Free chapter · Read without an account

Chapter 11

by Narrnarhh Bukar · BA NI DA MADOGARA

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*















*Bani da Madogara*
  (Sai Allah...)





 


011

Sosai Tahseen taba mahaifiyarta tausayi don tasan tun tasowan Tahseen take mutuwar son Arqam yaron yayanta Alhaji Imran, amma shi ɗan shegiyar yana bin zugar mahaifiyarsa Hajiya momma shi yasa baya sonta, bazata bari tilon ƴarta ta halaka ba saboda soyayya, dole ta yi wani abu, wannan dole ne. Kwanto da Tahseen mom tayi a jikinta tare da shafa mata baya cikin sigar lallashi ta fara magana

"It's ok Tahseen kisa a ranki Arqam naki ne ke kaɗai, zan yi maganin Hajiya momma da kanta za ta tirsasa shi ya aure ki ko baya so, cikin ruwan sanyi zan yi maganin ta bara na kira Hajiya Lubna" 

Ɗaukar waya ta yi ta kira aminiyarta Hajiya Lubna,tana ɗauka bayan sun gaisa ta ce

"Malamin nan da yake miki aiki, aikinsa na da kyau kuwa" 

A can Hajiya Lubna ta ce

"Sosai ma Kuwa Hajiya Ramla, wa kike so ayi ma aikin?" 

"Matar Yayana Hajiya momma nake so ayi ma aiki, Tahseen na mutuwar son ɗanta Aqram amma shegiyar matar nan don ta ga tana da dukiya shi yasa ta hana ya aureta, Ina so ayi mata aiki, a tursasata ita da kanta ta umurci yaron ya auri Tahseen" 

A can Hajiya Lubna ta ce

"Angama matar senata, zuwa jibi za ki ganni" 

"Yawwa aminiyar, don yaron saura kwana biyar ya dawo ƙasar nan, Ina so kafin ya dawo ayi mata aiki, daya dawo sai ta bijiro masa da maganar auran Tahseen, nasan zai aminci tunda baya saɓa umarninta" 

Ci gaba da tattauawarsu suka yi daga bisani suka yi sallama. Duban Tahseen ta yi sannan ta ce

"Kwantar da hankalinki kin ƴar gold ɗin Dadinta, kisa a ranki Arqam naki ne ke kaɗai, kamar yadda ban zauna da kishiya ba, Kema gidanki ke kaɗai ce babu wata shegiyar da ta isa ta shigo ciki" 

Murmushi Tahseen ta saki tare da rungume mahaifiyarta tana cewa

"You are the best mom ever in this world,I'm so so glad having you as my Everlasting mom, na gode sosai" 

Miƙewa  Tahseen ta yi tana murna har da rawa a gaban mahaifiyarta, ita kuma sai dariya take ganin ɗiyarta ta koma normal, haka take so akodayaushe tana ganin farin ciki shimfiɗe a fuskar tilon ɗiyarta. Tana rawa Tahseen ta ce

"Mom in few months I'm gonna be the wife of multi billionaire Arqam Imran Abdulfatah Gadau, wayyo Allah daɗi, zan taka wanda na so, na wulaƙanta wanda na so hankali kwance!, Ho ni Tahseen ɗiyar Senata! " 

Babu abinda Hajiya Ramla take sai dariya da farin ciki, suna a haka Senata ya shigo cikin falon. Ganin ahalin nasa cikin farin ciki da annuri sai fuskarsa ta faɗaɗa da murmushi har ya ƙaraso cikin falon. Tahseen na ganin Daddynta ta ruga da gudu kamar wata yarinya ƙarama ta rungumeshi tana faɗin

"Oyoyo Dad I will soon be the wife of multimillionaire Arqam Imran Abdulfatah Gaɗau" 

Fuskar Senata ɗauke da farin ciki ya ce

"Oh really my princess! Ya dawo ƙasar ne?" 

Girgiza masa kai Tahseen ta yi tana cewa

"In five days coming zai dawo Nijeriya" 

Yana maganar yana zama kusa da matarsa Hajiya Ramla. Dubanta ya yi tare da sakin murmushi yana faɗin

"Gimbiyar mata ki ce ƴar Gold ɗina is about to hatched" 

Mayar masa da martanin murmushin ta yi sannan ta ce
"Very soon kuwa tana son shi sosai, baka ga zallar farin cikin dake kwance a kyakkyawan fuskar ta ba" 

Juyo da kansa ya yi wurin Tahseen wacca har yanzu rawa take tana murna, Sannan ta ce

"Haka nake so naga ɗumbin farin ciki shimfiɗe a kyakkyawar fuskarta akodayaushe, Wai kin je gidan ɗayan yayan naki kuwa,da safe  yake faɗamin jikin Sabrin ya tashi"

"Laah wallahi ban ji ba, ko jiya munyi waya da Hajiya mariya har tana faɗamin Akmal jibi zai dawo Nijeriya ya kammala Masters ɗinsa Amma bata sanar min da jikin Sabrin ya motsa ba, ai da kuwa na je yau na dubata, baiwar Allah ciwo sai wahalar da ita yake, kasan masu sickle cell basa son lokacin damina saboda ciwonsu akai-akai yake tashi" 

"Ai yau da safe ciwon ya tasar mata,yanzu haka suna asibitin da ake dubata an kwantar da ita, sosai Sabrin take bani tausayi" 

"Dad Sabrin ce bata da lafiya? " cewar Tahseen wacca ta daina rawar jin cousin ɗinta bata da lafiya sai ta dawo suka da iyayenta tana tambayarsu

Mom ce ta gyaɗa mata kai, lokaci guda fuskarta Tahseen ta sauya daga yanayin farin ciki zuwa yanayin baƙin ciki, cike da damuwa ta ce

" Mom tare zamu je dubata daman two days na rabu da zuwa gidan Uncle Ayyub" 

"Ai an kwantar da ita a asibiti, yanzu dai je ki canja kaya ki zo mu ta fi asibitin mu dubata har da Daddynki" 

Babu musu ta ruga sama  ɗakinta a gurguje ta shirya  cikin wani arnan English wear brown colour doguwar riga, surar jikinta a bayyane saboda kayan sun matseta sosai sai ɗan wani yalolan gyale ta dauko ta yi rolling, high mai tsini ta saka tare da ɗaukar handbag ɗinta bayan ta saka sophisticated iPhone ɗinta  ciki ta fito. Tafiya take takalminta na bada sautin Kwas! Ƙwas! Har ta iso wurin iyayenta wa'inda ita suke jira su wuce. Basu damu da shigar dake a jikinta ba sai ma yaba kyawun da ta yi suke. Hajiya Ramla ce ta umurci masu aikinsu wasu ayyuka da za su yi kafin ta dawo sannan suka bar falon. 

    Suna fitowa bodyguard suka taka musu baya  zuwa wurin parking ɗin motoci. A wata Benz baƙa sabuwa wacca ake yayi wani bodygaurd ta buɗe musu suka shiga, sannan ya dawo front sit ya zauna, daman sauran bodyguard ɗin sun daɗe da shiga sauran motocin sai mai gadi ya hangame musu tanƙameman gate suka fita. Motocinsu na jiniya har suka je private hospital ɗin da ake duba Sabrin idan ciwonta ya tashi, tun a hanya Hajiya Ramla ta kira matar yayanta Ayyub akan suna hanyar zuwa asibiti gaishe da Sabrin. Bayan sun shiga asibitin motocin sun yi parking a inda aka tanadar, sai bodyguard ɗin nan ya fito da sauri ya buɗe musu ƙofar suka fito, kai tsaye suka nufa cikin asibitin zuwa wani ƙayattacan ɗakin da ake duba Sabrin idan jikinta ya motsa.Asibitin masu kuɗi ne sosai, sai wanda ya ci sunansa mai kuɗi yake zuwa asibitin don akwai ƙwararrun ma'aikata sosai har da turawa, basu da matsalar kayan aiki, asalin mai asibitin Ba'indiye ne hakan yasa masu kuɗi suke rige-rigan kawo ahalinsu saboda sun san ko a ƙasar waje sai haka. 

Har ɗakin da aka kwantar da Sabrin suka shiga,babu ko sallama suka shiga ɗakin, ahalin Sabrin ne  a ciki dukkaninsu,  sai  a sannan ne naga ashe Alhaji Sambo Dala ne da ahalinsa, yana zaune kusa da gadon Sabrin, Hajiya Mariya wacca ta kasance matar Alhaji Sambo dala uwa ga Sabrin tana zaune a ɗayan kujerar da yake kusa da Alhaji Sambo Dala, ƴarshi ta biyu mai suna Sakhiya na zaune a wata cushion a ɗakin kasancewar babban ɗaki ne mai ɗauke da kujeru da gado ɗaya wanda marar lafiya zai kwanta. Har da wurin cin abinda akwai a ɗakin da bayi mai kyau da tsafta. Fuskar Alhaji Sambo Dala ɗauke da murmushi yaba abokinsa hannu suka yi musabaha tare da nuna mishi wuri kusa dashi ya zauna. Ita kuma Hajiya Ramla sai ta je gun aminiyarta kuma matar yayanta wanda suka fito ciki ɗaya ta zauna kusa da ita suna gaisawa. Tahseen kuwa da gudu ta je gun favorite cousin ɗinta suka rungume juna, sosai suke rungume da juna kamar wani zai ɗauke ɗayansu, jikinsu a manne har na wani lokaci sannan suka cire jikinsu tare da sakin murmushi lokaci guda. Kasancewa sun yi nesa da idan iyayensu suka zauna sai hakan ya basu damar tattaunawa wanda iyayensu ba jin abinda suke cewa suka yi ba. Tahseen ce ya dubi Sakhiya ta ce

"My love na yi matuƙar missing ɗinki sosai wallahi, in fact gangan jikina a buƙace take dake" 

Riƙo hannun Tahseen Sakhiya ta yi fuskarta ɗauke da murmushi ta ce

"Bake kaɗai ba my love nima nan na yi missing ɗinki sosai, my soul is missing you too" 

"Kinsan jiya wallahi har mafarkinki sai da na yi, you are just incredible, ummm yau ma za ki club kuwa" cewar Tahseen tana ƙara mannewa cikin jikin Sakhiya 

"Mai zai hana Love" 

Murmushi Tahseen ta saki har haƙoranta farare na bayyana ta ce

"Let's make love kawai a can, koya kika ga" 

"Shiyasa nake matuƙar sonki Tahseen kin san kan daɗi, shi kenan sai mun haɗu" 

"Yawwa ya jikin Sabrin ɗa zu Dad ya ce kuna asibiti, Ina cikin farin ciki Mom ta min alƙawarin auran ya Arqam sai na ji Dad na cewa yau da safe ciwon Sabrin ya tashi" 

Tsaki Sakhiya ta yi tare da cewa

"Wai ke har yanzu ba za ki haƙura da Ya Aqram bane duk wulaƙancin da yake miki amma kina nan kina dakon sonsa, Haba kamar ba classy lady ba handsome guys nawa ne ke rushing ɗinki amma kin wani damu kanki da wanda bai san ma kina yi ba" 

Murmushi Tahseen ta yi tana duban Sakhiya ta ce

"Baki san What is called love bane Sakhiya, da kin san soyayya da baki ce haka ba, mata kawai ƴan uwanki kika sani" 

Gyara zama Sakhiya ta yi tare da ajiye wayar sannan ta ce

"Nasan mene ne so mana Tahseen amma ki gane *Son masu wani ƙoshin wahala ne* kin manta ba mata kaɗai nake making love dasu ba, har mazan ma wani lokacin ina yi dasu, idan naga handsome and classy guy naka yi making love dashi Sai dai ban yarda sonshi ya ɗarsu a raina" 

"Hakane kuma amma Mom ta yi min alƙawarin auransa ai" 

Murmushi Sakhiya ta yi cike da farin ciki ta ce

"Idan Hakane na taya ki murna sosai wallahi, saboda samun gwarzon namiji kamar Ya Arqam ɗaya tamkar dubu wahala ne, nima wani lokacin yana burgeni sai dai wulaƙancinsa yasa bana shiga harkarsa idan na je gidan Uncle Imran" 

Nan hira ta ɓarke a tsakaninsu wanda yawancin akan Arqam ne da kuma sharholiyar da suke a night Club. 

A wurinsu Hajiya Ramla da Hajiya Mariya hira ce ta ɓarke a tsakaninsu wanda yawanci akan ci gaban yaransu ne. Su kuma Alhaji Sambo Dala da amininsa wanda yake auran ƙanwarsa Senata suna hira akan  siyasar su cw. Baiwar Allah Sabrin an saka mata Oxygen lokaci guda ana mata ƙarin jini sai bacci take tare da taimakon Oxygen ɗin da aka saka mata. Wannan Kenan... ✍️

           🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*International Conference Centre Musa Usman Secreteriat Maiduguri, Borno State. Nijeriya*

Wani katafaran hall ne babba wanda ke ɗauke da ɗumbin mutane masu faɗa aji a jahar tare da manyan malamai masu bada gudunmuwa a ci gaban addinin musulunci da zaman lafiyar jahar. Wannan taron an assasashi ne saboda aba manyan malaman addinin musulunci wa'inda suke bada gudummawansu a ƙarƙashin jagorancin gwantin jahar.Manyan mutane kama daga ƙusoshin gwamnati, manyan ƴan kasuwa da sarakunan jahar sun halarci taron. Mai bama gwamna shawara ta fannin tsaro ya amshi mic ɗin aji  daga hannun Mc. Bayan ya yi dogon jawabi akan ci gaban da manyan malam suka kawo musamman na ganin zaman lafiya ya wanzu a jahar sannan ya ƙara da cewa

"Amadadin His Excellency za a karrama malaman tare da basu lambar yabo, yanzu ba tare da ɓata lokaci ba zamu fara kiran su, daga cikinsu akwai gwarzo mai taimakawa al'umma ciki da wajan jaha, malamin addini, shehin malami wato *SHEIKH MUNNIR HALADU ALMISRIYY* saboda gudunmuwar da yake badawa don ganin tsoro ya wanzu a jahar"

A cikin dubban mutanan Sheikh Munnir Haladu Almisriyy ya fito zuwa inda zai amsa lambar yabon,Sheikh Munnir babban malami ne ya sha babbar riga, irin manyan mutanan nan ne masu tsawo da ƙiba don ya ma aje tumbi, ya tara ƙasumbi mai ɗauke da furfura, a hannunsa na hagu agogo ne na silver mai kyau sai a yatsar ta manuniya ƙaton zobe ne mai kwalliya maciji, hular dake kansa ma abin kallo ce, don in ji Hausawa da suka ce abu namu ai maganin a kwaɓemu,ƙwararrun masu ɗinka huluna a  garin maiduguri suka ɗinka hular, baƙi ne sosai, cike da izza ya taka zuwa wurin tare da amsa lambar yabo wanda gwamna da kansa ya bada. Haka aka ci gaba da gudanar da taron ana kiran manyan malamai tare da karramasu saboda rawar ganin da suka taka a jahar. Daga bisani bayan anci an sha sai kowa ya kama hanyar garinsa. Shi ma Sheikh Munnir a rantsattsaiyar motarsa mai lumfashi ya wuce garinsu. 

     🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Legacy Housing Estate, Bulunkutu, Maiduguri, Borno State. Nijeriya*

A wani ƙayattacan gida wanda da yafi kowanne gida kyau da tsari a duk faɗin Estate ɗin, Sheikh Munnir ya shiga da motarsa ciki bayan mai gadi ya buɗe masa gate,fitowa ya yi daga motar tare da shiga cikin gidan. Babba   ne gidan sosai  mai hawa biyu,ya sha fenti ga parking load da garɗen ma'aikata sai ban ruwa suke ma flowowin kasancewa yamma ta yi.Yana shiga cikin falon sai wasu yara wa'inda basu wuce shekara huɗu ba ƴan biyu masu *ƙusumbi* a bayansu suka rugo da gudu  tare da rungumesa suna cewa

"Oyoyo Papy" 

Ɗaya bayan ɗaya ya ɗaukesu yana murmushi tare cillasu sama suna dariya. Wata kyakkyawar mata ce mai zubin Laraba,ƴar jinsin shuwa Arab ta shigo falon tare da yi masa sannu da zuwa. Riƙo hannunsu ya yi suka ƙaraso cikin falon, Zama ya yi sai ya ɗaura yaran saman cinyarsa yana musu wasa suna dariya. Matar ta dubi Sheikh Munnir ta ce

"Har kun dawo, ya taron? Fatan kun tashi lafiya kuma cin nasara" 

Still yana musu wasan ya amsa mata da cewa

"Taro ya tashi lafiya ina Halima  take" 

Taɓe baki matar  ta yi sannan ta ce

"Tana cikin ɗakinta tana kukan da ta saba" 

Daina ma yaran wasa ya yi sannan ya dubeta da cewa

"Au har yanzu bazata haƙura da zaɓin da na yi mata ba, ta manta dokar gidan ko" 

"Tana sane da dokar ai ba komai ke damunta ba illa iskanci, tana so ta nuna bamu isa da ita ba, sai wanda take so shi za ta aura ba zaɓinka ba"

"Turomin ita yanzun nan" iya abinda ya faɗa kenan sai ya ci gaba da yi ma yaran wasa. Miƙewa ta yi zuwa sama har ɗakin Halima . Babu sallama ta banko ɗakin,Halima dake t zaune ta yi ta gumi tana tunanin mahaifiyarta wacca ta kwanta dama a sanadiyyar haihuwata ta yi saurin ɗagowa ta dubi kofar. Tsaye take tana cillo mata wata uwar harara.Halima tun ɗagowanta na farko bata sake ɗagowa ba. Cike da izza matar ta ce

"Papy na jiranki a main falo" sai ta juya ta fice abinda. Miƙewa Halima ta yi sai ta fito zuwa ƙasa inda mahaifinta ke kiranta.Kyakkyawa ce sosai mai matsakaici tsawo wacca bazata wuce shekara 26 a duniya ba , fara tar! Kamar ɗiyar Larabawa ga hanci har baka, doguwa riga ce a jikinta sai ta yafa ɗankwalin rigar wanda kana iya kallon yalwataccan gashinta baƙi siɗik har gadon bayanta. A hankali ta tako har zuwa falon da mahaifinta yake. A zaune ta sameshi yana wasa da ƴan biyu, zama ta yi a ƙasa tare da gaidashi. cike da kulawa Sheikh Munnir ya amsa Mata tare da jefo mata tambaya

"Halima yanzu ban isa na zaɓa miki miji ba kamar sauran yarana sai zaɓinki? Eh!" 

Da ɗan zafafe ya ƙarasa maganar,cikin sanyin Murya Halima ta ce

"Papy ai na haƙura" 

"Mamy ta ce kina can kina kuka" 

Ɗan ɗagowa ta yi suka haɗa ido da Mamy sai kawai ta yi murmushin gefan baki sannan ta ce

"Na tuna daMahaifiyata  ne sai hakan ya saka ni kuka amma ba zancen aure ba" 

"Au saboda baki ɗauke ni a matsayin mahaifiyarki ba shiyasa kike kuka, duk abubuwan da nake miki na alkhairi tare da jawo ki a jikin da nake bana bambamtaki da yarana duk bai yi miki ba, Na gode!" cewar Mamy tana matsar ƙwalla na ƙarya 

Sheikh Munnir ya dubi Halima ya ce

" Ita rayuwar nan da kike gani ƴar haƙuri ce, kamar yadda Mamy ta ɗaukeki a matsayin ƴarta, ya kamata ace Kema kin ɗauketa a matsayin mahaifiyarki, hakan shi ne daidai Halima "

"To Papy in shaa Allah zan gyara"

"Yawwa yanzu tashi ki shiga ciki" 

Miƙewa ta yi zuwa ciki, Mamy da mugun kallo tabi Halima dashi a ranta bata so Sheikh Munnir ya tsaya akan wa'azi ba, ta so ya zazzageta mata masifa tare da nuna mata dole ta bita ko taƙi ko ta so. Ɗaki Halima ta koma sannan ta ɗauki wayanta ta shiga bayi ta kira wata lamba, ring ɗaya aka ɗau kiran, muryar ta can ƙasa ta ce

"Ya Abdul ina cikin matsala, aure na da yaron ɗan majalisa Papy yake son yimin, The worse part Ya Abdul Shi ne yana da Ego da mugun hali, Ya Abdul ku taimake ni kar Papy ya auramin shi, I hate him Ina da wanda nake so, please" 

A can Ya Abdul ya ce

"It's ok Halima shi saurayin naki is he from good home, Sannan yana da tarbiyya kuwa" 

"Eh Ya Abdul school mate ɗina ne, tare muka kammala school a Dubai" 

A can Ya Abdul ya ce

"Ok zan yi bincike sannan zan faɗama Mom idan yana da hali mai kyau Fine sai mu zo nan Maiduguri mu samu Papy da batun amma idan bai da hali Nothing we can do, Sai dai baza mu yarda a matsayinmu na ƴan uwan mahaifiyarki muna gani a aura miki tumun dare ba don haka ki kwantar da hanakalinki My Dear, babu mai aura miki wanda bakya so"

Sosai Halima ta ji sanyi a ranta saboda tasan Ya Abdul he will be serious about it, zai yi ruwa da tsaki wurin ganin bata aure yaron ɗan majalisar in dai ya gano ba mutumin kirki ba. Fitowa daga bayin ta yi sannan ta hau gadonta kwanta. 

A falo bayan Halima ta koma sama sai Sheikh Munnir ya sauke yaran tare da haurawa sama zuwa ɓangarensa. Babba ne part ɗinsa duk yafi kowanne part kyau, yana shiga bai zarce ko'ina sai a ƙarshen part ɗinsa daidai wani bango ya tsaya nan take   ya murɗa zobensa lokaci guda ya ɓace... ✍️

🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Giwa, Zaria city. Kaduna state. Nijeriya*

A ɓangaren Hannatu bayan Innayi da ƴan uwanta sun yi mata nasiha akan mugun halin da take yi, sai daga bisani suka ɓarke da hirar yaushe gamo. Sun ɗaɗe suna hira har jikarta ta ɗaura sawwan rana, bayan ta kammala girki suka ci abincin. Muntari tuntuni yabar gidan zuwa wurin malaminsa wanda ya yi sa a yana gida. Bayan sun gaisa sai ya faɗa masa abinda ya kawosa, bai ɓoye masa komai ba. Shi kuma malamin ya ce babu matsala zuwa anjima da daddare a kawo Jamilu gidan ya dubashi, sosai ya shiga yi masa godiya sannan ya koma gidan don sanar musu abinda malaminsa ya ce. 

Hmmmm zo kuga yadda Hannatu take farin ciki jin yaronta zai koma daidai, har ta kasa misalta ɗumbin farin cikin da take ciki. Har kusan ƙarfe 3:23pm tana Giwa daga baya ta shirya zuwa gida. Sosai Innayi ta sake mata faɗa akan ta canja hali sannan ta zauna da kowa lafiya. Kar ta sake bin kowa da sharri domin yanzu taga aya akan ɗanta. Alƙawari Hannatu ta ɗaukar ma Innayi akan daga yau za ta canja, tana fita sai ta ƙarasa cikin kasuwar garin ta yi siyayya har dasu Mammin Hujayrah ta yi musu siyayyan kayan miya, don ta ɗaukarwa a kanta alƙawarin bazata sake zuwa wurin boka ba ko kuma yi ma wasu mugunta. Laifukanta na baya ma yanzu za ta ci gaba da neman yafiya wurin mahaliccinta sannan za ta samu wata sana'a ta fara wanda kuɗi zai dinga shigo mata don ta rantse bazata sake amsar ƙudin hannun mijinta ba saboda tasan ƙudin haram ne. Tana gama siyayya ta hau mashin zuwa tasha sannan ta samu motar Kaduna ta shiga daman mutum ɗaya ya rage sai motar ta tashi. 

      🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Kwana kwara ƙwai, Kaduna state. Nijeriya*

Sai wurin magrib Hannatu da iso gida, kai tsaye ta wuce sashenta da yake tasan autanta Faisal yana wurin Harira, tun safe  tya ce can zai je mata wuni shi kuma Alhaji Zakari lokacin da take Giwa ta sanar masa akan Jamilu ne bashi da lafiya, Innayi ta kira ta akan ta zo, bai wani damu ba sai ya ce Allah ya ƙara sauƙi zuwa   anjima Anjima zai kira ya ji ya jikin nashi. Bayan ta buɗe ƙofarta ta shiga , sai ta ajiye kayan miyanta a kitchen, Wanda za ta ba mamminsu Hujayrah sai ta bar shi a falon. Kasancewa har an fara kiran sallah sai kawai ta shiga bayi ta ɗauro alwala don yanzu har sallah ma ta ce za ta dinga yinta a cikin lokaci. 

Bayan ta idar da sallah sai ta ɗora girkin dare, kan kace me har ta kammala da yake taliya ce ta girka musu. Abincin ta saka a food warmer ta ajiye a Centre Table na falo, Sannan ya shiga bedroom ta ɗauki hijab ta saka ta fito falon. Kayan miyan data ajiye ta ɗauka sai ta fito tare da rufe ƙofarta ta tafi sashen Mammin Hujayrah, ta daɗe rabonta da sashensu Mammin, tana tunanin tun haihuwar Haroon rabonta da sashen. Da sallama a bisa labɓanta ta shiga ciki, lokacin Mammin na girki sai ta amsa mata da mamaki a fuskarta wanda ya kasa ɓoyuwa. Ɗan murmushi Hannatu ta yi sannan ta ce

"Nasan za ki yi mamakin ganina sashenki Zaytuna, alkhairi ne ya kawoni ba sharri ba, idan da hali ko zamu iya shiga ciki don magana na zo muyi" 

"Maa shaa Allah, bismillah mu shiga ciki" tana maganar tana yi mata jagora zuwa cikin ɗakin. Abbu na  kan darduma yana lazimi suka shigo ɗakin, daman Salim ke taimaka mishi zuwa masallaci tun da suka tafi da Baba Musa sai ya zamana a gida yake sallah shi da Haroon. Amsa musu ya yi sai Mammi ta ce mata 

"Bismillah ga wuri" 

Babu musu ta zauna fuskarta ɗauke da murmushi, Mammi ma wuri ta samu ta zauna, Hannatu ce ta ce

"Zan so Fatsima na nan zan yi maganar, don Allah ki ɗan aiki Haroon ya kirata " 

Aikan Haroon Mammi ta yi ya kira mata Fatsima, ba a fi minti biyar ba suka shigo a tare. Ita ma wuri ta samu ta zauna, gaisawa suka yi sannan ɗakin ya yi shiru can sai Hannatu ta katse shirun da cewa

" Ummm daman na zo ne wurinku domin neman yafiya a gareku akan abubuwan da na yi muku a baya marasa daɗin faɗa, don Allah ba don ni ba ku yafe min sharrin shaiɗan ne, in shaa Allahu daga yau ina so mu koma tsintsiya maɗaurinki ɗaya, nasan ni mai laifi ce a gareku baki ɗaya to yanzu na zo ta ƙoƙon barana akan ku yafe min"

Shiru ɗakin ya yi kowa na karanta nasa watsiƙar zakin, zuwa can sai Mammi ta faɗaɗa murmushi sannan ta ce

"Haba Innar Harira baki min komai ba, idan ma kin yi na yafe miki duniya da lahira, daman zaman tare ya gaji haka, zo mu zauna zo mu saɓa, kar ki ji kin wani damu na yafe miki Allah ya yafe mana baki ɗaya" 

Ita Fatsima maganar ɗaya ce akan ita ma ta yafe mata Allah ya yafe musu baki ɗaya. Sosai Hannatu ta shiga farin ciki mara misaltuwa, ji take kamar an sauke mata dutsen Uhudu daga kafaɗunta, jinta take kamar yanzu ta fara rayuwa da can matacciya ce. Sosai ta shiga gode musu tana murna. Abbu ma hakan take a wurinsa, shima ya ce ya yafe mata. Sun ɗan ɗaɗe suna hira daga bisani kowa ya wuce ɗakinsa... ✍️

🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Gida dubu, Gubi Housing Estate, Bauchi state. Nijeriya*

A ɓangarensu Hujayrah bayan mai yi mata Lesson ya wuce. Zuwa can da rana Razina ta dawo daga School, a gurjuje suka shirya zuwa gidan Hajiya Nafisa, shigar dogayan kaya suka yi kala ɗaya sannan suka nufi part ɗin Hajiya momma don amsar saƙo. Hujayrah ta sha baƙin glass fashion one wanda baya nuna ƙwayar ido. Ita kuma Razina ta saka farin glass shi ma fashion one sosai suka fito gwanin ban sha'awa. Da sallama suka shiga falon Hajiya momma lokacin tana zaune tana Karatun jarida,ɗagowa ta yi ta zuba musu ido tare da sakin murmushi ta ce

"A'ahh ƴan matan nawa ne haka Maa shaa Allah Tabarakallah, a gaskiya zan ci kuɗin samari, auranku sai mai dollars ko sterlings" 

Dariya suka yi, Hujayrah har da rufe fuskarta ita ga mai kunya. Takowa suka yi zuwa inda take zaune Still fuskarsu ɗauke da murmushi. Razina ne ta ce

"Mom bamu saƙon sauri muke kar mu yi dare, Kin san gidan Aunty Nazima akwai daɗin zama, kar muje dare ya yi ma" 

"To shanshani mai ƙafar yawo daman na fito da saƙon, gashi ki kaima Hajiya Nafisa sannan Kice ina gaida ta" 

Tana maganar tana miƙa mata wata babbar leda wanda bansan meke ciki ba. Amsa ta yi sannan suka fito zuwa parking load, daman driver su Yake jira suna shiga ya taba mota suka bar gidan. 

Sun daɗe suna tafiya daga bisani suka iso unguwarsu Hajiya Nafisa,wata mota ce a gabansu lokacin da suka shigo unguwar, tana gaba suna biye. Ashe motar gidan da za su je nan motar ta shiga. Tana shiga sai mai gadin ya jira motarsu Hujayrah ta shiga sannan ya rufe gate ɗin. A kusan tare suka fito da mai motar. Hujayrah na fitowa ta yi arba da Mas'ud. Ai bata san lokacin da ta kira sunansa da ƙarfi tana faɗin

"Yaa Mas'ud kai ne!!! " 

Mas'ud dake shirin k+ rufe murfin motarsa ya ji an kira sunansa da ƙarfi, sai ya yi saurin waigowa yana kallon ƴan matan don shi tsakaninsa ga Allah bai ganesu ba, sai dai wacca ta kira shi sai ya ji kamar yasan mai muryar. Da gudu Hujayrah ta ƙaraso inda yake tare da cire glass ɗinta tana dubansa da murmushi. Lokaci guda ya ce

"Talkative Ashe kece!" 

Turo baki Hujayrah ta yi tana cewa

"Ni dai ka daina kirana da tankative, ai na daina surutu, ga ƴar uwata nan Razina, mun zo wurin Aunty Nazima ne da Hajiyarmu, hala kaima wurinsu ka zo" 

Dariya Razina ta yi sannan ta ce

"Ke Hujayrah yaron Hajiya Nafisa ne fa wacca take riƙon Aunty Nazima" 

Ai da sauri Hujayrah ta riƙe bakinta tana girgiza masa kai kamar wata yarinya. Shi abun ma dariya ya bashi, sai ya ce

"Hujayrah kenan yanzu kika ce kin daina surutu amma ko Second biyu ba a yi ma kin fara zubo min surutu kamar parrot, Ai shiyasa na saka miki suna Talkative Don shi yafi cancanta dake" 

Turo baki Hujayrah ta yi sannan ta ce

"Na kusa fara azumin magana ma" 

Dariya suka shiga yi mata daga bisani suka jera  tare zuwa cikin gidan. Gidan shi ma ya tsaru sosai, suna kusan yanayi da gidansu Razina, suna tafiya Hujayrah na zubama Mas'ud surutu sun kawo daidai inda wani tanki babba yake sai Hujayrah ta tsaya cak! Kamar a dasata tana kallon inda tankin yake. Mamaki ne ya cika Mas'ud da Razina ganin da kefa idanunta a wurin tankin. Mas'ud ne ya kasa haƙuri ya dubi Hujayrah ya ce

"Lafiya Hujayrah kika tsaya muna tafiya" 

Hujayrah ba tare da ta dubesa ba still idanunta na kallon tankin ta ce

"Yaa Mas'ud an binne sihiri mai ƙarfi a ƙasan tankin nan" 

Mamaki ne ta cika Mas'ud da Razina har Razina na waro idanunta wa je cike da mamaki ta ce

"Hujayrah! Taya aka yi kika san akwai sihiri a wurin nan" 

"Ta hanyar bugun zuciyata" 

Mas'ud ne ya ce

"OK fine, yanzu ku zo mu shiga ciki daga baya sai a san abun yi" 

Kasancewa daga parking load zuwa cikin gidan akwai ɗan tazara sai ya zamana Hujayrah ta tsaya a wurare kusan uku tana faɗin an binne sihiri, sosai hakan ya tada hankalin Mas'ud kenan akwai matsala a gidan, amma bara ya fara tabbatarwa sannan ya ɗau mataki akai. Suna shiga cikin main falon gidan sai suka yi arba da aminiyar Hajiyan Sama wacca Hujayrah da Razina suka sameta a falonta wato Hajiya Zinatu tana zaune a kujera. Hujayrah na haɗa ido da Hajiya Zinatu nan take gabanta ya yi matuƙar faɗuwa har sai da ta dafa ƙirji tana addu'a a cikin ranta. Akwai abinda take so ta tabbatar, tana so ta haɗu da Hajiya Nafisa kafin ta gasgata abinda take tunani akai. Cike da girmamawa Mas'ud ya gaida Hajiya Zinatu amma ciki-ciki ta amsa masa, Hujayrah da Razina suka gaisheta, a nan ma fuskarta babu yabo babu fallasa ta amsa musu, sai suka shiga ciki. Sashen Hajiya Nafisa suka wuce shiga wanda yake a ta gefan hagu. Mas'ud ne ya fara shiga da sallama sai su Razina suka biyo bayansa. 

Hajiya Nafisa ce da Nazima suna zauna a kujera ɗaya mai cin mutum biyu suna hira har da dariya suka amsa musu sallamar. Koda Hujayrah ta haɗa ido da Hajiya Nafisa ai bata ji bugun zuciyarta ya ƙaru ba, ko kuma ya buga da ƙarfi sai ma wani sanyi ta ji a ranta, zuciyarta na nuna amintuwa da Hajiya Nafisa, nan take Hujayrah ta yi concluding akan Wannan matar da ta gani a lokacin da za su shigo  ita ce muguwar, ita ce ta binne sihirin ko kaffara ba za ta yi,ai kuwa sai ta haƙo duk abubuwan da ta binne a ƙasa ta ƙonasu. 

Zama  Razina da Hujayrah suka  yi a kujerar mutum uku tare da gaishe da Hajiya Nafisa, da kulawa ta amsa musu fuskarta ɗauke da murmushi. Gaida Nazima su Razina suka yi ita ma ta amsa musu fuskarta faɗaɗe da murmushi. Hajiya Nafisa ce ta dubi Mas'ud ta ce

"My son tare kuka zo kenan" 

Girgiza  kai Mas'ud ya yi sannan ya ce

"Ummie motana ta fara shigowa ciki sai tasu ta biyo baya"

Murmushi ta yi sannan ta dubi su Hujayrah ta ce

"My new daughter zo kusa da Umminki mana" 

A kunyace Hujayrah ta miƙe zuwa wurin Hajiya Nafisa, zama ta yi a ƙasa kusa da ita. Duban ta Hajiya Nafisa ta yi sannan  ta ce

"Jiya Hajiya momma ta kirani take faɗamin munyi sabuwar ɗiyar kyakkyawa, cike da zumuɗi na ce Razina ta kawo min ita na ganta,maa shaa Allah Tabarakallah a gaskiya za mu sha dollars ranar bikinki" 

Da sauri Hujayrah ta rufe fuska tana murmushi, su Razina suka tintsire da dariya. Nazima ta ce

"Woooow ƙanwata ba dai kunya ba, ki saki jikinki kin ji, just feel free nan kamar a gidanku kike kin ji, kina kama da wata model wacca last year ta ci lambar yabo a African a gasar kyau da aka yi, u are Damm beautiful" 

Murmushi Hujayrah ta ƙara saki, a ranta tana farin cikin samunsu a cikin rayuwarta. 

"Ya sunanki my daughter" 

Gyara zama Hujayrah ta yi sannan ta ce

"Mammi sunana Hujayrah ɗiyar Abdullahi jikar Kamalu Angon Hindatu mai tsoran mutuwa" 

Mai su Hajiya Nafisa za su yi in ba dariya ba, har da Mas'ud sai da ya ɗan dara,su Nazima har da riƙe ciki saboda yadda take maganar ta yi in a funny way ne. Ƴan wasu tambayoyi Hajiya Nafisa ta yi mata sai suka ci gaba da hira bayan mai aiki ta kawo ma su Razina abin sha. 

Miƙewa Mas'ud ya yi zuwa part ɗinsa wanda yake a sashen Hajiya Nafisa. Watsa ruwa ya yi sannan ya fito falon, koda ya fito sai ya samu Hajiya Nafisa ta haura sama da baƙuwarta ita kuma Nazima ta taje ɗakinta ɗauko  abu. Su Hujayrah na falo suna kallo sai Mas'ud ya yi amfani da damar ya ce masu Razina su zo su je garɗen shaƙatawa, babu musu suka biyo shi, ita ma Nazima ta sauko daga ɗakinta sai ta biyosu zuwa garɗen. Bayan sun je garɗen  sai Mas'ud ya ce zai tambayi Hujayrah wani abu, su Nazima basu kawo komai a ransu ba Hujayrah ta miƙe zuwa wajan wani kujera mai tsawo wanda mutane huɗu za su iya zama suka zauna. Shiru wurin ya yi sannan Mas'ud ya fara magana

"Hujayrah na so washe garin ranar da naje gidan abincinku na sake zuwa amma a headquarter aka min kiran gaggawa, akwai wani babban case da ya zama dole ni zan jagorancesa, hakan nan na tafi port Harcourt na yi kwanaki sannan na dawo Bauchi, koda na dawo na zo gidan abincin a shekaran jiya sai suka cemin kin koma garinku, haƙiƙa na ji takaici sosai na rashin ganinki,na haƙura na dawo gida sai gashi cikin hukuncin Allah na ganki a cikin gidanmu, yanzu ina so ki bani cikakkiyan labarin har zuwa kasancewarki a gidan abokina kuma ɗan uwana Arqam wanda yake gab da dawowa Nijeriya"

Sauke numfashi Hujayrah ta yi sannan ta fara bama Mas'ud labarinta tun daga tasowanta a gidansu, rayuwar da suka tsinci kansu a ciki ita da iyayenta, auran dolan da aka mata da Alhaji Sambo dala, kowata gidansa da ya yi, sirrikansu da za ci shi da Senata har kuɓucewata daga gidan, rayuwarta a gidan abinda zuwa yanzu da take wurin Hajiya momma a matsayin ɗiyarta. Shiru Mas'ud ya yi yana sauraronta har ta ɗige aya. Wani nauyayyan ajiyar zuciya Mas'ud ya sauke sannan ya ce

"Yanzu haka za ki iya gane mutumin da ya aureki" 

Gyaɗa masa kai ta yi sannan ta ce

"Au na manta Ya Mas'ud lokacin da yake tattaunawa da abokinsa na ji ya faɗi asalin sunansa, bayan haka sanda zan gudu akwai wani hotonsa a bangon ɗakin har dashi na ɗauka na saka a jakana, yanzu haka akwai hoton Alhaji Sambo Dala a Jakarta" 

"Ya asalin sunansa yake" 

"Na ji ya ce sunansa Ayyub Abdulfatah Gaɗau" 

Da wani irin sauri Mas'ud ya miƙe tare da waro idanunsa wa je, jikinsa har ya fara rawa, zuciyarsa kuwa ba a magana domin dukan tara--tara take bama uku ba, cike da mamaki tare da ɗumbin al'ajabi Mas'ud ya ce 

"Kin tabbata sunansa kenan? "

Gyaɗa masa kai Hujayrah ta yi, cikin sanyin jiki Mas'ud ya koma ya zauna a kujerar tare da dafe kansa, he can just believe his own uncle Yake aika irin wa'innan abubuwa, no wanda shiyasa yake da kuɗi kamar na fitar hankali. Sake ta bayar Hujayrah ya yi

"Baki ji sunan abokin nasa ba" 

Ɗan tunani Hujayrah ta yi sannan ta ce

"Uhmmm kamar na ji yana ambaton Senata, har ma Senatan yana cewa wata shekarar takarar gwamna zai fito tunda sun kamani, dodon zai cire idanuna da zuciyata, daman su  kaɗai ya rage musu su gama ɗaukaka a duniya" 

A nan ma sake ruɗewa ya yi kenan Senata dai mijin Auntynsa Ramla maman Tahseen har dashi a cikin ƙungiyar. Akwai matsala dole ya yi wani abu, wannan ya zama dole. Ɗan tunani ya yi sannan ya dubi Hujayrah ya ce

"Hujayrah abinda nake so dake ummm! Wannan glass ɗin da kike amfani dashi ina so ki ci gaba da amfani dashi kinji, duk inda za ki je ya zamana kin saka shi kinji, Sannan idan za ku tafi zan baki wani haɗadɗan zobe daman don ke na siya zoban a can port harcourt, da na je gidan abincinku har da zoban na je miki dashi tunda yanzu Allah ya ƙaddara na ganki shikenan idan za ku wuce zan baki ki saka. Ina so duk wuya duk runtsi zoben ya zamana  yana a yatsarki, koda wasa Karki cire kin ji ƙanwata,in shaa Allah zan taimaka miki wurin ganin kin samu kariya daga sharrinsu, fatana dai duk abinda na umurceki ki yi"

Jingina masa kai ta yi sannan ta ce

"Ya Mas'ud Na gode sosai da taimakon da za ka min, Allah ya baka abinda kake nema a cikin ruwan sanyi, ya biya maka buƙatunka na alkhairi" 

Amsa mata ya yi da Ameen har cikin zuciyarsa ya ji daɗin wa'innan addu'o'in musamman wanda ta ce *Allah ya baka abinda kake nema cikin sauƙi* wannan addu'ar ta yi masa matuƙar daɗi a ransa, domin akwai abinda yake nema ruwa-ijallo amma ya gaza samu. Hujayrah ne ta ce

"Ya Mas'ud wannan matar da muka samu a falon farko muguwa ce, Duk ita take binne sihiri a gidan nan" 

Sosai mamaki ya cika Mas'ud,gyara zama ya yi sannan ya ce

"Bana son wasa Hujayrah ya aka yi kika san ita ɗin muguwa ce sannan ya aka yi kika san akwai sihiri a gidan nan" 

Nuna masa zuciyarta ta yi sannan ya ce

"Ya Mas'ud tun ina ƙarama nake yawan gane-ganan abubuwa,a duk lokacin da na zo wucewa na ji zuciyata ta buda da matuƙar ƙarfi to hakan na nufin a wurin nan an binne sihiri, idan kuma mutum ne na gani zuciya ta buga da matuƙar ƙarfi to hakan Yana nuni da abu biyu ne, kodai mutumin mugu ne ko kuma maye ne amma wannan matar gidan nan naku muguwa ce, sannan Mammi ta nan gida take cutarwa, idan aka ciro sihirin na karya shi to tabbas ɓoyayyan abinda ta yi ma Mammi zai karye idan kuma bata yi wasa ba zai koma kanta"

Idanunsa kyar! Akanta ya kasa motsawa sosai Hujayrah take burgesa, sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce

"Hujayrah Allah ya baki tarin baiwa, sai an zauna dake ake iya ganewa, da alama wannan shi ne dalilin da yasa wa'innan mutanan suke bibiyar rayuwarki, amma in shaa Allah ba za su ci galaba akan mu, Sannan batun gidan nan idan na samu lokaci mai kyau zan kiraki ki tone komai na cikin gidan" 

Mas'ud bai nuna ma Hujayrah yana da dangantaka da Alhaji Sambo Dala ba sannan Senatan da take faɗa abokin Alhaji Sambo Dala shima yana da dangantaka dashi domin matarsa Hajiya Ramla ubansu ɗaya da Umminsa Hajiya Nafisa sannan Wanda yake riƙonta mahaifinsu Arqam Ubansu ɗaya da Alhaji Sambo Dala duk da basa jituwa a tsakaninsu, ya ɓoye mata ne saboda ya ji daɗin bincike akan alhaji Sambo Dala da sauran ƴan ƙungiyar, idan ya faɗa mata ya sansu za ta iya guduwa daga gidan, shi kuma baya so ta gudu saboda ba tsira za ta yi daga hannunsu Alhaji Sambo Dala ba, amma idan tana gidan abokinsa Arqam ya tabbata babu abinda zai sameta saboda Alhaji Sambo dala baya zuwa gidan shi da Senata sai dai matansu, Sannan yasan da matuƙar wuya su faɗa ma matansu abinda suke yi.

Sun daɗe suna tattaunawa daga bisani su Hujayrah tabi su Nazima zuwa cikin gida.Shi kuma ya wuce masallacin gidan saboda jin an kira sallar Asr. Suma sallar suka yi sannan suka ci gaba da hira wanda sai kusan magrib suka bar gidan. Sun zo wucewa Mas'ud ya miƙama Hujayrah zoben, nan take ta saka a yatsanta tana mishi murmushi, shi ma murmushin ya sakar mata. Duk wanda abun babu wanda acikin su Nazima da Razina suka kula, har mota Mas'ud da Razina suka karasu sannan suka dawo gida. 

Motarsu Razina na parking Kowa ya buɗe murfin mota suka fito a kusan tare. Gidan ya yi shiru babu kowa  a farfajiyar gidan kasancewa idan dare ya yi duk ma'aikatan gida sashensu suke komawa, mazansu da matansu sai kuma da asuba za su fito aiki. Razina cewa a gaba za ta shiga ciki sai Fauziyya yayar Zahriyya ita ma ta zo wucewa, madadin da raɓa gefe da wuce tunda ƙofar babba ce mutane uku za su iya wucewa a tare, bata yi haka ba sai ta tunkuɗe Razina ta faɗu ƙasa har tana bigewa. Lokaci guda ta saki ƙara, ganin abinda Fauziyya ta yi ma Razina sai Hujayrah ta fusata, bata yi wata-wata ba ta ɗauke Fauziyya ta maruka hagu da dama tare da tureta ita ma, Allah yasa da bango Fauziyyan ta bugu amma haƙiƙa ta ji zafin marukan sosai, hannayanta biyu ta ɗaura a kumatunta ta dubi Hujayrah ta ce... ✍️

 





*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
 ***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol