Free chapter 路 Read without an account
7
by Asmy b Aliyu 路 OMRI HAYATII
OMRI HAYATII馃┓
Asmy b Aliyu
7.....
Ya Allah ya fada Yana dafe kirjinsa da yake jin Yana masa wani irin zafi da radadi
Banda kalaman Mamin da yake jin Suna masa yawo cikin kunnensa babu abunda yakeji.
no Mami!!"ya fada da Karfi Yana saka hannunsa duka biyu Yana dafe kunnuwansa,dan allah ya fada da muryar roko Yana wani irin rufe idanunsa,da wannan yanayin ya karasa bedroom dinsa
ya samu ya cire jallabiyyar jikinsa anan kasa ya jefar daita. daga shi sai boxer ajikinsa da farar vest din da ta kamasa sosai hannu ya saka Yana Kashe makunnin fitila. duhu ya bayyana kan bed dinsa ya kwanta ya jawo Karamun pillow ya manna cikin kirjinsa.a wannan lokacin shiru kawai yake bukata mafita yake nema,baya son jin motsi komai da kowa a kusa dashi Yana jin wayarsa ta fara ring acikin duhun ya lalubi wayar hannunsa
Yana kaiwa inda hasken wayar take
Kashe wayar yayi duka Yana yin jifa daita a gefe batareda ya damu da Wanda ke Kiran nasa ba......ko kadan bayada hakurin daukar tashin hankali shiyasa lokaci daya yaji kamar zai zare kan bed din kasa kwanciya yayi Sai ya dawo kasa kan rug ya kwanta Yana kankame jikinsa wuri daya
Yana jin sanyi dake cikin dakin Yana shiga cikin jikinsa Yana huda ko wace gaba ta jikinsa Yana daskarar da jinin dake aiki
cikin jikinsa.wani irin xarewa da xaucewa
yaji yanayi lokaci daya akan soyayyar malaak farook rano Wanda ya tabbatar idan Mami ta tsayarda wannan soyayyar
tamkar ta fisge masa sauran numfashin dake aiki ajikinsa ne .dan yasan soyayyar malaak din itace numfashinsa da bugun zuciyarsa......acikin dare banda mafarkin malaak din babu abunda yakeyi
haka ya kwana da mugun xaxxabi da ciwon Kai. ko sallar asuba bai samu fita ba,
adaddafe yayi sallar cikin dakinsa
Yana idar da sallar batareda yayi dogon azkar ba ya koma ya dukunkune kansa
cikin duvet banda rawar sanyi babu abunda yake a wannan lokacin.
acan Kuma bangaren Mami ganin har Karfe 7 mu'azzam din bai fito ba baizo ya gaisheta ba kamar yadda ya saba duk lokacin da ya fito daga massalaci Sai yazo bangaren Mamin Sun gaisa kafin ya koma nasa bangaren.Mami bata wani damuba
ta cigaba da harkokinta,ta shiga kitchen ta dafawa Abba bakin tea da yaji kayan yaji na gargajiya Wanda duk safiyar Allah Sai ya shasa kafin yaci komai,tayi wanka ta nufi bangaren maigidinta kamar yadda ta saba.banda kamshi babu abunda ke tashi ajikinta daman Kuma Mamin asalin ya'r gayuce duk da shekaru Sun ja
hakan bai sa ta daina gayu ba da kula da maigidanta da tattalinsa.da sallama ta shiga bangaren Abba dauke da madaidaicin tray a hannunta,cike da kulawa Abba ya kalleta gamida amsa sallamarta lokaci daya Kuma murmushi na bayyana a fuskar Abba.taja dan Karamin center table a gaban Abba ta dora tray din,zama kusa da abban tayi ta Kara gaishesa da respect jawota yayi a jikinsa
Yana subbatar goshinta yake fadin"kin tashi lafia maman Yarana."dan haka Abban ke kiranta yawancin lokutta,Kara lafewa tayi ajikin mijin nata ,take fadin lafia kalau Abbanmu."
dan janyewa tayi daga jikinsa ta dauki cup tana tsiyaya masa ruwan zafin,bayan ta zuba ta dauki xuma ta zuba kadan
Banda tiriri da kamshin babu abunda ke fita cikin bakin tea.bissimillah mami ta fada tana mika masa cup din hannu
yasa ya amsa Yana fadin nagode."gyada Kai kawai tayi ,shi dai Abba Yana kula da yanayinta tamkar akwai abunda ke damunta ya kula ko kadan batada walwala.......yau mu'azzam bai fita massalaci ba hop all is well?"juyawa Mami tayi tana kallonsa kafin tace nima tun jiya da dare bamu sake haduwa ba.
tunda kaji shiru Kaima kasan lafia."da haka Mami bata Kara magana ba.da alamar batason hirar mu'azzam din da Abba ya kawo mata ,shiru abba yayi ya cigaba da sipping bakin shayinsa haka Yana nazari
yanayin Mami,inaga nan da jibi zamuje kasar Italy nida mu'azzam zamuyi meeting na gaggawa a daya daga cikin companys dinmu dake acan.bazamu dai wuce sati daya ba insha Allahu."mami ta gyada Kai
tana fadin"Allah ya kaiku lafia ya dawo daku lafia ya bada Kuma nasara akan abunda akaje nema."
"Ameen ya hayyu ya kayyum."
wuraren qarfe 9 ya shigo bangaren Mami,
dan Sai lokacin ya samu zazzabin da ya lullubesa ya sauka,Sai da yayiwa kansa
allurar da Zata saukar masa da xaxxabin.
Mami ta amsa sallamarsa tana dauke kanta akansa ta cigaba da yiwa kaka bayanin kayan cefanen da Zata hado masu a kasuwa wanda driver ne zai kaita idan tagama ya dawo daita.ya xauna Yana gaisheda kaaka da respect,ta amsa cike da kulawa da fara'a take fadin"mai babban suna bakada lafia ne ya naji muryarka haka??"ta fada cike da damuwa da Kuma kulawa .dan gyaran murya yayi Yana fadin"lafia kalau kawai mura ce ke damuna.to Allah ya Kara sauki
bara na hadamaka bakin tea mai kayan yaji aciki zakaji dama dama,da haka kaaka ta mike ta kalli Mami tana fadin"hajia
ayimun afuwa bari na hadamasa Sai na taho na tafi.mami ta gyada Kai batareda tace komai ba kaaka ta juya ta nufi hanyar kitchen.
"Mami!!"
ya fada cikin rawar murya,ganin yadda Mami ta wani sharesa da alamar ma fushi
take dashi ,shi ya kamata yayi fushi ba mamin ba.sai dai ko kadan bayason yaga mamin fuskarta ta sauya nan take zai Shiga tashin hankali,Mami!......wannan karon ya Kara fada da dan sauti a muryarsa sautin da ya tabbatarwa da mamin da gaske mura yake.mikewa tsaye Mami tayi tana masa wani irin kallo
da yaji wani abu ya tsaya masa a wuya.......
"zan baka lokaci harka dawo daidai
baxan takura Kaba take your time."
Sai dai ka sani har abada aure ya haramta tsakaninka da malaak farook rano!!!..wata irin kwallah yaji tana cika idanunsa,
haka yaji zuciyarsa yaji ta Kara yimasa wani irin nauyi da wani irin radadi da yakeji
yabi Mami da ido da idanunsa da suka dade da canja Kala.
jinginar da kansa yayi jikin kujerar ya runtse ido Yana fitar da wani irin numfashi mai zafi ta cikin bakinsa.bayan wasu mintuna yaji muryar kaaka akansa tana fadin"yawwa gashi kayi kokari ka shanye insha allahu zaka samu sauki,harda AC.nan da kake Sha kullum gida AC mota AC,office ma AC.ba dole mura ta riqeka ba.allah dai ya sauwakka,ga abincin Karin kumallo can kona debo na kawo maka.??"da sauri ya karbi cup din hannun kaka Yana girgiza mata Kai wani abu mai daci da nauyi ya hade kafin yacewa kaka ya gode...juyawa kaka tayi ta nufi dakinta da shiryawa ta wuce kasuwa.
yafi awa daya zaune a falon ya dauka Mamin Zata dawo Sai dai tsit kakeji
ga gidan yayi wani irin shiru daga fareeda har Ayusherh Sun tafi makaranta tun safe,dakyar ya shanye bakin tea hannunsa
ko mai baya masa dadi a baki.yana gama Sha ya miqe ya nufi kitchen ya wanke cup din ya mayar dashi inda aka tana dan ajesu ya juya yabar kitchen din,bayason Abba ya gansa cikin wannan yanayin shiyasa baiyi tunanin zuwa bangaren Abba ba,Kai tsaye bangarensa ya koma
Yana jin wani sabon xaxxabi na Kara saukar masa.har lokacin Kuma bai kunna wayarsa ba saboda yasan halin naci
irin na malaak.......a ranar haka ya Yini a daki itama mamin fili ta basa
ya sauke duk abunda yakeji a zuciyarsa bata wani takura masa ba ta cigaba da hidimominta ,da rana ta saka fareeda ta shigar masa da abincin rana har bangarensa saboda a ranar Kasa zuwa clinic yayi.a falo fareeda ta tarar dashi
itama da ta gansa cike da damuwa take fadin"yayanmu baka lafia ne??"idan kin aje ki fita ."Ya fada fuska daure,ganin haka yasa fareeda ta fita batareda ta Kara furta kalma ko daya ba.....Sai da Abban ya dawo bayan ishaai ya tafi bangaren Abban dan duk ranar basu hadu ba ,
bayan shigansa bangaren Abba ya gaishesa cike da kulawa Abba ya amsa Yana karewa yanayin mu'azzam din kallo kamar an cire masa kuzari yadda yake yin abubuwa a sanyaye.ya dade falon na Abba
suna tatauna tafiar da zasuyi kasar Italy,
duk damuwar da yake ciki kasa gayawa Abba yayi Shima abban bai matsa masa,
tare sukaci abincin dare da Abba,
itama fareeda tana gefen Abba
ta kawo masa list din kayan kwaliyyarta
da suka Kare haka ta hada da perfumes duka tayiwa Abba list ga nata gefe gana Ayusherh a gefe.dan kusan komai iri daya ake yimasu itada Ayusherh,daga Mami har Abba babu Wanda yake banbanta tsakaninsu
"ki baiwa yayanku list din ya duba.dan Jim fareeda tayi dan idan Zata shopping haka ko kadan batason Abba ya hadata da Yaaya mu'azzam.
mika masa list din hannunta tayi
ya duba takardar yaga total din ko wane kudi a kasa,ya daga Kai Yana zuba mata idanunsa masu kasheta da gigitata
kafin ya bude baki Yana fadin"are you crazy?""""dan tura baki tayi ta murtuqe Fuska ba kudin dana Kara wallahi
komai yadda kudinsa yake haka na rubuta."ta fada tamkar xata fashe da Kuka,
a zafafe ya kalli Abba Yana fadin Abba
kusan 800k fa na Ayusherh 400k
Yarinyyar nan bata da saiti.
cikin dacin rai take fadin"Ayusherh abubuwa kadan zata siya saboda tana da sauran abubuwa nikuma abubuwan da zan siya sunada yawa.yadda zuciyarsa ke tafasa tamkar zai kaimata mari
Sai kawai ya jefa mata list din
ya miqe yayiwa Abba Sai da safe ya nufi
kofa.daga fareeda har Abba binsa sukayi da ido,fareeda ta kalli Abba tuni hawaye suka cika idonta take fadin"nidai dan Allah Abba Kar kace shi xai bamu card dinsa
idan zamu tafi shopping kaga yadda yake behaving tun yanzu."
Yana iya fadin kowace 100k xata dauka ba wani babban aikinsa bane,shi idan ransa na a bace na kowa ma Sai ya baci
nidai wallahi babu ruwana Abba karka hadamu dashi ka bamu card dinka muyi using dashi......."Fareeda ta karasa maganar cike da rigima tana wani harde hannunta akan kirjinta tana jiran taji hukuncin da Abban zai yanke......
#ASMY B ALIYU
#LOVE/FATE
#BEST LOVE
#BEST STORY
#MU'ZZAM MARAFA
#FAREEDA MARAFA
#AYUSHERH MARAFA
#OMRI HAYATII
#***