila ta ɗaka mata duka a cinya 

'' kace biki muke da shi nan kusa kai shagali, ai dole in cancare, kin San na kwana biyu ban dan rage kitse ba'' Nabila ta faɗa suna kashe hannu da Anisa 

Yatsi ne fuska tayi tace 
'' tun kika shigo na ce miki wallahi wannan turaren naki ba daɗi, yayi ƙarfi da yawa, hawar mun kai yake yi, kuma kin ki ki je ki canjo, baki ji zuciya ta ba shiyasa fa na dawo nan gashi kin wani biyo ni''

'' eyye kiji wani iyayi'' faɗin Nabila tana hararar ta, kai ta kawar dan da gaske warin turaren na damun ta sosai take jin shi har tsakiyar kanta 

'' wai har yanzu abinda kika dafa bai dahu bane, ko baza a bamu muci ba ne'' faɗin Jalila 
'' au ni zan muku girki, zaku kwana da yunwa kuwa'' 

'' to idan mijin naki ya dawo me zai ci'' 
'' to daman zama zan yi ina kallon ku ban girka mai ba ai shi na gama wa girki ku kuwa idan kuna jin yunwa gaku ga kitchen''

'' au ke ba kya jin yunwar kenan'' 

'' nifa a kwanakin nan idan ba kayan gishiri ko ƙuli ba ba wani abin da nake so sai kuma moltina duk yanda wai na tsani multina amma wai yanzu idan ban sha ba har ji nake kamar zan mutu'' ta faɗa tana yar dariya 

'' amma dai Anisa ciki ne dake koh?"
'' yauwa dai pookie taya ni tambaya tun ɗazu nima nake ma kaina wannan tambayar '' faɗin Jalila 

'' yoo ke har sai kin tambaya ma ga alama Kuru Kuru'' faɗin Nabila 

'' da yake a ruwa ake sha ko, daga zuwa 4 months har na ɗauka, baku da hankali, ba yanzu ba ni yarinya ce'' ta faɗa tana kauda kanta duk da dai itama tana ta tunanin nan 

Canja maganar tayi da cewa
'' wai baza ku je ku dafa ba'' 
'' kina da flour?''
''eh akwai meya faru?"
'' wainar fulawa zan yi dan shi kawai nake sha'awar ci''
'' yauwa nima dai har kin sa mun kwaɗayin ta Wallahi Jalila, amma ke zaki mana'' 
'' idan kuwa ni kaɗai zan yi baza ki ci ba, kefa Nabila za ki ci'' 
'' eh amma indai sai na taya ki na ƙoshi'' 

'' amma ku fa yan rainin hankali ne, wallahi pickles ki barsu kiyi iya na cikin ki duk wacce ta matsu ta tashi tayi da kanta, amma ni ki ɗan taimaka ki mun ɗanwake ya ji manja da yaji da yawa kin ji rabin ran'' 

'' ke yarinyar nan wallahi ciki ne dake''. Faɗin Fareedah, zata bata amsa Ya Umar ya shigo parlourn da sallama 

Amsawa suka yi suka gaida shi, amsa musu yayi cike da raha kamar bashi ba yana kashe mata ido, tashi tayi tabi bayan shi tana ce musu
'' minti biyu ina zuwa'' 

Jalila ce cike da shaƙiyan ci tace. '' kamar ba wanga ɗiya ta gama kukan ba tason auren ga ba''. Suna kashe hannu ita da Nabila, kai Fareedah ta jijjiga tace

'' Allah dai ya kyauta muku'' 

------

Tana shigowa ya rungumo ta jikin sa 
'' I missed you so bad yau ɗinnan, tun na fita tunanin ki kawai nake yi''

'' hmmmm'' kawai ta iya cewa dan yanda turaren sa ke dukan mata hanci yana hautsina mata ciki 

'' gobe zan tafi portharcourt fah'' kallon sa tayi tana kwaɓe fuska amma ta kasa cewa komai 
'' wai yau fushi kike dani da ba kya son mun magana ko welcome back baki yi mun ba''

Ganin dai bashi da niyyar kyale ta yasa ta fara ƙoƙarin barin jikin sa jin amai na taho mata, amma ya ƙara rike ta
'' nima fa ba a son raina bane zan yi tafiyar nan zan amsa transfer letter na ne za'a maida ni Abuja, wannan bata ran da kike yi kodai an fara so na ne ba'a son in tafi, ni fa har yau Amor baki taɓa cewa kina son Umar Faruq ba'' ya riƙe ta gam yana haɗa goshin su, 

'' Yah ka kyale ni dan Allah amai '' kafin ta gama magana ta fara kakari da sauri ya sake ta ya ja hannun ta har toilet ɗin, kafin su karasa ma ta fara yi a wajen, sai da ta gama, ya cire mata rigar jikin nata dan duk ta ɓata har nashi sannan ya ɗauraye mata baki ya dawo da ita ɗakin bayan ya cire nashi rigar 

Sannan ya koma ya gyara duk inda ta ɓata ya dawo yana mata sannu, ɗago ta yayi amman tayi saurin goce wa tace

'' Yah turaren ka, hawar mun kai yake yi'' 
'' turare na!!, shine wanda nake saka wa kullum fa'' 
'' ni wallahi wani aman nake ji ka canja kayan'' 
Da sauri ya miƙe, Allah sarki duk yabi ya ruɗe

Toilet ya shiga ya ƙara yin wanka sannan ya fito ya saka wasu kayan amma be shafa turaren ba, dawowa yayi har lokacin tana kwance zuciyar ta bata dai na mata ba daɗi ba yace
'' baki yi bacci ba?''
'' uhm'' 
'' to kiyi bacci, ko hayaniyar yaran can na damun ki''
'' A'a, bana jin baccin ne kawai'' 
'' a'a dai kiyi ko kaɗan ne kin ji Amor''
Kai ta gyaɗa dan ba magana take son yi ba ya tashi ya fice daga ɗakin 

''amm Jalila ku koma part ɗin Nabila, Amor bata da lapiya, so ta kwanta bacci ku ɗan koma kar ku dame ta'' 

'' subhanallah meke damun ta'' faɗin Nabila hankalin su duk a tashe, yanzu yanzu ta tashi fa lafiya kalau 

Da ba zai bata amsa ba amma ganin yanayin su yace
'' Amai tayi yanzu, so nace ta huta''. Faɗa yana yin hanyar waje 

Kallon juna suka yi Jalila ta sauke ajiyar zuciya dan tayi tunanin wani abu ne ya same ta tace
'' kin san Allah ko da yake abar kaza cikin gashin ta mu tashi mu tafi'' 

'' hmmm ai ba ke kaɗai kike wannan zargin ba ni tun kwanaki nake mata tsiya'' faɗin Nabila 

-----

'' Yah yanzu ni kaɗai zaka bari''. 
'' missing ɗina kika fara yi tun kafin in tafi, ke da kika ce ba kya so na, maisa kike son Kar in tafi'' kai ta kawar gefe tace

'' ni a yaushe na ce haka, kuma ai tsoro nake ka barni ni kaɗai shiyasa'' 

'' to ai shikenan tunda ba kya son Faruq idan naje sai in samo wata acan ita mu zauna a Abujan da ita wadda idan nace ina son ta itama zata ce tana sona, ke ki zauna anan tunda indan nace babyn Faruq I love you saidai kice naji ko ki ɗan yi murmushi baza a mun reply ba'' ya faɗa yana haɗe rai kamar da gaske 

Tsayawa tayi cak da haɗa kayan da take yi ta kalle shi, idon ta na cikowa da kwalla, rigar hannun ta ta ajje ta fita daga ɗakin 

Wani murmushi yayi ya cigaba da haɗa kayan yana girgiza kai, a da idan Ahmad ya faɗa mai tana son shi furta mai ne kawai baza ta yi ba, baya gazgatawa, yayi tunanin tana biye mai ne kawai dan bin umarni da sanin haƙƙin aure, amman ahankali yana gane tana son shi furta wa ne kawai baza tayi ba, amma zai saka ta furta da bakinta 

Ɗakin ta ya buɗe a hankali, ta dunƙule kan gadon sai kuka take mara sauti, tsayawa yayi bakin gadon, tana jin sa amma bata juyo ba sai ma bargon da ta janyo ta rufe har kanta, hawo wa kan gadon yayi yana murmushi yace 

'' me ya faru kuma kike kuka, shine kika taho ma kika ƙyale ni in haɗa kaya na ni kaɗai koh'' tana jin sa amma ta mai banza, duk maganganun da yake mata tana ji amma ta kyale shi, ganin ya janyo wa kansa ruwa ya kwanta ta bayan ta ya janyo ta jikinsa ya saka ta a jikin sa yace daidai kunnen ta

''haba Mon Cherie, kukan duk akan nace zan tafi portharcourt ne, two days fa kawai zan yi, shiyasa kika ƙi haɗa mun kayan nawa'' juyowa tayi cike da tsiwa tace

'' to kama yi two weeks ni ina ruwa na, sai ka kira sabowar matar da zaka yi ta haɗa maka kayan in yaso ma ku tafi tare ta taya ka kwanakin da zaka yi'' dariya yayi me sauti a saman kanta, ya ƙara janyo ta jikinsa yace

'' to wace ce ita ɗin'' 
''ai kai zan tambaya'' ta faɗa tana ƙoƙarin barin jikin sa 
'' wai duk akan maganar nan ne ya saka ki kuka?''
 Ƙirjin sa ta buga tace
'' ni ka ƙyale ni, nima ban sani ba'' ta faɗa tana sake fashewa da kuka jin shi ko a jikin sa ma

Dariya ya ƙara yi ya rike ta yace
'' da zafi fah'' '' hmmm'' ta faɗa dan ita kaɗai tasan zafin da take ji 

Ganin dai da gaske baza ta daina kukan ba, kuma ya fara damun sa da yawa dan baya ƙaunar kukan ta, janyo ta yayi dan ta bar jikin sa yace
'' to yi hakuri kin ji mie Amor, bazan sake ba kin ji kiyi shiru, am sorry kinji love'' 

Baki ta turo gaba ta kauda kanta gefe 
'' haba mana ki kalle ni Faruq din ki ne fah, ai daga ke na rufe ƙofa, keda ma ba kya so na,maisa zaki na kishi na'' 

'' ni ba kishin ka nace ba''. '' dagaske'' ya faɗi hannun sa na yawo cikin rigar ta, jin zai iya canja salo tayi saurin zame wa ta mike tana mai gwalo dan sallar azahar ake kira ta fice da sauri, koma wa yayi ya kwanta kan bayan sa ya na maida numfashi, dariya yayi yana bin hanyar da tayi da kallo 

Lumshe ido yayi a zuciyar sa yana gode wa Allah, koda ace bata son shi, koda ace baza ta furta ba a hakan ma ya gode, dan a duk zaman su bata taɓa mai abinda zai ji ba daɗi ba ko ta saɓa umarnin sa, da gaskiyar Ahmad da yace idan kana son mutum ba za ka ringa fargabar raini ko wani naƙasu da zaka samu tattare da shi ba, yanzu koda ace bata son shi, da ya sauke attitude ɗin shi ya ja ta a jiki gashi nan suna zaman lafiya 

-------

8 months later 


'' lailahaillah!!! Wayo Allah na Ammi na, Allah Ya Faruq ba ruwa na da kai, ka cuce ni, ka gama da ni, na barka da Allah!!''

'' kiyi hakuri kiyi shiru'' faɗin doctor ɗin

'' lahaula wala ƙuwwata illa billa'' ta faɗa tana sake sakin wani kuka, gaba ɗaya zufa sai keto mata yake yi 

'' doctor danAllah kice a kira mun hayaty na kar in mutu ban sake ganin ta ba nima in tafi kamar yanda Abhie ya tafi ''

'' Ai bata nan, amma zan sa ace mata tazo ''
'' to a kira mun ya Faruq'' 

'' kira mata shi'' 
Doctorn ta faɗa tana kallon wata nurse ɗin dake wajen 

Fito wa tayi tace. ''wai waye Faruq'' 

Ya Faruq dake ta sintiri a bakin dakin duk ya hada zufa shima, hankalin sa in yayi dubu ya tashi, Ahmad ke ta kwantar musu da hankali, ga Nabila ma da itama tayi nauyi haihuwa yau ko gobe amma duk da haka sai da ta biyo su, gashi itama ta tada hankalinta 

Da sauri ya bi ta suka shiga ɗakin, kanta yayi da sauri yace
'' Amor'' ya ma kasa magana ganin yanayin ta 
'' hannun sa ta riƙe da ƙarfi 

'' Ya Umar duk kai ka ja mun wannan abu, Allah bazan ƙara yarda ba, idan kuma na mutu kacewa Ammi ta yafe mun, ka faɗa wa su Jalila ma su yafe mun, kace wa Nabila fa ta kwantar da hankalin ta, Ya Ahmad ya maida ta gida, ta daina damuwr da nagani a fuskar ta kafin mu shigo''

'' kiyi shiru kin ji Cherie'' 
'' ni wallahi ka kyale ni, ai kai ka saka ni a cikin halin da nake a yanzu dan haka ka barni, lailahaillah ''

'' na fara ganin kan jaririn kiyi nishi''. Wani nishin tayi da karfi tace

'' lailaha illalla Muhammadur Rasulullah, Ya faruqqqqq!!!''. Ta riƙe hannunsa tana jan numfashi da ƙarfi

Hannu doctorn ta saka ta talla fo jaririn da sauri,
'' Mashallah mace aka samu'' ta faɗi tana juya ma Ya Umar ita

Kwallar farin ciki ne ya zubo mai ya juya ya rungume Anisa da ta fara jin wani sabon ciwon, kafin kace me, wani labourn ya ƙara zuwar mata, nurse ɗin ce tace

'' doctor wani labourn zata ƙara''
Zaro ido Umar yayi, yana kallon ta 

 suma a waje da nurse ɗin ta fitar zata karo wasu abubuwan suke tambayar ta, ta sanar da su ta sake sabon labour,

Aikam hankalin Nabila itama ya ƙara tashi, tana a zaune nan ruwa ya fara bin ƙafafuwan ta wani azababben zafi ya ziyarci kwakwalwar ta, itama labourn room ɗin aka shiga da ita, tashin hankalin Ya Ahmad kam ba'a magana, ga matar sa ga ƙanwar sa


Wannan labourn beyi tsawo kamar wancan ba aka fito da wata jaririyar, dukan su lapiya kalau, sujudur shukur yayi yana hamdala, jikin ta duk ya gama yin weak 

Doctor ce tace ya fita a gyara su, jiki ba kwari haka ya fice yana leƙen ta, 

A ɓangaren Nabila ma ta haihuwa cikin koshin lafiya, ta samu ɗan saurayi mai kama da Ya Ahmad, bakin ya Ahmad kuwa ba'a magana dan murna ga Faruq ma ya faɗa mai Anisa ta sauka lapiya ƴan biyu 

Su Amma kam duk sun zo sun cika asibitin dan murna sun ma rasa wajen wa zasu je Nabila ko Anisa gashi duk an hana su gansu

Sai bayan da aka kai su resting room aka fito musu da yaran, Ya Umar kam hankalin sa na kan matar sa ana fito da su ya tambayi ɗakin da aka kai ta, shiga yayi da sallama, ɗagowa tayi tana sakar mai murmushi da sauri ya ƙarasa inda take wasu hawayen farin ciki na zuwan mai

Cike da zolaya tace 
'' ni dai ban san sanda soja na ya koma rago ba, kuka kamar ba kai ba Ya Faruq fa baya ma dariya bare kuka'' ta faɗa da kyar dan ba kwari jikin ta

'' ke ko'' ya ɗan ja hancin ta yana sakin murmushi 
'' ina yaran'' ta tambaya tana kalle kalle 
'' suna wajen su Ammi, ni ban ma ɗauke su ba, bara in amso miki ki gansu'' 
'' a'a ka bari su kawo su, su gama daukar su tukuna''

Hararar ta yayi yace
'' ai baza su daina ganin su ba bara in amso su, kema ya kamata ki fara ganin su kafin kowa bawai ki gansu a ƙarshe ba'' murmushi tayi ta bi shi da kallo har ya fice, wani azababben son mijinta na taso mata, tuna yanda yatsa tare da ita ɗazu har ta sauka lapiya, da yanda ya haɗa uwar zufa ga ido duk hawaye kamar shi ke labourn, dariya tayi tuna hakan ta girgiza kai 


'' au kaima yaran kazo amsa, shima wancan gogan ya zo ya amshe nashi wai matar sa na nema, ku yaran zamani ba kuda kawaici ɗan fari fa'' Amma ta faɗi tana sakin dariya ta juya ta kalla su Anty 

Ammi dai bata ce komai ba sai murmushi, Anty da Mommy ke ta musu tsiya dan su Mommy tun ana wata 3 da bikin suka dawo Kano gaba ɗaya 

'' ai Amma yanzu babu wani kunyar ɗan fari a zamanin kune dai ake yi amma ba yanzu ba''. Ya tusa kansa yayi ciki, kai Amma ta girgiza yana kama haɓa

-----

'' sweet dani fa yake kama'' 
'' a'a dai bakin sa ne kawai irin naka amman da ni yake kama, baka ga har irin ido nane da shi ba'' dariya yayi cike da farin ciki yana ƙara rike yaron a jikin sa yana godewa Allah 

----

Miƙa mata yaran yayi duk su biyun masu kama da ita saidai hasken sa da suka kwaso, da tsayin hancin su da yaɗan fi nata 

Cike da wani tsantsar so da kaunar yaran ta amshe su da basmala a bakin ta addu'a ta musu sannan ta ɗaugo ta kalli Ya Umar dake zaune da ita tace

'' Allah ya raya mana su'' hawaye wani na bin bayan wani 
'' Ya Faruq'' kallon ta yayi a hankali ta sunkuyar da kanta tace
'' thank you so much, da duk irin kulawar da kamun, ina alfaharin kiran ka miji na kuma wani bango a rayuwarta, I love you Soo so much fiye da yadda kake tsammani, ina maka son da baki na bazai iya furta wa ba''

Numfashi ya sauke ya ƙara rike ta a jikin sa, kalmar da ya daɗe yana jiran jin sa daga bakin sa yau ya ji, yau Anisa ke furta tana so da kaunar sa


------


Sahla, Salwa ina suhaima?''. 
'' tana ɗaki tana wasa munce ta zo muje wajen su mahbub ta ma ƙi kula mu'' faɗin Salwa yar shekara tara, 

'' to kuje kuyi wasan ku, daman so nake inga inda kuke''. Aikam da gudu suka ruga part ɗin Nabila suna murna 

Tashi tayi ta shiga ɗakin su, ita wannan halin na Suhaima bata san yanda zata yi da ita ba, halin uban ta ta gado sak, ita har ta ɗara shi da miskilanci, da rashin son mutane, idan tana haka ko faɗa take mata tana ji baza ta ce uppan ba, ko kuka idan ta dake ta bata yi, gaba ɗaya bata fi shekara biyar ba

'' Suhaima ina kike''. Tana jin ta amma ta cigaba da wasa da babyn ta, tana zuwa tagan tana wasan ta hankali kwance, tsayawa tayi tana kallon ta, ganin haka kawai ta girgiza kai ta koma itama ɗaki 

A gaban mirror ta ganshi yana shiryawa fuska ta kwabe tace, 
'' Allah Suhaima kai ta gado gaba ɗaya har ta ɗara ka, shiyasa tafi ƙulafucin ka ma'' takowa yayi inda take ya riƙo ta jikinsa yana zagaye hannun sa akan lips ɗin da take turowa yace 

'' haba dai ke dai, me tayi kuma yanzu''. '' hmm babu'' '' to tunda haka ne a daina takura wa baby na'' 
'' hmm ni sake ni inje inyi abinda ya kama ce ni'' 
'' me ya kama ce ki banda kula da ni'' 
'' in wanka inyi bacci, ai fita zaka yi idan kaje kace ina gaida ita'' 
Ta faɗa tana ɗan dariya 

'' to na fasa fitar tunda haka ne bara in zauna nima a saka ni a cikin agender taki na abubuwan da suke da muhimmanci a kula da wannan Faruq ɗin'' ya faɗa yana ƙara matse ta a jikin sa ya haɗa bakin su 


---------


Zaune suke gaba dayansu yaran na can waje suna wasa su kuma suna hira wanda hakan ya zamar musu dabi'a duk bayan ƙarshen wata za su haɗu a gidan dasuka hadu suka gina dan ƙarin zumuncin su duk su shidan da iyalen su

Ya Faruq da Anisa, Ya Usman da Jalila, Ya Ahmad da Nabila, Ya Jamal da yaya Saudat, Ya Haydar da Fareedah, Ya Muazzam da Leema 

Kallon su Anisa tayi cike da farin ciki, yanda suke raha da dariya da nishadi, a zuciyar ta ta ce 

'' alhamdulillahi yarabb, Allah na gode maka da kasa na bi umarnin iyaye na, da yanzu ace banyi aiki da abinda Amma ta faɗa mun ba da wata ƙila yanzu ban samu mijin da zai kula da ni ya so ni haka ya tarairaye ni kamar yanda Ya Faruq ke mun ba, alhamdulillah ala kulli halin, Allah Nagode da wannan ni'ima daka mun na ƴanuwa da miji da yara masu albarka'' 

Idonta da suka ciko da hawaye akan sa da ya dage sai faman surutu yake kamar ba Ya Faruq ba wannan me shegen haɗe rai dan kar a kawo mai raini ko wani shirme 

Gira ya ɗaga mata, da sauri ta girgiza kai, ta so wa yayi har inda take ya ja hannun ta suka yi ɗaki 

'' me ya faru Amor?'' 
'' ba komai '' ta faɗa tana kwantar da kanta a kan ƙirjin sa, riƙe ta yayi ƙam, kamar wadda za'a kwace yace 

'' kin tabbatar ''
''uhmm, kawai ina godiya ga Allah ne da ya bani kai matsayin mijina abin alfahari na ''

Goshin ta yayi pecking shima yana murmushi, yana tunanin ma ya fita alfahari da kasancewar ta mata a gare shi, wannan ne NUFIN ALLAHn da basu taɓa tsammani ba daga shi har ita akwai lokutan daya ke jin bazai taɓa samun ta ba, ko baza ta taɓa aminta da soyayyar sa ba, ko baza ta taɓa furta kalmar so a gare shi ba, amma a yanzu kam ya gode Allah 


'' ALHAMDULILLAHI YARABBIL ALAMEEN '' ya faɗa a sarari 



Nima nace

TAMMAT BIHAMDALLAH 

Alhamdulillah alhamdulillah anan muka kawo ƙarshen littafin mu na

💕 NUFIN ALLAH 💕 

Godiya mai tarin yawa ga wanda muka kasance a wannan tafiyar tare har zuwa yanzu Nagode sosai Allah ya bar ƙauna,


Abubuwan da na rubuta na alkhairi da na illimantar wa Allah ya sada mu da alkhairin cikin sa, wanda suke na kuskure kuma Allah ya yafe mana ya bamu ikon gyarawa 


Nagode sosai sai mun haɗu a wani littafin nan bada jimawa ba sosai in Sha Allah 




By
Anisa Muhammad Yahaya 🌺 
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol