Free chapter · Read without an account
Page 24
SAWU BIYU
Khadijah Sulaiman
YOTA
Book 1
Page 24
Da mamaki ya dinga maimaita text ɗin,ganin babu number yasa ya taɓe baki ya ajiye wayar ya cigaba da abinda yake.
Bilal ya turo ƙofar yana cewa"wai har yanzu ba ka gama ba, baƙi sun fara zuwa fa?"
"Ban aike ku gayyato kowa ba".
Bilal ya ɗan kalle shi kamar zai ce wani abu sai ya fasa,ya ɗauki wayarsa da wristwatch ya buɗe ƙofa ya fita Bilal ya bishi da kallo.
A hararbar gidan ya tarar da Lieutenant da dama da suka zo taya shi farin ciki,dole ya saki ranshi ya shiga cikin su.
Kallon Idayat kawai yake ganin ita kaɗai ce mace a cikinsu,ya ɗauke kai ya ja tsaki.
Sai kusan sha biyu na dare aka tashi,zuwa sannan a matuƙar takure yake,ko ta kan Bilal bai sake bi ba bayan sun gama sallamar baƙi ya shiga ciki.
**********
Shirye shiryen biki kawai ake,sauran ƴan uwa dake nesa duk sun fara cika gidan.
Aunty Maryam babbar ƴar Hajiya Mama ta iso tare da nata ƴaƴan.
Bayan ta haifi Maryam a gidan Daddy suka sami matsala da shi har ya kai ga sun rabu,tana fita ta auri wani tsohon saurayinta da ya nemeta tun tana budurwa,a nan ta haifi Sudais,sai dai kishiyoyi sun hanata saƙat ganin yadda gabaɗaya hankalin mijin nasu ya koma kanta.
Haka suka shiga suka fita har sai da ya ji babu wacce ya tsani ya buɗi ido ya gani kamarta,da yake da sauran zama tsakaninta da Daddy sai gashi ya dawo da ita.
Tana dawowa ta tarar ya auro Mami,ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba,a duniya babu wacce ta tsana kamar Mami,gani take ta kanainaye miji ta asirce shi babu wacce yake gani sai ita.
A haka suka cigaba da zama har zuwa yau.
Ƴan Canada sun iso,Hajiya Oum tare da babban yaya Abdullahi,babban likitan zuciya wato Cardiologist,yana aiki a Peter Munk Cardiac Centre, Ontario, Canada.
Sai autarta Aneesah,su kaɗai kawai ta haifa,wanda ikon Allah yasa zasu zo duniya.
A lokacin idan ta samu ciki ba ya kai wata biyu zai ɓare,tayi ɓarin ciki babu adadi har sai lokacin da aiki ya kai mijinta India,a nan ta sami ganin Gynaecologist,cikin ikon Allah ta fara shan magani har Allah ya taimaketa ta sami cikin Abdallah.
Bayan ta haife shi sai da ya kai shekaru goma sannan ta sami cikin Aneesah.
Suna zaune gabaɗaya a parlourn Hajja Jidda ta shigo da manyan warmers,ta ajiye warmer ɗin ta gaida Oum tana ƙoƙarin wucewa.
Oum ta daka mata tsawa ta ce"dawo nan".
Jiki na rawa ta dawo don sosai suke shakkar ta.
"Kina hauka ne,haka ake gaisuwa,kin san wacece ni kuwa?"
Jidda tayi shiru,jikinta in banda rawa babu abinda yake.
"Tambayar ki nake,kin san matsayi na a nan gidan ko ba'a sanar da ke ba?"
"Na sani".
"Kin sani?shine za ki gaida ni a wulaƙance,who does that?"
Hajja ta zabga tagumi ta ce"in dai yaran Ramla ne kaɗan ke nan wallahi,babu abinda suka iya sai munafurci gashi za'a je gidan miji,idan kun nunawa dangin miji wannan banzan halin naku ku ke da jin kunya wallahi,babu abinda ya dame ni".
Jidda ta durƙusa da sauri ganin kuka na son kufce mata ta ce"sannu da zuwa Oum,ya hanya?"
"Daga yau,idan har za ki gaida babba ko mutum mai muhimmanci make sure kin nutsu before doing that,ki zauna ko ki ɗurkusa,yanzu aure za ki yi,za ki haɗu da mutane daban daban,try to show some respect please,am I clear?"
Ta gyaɗa kai da sauri.
"Za ki iya tafiya."
Ta miƙe da sauri ta fita,Hajja ta taɓe baki ta ce"gaskiya Ramlah ta cucemu ta ɓata mana tarbiyyar yara,kai tir".
Abdallah dai na zaune sai danna wayarsa yake kamar baya parlourn,dai dai nan Zarah ta shigo riƙe da manyan basket guda biyu.
Tana ganin Oum tayi murmushi ta ajiye basket ɗin ta karaso kusa da ita ta rungumeta,Oum ta rungumeta tana murmushi.
A hankali ta zame jikinta ta durƙusa ƙasa ta ce"Oum ina wuni,kun zo lafiya?"
"Lafiya ƙalau my baby,ya gida ya School?"
"Alhamdulilah Oum".
Hajja dai sai kallon su take,Zarah ta miƙe tana gyara mayafin Abayar jikinta, Abdallah ya tsaya cak da danna wayar da yake ya zuba mata ido,suna haɗa ido ta ɗauke kai da sauri ta ce"ina wuni".
Ya cigaba da kallon ta from head to toe har sai da Hajja ta ce"ana gaisuwa Abdullahi".
Ya juyo ya kalli Hajja,ya sake dawo da idon shi kanta ya buɗe baki da ƙyar ya ce"lafiya".
Ta ɗauko basket ɗin ta ajiye kusa da Oum ta ce"Oum ga abinci".
Oum tayi murmushi ta ce"zuba min mamana".
Ta amsa da toh ta wuce kitchen,kasa haƙura yayi ya ɗauke kai daga danna wayar da yake ya sake binta da kallo.
Riƙe da plate da spoon ta dawo parlourn,tana ɗaga kai suka sake haɗa ido,lokaci ɗaya ƙirjinta ya buga,ta ɗauke kai da sauri ta ƙarasa gaban Oum ta zuba mata abincin ta ajiye kusa da ita,ta wuce ta buɗe fridge ta ɗauko ruwa ta ajiye mata.
Oum tayi murmushi ta ce"thank you mamana".
Ta miƙe zata bar parlourn ta ji ya ce"zo ki zuba min".
Ta juyo da sauri ta kalle shi,ya sake gyara zama yana kallon idonta,Hajja ta ƙanƙance ido tana bin su da kallo.
Babu yadda ta iya ta shiga kitchen ta ɗauko plate da spoon ta zuba abincin ta ajiye kusa dashi,kamar ya sami television haka yake kallonta.
Ta miƙe da sauri za ta fita ya ce"bani ruwa".
Kamar ta fashe da kuka ta wuce ta ɗauko ruwa ta ajiye ta bar parlourn da sauri.
Hajja dai tayi tsit kamar ba ta wurin.
Da daddare tana kallo Aneesah ta shigo,ta zauna kusa da ita ta ce"Hajja na kiran ki".
Ta ɓata fuska ta ce"me zan mata?"
Ta buɗe hannu alamar ita ma bata sani ba.
Ta ja guntun tsaki ta ajiye wayar ta ɗauki hijabinta ta fita,a ɗaki ta tarar da Mami ta sanar da ita.
Suna zaune a parlour shi da Hajja,ta turo baki ta gaida Hajja sannan ta gaida shi.
Yana kallon ball ya juyo ya zuba mata ido.
Ta tsaya jikin kujera tana turo baki ta ce"Hajja gani".
"Yayanki ke neman ki,ni babu abinda zaki min tunda ba kuturwa nake ba,za ki wani tsaya min ƙerere a ka wai Hajja gani".
Ta juya ta kalle shi kamar ta fashe da kuka,ya ɗauke kai ya cigaba da kallon da yake,kamar ba zai tanka ba ya ce"ki shiga kitchen ki haɗo min tea".
Ta watsa mishi harara ƙasa ƙasa ta bar wurin,Hajja ta bishi da kallon ƙasan ido.
"Yanzu kai shayin ne sai ka aika an kira ta?"
Ba tare da ya kalle ta ba ya ce"babu ruwan ki".
Ta gyaɗa kai ta ce"lallai kam babu shakka babu ruwana".
Sadauki yayi sallama ya shigo,Hajja ta amsa mishi da fara'a.
Ya zauna kan carpet ya ce"ina wuni Hajja".
"Lafiya ƙalau Umaru ,ya wurin aikin naku?"
"Lafiya Alhamdulilah Hajja".
Hajja ta ce"to Madallah,na ji labarin ka sami ƙarin matsayi Allah ya sa albarka".
Ya shafa kai ya ce"Amin Hajja".
"Bari a kawo abinci".
Da sauri ya dakatar da ita ya ce"Nagode Hajja,yanzu na ci abinci wurin Mami".
Ta ɓata rai ta ce"ko dai Hafsah ce ta hana ka cin abinci a wuri na,ko ruwan ɗaki na ba ka taɓa sha ba don masifa".
"Ki yi haƙuri Hajja,zan sha ruwan".
Zarah ta fito riƙe da ƙaramin tray mai ɗauke da tea cup da spoon, Sadauki ya ɗan bita da kallo.
Ta sunkuyar da kai ta ce"ina wuni".
A hankali ya amsa tare da ɗauke kai,sake ɗago kai yayi ganin irin kallon da Abdallah ke bin ta da shi kamar zai haɗiyeta.
Ta ajiye tray ɗin kusa dashi ta juya ta fita.
Har ta fita bai ɗauke ido a kanta ba Sadauki kuma bai daina kallon shi ba,Hajja ta zuba tagumi ta shiga ƙare musu kallo duk su biyun,idan ta kalli wannan sai ta juya ta kalli wancan.
Sadauki ya fara ɗauke kan shi,ya miƙe yana kallon Hajja ya ce"zan tafi Hajja, sai da safe".
"Na gode,sai da safe".
Yana fita Hajja ta gyara zama ta ɗauki tooth pick ta kai baki ta ce"yaron kirki,ga hankali da nutsuwa,gashi son Zara'u yake kamar me".
Da sauri Abdallah ya juyo ya kalleta,Hajja na lure da shi ta cigaba da abinda ta ke,can ya buɗe baki da ƙyar ya ce"ta gama makaranta ne?"
"Makaranta na yaushe kuma,ba dai sakandiri ba?ta gama tun tuni wani ake nema,idan sun yi auren sai ta cigaba a ɗakin aurenta".
"An sa auren ne?"
"Ka ji ka da wani zance, za'a sa auren ƴar uwar ka ba ka da labari ne,ai ko mahaifinta bai san suna wani son junan su ba".
Ya cigaba da shan shayin a nutse,bayan ya gama ya miƙe ya kai kitchen daga nan ya wuce ɗaki.
Hajja ta bishi da kallo ta ce"Ja'iri".
Washegari aka tashi da shirin Henna, gabaɗaya gidan a cike yake da jama'a. Zarah ta gudu ɗakin Mami don hayaniyar mutane ya fara damunta.
Tana kwance Sudais ya kirata,sai da ta tabbatar Mami bata ɗakin sannan tayi picking.
Ya sauke ajiyar zuciya ya ce"love ki na ina?yau kwata kwata ban ga kyakkyawar fuskarki ba."
"Ina ɗakin Mami".
"Nayi kewar ki my love".
Ta lumshe ido ta ce"nima haka".
"Ki min alƙawari idan na dawo za ki fito".
"In sha Allah".
Ya ce"alright,take care,I love you".
"Love you too".
Da yamma aka yi Henna,da kyar Zarah ta yarda aka mata,sai da Mami tayi da gaske sannan ta zauna.
********
Ƙarfe biyar na yamma ya tsaida mota a wani madaidaicin gida,ya fito yana sake bin Street ɗin da kallo sannan ya karasa gaban gidan ya ƙwanƙwasa.
Wata mata ta buɗe tana kallon sa da alamar rashin sani,ya ɗan mata murmushi ya ce"I'm Umar Sadauki,Your husband colleague Olatunji,if you don’t mind, I’d like to ask you some few questions.”
Yayi maganar tare da nuna mata ID card ɗin sa.
Ta ɗan yi jim sannan ta ce"alright you can come in".
Ya cire takalmansa ya shiga,yara biyu ya gani mace da namiji suna cin abinci.
Ya ɗurkusa kusa dasu ya basu hannu ya ce"hello,how are you?"
A tare suka ce"were fine".
Ya kalli namijin ya ce"your name?"
"My name is Tobi".
"Wonderful,and you?"
"Bisola".
Ya shafa kanta ya ce"beautiful".
Ya miƙe ya zauna kan kujera,kana ganinta ka san tana cikin damuwa.
Ya maida hankalinsa gabaɗaya kanta ya ce"thank you ma'am".
Tayi murmuhsi ta ce"don't mention".
Sadauki ya ce"shekarar ku nawa da aure da mijin ki?"
A hankali ta ce"goma".
Ya gyaɗa kai ya ce"wani irin mutum ne shi a gida?"
"Gaskiya mutum ne mai sauƙin kai sosai,kullum burinsa ya faranta mana rai".
Ta fashe da kuka mai zafin gaske,shiru kawai yayi yana kallon ta.
Sai da tayi mai isar ta sannan tayi shiru.
A hankali ya ce"I'm very sorry".
Tayi murmushi mai ciwo ta ce"kar ka damu,tunda mijina ya mutu nake kuka,ba zan daina kuka ba sai ranar da nima na mutu".
Gabaɗaya jikin Sadauki ya gama sanyi,ya ƙarfafa kan shi ya sake bata haƙuri sannan ya ce"mijin ki na da matsala da wani ne,kamar abokin faɗa haka?"
Ta girgiza kai ta ce"babu gaskiya,kowa na shi ne,he's very jovial".
Ya gyaɗa kai don shima shaida ne,ya ce"kafin ya rasu,kin fahimci wani sabon hali haka da ba nasa ba?"
Ta ɗago ta kalle shi da sauri,sai kuma ta sunkuyar da kai ta ce"eh,sati biyu kafin ya rasu na lura kamar ya na cikin damuwa,idan na tambaye shi sai ya ce babu komai,gajiyar aiki ne kawai,daga baya sai na lura ana yawan kiran shi a waya".
"Kin san me kiran?"
Ta girgiza kai ta ce"ban sani ba gaskiya,idan an kira ya kan miƙe ya fita waje".
"Kuma ba ki taɓa jin abinda yake faɗa ba?"
Ta girgiza kai ta ce"sau ɗaya na taɓa zuwa na leƙa sa saboda hankalina ya kasa kwanciya da wayar da yake,rai ɓace na ji ya ce shi dai ba zai yi wannan abin da suke so ba,daga nan ya kashe wayar".
"Akwai wanda ya taɓa zuwa wurin sa?"
"Babu gaskiya,amma tun daga lokacin na fahimci a tsorace yake,da wuri yake dawowa gida ya kulle ko'ina,ya daina samun isasshen bacci tun daga lokacin har ya mutu".
Sadauki ya sauke numfashi ya ce"Nagode sosai,zan iya dawowa kowanne lokaci,take care of yourself and the children".
Ya miƙe ya ajiye mata envelope kusa da ita ya juya ya fita.
**********
Da safe aka yi walima,amare sun sha kyau,ko wacce ta shirya cikin atamfarta da babban mayafi.
Zarah na zaune kusa da Aunty Zeenah ta riƙe mata hannu kamar za'a kwace ta daga hannunta,sanye take da Abaya baƙi, tayi wani irin kyau kamar ita ce amaryar.
Tun jiya hankalinta ke tashe ganin Aunty Zeenah zata tafi ta bar ta,idan dai Aunty Naima ne ko a jikinta don ba wani shiri suke ba.
Ƙarfe sha biyu na rana aka gama walima,tana ƙoƙarin shiga ciki ta ji an kira sunanta,ta juya da sauri,ganin Ya Abdallah yasa ta ɗan tsaya tana kallon shi.
Ya mata alamar ta zo da hannu,a sanyaye ta nufi inda yake tsaye yana danna waya.
Sai da ta iso kusa sannan ya ɗago ya zuba mata ido,ta ɗauke kai da sauri.
"Kawo min abinci,ina ɗakin Oum".
Ta juya ta bar wurin ya bi ta da kallo.
Kitchen ta shiga ta haɗa fried rice da pepperd chicken cikin kula ta fito,part ɗin Hajja ta shiga dake nan shiru babu hayaniyar mutane.
Ta buɗe ƙofar ɗakin Oum ta shiga da sallama,yana zaune kan gado ya ɗago ya zuba mata ido.
Ta ajiye kulan a ƙasa tana ƙoƙarin miƙewa ta ji an riƙe mata hannu.
***********
Yana zaune a office yana duba wasu file aka turo ƙofa da ƙarfi,rai ɓace ya ɗago don ganin wani isasshen ne.
Bilal ya karaso gaban shi da sauri ya ce"Falcon".
Ya zuba mishi ido ganin yadda hankalinsa ke tashe.
Da ƙyar ya iya cewa"lafiya?"
"matar Ola ta mutu tare da yaranta".
Book 1 ya kusa ƙarewa which is free,Book 2 na kuɗi ne.
***