Free chapter · Read without an account
Chapter 10
╔══════════════════════╗
🌺🌺 *KOWA DA RABONSA* 🌺🌺
╚══════════════════════╝
🌺 A Story Filled With Lessons, Destiny and Love🌺
✍️
> BY MARYAM USMAN MAMYY WRITER (FULANIN JAJIRTATTU)
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
✨ FIVE STAR WRITERS✨
📞 ***
📚 BOOK 1
📖 Page 5
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
Bismillahir Rahmanir Rahim.
> Wane lokacin kaddara ce take zaɓa maka rabonka, wani kuma rabon nasa ne kaddara. Duk abin da ya zama rabonka dole ne ka yi haƙuri da shi.
~NOTE: Ban yarda da wani ko wata su yi amfani da littafina ba. Ban yi littafin nan da wata ko wani ba. Duk abin da kuka gani mallakina ne, bana so wani ya yi min copy ba tare da sanina ba.~
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Ɗaga mata kai Shatu ta yi tana karɓar chocolate ɗin da take bata.🌺
_______________________
_____________________________________________
A ranar A.Maina ya saka shi a gaba suka je gidansu Hajarah, gida ne na masu matsakaicin karfi, Sunan mai gidan Malam Sani yaransa uku Hajarah ita ce babba sai mai binta Abdul Rahman sai autarsu Halimatu.
Hajarah ta kamu da soyayya M.Madawaki ne tun bayan kammala Degree ɗinta lokacin su M.Madawaki na bikin buɗe sabon kamfaninsu shi da A.Maina MAMUB Group of Companies, ita kuma Allah ya kaita wajen ta yi naci sosai wajen ganin ta samu shiga, amma hakan ya gagara, shi ne ta haƙura ta yi aurenta.
Shekararta uku auren ya mutu lokacin tana da ciki, sai a gida ta haihu, ta haifi yaronta namiji mai suna Nasir, shekarar Nasir biyu mahaifinsa ya karɓe shi, gaje ta yi da zaman gida ta kuma koyarwa a private school na yaran manyan masu kuɗi.
A yawan koyarwarta ne Allah ya kaita school ɗin da aka maida Shatu, da farko su Meerah take ja a jikin sanin su ɗin family Madawaki ne, rana tsaka ta ga M Madawaki ya kawo Shatu a ranar ta yi farinciki sosai, bata taɓa tunanin za ta sake ganinsa ba sai gashi a cikin makarantar da take aiki ya kawo gudan jininsa.
Bayan sun gama magana da shugaban makarantar zai tafi Shatu tana kuka ita ce ta kamo ta tana rarrashinta, tun daga ranar ta koma jan Shatu a jiki tana kawo mata chocolate har ta saba da ita, cikin nutsuwa take cusawa Shatu magana take nuna mata yadda take son M Madawaki.
Bayan rasuwar Ruƙayyah ne ta sake takurawa Shatu da maganar tana so ta zama Mummynta tun da yanzu bata da Mummy tun maganar bata shiga kunnuwanta har Hajara ta yi nasara.
Tun shigarsu gidan Malam Sani M.Madawaki bai yi magana bayan gaisawa da suka yi, A.Maina bakinsa shi ne yake cewa komai, Malam Sani ya amince da su har ya basu damar turo magabatansu, a satin Baba Malam da ƙasaninsa Baba Haruna wanda yake zaune a Gombe shi da Matarsa da suke kira da Anne duk yaransa suna Madawaki Dynasty a zaune shi da matarsa ne kawai a Gombe.
Auren Hajarah Malam Sani ya basu tare da tsayar da rana sati mai zuwa, cike da farinciki suka dawo gida a ranar Shatu kasa cin abincin ta yi saboda murnar samun Mummy sai da M.Madawaki ya dawo Daada ta sanar da shi Shatu bata ci abinci ba.
A falonsa ya sameta ta yi bacci da alamu shi take jira har bacci ya kamta, gyara mata kwanciyar ya yi tare da shiga master bedroom ɗinsa ya jima sosai sannan ya fito cikin shirin kwanciya, kitchen ya shiga yana haɗa mata abu da zata ci marar nauya.
Tashinta ya yi yana rakata toilet bakinta ya wanke mata sannan suka dawo kallonsa ta tsaya yi, murmushi ya yi yana bushe mata ido rufe fuska ta yi tana dariya.
"Abbana ina ta jiranka har na yi bacci."
Yatsan hannunsa ya ɗora saman lips ɗinta yana girgiza mata kai, shiru ta yi san abin da yake nufi, abincin ya fara bata, a hankali take ci tana kallon fuskarsa har ta ƙoshi, coffee ɗin da ya haɗawa kansa ya fara sha cikin nutsuwa kwanciya Shatu ta yi a jikinsa har wani bacci ya sake ɗaukarta.
Sai da ya gama abubuwansa sannan ya kaita nata bedroom ɗin da yake kusa da nasa, tun bayan rasuwar Ruƙayyah ya dawo da ita bedroom ɗin da yake falonsa, ya rufe falon Ruƙayyah tun da ya fahimci Shatu in ta shiga sai ta yi kuka.
Addu'a ya yi mata yana rage ƙarfin AC room ɗin, ɓangarensu Daada ya nufa sanin bata yi bacci ba, a zaune ya same su ita da Anne da suka zo ita da Baba Haruna, gaida su ya yi yana sanar da Daada Shatu ta ci abinci.
A hankali ya fita saboda baya so Anne ta yi masa wata maganar domin ita har tafi Daada rashin haƙura, Anne da Daada Uwarsu ɗaya Ubansu ɗaya kamar yadda Baba Malam yake shi da Baba Haruna, Daada ce babba sai Anne.
__________________
Washegari ranar tun asuba da M.Madawaki ya tashi Shatu, bata koma bacci ba bakin ƙofar master bedroom ɗinsa ta je tana Knocking duk da a buɗe yake amma bata shiga ba domin Mummynta ta hanata shiga, ta ce master bedroom ɗin Abban nata yara basa shiga.
Aiki yake amma dole ya taso sanin ba daina knocking ɗin zata yi ba, a zaune ya sameta idanuwanta duk bacci ɗagota ya yi suna dawowa tsakiyar falon, yana zama ta kwanta a jikinsa tare da cewa.
"Good morning Abbana jiya Baba Malam da Baba Haruna suka ce wai Aunty Hajarah au Mummy za ta dawo gidanmu sati mai zuwa wai haka ne?"
Hannayensa ya saka yana rufe bakinsa tare da yin siririn murmushi, da sauri Shatu ta sauka daga jikinsa tana dariya, shi ma dariyar ya yi yana tashi zai koma bedroom ɗin ta riƙe hannunsa.
" Abbana!"
Juyowa ya yi yana kallon fuskarta.
"Bakin nawa yana wari da yawa?"
Ɗaga mata kai ya yi yana sake rufe bakinsa, dariya ta yi tana shiga bedroom ɗinta da gudu wanke bakinta ta yi tare da yin wanka ta yi shirin makaranta sannan ta dawo ƙofar master bedroom ɗin nasa.
Tana zuwa ta ganshi ya shirya yana ƙoƙarin rufe ƙofar rufe fuska ta yi, ya kamo hannunta suka nufi ɓangaren Daada lokacin da suka shiga duk yaran sun shirya suna zaune a dinning room ɗin, shiru yau dinning ɗin dalilin zuwan Anne duk tsoronta suke daga iyayensu mata har mazan har jikokin gidan.
Sautin maganar Shatu suka ji duk suka juya murmushi suka ga a fuskar M.Madawaki yana kamo fuskarta da take dariya, mamaki wasu daga cikinsu suka domin ganin murmushi da yake, matan yan uwansa za su iya rantsuwa ba su taɓa ganin yana murmushi haka ba sai yau.
Ganin suna kallonsa ne ya saka shi haɗe fuska yana gaida iyayensu da Yayunsa Sayyid Ali Madawaki da Abubakar Ali Madawaki, sune yaran Daada manya sannan sai shi da Hajiya Maryam sai autarsu Hajiya Safiya, duk suna Abuja a can suke aure.
Aminu H Madawaki da Yakub H Madawaki da Fatimah H Madawaki duk yaran Baba Haruna ne da Anne kuma duk M.Madawaki ya fi su Aminu H Madawaki ne ma aka haifesu shekara guda amma dai M.Madawaki yafi shi.
Zama Shatu ta yi tana gaida kowa har yan matan gidan domin ita ce ƙarama, dariya ta yi cikin ƙaramin sauti tana kallon gefen M.Madawaki.
Shamsudeen A Madawaki ne ya taɓo ta suna magana da ido domin tasu ta zo ɗaya, bai fiya magana ba amma yana kula Shatu yana biyewa duk wani shirmeta.
Ƙasa ta yi da murya ta ce.
"Yaya Shamsudeen A Madawaki yau Abbana ya sha warin bakina shi ne yake rufe baki kuma Allah bakina baya wari kawai Abbana ne yake cewa wai mutum baya magana sai ya wanke baki..."
Dariya duk suka yi, suna tsokanarta yau ta zama ƙazama ta yi magana bata wanke bakinta ba, ɓata fuska ta yi za ta fara kuka Anne ta hau masifa, dole suka yi shiru suna cin abincin su.
Suna cikin cin abincin A.Maina ya shigo washe baki Anne ta yi tare da nuna masa wajen zama, dole ba dan ya so ba ya zauna domin shi ya yi breakfast a gida kafin ya fito, gaida iyayensu ya yi yana kallon fuskar Shatu da take turo baki.
"Shatu M Madawaki yau babu gaisuwar?"
Kallon fuskarta M.Madawaki ya yi yana ƙaramin murmushi hawaye ta fara tana nuna masa M Madawaki da ya kawar da kai gefe.
"Abbansu Nadiya wai bakina wari yake yi?"
Dariya ya yi yana kallon M.Madawaki ya san dole shi ne zai faɗa mata haka, sanin abubuwan da yake koya mata da ya shafi rayuwa, tun Ruƙayyah na da rai yake koyawa Shatu tsafta da kula da jikinta cikin hikima.
"Gaskiya duk wanda yake shiga cikin mutane bai wanke bakinsa ba ƙazami ne kuma bakinsa wari yake yi sosai..."
Fashewa ta yi da kuka, cikin jin haushin Daada ta ce.
"Kai Abubakar zo ka fita kai ma Muhammad fita min daga falon kuma bakin Shatu ba ya wuri sai dai naku zo nan Shatu."
Dariya A Maina ya yi yana tashi tsaye ya san halin Daada sai ta kawo duka, a hankalin M Madawaki ya tashi yana fita daga falon kamar yadda Daada ta buƙata, Baba Malam A Maina ya kallo yana sosa kansa ya ce.
"Uhm Baba Malam,Baba Haruna wai ya maganar ne mun ji shiru ga tafiya ta kama mu."
Shamsudeen A Madawaki ne ya kalle yaran masu school ya ce su fito yau shi zai rakasu da farinciki duk suka fita har Shatu da take hawaye, shi ne ya raka su school ɗin sannan ya tafi wajen aikinsa.
A Maina kuwa bayan Baba Malam ya bi zuwa falonsa, bayani ya yi masa na auren Hajarah da aka basu har ranar da aka tsayar domin ɗaurin aure, godiya A Maina ya yi musu sannan ya shiga ɓangaren M Madawaki.
Tattaunawa suka akan business ɗinsu sannan A Maina ya yi masa bayanin da Baba Malam ya yi masa, ko ɗago kansa bai yi, murmushi kawai A Maina ya yi, suka koma batun tafiyarsu US da zasu yi a cikin satin nan.
____________________________________________________________________________________
A satin da aka saka a ranar aka ɗaura auran lokacin M Madawaki baya ƙasar amma ya ba da duk abin da ake buƙata haka suka yi bikinsu babu shi har amarya ta tare bai dawo ba.
A ɓangaren Ruƙayyah ta tare amma sai da aka sake komai har fenti, Shatu tana murna a ranar farko a ɗakin Hajara ta kwanta, haka ma rana ta biyu sai da ta yi sati guda suna kwana da Hajarah sannan Daada ta fara faɗa aka tana kwana a ɗakin, kuma har lokacin M Madawaki bai dawo ba.
Hajarah nunawa Daada ta yi babu komai dan Shatu ta kwana a ɗakin nata, Anne ce ta saka baki tana nunawa Hajarah hakan bai kamata ba.
A ranar Rahmah ta shigo gidan ita ma ta nuna wa Hajarah hakan bai kamata ba, murmushi kawai Hajarah ta yi a zuciyarta tana cewa dole ne ta kwana da Shatu tun da shi wanda yake auren nata bai da lokacin kwana da ita.
Faɗan da suka yi wa Shatu ne ya sakata a ranar ta koma ɓangaren M Madawaki ta yi kwanciyarta, cikin dare M Madawaki ya dawo babu wanda ya sani sai Shatu da ya shiga bedroom ɗinta tana ganinsa ta tashi zaune tana rungumeshi.
Saman gadon nata ya hau yana kallon fuskarta.
"Welcome Abbana,Mummy ta dawo da baka nan kullum a bedroom ɗinta nake kwana yau kuma Daada ta yi faɗa na dawo nan."
Hancinta ya ɗan ja yana gyara mata gashinta da ya rufe mata fuska.
"Eshaa!"
Dariya ta yi tana kwantar da kanta a cinyarsa.
"One week kenan bakya zuwa islamiyya school and..."
"Sorry Abbana Mummy ta ce na huta akwai gajiyar biki a jikin.."
"Shii bana so ki kula, ita da ta hanaki ita ce ta saka ki?"
Shiru ta yi a jikinsa, ganin rainsa ya ɓace, haƙuri ta sake bashi har ta yi bacci tana bashi haƙuri.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Washegari ranar sai ganinsu aka yi tare sun fito kamar yadda suka saba hannunsa cikin nasa, sakin baki Hajarah ta yi ganinsu tare.
Har suka zauna tana kallonsu, muryarsa ce ta dawo da ita daga duniyar tunani, Baba Malam ta ji yana gaidawa sannan ya gaida Daada da su Abubakar Madawaki.
Gaida shi ta yi tana kallon fuskarsa, ba tare da ya ɗago ba ya amsa yana nunawa Shatu ta haɗa masa coffee, tashi ta yi domin ta haɗa masa, Hajarah ta zaunar da ita tana murmushi haɗa masa ta yi tare da miƙa masa Shatu ce karɓa tana dariya.
A gabansa ta ajiye tana masa magana a kunne "Abbana ka kalle kwalliyar Mummy ta yi kyau."
girgiza kansa ya yi yana zaunar da ita, baki ta turo tana ɓata fuska, serving ɗinsu Baba Jamila ta yi sannan suka fara breakfast ɗin kallon fuskar M Madawaki Hajarah take ganin babu abun aka zuba masa, iya coffee da ta haɗa yake sha.
Hajarah kasa ɗauke idanuwanta ta yi daga kan M Madawaki abu ɗaya ta lura,shi ne yadda Shatu take manne da shi, tana magana ƙasa ƙasa kuma da alama sauraronta yake.
Shi ne ya fara miƙewa tsaye da saurin Shatu ta tashi tana kallon Daada.
"Bey Daada mun tafi school ni da Abbana Meerah ku zo mu tafi."
Tashi duk yaran suka yi suna fita da gudu, hannayensa Shatu ta riƙe yana magana da Abubakar Madawaki, sai da ya gama sannan Shatu ta kalle Hajarah tana yi mata sallama, dole ce ta saka Hajarah yin murmushi tana ɗaga mata hannu har suka fita.
A ranar Hajara yinin farinciki ta yi, falonsa da Shatu ta nuna mata ta shiga, gyara falon ta yi tana shiga bedroom ɗin Shatu wanda shi ne yake a buɗe domin nasa kullum a rufe yake ko yana ciki, kayan Shatu da ta ga a wardrobe ne ya bata mamaki, sanin nan ɗin ɓangarensa ne.
Haka ta gyara komai, sannan ta fito bedroom ɗinsa ta taɓa ta ji a rufe, Baba Jamila ta kira tana tambayar wanne ne bedroom ɗinsa,shiru Baba Jamila ta yi domin ita tun da take ba taɓa shigowa falonsa ba sai yau ɗin da Hajarah ta shigo da ita, suna tsaye sai ga Shatu ta shigo da gudu tsayawa ta yi tana kallonsu, ganin suna tsaye a bakin ƙofar master bedroom ɗinsa.
Baki na rawa ta ce.
"Abbana ne ba shi da lafiya? Baba Jamila me ya shigo da ke falon Abbana? kai! kai! kai! to sai na faɗa masa na ce da Mummy da Baba Jamila sun shigo masa falonsa har.."
Rungumeta da Hajarah ta yi ne ya saka yin shiru tana murmushi.
" Welcome My Angel."
Da sauri Baba Jamila ta fita jikinta na rawa,domin bata son abin da zai haɗa ta da uban gidan nata, kuma ta san halin Shatu sai ta faɗa masa.
Shatu kuwa Hajarah ce ta yi mata wayo ta manta da maganar, ita ce ta taimaka mata ta shirya, sannan suka shiga kitchen ɗin falon, abincin mai rai da lafiya Hajarah ta yi,Shatu na yi mata surutu, cikin dabara Hajarah ce take faɗawa Shatu za ta dawo bedroom ɗinta suna kwana tare farinciki ne ya kama Shatu sosai ta rungumeta tana dariya.
Sai bakwai da arba'in suka gama aiki sannan Hajarah ta koma falonta ta kwaso wasu daga cikin kayanta ta dawo da su bedroom ɗin Shatu domin samun kusanci da mijin nata, wanka ta shiga ita kuma Shatu ta gama shiryawa tana karatun Alkur'ani wanda Baba Malam zai karɓi hadda karfe tara na dare.