Free chapter · Read without an account

Chapter 12

by Narrnarhh Bukar · BA NI DA MADOGARA

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*














*Bani da Madogara*
  (Sai Allah...)




 

 
012

Razina ce a gaba za ta shiga ciki sai Fauziyya yayar Zahriyya ita ma ta zo wucewa, madadin Fauziyya ta raɓa gefe da wuce tunda ƙofar babba ce mutane uku za su iya wucewa a tare sai bata yi hakan ba,tunkuɗe Razina ta yi ta faɗi ƙasa har tana bigewa . Lokaci guda ta saki ƙara, ganin abinda Fauziyya ta yi ma Razina sai Hujayrah ta fusata, bata yi wata-wata ba ta ɗauke Fauziyya ta maruka hagu da dama tare da tureta ita ma, Allah yasa da bango Fauziyyan ta bugu amma haƙiƙa ta ji zafin marukan sosai, hannayanta biyu ta ɗaura a kumatunta ta dubi Hujayrah ta ce

"Ke ƴar gidan uban waye ce da za ki ɗauki ƙazaman hannayanki ki zubesu a tsafatacciyar fuskata! How dare you ! Yau sai kin san koni wace ce a gidan nan! "

Ta yi maganar hannunta riƙe a ƙugu. Taimaka ma Razina ta miƙe Hujayrah ta yi sannan ta dubi Fauziyya da kyau madadin maganarta ta tsoratata sai ma ta saki murmushi tana mata kallon ƙasa da sama sannan ta ce

"Ashe ko za ki ci ubanki a gidan nan, sanin ko ni wace ce ba matsalarki bace, amma ki sani ni Hujayrah bazan bari a gaban ido ki lahanta ƴar uwata wacca nake jinta kamar jinina ba, ko harar kika mata ba kyaleki zan yi ba balle ki ɗauki hannunki ki bigeta"

Sosai maganganun Hujayrah suka ɓata ma Fauziyya rai, wani kukan kura Fauziyya ta yi za ta damƙi wuyan Hujayrah caraf! Hujayrah ta riƙe hannayanta ta matsesu sosai wanda hakan ya saka Fauziyya sakin wata razananniyar ƙara wanda ta kusan karaɗe ko'ina a gidan, abunka da Ajebotas wa'inda basu san wata aba wai ita wahala ba sai jin daɗi shi yasa ta ji zafin sosai, ita ko Hujayrah girman ƙauye ce tasan me ake kira da wahala ƙarin daɗi ita daman ba mai ɗaukar raini bace shiyasa take so ta koya ma Fauziyya hankali, bayan ta saki ƙara Still Hujayrah bata saki hannunta ba sai ma taɗiyeta ta yi ai kuwa sai ta faɗi ƙasa tana ƙara sakin wata sabuwar razananniyar ƙara. Juyawa Hujayrah ta yi sai ta taimaka ma Razina suka shiga cikin main falon, zuciyar Razina fal! Da farin ciki ganin yanzu tana da mai shige mata faɗa musamman Fauziyya wacca take mata mugunta a duk lokacin da za su haɗu, sannan idan aka je wurin Abba yin sasanci Hajiyan sama sai ta kare Fauziyya ta ce wai Razina ce take ma Fauziyya rashin kunya, Hajiya momma bata cewa komai duk da tasan gaskiyar haka Abba sai kawai ya Share zancen. Sun zo wucewa zuwa part ɗin Hajiya momma sai suka ga Hajiyan Sama da Zahriyya sun wucesu fuuu! Zuwa waje. Taɓe baki Hujayrah ta yi sannan suka ci gaba da tafiya har suka isa part ɗin Hajiya momma. Da sallama a bakunansu suka shiga ciki, lokacin har Hajiya momma ta kammala sallah a falonta tana lazimi suka shigo. Ganin Razina na ɗan ɗingishi sai hankalin Hajiya momma ya tashi da sauri ta ce

"Hujayrah mai ya samu Razina take ɗingishi"

Zaunar da ita ta yi a saman kujera sannan ta dubi Hajiya momma fuskarta shimfiɗe da damuwa ta ce

"Mammi wannan babbar yarinyar Hajiyan sama ce ta tunkuɗeta ta faɗi ƙasa hakan nan bata mata komai ba, ni kuma ganin muguntar da ta yi mata yasa na ɗauketa da maruka har biyu don a gaskiya bazan bari a gabana a ci zarafin Razina ina kallo ba, bayan marukan ma na tunkuɗeta itama, amma sai ta bige da bango madadin bata faɗi ba, buɗar bakinta ta ce *ni ƴar gidan uban waye ce da zan ɗauki ƙazaman hannayena na zube mata su a tsaftatacciyar fuskarta, zan gane ko ita wace ce* bayan na taimaka ma Razina ta miƙe sai yarinyar ta yi kukan kura za ta cacumi wuyana sai na yi saurin riƙe hannayanta na matsesu da ƙarfi sannan na taɗiyeta ta faɗi ƙasa sai na taimaka ma Razina muka shigo ciki "

Shiru Hajiya momma ta yi tana tunanin mafita don tasan yau akwai tashin hankali a gidan saboda tasan Hajiyan sama sai ta ɗauki mummunan mataki akan Hujayrah sannan ta faɗa ma Alhaji. Duban Hujayrah ta yi sannan ta ce

" Kunyi Sallah? "

Girgiza mata kai Hujayrah ta yi tana duƙawa don duba inda Razina ta bige, da sauri ta dubi Hajiya momma ta ce

"Mammi akwai matsala fa Razina ta yi targaɗe a babban yatsar ƙafarta" 

Waro ido Hajiya momma ta yi tana ƙarasowa inda Hujayrah take tana duba wurin, hankalinta a tashe ta ce

"Ɗauko min wayana na kira driver mu kai ta asibiti a duba ƙafar " 

Saurin girgiza mata kai Hujayrah ta yi tana cewa

"Mammi ba sai an kai ta asibiti ba, zan gyara mata ƙafar yanzu bara na ɗauko jakata a ɗakinmu " 

Fuskarta ɗauke da mamaki take kallon Hujayrah tare da cewa

"Kin iya gyaran karaya ne Hujayrah?" 

Murmushi Hujayrah ta yi sannan ta ce

"Eh Mammi na iya ɗauri sosai duk inda ƙashi yake a jikin ɗan Adam zan iya gyarashi da yardar Allah, bayan haka ma ina da sani akan magunguna irin da ciwon kai, zazzaɓi, abinda ya shafi sihiri da dai saurarunsu" 

Gwalalo ido Hajiya momma ta yi tana cewa

"A ina kika san duk wa'innan abubuwan" 

Wannan Karon ma murmushi ta sakar ma Hajiya momma sannan ta ce

"Kakulleta ce ta bani laƙanin tun lokacin da mahaifina ya samu matsalar ido, daman shi taba laƙanin sai daga baya ta bani ganin Abbuna ya makance ba zai iya badawa ba, ita ma Kakulleta mahaifinta ne ya bata, tana zuwa dani daji idan za ta samu ganyayyaki da saƙe-saƙin da take amfani dasu wurin bada maganin, tare da nuna min yadda ake badawa, haka gyaran karaya ma duk ta koyamin, bara na je na ɗauko kayan aikin"

Bata jira cewar Hajiya momma ba ta miƙe da sauri tabar falon, da kallo Hajiya momma tabi Hujayrah dashi a zuciyarta tana ƙara son yarinyar don ko ba komai yau Allah ya yi an rama ba Razina muguntar da Fauziyya take yi mata idan sun haɗu duk da wani ɓangaren tana jin tsoran abinda zai je ya dawo. Juyowa ta yi gun Razina wacca take hawaye saboda zafi da zugin da wurin yake mata, ko magana ma ta kasa yi saboda azaba. Hajiya momma take mata sannu har Hujayrah ta dawo da wata babbar leda a hannunta. Samun wuri ta yi kusa da inda ƙafar Razina take ta zauna, kafin ta buɗe ledar sai ga sallamar Alhaji, juyawa dukkaninsu suka yi,a da ya zo ya yi ma Hujayrah faɗa ne akan abinda ta yi ma Fauziyya saboda tun yana masallaci Hajiyan sama ta kirashi tare da faɗa mishi ƙarya da gaskiyar akan abinda Hujayrah ta yi ma Fauziyya, sai kuma yaga autarsa na matsar ƙwalla, da sauri ya zo wurinsu yana faɗin 

"Autana meya sameki kike kuka" 

Buɗar bakin Hujayrah ta ce

"Abbu babbar yarinyar Hajiyan sama ce ta tunkuɗe Razina ta faɗin kasa har babban yatsanta ya goce" 

Mamaki ne ya cika shi jin abinda Hujayrah take faɗa, don ba haka Hajiyan sama ta faɗa mishi ba, ta ce Hujayrah ta mari Fauziyya ba tare da ta yi mata komai ba har da tunkuɗeta ta faɗi ƙasa yanzu haka Fauziyya sai kuka take za su je asibiti a dubata , Sannan Razina ma ta yi mata rashin kunya amma bata mata komai ba. Cike da mamaki Alhaji ya ce

"Amma Izzatu bata faɗamin Razina ta bige ba?" 

"Ƙila bata sani bane" cewar Hajiya momma duk da Hujayrah ta faɗa mata komai, tasan halin Hajiyan sama indai akan yaranta ne bata da mutunci 

"To bara a kai ta asibiti likita ya duba ƙafar" cewar Alhaji yana juyawa

Hajiya momma ce ta ce

"Ai muna da mai gyaran ƙashi a gidan ba sai an kai ta asibiti ba, Hujayrah ta ce ta iya" 

Da mamaki Alhaji ya juyo da kansa yana duban Hajiya momma ya ce

"Hujayrah ta iya kika ce, how?" 

"Nima haka ta sanar min, ga kayan gyaran ma nan ta zo dasu" 

Nuna masa ledar da Hujayrah ta shigo da ita ta yi, ba tare da ya ce komai ba ya samu wuri ya zauna. Buɗe ledar Hujayrah ta yi wanda kayan gyaran ƙashi ne kala-kala a ciki, abubuwan da take buƙata ta ɗauko sannan ta fara aikinta da bismillah a bisa labɓanta. Cike da ƙwarewa Hujayrah take aikin, Razina babu abinda take sai darzar kuka Hajiya momma na yi mata sannu har Hujayrah ta gama tare da shafa mata wani mai a saman babban yatsar sai ta mai da kayan cikin ledar ta ƙulle sannan ta dubi Razina ta ce

"Shifakillah ya Ukhti in shaa Allah za ki samu sauƙin yatsar kin ji, Allah sai ya saka miki muguntar da ta yi miki" 

Jinjina mata kai Razina ta yi don bakinta ba zai iya furta koda kalma ɗaya cd balle ta iya bata amsa mata, Alhaji ne ya yi magana da cewa

"Autana ya ƙafar naki" 

Shima ɗin jinjina masa kai tashi, Hajiya momma ma haka, miƙewa Hujayrah ta yi sannan ta ce

"Razina bara na tayaki miƙewa muje ɗinkin mu muyi sallah kafin a kira sallar Isha'i" 

Tana maganar tana miƙa mata hannu, a hankali Razina ta miƙe nata hannun sai ta tayata miƙewa sannan suka fara tafiya a hankali, Razina ta ɗora hannunta a bisa kafaɗar Hujayrah na hagu sai hannun Hujayrah na dama na riƙe ledar maganin. Kafin su bar ɗakin Alhaji ya ce su sameshi ɓangaren bayan sallar Isha'i. Amsa masa Hujayrah ta yi da to sai suka ƙarasa ficewa daga ɗakin. Miƙewa Alhaji ya yi tare da faɗin 

"Kema ki sameni a can part ɗina don ina so na ji ta bakin yaran, don abin da Izzatu ta faɗamin ya bambamta da abinda Hujayrah ta faɗa, gwara kowa na nan a yi solving case ɗin" 

"To Allah ya kaimu bayan Isha ɗin lafiya abincin ka ma dashi zan tafk" 

Ficewa ya yi sai ita ma ta wuce bedroom ɗinta.Su Hujayrah na kammala sallah suka tsaya bayan an kira sallar isha'i sannan suka yi sallar daga bisani suka wuce part ɗin Alhaji wanda sai an ɗan fita daga ɓangarensu baki daya sannan aje part ɗinsa. Haka suka tako har part ɗin Alhaji, Hujayrah na taimaka ma Razina . Koda suka zo sai suka iske takalman mutane hakan ya tabbatar musu wasu na ciki. Da sallama suka shiga ciki, Hajiya momma ce da Alhaji suka amsa musu amma Hajiyan sama da mugun kallo take binsu dashi musamman Hujayrah. Cikin falo suka ƙaraso tare da zama, Razina na zaune a saman kujera saboda ƙafarta ita kuma Hujayrah na zaune a saman centre carpet wanda yake a tsakiyar ɗakin. Hajiya momma da Hajiyan sama na zaune a kujera ɗaya Alhaji na a tsakiyarsu, sai a ɗayan kujerar Fauziyya ce da bandage a goshinta da alama Hajiyan sama ta kai ta asibitin kenan wanda yake a cikin Estate ɗin, Ashe lokacin da Hujayrah ta taɗiya Fauziyya ta faɗi sai ta bige kanta da bango ta ji rauni a ƙafa. Gyaran murya Alhaji ya yi sannan ya ce

"To Alhamdulillah tunda kowa ya zo yanzu ina so na ji da bakinki Fauziyya sannan na ji ta bakinsu Auta" 

Fauziyya dake aikawa Hujayrah mugun kallo ta dubi Alhaji ta ce

"Alhaji kawai ina tafiyana na zo wucewa Razina ta zageni sannan waccar yarinyar da wanka min mari har biyu ba tare da na ce mata komai ba sai ta kuma taɗiyeni na faɗi ƙasa na bige a goshi naji rauni a ƙafata" 

Tana ƙarasa maganar ta cilla ma Hujayrah harara, ko kallon inda Fauziyya take Hujayrah bata yi amma tana ji a jikinta ana mata kallon banza da alama har yanzu bata shiga taitaiyinta ba sai ta fito mata a mutum ta nuna mata na asalinta sannan za ta shiga taitaiyinta. Hajiyan sama ne bayan Fauziyya ta gama shafto ƙarya sai ta ɗora da cewa

"Yanzu Alhaji kana ganin hakan ya dace kuwa, a ce tsintsacciyar mage tana yiwa ƴan gida mugunta, a gaskiya ban yarda da zaman wannan yarinyar a gidan nan ba saboda wata rana za ta iya hallaka mutum da gudu tunda ba a san daga ina ta fito ba, Ina so kawai tabar mana gida"

Sauke ajiyar zuciya Alhaji ya yi sannan ya ce

"Ammmm Izzatu ban tari lumfashinki ba naga ai ita kaɗai ta yi maganar mai zai hana aji ta bakinsu Auta ko Hujayrah tunda suna a wurin" 

"Haba Alhaji Fauziyya ƙarya za ta musu ne, ai tunda nake da Fauziyya bata taɓa faɗamin abinda ba haka ba, shiyasa data faɗin abinda Hujayrah ta yi mata ban ƙaryata ta ba tunda nasan bata faɗin ƙarya" cewar Hajiyan sama duk ta ƙosa a hukunta Hujayrah sannan tabar musu gida don ita hakanan ta ji ta tsaneta, Alhaji ne ya dubi Hujayrah ta ce

"A yadda Razina take da wuya da ita iya cewa komai amma Hujayrah bamu labarin abinda ya faru" 

Da kyau an zo wurin cewa Hujayrah a zuciyarta, zama ta gyara sannan ta dubi Alhaji cike da girmamawa ta ce

"Abbunmu mai fidda aya daga tsakuwa, mai banbance fari tsakanin baƙi, alƙalin alƙalai wallahi duk abubuwan da waccan Fauziyyar ta faɗa duk ƙarya ce babu gaskiya ko ɗaya a..." 

Bata ƙarasa maganar ba Hajiyan sama ta hayayyaƙo mat da masifa tana faɗin

"ƙarya kike yarinya! a gidan ubanwa ta faɗi karyar! Ke ga munafuka , mai iya zance don siyan mutane da daɗin bakinki ai sai kin bar gidan tunda na gidan ubanki bane wanda ya gina! "

Alhaji ne ya taka ma Hajiyan sama birki da cewa 

" Ya isa haka Izzatu! Hujayrah!" 

"Na'am Abbu" 

"Ci gaba da maganar" a ɗan zafafe ya yi maganar saboda ya fara gane halin Hajiyan sama wato yaranta ta sani, suke da gaskiya ko ganin Razina da ta yi targaɗe bata damu ba. Ci gaba da magana Hujayrah ta yi da cewa

"Abbu kamar yadda na faɗa maka a farko Fauziyya ce bata da gaskiya, ita ce ta tunkuɗe Razina lokacin da Razina za ta shigowa cikin babban falo, alhalin ƙofar na da faɗin da mutane kusan uku za su iya wucewa sai kawai ta zaɓi tureta, sosai Razina ta faɗi wanda hakan ya sakata ƙwalla ƙara saboda zafin da ta ji a ƙafanta, ni kuma a gaskiya bazan iya ganin ana zalunci a gabana na ƙyale ba musamman ma ga ƴar uwarta Razina, a matsayin Fauziyya na wacca tafi mu shekaru da hangen nesa ta kasa riƙe girmanta sai kawai ta zaɓi mugunta da son kai ga ƙannant, ni kuma ganin abinda ta yi ma Razina da gangan yasa kawai na shatatama kumatunta maruka har biyu sannan na tunkuɗeta kamar yadda ta yi ma Razina, a madadin da faɗi sai ta bige da bango, Abbu madadin ta ƙyale mu sai buɗar bakinta ta ce *Ni ƴar gidan uban waye ce da zan ɗauki ƙazaman hannayena na zube mata su a tsaftatacciyar fuskarta, yau sai nasan ko ita wace ce* Abbu tana gama maganar tayo kukan kura za ta cakumi wuyana, ni kuma ganin za ta cakumi wuyana sai kawai na damƙe tsintsiyar hannunta wanda hakan ya haifar mata da sakin ƙara sannan na taɗiyeta ta faɗi ƙasa, daman na taimaka ma Razina ta miƙe sai kawai na saka hannunta na hagu a kafaɗana muka bar wajen, Abbu wannan shi ne asalin abinda ya faru ban ƙara komai ba sannan ba rage komai ba, Abbu koda za a kasheni ne ba zan taɓa faɗi karya ba saboda a haka aka tarbiyantar dani a gidan mu"

Ɗakin shiru baka jin motsin komai sai sautin muryar Hujayrah wanda tana maganar tana ankare da mugun kallon da Hajiyan sama da Fauziyya suke aika mata, ko ɗar! Bata ji a ranta ba har ta kai ƙarshen zance. Alhaji da yake sauraronta har ta ɗige aya sai ya dubi Razina ya ce

"Auta shin abinda Hujayrah ta ce gaskiya ne ko kuwa ita ma ta yi ƙaryar" 

Razina dake zaune tana bin kowa da ido sai ta ɗago a hankali ta dubi Alhaji sannan ta fara magana a hankali 

"Abba Aunty Fauziyya ce bata da gaskiya tun ba yau ba haka take min mugunta" 

Mai Hajiyan sama za ta yi inba tafi tana salati da sallallami ba tare da faɗin

"Yau ni Izzatu naga abinda yafi ƙarfin kaina, Muhammadu ya rasulallah! Razina! ashe haka kike da sharri ban sani ba! A ce ki rasa wacca za ki goyama baya sai tsintsacciyar mage wacca Hausawa suka ce baza ta taɓa zamantowa mage ba, ke duniya ina za ki damu" 

Babu wanda ya tanka mata har ta ƙara ci maganganunta ta yi shiru, Hajiya momma da tun lokacin da aka fara tattaunawa bata ce komai ba yanzu ma haka bata da niyyar cewa komai don a ranta ba ƙaramin daɗi ta ji da Hujayrah ta yi maganin Fauziyya ba, Sannan tafi su baki wurin zubo zance, ita daman ba mai surutu ko hayaniya bace, idan da a baya ne haka nan Hajiyan sama za ta ƙaƙabama Razina laifi sannan ta wanke ƴarta amma yanzu kan Alhamdulillah ta haɗu da daidai ta ita. Gyaran murya Alhaji ya yi sannan ya fara magana 

"Yanzu dai kowa yasan gaskiya sannan komai ya fito fili ma'ana an gane inda aka samu matsalar, Fauziyya a nan gaskiya baki kyauta ba domin a matsayinki na wacca ta girmesu bai dace a ce ki tunkuɗe Razina alhalin akwai enough space da za ki iya wucewa ba, sannan ke Hujayrah idan irin haka ta faru ba saurin duka za ki yi ba, zuwa za ki yi wurinsu Izzatu ko Mubina ki sanar mu kinga sai su ɗauki mataki a kai, don haka ki daina ɗaukar mataki a hannunki kin ji"

Gyaɗa masa kai Hujayrah ta yi sannan ta ce

"In shaa Allah Abbu zan gyara" 

A nan ya ci gaba da yi musu nasiha wanda daga bisani ya sallamesu ya shigewarsa bedroom ɗinsa, Hajiya momma ta bisa ciki saboda ita keda kwana, Hajiyan sama da Fauziyya suka fara fita sai Hujayrah ta taimaka ma Razina suka fita suma. A kusan tare suke tafiyar da su Hajiyan Sama, buɗar bakin Hajiyan sama sai ta ce

"Hujayrah ki taka a sannu wallahi domin wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa, da Sannu zan yi maganinki a gidan nan sai kin yi da nasanin taɓa Fauziyya tsintsacciyar mage kawai" 

Martani Hujayrah ta bata da cewa

"Ashe kuwa kina da aiki ja a gabanki wai sarar dawa da haƙori, Ina nan daram! a gidan Karki manta da ɗiyar Audu kike, idan ke baki yi magani na ba to ni nan zan yi maganinki, mu zuba mu gani" 

Mamaki ne ya cika Hajiyan sama jin yadda Hujayrah ke zubo mata maƙaken maganganu hankalinta kwance ba tare da ta ji tsoro ko tunanin abinda zai je ya dawo ba, lallai kuwa za ta gane shayi ruwa ne a gidan nan, idan ta kai ta bango za ta iya sakawa a ɓatar da ita a garin. Fauziyya ce ta ce ma Hajiyan sama

"Mum bar shegiya wallahi wannan ciwon da za ta ji min bazai tafi a banza ba, sai na ɗauki mummuna mataki akanta, jiki Duk baƙi kamar baƙin tukunya" 

Maimakon Hujayrah taba Fauziyya amsa sai kawai ta fara waƙarta wanda kusan dasu Hajiyan sama take tana cewa

" *_Haka za su ji ni ayye!!! Haka za su ganni ayye!!! Haka za su bari!!! Haka za ku ga Hujayrah ku ƙyale warr! Warr! Warr! Kuma nafi ƙarfin maƙiyana warrrr!!!Domin idan masu yi wasa ba sai na ci ubansu warrrrr!!! _* " 

Basu tanka mata ba daman sun zo gaɓar da za su rabu sai kawai suka wuce part ɗinsu, kowa sai ya yabi hanyarsa. Su Hujayrah na isa ɗakinsu sai suka fara cin abinci dag baya kowa ya watsa ruwa sannan suka kwanta. 

*Bayan kwana uku*

A yau gidan Alhaji Imran Abdulfatah Gaɗau ya tashi da shirye-shiryan tarbar babban ɗa ga Alhaji Imran Abdulfatah Gaɗau wato Arqam wanda ya kusan shekara biyar baya rabonsa da Nijeriya zuwa gobe ake saka ran dawowarsa ƙasar daga Germany shi yasa aka fara shirye-shirye tun a yau. Ƙwararre ne a wurin ilimin saffara na'urar computer sannan ya gogu a harkar kasuwanci , tunda yana ɗan secondary yake iya sarrafa computer, wanda dalilin wannan baiwar tashi yasa Alhaji Imrana kai shi ƙasar China karatu ta ɓangaren computer engineering, bayan Arqam ya kammala degree ɗinsa a fannin computer engineering Sai ya dawo Nigeria ya yi bautar ƙasa daga baya ya koma Germany inda a can ya kammala masters ɗinsa ya ci gaba da business ɗinsa a can.

Kasancewar Arqam akwai shi da ƙwazo da fikira sai mahaifiyarsa da tanƙamai dukiyarta kacokar ya dinga juyawa mata wanda a cikin dukiyar ta bashi kusan rabinta kyauta shima ya gina kansa, wannan ya rafu ne tun lokacin da ya dawo Nijeriya bautar ƙasa, mahaifin Hajiya Mubina shahararran mai kuɗi ne kuma sananne a Nijar , sannan ita ce kaɗai ya ɗiyarsa a duniya . Cikin hukuncin Allah Arqam ya fara juya dukiyar nan yana gina kamfanonin da suke haɗa computers da wayoyin zamani masu kyau da ɗaukar hankali a wajan Nijeriya, kamarsu Dubai, America, London da Germany, ƙwararrun ma'aikata ya samu wa'inda suke da ilimin both Hardware da software tare da masu programing shiyasa kamfanoninsa suke ɗaya daga cikin companies da ake siyan product ɗinsu sosai saboda ingancinsu . A can Germany babban kamfaninsa yake yanzu haka ana gina wani katafaran kamfanin haɗa computers da smart phones a Nijeriya don ci gaban ƙasarsa da kuma samar ma matasa aikin yi musamman wa'inda suka ƙware a fannin computer engineering da programing .

Bayan buɗe companies na ƙera latest computers da smart phones sai ya koma harkar noma, don a ƙalla yana da gidajen kona sun kai bakwai a Nijeriya a cikin jahohi mabambamta. Ƙarin daɗi Alhaji Imran ya sake ba Arqam kamfaninsa biyu kyauta don sake gina shi, haƙiƙa Arqam bai watsama iyayensa ƙasa a ido ba domin kwalliya ta biya kuɗin sabulu saboda tun lokacin da iyayensa suka danƙa masa kaddarorin zuwa yanzu dukiyar ta lunku iya lunkuwa, harkokin kasuwancinsa sai ƙara bunƙasa suke na cikin gida da wajen Nijeriya, dalilin rashin dawowansa ƙasa tun bayan tafiyarsa Germany masters Saboda business ɗinsa ne, baya waccan ƙasar baya wacca dashi da masu taimaka masa wurin tafiyar da companies ɗin. 

*Ya kamata musan su waye ahalin Alhaji Abdulfatah Al Mu'azz Gaɗau*

Alhaji Abdulfatah Al Mu'azz Gaɗau shi ne asalin sunansa,wanda ya taso a cikin ƙauyan Gaɗau a jihar Bauchi State Nijeriya. A can ya taso kuma ya yi auransa na farko da ta na biyu. Sunan matarsa ta farko Hajara, mahaifiyar Alhaji Imran Abdulfatah Gaɗau wato mahafin Aqram dasu Razina. Yaranta uku ne amma ɗaya ya rasu wanda yake bin Alhaji Imran. Hajara ta daɗe kafin ta sake wata haihuwa tun bayan da mai bima Alhaji Imran ya rasu wanda a lokacin Alhaji Imran yana ɗan shekara uku mahaifinsa ya ƙara aure. Sunanta Sumayya ita ce mahaifiyar Alhaji Sambo Dala, saida ta yi haihuwa biyu kafin mahaifiyar Alhaji Imran ta sake haihuwar mace wato Hajiya Nafisa wacca take riƙon Nazima. Hajiya Ramla mafhaifiyar Tahseen ita ce ƙanwa ga Alhaji Sambo Dala wacca suke ciki ɗaya. Hajiya Nafisa ta kasance Auta ga Alhaji Abdulfatah saboda ita ce ƙarshe a haihuwa don Hajiya Ramla ta girma Hajiya Nafisa da kusan shekara uku. 

Matan Alhaji Abdulfatah basu cika jituwa ba sannan mai assasa rashin zaman lafiyan ita ce Sumayya mahaifiyar Alhaji Sambo Dala, a kullum cikin tsokana da tonan faɗa take ma mahaifiyar Alhaji Imran, da yake Mahaifiyar Imran bata biye mata saboda sanyin halinta shiyasa suke zaman doya da manja. A kullum Sumayya faɗama yaranta take su tashi tsaye ga neman kuɗi ko ta halin ya ya ne saboda kuɗi su ne martabar ɗan Adam idan baida su to ya gama wulaƙanta a duniya. Da son kuɗi Alhaji Sambo Dala ya tashi, burinsa a kullum bai wuce ya zama wani hamshaƙin mai kuɗi wanda duniya ta sanshi. Ita kuma Hajara ta ba su Alhaji Imran tarbiyya, a kullum cikin nusar dasu take a kan subi Allah sannan su tsarkake zukatansu, da neman na halal duk ƙanƙantarsa, da haka Alhaji Imran ya taso. Matan kuma Kowa da halinsa ita Hajiya Nafisa ta taso cikin natsuwa da kamala amma Hajiya Ramla son kuɗi da nuna isa ta tashi dashi . Babu laifi Alhaji Alhaji Abdulfatah ya yi rawar gani a kan Karatun yaransa daga bokon har na muhammadiyya. Daga baya suka taso daga Gaɗau zuwa cikin garin Bauchi da zama. A nan suka ci gaba da karatu, Alhaji Abdulfatah ne ya fara rasuwa sai suka ci gaba da rayuwa a gidan da ya bari. 

Alhaji Imran ne ya fara aure ya aura Izzatu sai daga baya Alhaji Sambo dala shima ya yi auran ya aura Mariya. A dalilin rashin haihuwa Izzatu sai Alhaji Imran ya auri Mubina mahaifiyar su Razina a can Nijar ya aureta, buzuwa ce Hajiya Mubina . Hajiya Nafisa ta auri abokin yayanta Prof. Abdulrahman Saminu Kwankiyal, ita kuma Hajiya Ramla ta auri Alhaji Shu'aibu Abubakar wanda yake riƙe da muƙamin senata a yanzu. Ganin Alhaji Imran yafi Alhaji Sambo Dala kuɗi sai hankalin Sumayya ya tashi har daga ƙarshe ta yi sanadiyyar jefa ɗanta ga halaka saboda duniya, kullum bata da abinda faɗa sai *Ayyub ka bani kunya, a ce Imrana ya fika kuɗi, ka tashi tsaye ka nemi sana'a, kar ka dogara da aikin gwamnati, ka dage da neman kudi* a dalilin wa'innan kalaman da mahaifiyarsa take masa ya yi sanadiyyar jefa kansa da abokinsa senata ga halaka wanda suke a cikinta yanzu. Sannan duka iyayensu mata sun rasu a yanzu haka. Daman tun fik-azal Alhaji Imran da Alhaji Sambo Dala basa jituwa koda kuwa a hanya suka haɗu kuma hakan ya samo asali ne a dalilin zugar d mahaifiyar Alhaji Sambo Dala take yi ma Alhaji Sambo Dala tare da cusa masa ƙiyayyar ɗan uwansa , amma su Hajiya Ramla da Nafisa suna zumunci sama-sama. 

Alhaji Sambo Dala yanada mata ɗaya Hajiya Mariya sai yaransa uku, Akmal wanda ya kasance babba yanzu haka ya dawo Nijeriya bayan ya kammala masters ɗinsa, Sai Sakhiya Wacca take bin sa ita ma ta kammala bautar ƙasa, ta ukunsu Sabrin wacca take sickler gashi Allah ya ɗora ma Alhaji Sambo dala mutuwa sonta. Hajiya Ramla da mijinta Senata suna yarinya ɗaya tilo mai suna Tahseen, sun ɗora sonsu kacokar a kanta ita ma ta kammala karatunta. Alhaji Imran yana da mata biyu, Hajiya Izzatu itace matarsa ta farko, Allah bai bata haihuwa ba amma tana riƙon yaran ƴan uwanta su uku, Khalil shi ne babba amma baya ƙasar ya tafi wani course zuwa ƙasar Japan amma ana saka ran dawowansa nan da sati ɗaya, sai Fauziyya Wacca ta kammala bautar ƙasa sai ta ukunsu Zahriyya wacca take sa'an Razina. Matar shi ta biyu wato Hajiya Mubina tana da yara uku, Arqam wanda ya kasance babba sai Nazima wacca take hannun Hajiya Nafisa ita ma ta kammala karatunta sai auta Razina aminiyar Hujayrah, Hajiya Nafisa tana da yaro ɗaya Mas'ud sai Nazima wacca take riƙo. To wannan shi ne asalin tarihin su Alhaji Sambo dala da alaƙarsu da Mahaifin Arqam 

*Cikin Labari*

A yau ne Hajiya Ramla ta shirya zuwa gidan ɗan uwanta Alhaji Imran. Zuwan nata don ta tabbatar da aikin ya ci Hajiya momma ko a'a. Tare da excort suka tafi, Hajiya Ramla ba shiri take da Hajiyan Sama ba tun fil-azal, shi yasa da ta zo gidan sai kawai ta wuce direct part ɗin Hajiya momma. Lokacin Hajiya momma tana falo kamar kullum tana karatun jarida sai ta ɗago tare da amsa mata sallama. Samun wuri Hajiya Ramla ta yi ta zauna a kujerar mai cin mutum ɗaya. Bayan sun gaisa sai ɗakin ya shiru baka jin motsin komai sai ƙarar A.C. Hajiya Ramla na tunanin ta yi mata zancen auran Tahseen da Arqam ta ji ko asirin ya ci ko kuma ta yi shiru sai bayan ya dawo ta yi mata maganar. Kai! Ina wata zuciyar ta raya mata akan ta gwadata kawai ai da zafi-zafi ake bugun ƙarfe. Ƙundumbala Hajiya Ramla ta yi duk da tana tsoron abinda zai je ya dawo amma ta cire tsoran, cike da natsuwa ta dubi Hajiya momma ta ce 

"Hajiya momma ya batun auran Arqam da Tahseen, idan ya dawo ne za ayi maganar ko yanzu" da matuƙar tsoro ta ƙarasa zancen. Shiru Hajiya momma ta yi tana kallon Hajiya Ramla sai can fuskarta ta faɗaɗa da murmushi wanda ya ƙara ƙawata fuskarta ta ce

"Haba Hajiya Ramla ai ba sai kin wani tada hankalinki a kai ba, da Arqam sa Tahseen duk ɗaya suke a wurina, da ya dawo zan bijiro masa da zancen" 

Wani irin farin ciki ta ji a ranta wanda baya iya misaltuwa, aikin boka ya yi, don sake tabbatarwa Hajiya Ramla ta ce

"Hajiya momma Arqam ba wani son Tahseen yake ba, shi yasa kika ga duk na damu, gashi ita tana ƙaunarsa sosai" 

"Ya isa ya ce baya son Tahseen Hajiya Ramla, Arqam baya saɓa umarnina duk ƙin da yake ma abu idan ya ci karo da umarnina haka yake bi ba tare da ya yi jayayya da ni ba, don haka kwantar da hankalinki, Sannan ki ce ma Tahseen gobe ta shirya ta zo gidan nan ta ɗan yi kwana biyu saboda bayan dawowansa da kwana biyu za a yi bikin murnar dawowansa tare da murnar zagayowan shekarar haihuwansa, sannan Alhaji ma zan sanar masa a yau in shaa Allah, kinga da an yi kwana biyu ya huta sai a fara shirye-shiryen auransu ko ya kika gani"

"Haba ai da kai da wuya duk mallakar kai ne, duk abinda kika ce shi zan bi, Ina komawa gida zan sanar mata" 

Tana maganar cike da ɗumbin farin cikin da ya lulluɓeta tare da ƙara jinjina ma aikin boka da kuma wacca ma'aikaciyan gidan da ta tayasu aikin har suka yi nasara. 

*Waiwaye*

Kamar yadda Hajiya Lubna ta yi alƙawarin zuwa nan da jibi za ta ji ta, hakan kuwa a ka yi don ta cika alƙawarinta. Bayan ta zo gidan Hajiya Ramla sun gaisa sai ta buɗe jakarta ta ciro wani ƙullin Leda. Matsowa Hajiya Ramla ta yi kusa da Hajiya Lubna don ta ji abinda za ta faɗa. Hajiya Lubna ta buɗe ledar ta ciro wata laya baƙa ta miƙa ma Hajiya Ramla sannan ta ce

"Hajiya Ramla kin ga wannan layar duk wuya duk runtsi ki tabbatar an sakata a cikin katifar da take kwana a kai, ma'ana ya ɗan yage katifar sai a cusa layar ciki musamman a inda take kwanciya,Idan kika yi hakan, hmmm Hajiya momma za ta dawo a tafin hannunki sai yadda kika so da ita, maganar aure kuma kamar an yi angama"

Wata guɗa Hajiya Ramla ta cillara tana murna, sosai ta shiga farin ciki tana cewa 

"Kai Hajiya Lubna a gaskiya na ji daɗin wannan abu sannan zan yi kamar yadda kika ce don akwai mai aikin Hajiya momma da take min C.I.D a gidan kin ga shikenan faɗuwa ta zo daidai da zama, bara yanzu na kirata ta saci hanya ta zo nan gidan" 

Tana maganar tana ɗaukar wayarta daga hannun kujera, wata lamba ta kira wanda kiran biyu wayar ta yi aka ɗau kiran, a can matar ta ce

"Barkha da rana ranki shi daɗe " 

" Salame duk abinda kike ina so ki saci hanya ki zo don ina da wani gagarumin aiki da nake so ki min a yau ɗin nan" 

Cike da girmamawa ta ce

"An gama ranki shi daɗe" 

Katse kiran Hajiya Ramla ta yi sannan ta dubi Hajiya Lubna ta ce

"Ammm nawa ne kuɗin aikin boka" 

"Dubu dari biyar ne kawai babu yawa" 

Murmushi Hajiya Ramla ta yi sannan ta ce

"Bani account numba zan tura miki dubu ɗari takwas ,sai ki riƙe sauran kuɗin" 

Babu musu ta zayyano mata Account numba tana murmushi. Bayan minti huɗu da faɗin Account numba sai Hajiya Lubna ta ji shigowan saƙo a wayanta wanda tana dubawa ta ga kuɗin ne suka shigo. A nan gidan Hajiya Ramla ta wuni har Salame ta zo gidan, kamar yadda Hajiya Lubna ta sanar ma Hajiya Ramla yadda za a yi saka layar, haka ta sanar ma Salame sannan ta bata zunzurutun kuɗi har dubu ɗari da hamsin, sosai Salame ta shiga farin cikin jiki na rawa ta amsa kuɗin sannan ta yi musu sallama ta bar gidan saboda satar hanya ta yi. 

Kamar yadda Hajiya Ramla ta shaida mata yadda za ta saka layar a cikin katifar da Hajiya momma take kwana a kai to haka ta yi kasancewar Salame ce mai yi mata gyaran ɗaki har uwar ɗaka sannan akodayaushe tana shiga uwar ɗakanta ba tare da shamaki ba. Bayan ta yanka wani wuri a jikin kafitar sai ta tusa layar sannan ta ɗinke wurin ta gyara gadon. Salame na komawa sashensu sai ta keɓe a wani wurin da babu kowa, ta ɗauki waya ta kira Hajiya Ramla tare da sanar mata ta yi yadda ta ce. Cike da farin ciki ta ce mata ta gama aikinta, sai suka katse kiran. Murmushi Hajiya Ramla ta yi sannan ta shirya zuwa gidan washe gari. Daman ba ɗan komai yasa ta zo gidan ba sai don ta tabbatar aikin ya yi. Wannan kenan. 

*Cikin labari*

Sun ɗan taɓa hira daga bisani ta ce zata wuce gida, ta fito daga part ɗin Hajiya momma sai ta yi kiciɓis! Da Hajiyan Sama za ta fita anguwa. Wani irin mugun kallo suke bin junansu dashi. A gadaran ce Hajiya sama ta ce

"Ummm an zo shisshigi don an ga maiƙo a jikinta za a lashe, to a yi mu gani in tusa za ta hura wuta, kifi na ganinka mai jarkoma" 

Wani munafikin murmushi Hajiya Ramla ta yi sannan ta ce

"A'aahhh su *Hajiya juya* manja, ke har kina da bakin faɗar ina shisshigi, naga wasu kika ɗauko suna cinyema yayana dukiyarsa, Ina sane da makircin da kike yi a cikin gidan nan, mu zuba mu gani shege ka fasa ɗan halak sai yanka, baki da aiki sai dai ki ci ki ƙoshi ki je masai ki zazzaga kashi aikinki kenan kullum, mtws! Banda lokacinki wallahi, tafi can juya kawai"

Fuuu! Hajiya Ramla ta bi ta gaban Hajiya momma ta wuce tare da watsa mata harara. Da wani mugun kallo Hajiyan Sama tabi Hajiya Ramla a ranta tana cewa 'Da Izzatu kike wallahi sai na yi maganinki, bara na gaba cika ƙudirina akan Hajiya momma, zan dawo agareki, mtws!' Fasa tafiya unguwar ta yi sai kawai ta koma ɗakinta don kalmar *Juya* da Hajiya Ramla ta ambata mata ba ƙaramin ƙona mata rai ya yi ba. Ranar ta wuni fuskarta babu annuri. Wannan kenan. 

🌎🌎🌎🌎🌎🌎

Da sauri ya miƙe yana faɗin

" What! Baku ganta ba!" 

Alhaji Sambo Dala kenan yana waya da yaronsa Nasir dake can Kaduna, da yake ya sanar masa Hujayrah ta gudo gida su tabbata da sun saceta ba tare da an ankare dasu ba. Tun a ranar da Alhaji Sambo Dala ya umurcesu da aikin, suka shiga ƙauyan suna bincike har na tsawan kwana biyar amma basu samu labarin dawowanta ba. Nasir shi ne babban yaron Alhaji Sambo Dala wanda yake masa aiki a garin Kaduna kuma tare dashi ake binciken, ganin bai samu yarinyar ba kuma yasan halin mai gidansa zai iya illata shi ko ahalinsa don ya ji kisan da ya yi wa yarinyar Eze wanda a sanadiyyar mutuwarta Eze ya kamu da cutar Depression. Tsoron kar Hakan ta faru ga iyalinsa sai kawai ya shafto masa ƙarya akan basu ganta ba amma sun ji a ce lokacin da ta dowa garin sai yayan mahaifinta ya kaita wani garin da yake yasan Alhaji Zakari. Jin wannan batu ya saka Alhaji Sambo Dala saurin miƙewa hankalinsa ya yi ƙololuwan tashi don yasan idan ba ga yarinyar nan ba to kashinsa ya gama bushewa, sannan yana tsoran kar Demon king da DODO ƘURNUSSA su taɓa masa iyali don zai iya komai akan ahalisa. Cike da ɓakin ciki wanda yake bayyane a fuskar Alhaji Sambo Dala ya ce
"Fine, yanzu ka gama aikinka Nasir, zan kira yayan babanta yanzun nan ya fito da ita ko kuma ya karɓi hukunci mai tsanani daga hannun akan cin amanar da ya yi min, yanzu dai ku ci gaba da aiko da yaran kamar yadda kuka saba, ni zan ji da komai akan batun yarinyar, You're free now"

"OK Boss, muna nan muna aiki tuƙuru" cike da farin ciki yake maganar ko ba komai he is free from Alhaji Sambo Dala, tunda jifa ta tashi kansa da iyalansa to ta faɗa kan koma wane ne, non of his business. Alhaji Sambo Dala na kammala wayan ya nema numban Alhaji Zakari ring ɗaya-biyu ya ɗau kiran, cike da girmamawa zai gaishe da Alhaji Sambo Dala sai ya katse sa da cewa

"How dare you on earth ka ci amanata! How dare you!!! Baka san ko ni wane ne ba ko? Baka san abinda zan iya maka da iyalinka ba ko? Ya za a yi bayan shekaru kusan goma ina turoma da kuɗin raino yarinya ace ta gudo madadin ka kirani sai kawai ka gudu da ita wani gari, wato ka ci kuɗina a banza ko"

Da wani irin ƙarfi ƙirjin Alhaji Zakari ya bada sautin Dummmmmm!!! Lokaci guda hantar cikinsa ta kaɗa, sosai ya ji cikinsa ya murɗa tare da bada sautin Kulululu!!! Nan take ya fara jin kashi, jikinsa da ɗaukar ɗan mazari, muryar na rawa ya ce

"Ranka ya daɗe wallahi tallahi na rantse da Allah bansan Hujayrah ta dawo garin nan ba, sannan ban ji labarin ba, ka yarda dani wallahi bansan da zancen dawowanta ba sannan bana tunanin Hujayrah ta dawo gari...." 

"Rufemin baki!!! An faɗa maka bana bincike ne Eh! An faɗamin ta dawo garin kai ka ɗauketa ka gudu da ita wani gari sannan wanda ya faɗamin ba zai taɓa min ƙarya ba! Ka saurareni da kyau da kuma kunnan basira! na bata nan da kwana goma ka ɗaukota daga garin da ka kai ta ka kirani na zo na amsheta idan ba haka ba, Hmmmm sai na illata ahalinki illa mai munin gaske! "

Kit! Ya katse kiran. Sai faman kai kawo yake a ƙayattacan secret room ɗinsa wanda yake ƙarƙashin ƙasa, ya rasa meke mai daɗi a rai, babban tashin hankalinsa shi ne ya yi ma Demon king alƙawarin kafin wata biyun da aka ɗiban masa su cika zai kawo yarinya cikin ƙungiya, yanzu haka da maganar an kusa cin wata ɗaya, lokaci ƙara kusantowa yake, dole ya yi wani abu a kai, dole ya nemota kafin lokacin ya cika. Haka ya ci gaba da saƙa da warwara daga bisani ya murza zobensa sai kawai ya ɓace ɓat! Daga ɗakin. Wannan kenan 

🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Kwanar kwara ƙwai, Kaduna state. Nijeriya*

A ɓangaren Alhaji Zakari sosai hankalinsa ya dugunzuma ya yi ƙololuwan tashi, ya Raya ina zai saka ransa ya ji daɗi, wannan shi ake kira da *Tsaka mai wuyar fita* gaba wuta baya bala'i. Gashi yau ya kama ƙashen ranar da Murja ta ɗiban masa akan maganar auran ƙanwarta Zaliha, kuma yasan idan bai amince ba to shikenan za ta kwance masa zani a tsakiyar kasuwa don kaɗan daga cikin aikinta ne. Ga wata sabuwa in ji ƴan caca, Alhaji Sambo Dala ya zo da nashi bala'in wanda bai san hawa ba balle sauka.Bai san Hujayrah ta dawo gida ba kuma bai ji labarin ba amma gashi an samu wani annamimin ya ce shi ya kai ta wani gari ya ɓoye, to ma idan da yaga Hujayrah ai a nan take zai kira shi ya sanar masa ya zo ya ɗauki shegiyar. Amma yanzu ya rasa madafa. Yana zaune yana wannan tunanin ya ji wayarsa na ringing da sauri ya ɗau wayar a tunaninsa ko Alhaji Sambo Dala ne ya kirasa ya shaida masa da ya ganta amma ina sai yaga akasin haka, sunan *MATI* ke yawo a screen ɗin wayarsa nan take jikinsa ya ƙara sanyi hankalinsa ya ƙara tashi, jiki baɓu ƙwari ya ɗauki kiran tare da kara wayar a kunnansa ba tare da yake komai ba. A can Murja ta ce... ✍️

 




*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
 ***










Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol