Free chapter · Read without an account
The price of pride
CHAPTER SIX: THE PRICE OF PRIDE AND THE UNEXPECTED VISIT
by Rabi Muhammad Shariff
Ramsha Tales
Hibba ta kalle shi, sannan ta ce, “To, har gida ma ka biyo ni? Ai na gaya maka cewa ba zan koma ba!”
Latif ya yi shiru yana kallonta, zuciyarsa cike da takaici. Bayan ɗan lokaci, ya ce, “You are always talking about kindness, amma ina baƙonki haka ake tarbar mutum?”
Hibba ta sake kallonsa, ta ce, “Baƙon da ya san darajarsa, shi ake tarba da girmamawa ai. Kuma na riga na ba ka amsa. Me ya kawo ka gidana? Sannan, haka ake roƙon mutum?”
Latif ya gyara tsayuwarsa, sannan ya yi ƙasa da murya ya ce, “Please, Hibba, ki dawo aikinki.”
Hibba ta ɗan yi murmushi, domin a ranta ta ji wani irin daɗi. Amma saboda ta rama irin izzar da Latif yake nuna mata a baya, sai ta ƙuduri aniyar ganin ta sa shi ya rage girman kan nasa a yau.
Ta kalle shi, ta ce, “Ka roƙe ni cikin girmamawa mana! Haba, Latif Abdurrahman! Mutumin da yake daraja kuɗi fiye da komai, wanda yanzu yake ganin zai rasa kuɗin, amma a haka kawai zai roƙe ni?”
Latif ya san sarai abin da ya sa Hibba take masa haka. Amma maimakon ya ci gaba da roƙonta, sai ya ce, “Nawa kike so zan biya ki domin ki dawo? Ko da ba za ki dawo aiki na dindindin ba, please, ki dawo mu kammala wannan aikin.”
Abin da Latif ya faɗa ya ba Hibba haushi sosai.
Ta kalle shi cikin mamaki, sannan ta ce, “Wai kai kana ganin komai kuɗinka zai saya maka ne? Shi ke nan, tunda kana tunanin kuɗi za ka biya ni, sai ka juya ka tafi. Ba zan dawo ba!”
Ta juya da niyyar shiga cikin gida. Latif ya daure fuska, amma daga bisani ya danne girman kansa ya ce, “Please, Hibba, I’m sorry, but my company needs you. I need you, and I will suffer a great loss if you refuse. Hibba, please!”
Hibba ta tsaya, sannan ta juyo tana murmushi.
“Me ka ce? Don Allah ka sake maimaitawa, ban ji ba.”
Latif ya san sarai cewa ta ji shi. Amma saboda a wannan karon shi ne yake buƙatarta, sai ya sake cewa, “Don Allah, ki dawo. Ina buƙatarki.”
Hibba ta yi murmushi, tana jin daɗin yadda wannan mutumin mai girman kai yake ƙoƙarin danne kansa a gabanta. Daga bisani, ta amince za ta koma aiki, amma ta gindaya masa wasu sharuɗɗa.
Na farko, ba zai sake ɗora mata aikin da ya fi ƙarfinta ba. Na biyu, dole ne ya riƙa yaba mata idan ta yi aiki mai kyau, maimakon ya riƙa nuna mata kamar ba ta iya komai ba. Sannan ta ƙara da wasu sharuɗɗa nata.
Latif ya amince da dukkan sharuɗɗan, domin a yanzu ba shi da wani zaɓi face ya yi hakan. Bayan sun kammala maganar, ya yi mata sallama, sannan ya koma motarsa ya tafi.
Daga wannan rana, Hibba ta koma aiki, kuma ta ci gaba da gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.
---
Wata safiya, Latif ya tashi da matsanancin ciwon ciki. Ciwon ya hana shi ko fitowa ya yi karin kumallo. Yana kwance a kan gadonsa, ya lullube jikinsa da bargo, sai ga Jaddah ta shigo ɗakin.
Ta tsaya tana kallonsa, sannan ta ce, “Ahmadudu, lafiya? Me ya sa ba ka fito ba?”
Latif ya tashi zaune da ƙyar, ya kalle ta cikin fuskar wanda ba ya jin daɗi, sannan ya ce, “Haba, Jaddah! Ni dai ki daina ce min Ahmadudu. Sunana fa Latif!”
Jaddah ta ɗaga gira, ta ce, “To, ni da Ahmadu na san ubanka ya rada maka suna. Kai kuma za ka canza min shi ne?”
Latif ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya ce, “Na ji, yanzu. Ni dai, Jaddah, don Allah cikina ne yake ciwo. Ki bar ni in huta.”
Jaddah ta gyara zama, sannan ta ce, “To, Ahmadu, ba dole cikinka ya riƙa ciwo ba? Ai tun da ka ƙi yin aure, ka zauna kana fama da kanka! Gaya min gaskiya, me yake damunka?”
Latif ya tashi zaune sosai, yana kallonta cikin takaici.
“Haba, Jaddah! Wai ke komai sai kin yi wani tunani? To, ni dai ciwon ciki nake yi. Don Allah ki bar ni in kwanta kawai.”
Bayan ya faɗi haka, sai ya koma ya kwanta, ya ja bargonsa ya rufe jikinsa, ya bar Jaddah a tsaye tana kallonsa.
Jaddah ta girgiza kai, tana mamakin halin jikanta.
---
Da rana, wajen ƙarfe goma sha biyu, wayar Latif ta fara ringing. Ya miƙa hannu ya ɗauka, sai ya ga sunan Hibba a allon wayarsa.
“Why is she calling me?” ya tambayi kansa cikin mamaki, kafin ya ɗaga wayar.
Yana ɗagawa, Hibba ta gaishe shi, sannan ta sanar da shi cewa akwai wani file da yake buƙatar dubawa da sanya hannu a kai. Ta kuma bayyana masa cewa dole ne a kammala komai a ranar, amma shi bai zo ofis ba.
Latif ya yi ajiyar zuciya, sannan ya ce, “Ba na jin daɗi ne yau. Cikina yake ciwo, shi ya sa ban zo ofis ba.”
Hibba ta yi shiru na ɗan lokaci, kafin ta tambaye shi abin da za su yi game da file ɗin.
Sai Latif ya ce, “Idan ba damuwa, za ki iya kawo min shi gida? Zan tura miki address ɗina.”
Hibba ta amsa, “To, babu matsala.”
Bayan sun katse wayar, Latif ya tura mata address ɗinsa.
---
Wajen ƙarfe biyu na rana, sai ga Hibba ta iso gidan Latif. A hannunta akwai wasu files tare da na’urar kwamfutarta.
Ta tsaya a bakin ƙofar gidan, sannan ta kira Latif.
“Sir, ga ni a gidan.”
Latif ya amsa, “To, ki shigo ki zauna. Ga ni nan zuwa.”
Hibba ta shiga cikin gidan. Da ta isa falo, sai ta lura babu kowa a wurin. Ta ɗan duba ko’ina, kafin ta nemi wuri ta zauna.
Bayan ɗan lokaci, sai ga Latif ya shigo. Suka gaisa, sannan ya ce mata ta ba shi file ɗin.
Hibba ta miƙa masa file ɗin, shi kuma ya fara dubawa a hankali.
Yana cikin duba file ɗin ne, sai ga Jaddah ta shigo falon.
“Ahmadudu!”
Hibba ta kasa riƙe dariyarta. Da ta ji yadda Jaddah ta kira Latif da sunan Ahmadudu, sai ta yi dariya a hankali.
Latif ya haɗe fuska, ya kalli Jaddah, sannan ya ce, “Haba, Jaddah! Ba kya ganin ina da baƙuwa ne?”
Hibba ta miƙe kaɗan, ta gaishe da Jaddah cikin ladabi.
“Ina wuni?”
Jaddah ta amsa mata cikin fara’a, tana kallonta da kyau.
“Lafiya lau, yarinya. Ina wuni.”
Latif ya juya ya kalli Hibba, sannan ya ce, “Please, ki zo mu shiga ciki.”
Jaddah ta yi saurin katse shi.
“Ku shiga ciki? Ciki ina? Kai baligi, ita ma baliga! Wallahi, ku zauna a nan!”
Latif ya ji haushi sosai, amma ya san halin Jaddah. Bai san yadda zai yi da ita ba.
Ya juya ya kalli Hibba, sannan ya ce, “Hibba, sorry. Please, you know how these old people behave. And she’s my grandma.”
Hibba ta yi murmushi kawai, ba tare da ta ce komai ba.
Jaddah ta zaro ido, ta kalli Latif, sannan ta ce, “Ni za ka yi wa Turanci? Eye, ja’iri! To, ko zagi na ka yi kai ka sani. Amma wallahi, yau matan nan za su zo, ka zaɓi ɗaya. Ko kuma ni in aura maka wadda nake ganin ta fi maka!”
Latif bai ce mata komai ba. Ya kalli Hibba, sannan ya ce, “Let’s go.”
Hibba ta miƙe ta bi shi zuwa cikin ɗakin.
Jaddah ta zauna a kan kujera tana huci, kamar wadda ta fito daga filin yaƙi.
Ta girgiza kai, sannan ta ce, “Lallai wannan yaron!”
---
Da suka shiga ɗakin, Latif ya nuna wa Hibba wata laushiyar sofa da ke gefe, yana nufin ta zauna.
Hibba ta zauna, shi kuma ya zauna a gefen gadonsa.
Hibba ta kasa riƙe dariyarta. Latif ya haɗe fuska, sannan ya tambaye ta, “Me ya faru?”
Hibba tana dariya ta ce, “Ba komai, Sir.”
Latif ya kalle ta cikin mamaki.
“Ba komai kike dariya?”
Hibba ta ɗan rage muryarta, sannan ta ce, “Wai Ahmadudu!”
Latif ya ji abin da ta faɗa, sai ya ƙara haɗe fuska.
“Me kika ce, Hibba?”
Hibba ta girgiza kai, tana ƙoƙarin danne dariyarta.
“Ba komai.”
Latif ya yi shiru, sannan ya karɓi files ɗin daga hannunta. Ya sake dubawa a hankali, ya tabbatar da komai, sannan ya sanya hannu a wuraren da ake buƙata.
Da ya gama, sai ya miƙa mata files ɗin.
Hibba ta karɓa, ta miƙe da niyyar tafiya. Amma kafin ta fita, sai ta juyo ta kalle shi, murmushi ɗauke a fuskarta.
“Sir, yaushe ne auren naka?”
Latif ya haɗe fuska sosai, sannan ya ce, “Oya! Ki fice min daga ɗaki!”
Hibba ta fashe da dariya, ta juya ta nufi ƙofa.
Kafin ta fita gaba ɗaya, sai Latif ya kira ta.
“Hibba, please! Kada ki je kina ba kowa labari!”
Hibba ta ƙara yin dariya, ta ɗaga masa hannu kamar tana yi masa alƙawari, sannan ta fice daga ɗakin.
Latif ya zauna yana kallon ƙofar da ta fita, fuskarsa cike da takaici.
Amma a cikin zuciyarsa, ya kasa musanta cewa Hibba ta fara zama wani abu na daban a rayuwarsa.
Kuma duk da girman kansa, kasancewarta a kusa da shi ya fara zama abin da ba ya son ya rasa.