Free chapter · Read without an account

THE FINAL TRUTH

by Jiddaah Barkum · KADDARAR ZUCIYA

KADDARAR ZUCIYA


CHAPTER TWENTY-SIX: 26


THE FINAL TRUTH


JIDDAAH BARKUM


———

“Take na ji, ban yarda da cewa wai matata da na kawo yanzu-yanzu, ƙasa da awa ɗaya da ta gabata, ta rasu ba. Zuciyata ta ƙi mini daɗi, my mind completely rejected the news. Kai tsaye ban saurari kowa ba, na wuce ɗakin da take kwance. Sai dai abin da na iske ya daki ƙirjina, leaving me completely shattered. Tana kwance sambal a kan gado, an riga an saka mata zani an rufe ta tun daga kai har ƙafa.

Cikin sanyin gwiwa na ƙarasa a gefen gadon. A daidai wurin akwai ƙaramin gado na jarirai, kuma jaririyar tana ciki tana baccinta cikin tsantsar kwanciyar hankali, sleeping so peacefully, unaware of the pain that had just entered our lives.

Na ƙarasa gaban gawar Fateema, na ɗaga zanin da aka rufe ta da shi. Fuskarta tana nan fes, tamkar barci take yi ne, ba mutuwa ta yi ba. I couldn’t believe what I was seeing. Na juya na kalli jaririyata, sai na ga kamar fuskar Fateema aka ɗauko aka ɗora a fuskar yarinyar saboda tsananin kamanninsu da ke fitowa fili.

Na saka hannu na ɗauko ta na rungume a ƙirjina, sai na ji wani matsanancin ƙaunarta yana shigata, ya fi gaban yadda na taɓa zaton zan iya son wani a rayuwata. Na durƙusa a gaban gadon, jaririyar a hannuna, hawaye na wanke mini fuska, na ce:

‘Fateema, ki tashi… Fateema, kin yi mini alƙawarin ba za ki tafi ki bar ni ba. Ki tashi ki ga ’yarmu. Kin ga? Allah Ya ba mu yarinya mai tsananin kama da ke… Ki tashi ki ganta, my love. Please, ki buɗe idanunki.’

Na faɗa ina jin kamar ba na cikin duniyar nan, saboda wani irin yanayi mara daɗin ambato ya baibaye ni. It felt like I was trapped in a nightmare I couldn’t wake up from. Ganin ba ta ko motsi, sai na fara gasgata maganar da aka gaya mini. Ashe dai Fateema tafiya za ta yi ta bar ni.

Ina kallon gawar Fateema, ina riƙe da jaririyar a hannuna, na ce:

‘Kin tafi kika bar mini amanarki… To, na rantse da Allah, zan so ta sau biyu. Zan so ta saboda ni… kuma zan so ta saboda ke. I promise you, Fateema. I will love her with everything I have.’

Haka likita da ’yan uwa suka zo da ƙyar suka fitar da ni daga ɗakin, ina rungume da ke a ƙirjina.”

Alhaji Kabeeru ya faɗa yana kallon Inteesar da ke kuka kamar ranta zai fita. Haka ma sauran yayyenta maza da Mommy Haleema, kowa kuka yake yi sosai. The pain in the room was almost unbearable, tamkar kowa yana sake rayuwa a cikin wannan mummunan ranar.

Alhaji Kabeeru ya haɗiye yawu da ƙyar, sannan ya ɗora:

“Ina fitowa daga ɗakin, na ga yayyenki a tsaye a corridor ɗin asibitin. Da alama sun ji labarin mutuwar mahaifiyarsu, domin kowa fuskarsa da hawaye. Sai Khalil, wanda shi ne ƙarami kuma bai san mene ne mutuwa ba, ya taho da sauri ya rungume ƙafata ya ce:

‘Daddy, wannan ce baby mu? To, ina Mommy kuma take?’

Wannan tambayar tasa ta sake ɗaga mini hankali. I broke down all over again, na fashe da wani sabon kukan, tare da dukkan wani da ke wajen. Ban san ta inda zan fara ba, balle ta inda zan ƙare. Ta yaya zan bayyana wa ƙaramin yaro cewa mahaifiyarsa ba za ta sake dawowa ba?”

“Bayan mun ɗauki gawar Fateema, aka sanar da ‘yan uwanta da nawa da kowa. Aka zo gida aka yi jana’iza, aka kai ta gidanta na gaskiya. Abin da nake kallo kamar wasa, ashe gaske ne Fateema ta tafi har abada.

Ke kuma a lokacin kina hannun ƙanwar mahaifiyarki, Hajiya Murja. An yi miki wanka, an ba ki madara kin sha, kina ta baccinki hankalinki a kwance. You were so innocent, ba ki san irin baƙin cikin da zuwanki duniya ya zo da shi ba.

Bayan an yi sadakar bakwai, sai ’yan uwan mahaifiyarki suka zo da maganar tafiya da yayyenki gaba ɗaya, kuma suka ce za su karɓe ki su riƙe ki. A nan ne hankalina ya dawo kan tashi! Na ce sam ba zan ba da yarana ga kowa ba. Za mu ci gaba da zama tare, za mu raine ki tare da su a tare. Sun ja, na ja. From the depth of my heart, na ƙi amincewa da rabuwa da ku. Daga ƙarshe dole suka haƙura suka bar ku tare da yayyenki.”

“Bayan komai ya lafa, Haleema ta shirya kayanta za ta koma garinsu, saboda babu matar gidan, zamanta a cikin gidan ba zai yuwu ba ta fuskar addini da mutunci.

A lokacin ne na yi tunanin na auri Haleema. Ba don ina jin soyayya irin ta aure a raina ba, a’a, sai don ta taimaka mini wajen kula da ke da yayyenki, tunda ta kasance amintacciyar mahaifiyarku wadda ta san halinku.

Ko da na je mata da maganar, ta yi shiru cike da jin nauyi. Na ce mata ta taimaka mini, ko biyanta ne zan dinga yi ta riƙe mini ke, idan kin ƙara girma sai na sake ta ta tafi abunta.”

Alhaji Kabeeru ya ɗago ya dubi Mommy Haleema da ke kuka a sanyaye, ya ce:

“Amma Haleema ta kalle ni a ranar, ta ce:

‘Zan sadaukar da rayuwata wajen rainonta, Alhaji. Abin da Hajiya ta haifa, zan riƙe shi da amana.’

Ta sa hannu ta karɓe ki daga hannuna, sannan ta sake furtawa cewa:

‘Wallahi, zan kula da amanarki.’

That day, Haleema didn’t just accept you into her arms; ta karɓe ki a zuciyarta ma. Ta ɗauke ki a matsayin ɗiyarta tun kafin ki iya fahimtar ma’anar uwa.

Yara duka suna son Haleema saboda sun saba da ita tun mahaifiyarsu tana raye. Haleema ta zame miki uwa, bango, kuma jigo a rayuwa. Haka yayyenki ba za su taɓa mantawa da karamcinta a gare ni da kuma gare su ba.”

Alhaji Kabeeru ya canza kallonsa a hankali zuwa kan Mommy Haleema, sannan ya dawo kan Inteesar cikin muryar tabbatarwa da umarni:

“Ba ke kika haifi Inteesar ba, Haleema… amma babu wanda ya fi ki sanin darajarta.”

Sannan ya kalli Inteesar da idanunsa da ke cike da hawaye, yana son tabbatar mata da gaskiyar da ta kamata ta fahimta:

“Kada ki taɓa bambanta tsakanin Mommy Haleema da Hajiya Fateema. Duk wanda ya girmama ni, ya girmama Haleema! She deserves that respect, because she has given you the love of a mother without ever asking for anything in return.”

Muna cikin wannan halin na kuka da juyayi, kowa yana ƙoƙarin karɓar ƙaddarar da ta faɗa mana, sai ga ƙofar ɗakin asibitin ta buɗe. Likitan ne ya shigo da sauri, fuskarsa ɗauke da alamun tsawatawa amma cikin ladabi.

Ya kalli yadda dukanmu iyalin muka kewaye gadon Alhaji Kabeeru muna kuka, ya girgiza kansa, sannan ya ce:

“Don Allah, ku yi haƙuri ku fita haka nan. Gaskiya kuna damun patient ɗinmu. Jinin Alhaji yana buƙatar daidaituwa, kuma a halin yanzu yana buƙatar tsantsar hutu, ba hayaniya ko abin da zai ɗaga masa hankali ba. Don Allah ku ba shi wuri ya huta.”

Alhaji Kabeeru ya ɗan lumshe idanuwansa, alamun gajiyawa sun bayyana a fuskarsa. Ya saki hannun Inteesar a hankali, ya yi mata nuni da ta tafi ta huta ita ma.

Cikin sanyin jiki da sanyin gwiwa, Mommy Haleema ta ja hannun Inteesar, yayyenta maza kuma suka bi bayansu. Dukkanmu muka fito zuwa corridor ɗin asibitin, muka bar Daddy yana ƙoƙarin samun ɗan natsuwa da hutu bayan ya sake buɗe tsofaffin raunukan da ya daɗe yana ɓoye wa a zuciyarsa.


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol