Free chapter 路 Read without an account

Page 13

by khadijah danasabe 路 TASWIRAR KADDARA



*TASWIRAR KADDARA*




  DijahAM(Oum Amani)




Page 13




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM






  Shiru su Abba sukai kawai suna binta da kallo ganin kukan da take, ni kuwa sai da naga Mimi tana kara volume dn kukan ta sannan nayi shiru na goge hawayena ina rarrashin ta cikin lokaci kankani tai bacci.




Ajiyar zuciya Abba ya sauke yace "Batul bawai muna son takura ki bane ko mun gaji dake, a'a kawai muna son ki samu farin ciki ne kema. Yusuf ya yadda da dukka abinda ya Faru yace zai aureki kuma zai rike Mimi, ba dama shine damuwar ki ba?"




Shesshekar kuka kawai nake na kasa magana taya Abba suke tunanin ma wai Zan iya auren Yusuf, ai baxan taba wannan cin amanar ba.




Tsaki Umma tai tace "kai ne kake lallaba ta Abba, ai ita ba yarinya bace shekara 19 zata shiga sa'annin ta sun fara aure suna zaune dakunan mazajen su, amma ita tana nan tana shirmen baza tai aure ba, nidai a matsayina na Mahaifiyarki ina baki shawara daki zauna kiyi tunani da kyau, har yaushe zaki cigaba da zama da tabon dake cikin zuciyar ki?"




Lumshe ido nai kawai ban yi magana ba, Dan murmushi Abba yai yace "bazan Miki dole ba Batul, amma ta bakin mahaifiyar kine ki zauna kiyi tunani Allah ya zaba Miki abinda yafi alkhairi, zan bawa shi Yusuf din numbern ki kuna gaisawa"




Daga haka ya kalli Umma yace suje su kwanta, na dade a zaune a gurin kafin na mike na dau Mimi na shiga dakin mu, kwantar da ita nai na Mata addu'a na zubawa Aisha ido dake bacci.




Nima kwanciya nai na lumshe idona ina tunanin shin su Abba basa jin kamar cin amana zanyi in na auri Yusuf?




Shiru nai na dade ina tunani ganin kwakwalwata tana daukar zafi yasa ni mikewa naje nayi alwala nazo na tayar da sallah ina neman zabin Allah akan wannan al'amarin daya danno kai cikin rayuwata.














**********




 Shan fruit dinsa yake hankali kwance yana kallo, dagowa yai a karo na uku ya kalli Zainab data ke kaiwa da komawa tunda ta gansa a Palourn tana sanye da English wear riga da skirt da suka kamata, sai turo kirji take tana wani karairaya kamar zata karye.




Maida dubansa gurin Mami yai ta dago itama ta kalle sa, murmushi yai yace "Maa wai ni ake son a yaudara ake wani ciko ana turo kirji"




Kama baki Mami tai ta dan saci kallon Zainab data fito daga kitchen hannun ta rike da cup, maida dubanta gurin Azlan tai tace "ban gane ba?"




Murmushin gefen baki yai ya dan sosa bayan kunnen sa yace "turo ta uwar tai tazo tana ciko tana karairaya saboda nace mata kwaila ce ta min yarinya bata san ina gane ciko bane hala"




Girgiza kai Mami tai tace "wai yaushe zaka nutsu Ka rage rashin kunya ne Azlan?"




Waro idonsa yai sosai yace "Maa wani abun nai kawai fa gaskia na fada"




Girgiza kai Mami tai tana masa addu'ar shirya a zuciyar ta.




Cikin fushi zainab data gama Jin komai ta shige dakin da aka sauke ta a Palourn ta rufe kofa, gaban mudubi taje ta zubawa kanta ido tasha heavy makeup sosai duk sbd ta birge sa gashi yau bra har 3 tasa Ashe ya gane ciko tai.




Cikin bakin ciki ta fashe da kuka, tunda tazo gidan basu hadu ba sai yau kamar yasan tana nan baya shigowa sai ya daidaici bata nan, gashi ita gaba daya zaman gidan ya gundureta bata wani sakewa, da sassafe take fita gidan kawayen ta suyi ta yawo joint joint suna chilling sai ta kwana ta yini ma basu hadu da Mami ba.




Wayar ta ta janyo dan kiran Mummy saboda ta gaji so take ta koma gida gaskia, asan kuma yadda za'a yi tunda wannan hanyar da suka dauka tun ba'a je ko ina ba ya gane.






A Palourn kuwa Azlan ajiye bowl din da yake shan fruit dn yai ya kalli Mami yace "Maa in tambaye ki don Allah"




Maida hankalin ta Mami tai gunsa Jin yai magana cikin nutsuwa sosai kamar ba Azlan ba, ajiyar zuciya ta sauke tace "ina Jin Ka"




Sai da ya dan yi shiru na kamar 2 minutes sannan yace "mai yasa wasu suke sa hijab kullum ne wai Mami basa jin zafi suna yawo da hijab dogo har kasa kullum a cikin rana"




Bin sa da kallon mamaki Mami tai tunda take da Azlan bai taba mata maganar abinda ya shafi Mata ba ko kuma yanayin shigar su ba, ganin kallon da take masa yasa shi fadin "shiknn ma"




Murmushi Mami tai tace "Hijab mutunci ne ai Azlan, kuma Allah ne ya umarci mace data rufe jikinta, kawai ba'a amfani da koyarwar musulunci ne amma duk wadda kaga tana sa hijab tana yi ne don rufe jikinta da kuma killace jikinta, abinda matan ynxu basa ganewa ita mace Mai DARAJA ce ZAKI bai kamata komai nata a same sa a arha ba"




Ruwa tasha tana kallon yadda ya mai da hankalin sa sosai kanta yana sauraran ta hakan yasa ta cigaba da fadin "dukda ynxu wasu suna amfani da hijab din gurin fitsara sai kaga yarinya tasha dogon Hijab har kasa amma da zaka bude hijab din tsirara take amma ba duka aka zama daya ba, Shi Hijab rigar mutumci ne kuma ana ma duk wacce take yawan sa shi tana rufe jikinta kallon Kamila."




Gyada kai yai ya juya, murmushi mami tai tace "amma dai mai yasa Ka tambaya Zaki"




Dan tabe bakinsa yai yace "wata fitsararriyar yarinya ce take sashi kullum na ganta dashi nake ganin ta, amma abinda yake ban mamaki meyasa mara kunyar yarinya zata dinga sa hijab a university kullum, kowa dai yasan bata da kunya tunda bata ma yawo da Mata sai Maza kullum zaka ganta ita da wani gardi a gefen ta sun jera suna tafiya," sai kuma yai tsaki ya kalli Mami yace "wai uwar dakina gardin yake ce Mata fa katon saurayi yana fadawa karamar kanwar sa uwar dakina ita kuma amsawa take. Ita ke fada amma ni ke ji mata kunya"




Murmushi kawai Mami take zatai magana Junaid da tunda Azlan ya fara magana ya shigo ya tsaya yana ji yace "Wace mai sa'ar ce wannan datai tsaye a xuciyar mazage har yake maganar ta yau, Mami da gaske ne abinda kunne na ya jiyo min yau Azlan ne yake maganar wata mace gaskia yau ranar ta musamman ce har sadaka zanyi Ashe dai aljanar da muke zargin ta aure Ka ta sake Ka"




Kallon Junaid yake yana kankance idonsa yace "Junaidu yaushe na fara wasan banza dakai?"




Kama baki Junaid yai yace "wai Azlan nida kai waye babba ne?"




Mitsi mitsi yai da idonsa har ya bude baki zai magana kawai kuma sai yai shiru ya janyo lip dinsa na kasa yana tsotsa ahankali.




Murmushi Junaid yai ya zauna a kasa kusa da kafar Mami suna gaisawa, juyawa yai ya kalli Azlan daya hade rai yana kallo yace "Zakin Baffa yaushe zaka zo gidana ne wai kaci abinci, kullum sai Samira tamin korafi akan baka zuwa Ka daure kazo don Allah ko weekend ne"




Juyowa yai ya zubawa Junaid idonsa daya sha kwalli sai sheki suke kafin yai tsaki yace "Allah ya kiyaye naje gidan kanwata cin abinci sai kace wani mayunwaci zaka ce nazo gidan Ka cin abinci"




Girgiza kai Junaid yai yace "koma meye ai ta zama yayarka tunda tana auren yayanka ko?"




Mikewa Azlan yai ya kalli Mami yace "Maa bara naje gurin Abie ina son magana da shi, sannan ki dinga min addu'a sosai MAA plz ana kawowa budurcina hare hare sosai. Yau da kyar na sha baki ga ba wata student tazo min duk kirjin ta a waje sai nuna min take, in ba karfin addua ba da tuni yau an kawar da abinda nake wa Iyalina tanadi"




Daga haka ya sa kai ya fita daga palourn, yana takunsa cikin jarumta, binsa da kallo dukansu sukai kafin Junaid ya kalli mami a tare suka saki dariya...






Part din Abie ya nufa don yasan ynxu haka yana gida, sai da ya tsaya yai knocking kofar aka basa ikon shiga sannan ya shiga, Abie ne kawai a Palourn sai Mama a gefensa tana hada masa tea.




Karasowa yai ya zauna a kan kujerar dake kallon ta Abie yace "Ina wuni"




Binsa da kallo Abie yake yana karantar sa yace "lafia qalau ya aikin"




Gyada kai kawai yai ya kalli Mama da tun shigowar sa ta maida hankalin ta kan abinda take yace "Evening Hajia"




Dan dagowa tai ta daga masa kai kurum ta mikawa Abie tea dinsa tana gyara zaman ta don ba inda zata je zama zatai duk abinda zasu tattauna itama ayi agaban ta taji.




Jin yaki magana yasa Abie fadin "Ina sauraren ka"




Dagowa yai ya kalli Abba yace "so nake nabar lecturing din da nake don bana jin zan iya Abie"




Jinjina kai Abie yai shidama yasan ba'a banza ba Azlan zai shigo gurinsa saidai in wani abun ne, ya dan Jima yana nazarin sa saidai ba alamar ko da Wasa yake dukda dama yasan in har zaiyi magana Abaya fada da Wasa iya gaskiar sa yake fada.




Gyada kai Abie yai yace "ko Zan iya sanin dalilin dayasa kake son barin lecturing din?"




Kai tsaye yace "fyade ake son min yau saura kadan wata ta rabani da budurcina da kyar na sha"




Sunkuyar da kai Abie yai yana shan tea din sa yayinda Mama ta shiga girmama lamarin rashin kunyar Azlan wai fyade aka kusa masa.




Dagowa Abie yai yace "dama ana yiwa namiji fyade ne Azlan"




Gyara zaman sa yai yadan lashi jajayen lips dinsa yace "sosai ma tunda naje makarantar nan Mata suke kawo min hari, sai suna shiga ta banxa suna zuwar min office da sunan wai Zan koya musu abu basu gane ba ko kuma kai tsaye su aiko min da letter wai suna Sona"




Shiru yai ya kalli Abie ganin Shi din Abie yake kalla yasa shi fadin "yau wata shigo min tai cikin masassun Kaya ya bude Rabin kirjin ta haka ta janye mayafi kuma ta sunkuyo yadda in na dago dole idona zai fada cikin rigar ta, ina dalili ina da lafia fa Abie don banyi aure ba bawai hakan na nufin ina da nakasu bane lafiyayyan namiji ne ni, toh shiyasa tun kan wataran sufi karfina su hadu su lalata ni na shiga uku nace xan yi resigning"




Murmushi Abie yai yace "mai yasa kai baza Ka dau mataki ba da kanka"




Shiru yai don ya fuskanci Abie bawai xai goya masa baya bane gashi yai wa Baffa alkawarin bazai yi resigning ba sai da izinin Abie.




Mikewa kawai yai ya tura hannun sa cikin aljihu yace "sai da safe"






Binsa da kallo Abie yai yace "Allah ya cigaba da tsare min kai"




Tabe baki Mama tai ta juya keya tana kallo, itafa iskanci Azlan yana isar ta komai budurci ta rasa gidan uban waye yake da budurcin, bayan kowa sheda ne akan rashin jinsa da yadda yake zuwa club duk dare..








********




Washe gari da ciwon kai na tashi hakan yasa Abba cemin na kwanta basai naje makaranta ba, Asma'u na Kira nace don Allah tamin attendance baxan samu zuwa ba banda lafia, sosai ta nuna damuwar ta har tace da zata biyo in an tashi nace mata da sauki ai ciwon kan kafin muyi sallama.




Ina kwance a daki ina kallon Aisha dake shirya Mimi don bana Jin zan iya shirya ta da kaina sbd yadda kaina yake min ciwo, tun ina kallon su har bacci ya dauke ni bansan yaushe suka tafi ba.




Ban tashi ba sai karfe 11 saura, a hankali na mike ina mika duk jikina ciwo yake min kodan sbd baccin da bana yi ne na safe yau kuma na samu nai.




Fitowa waje nai banga Umma ba nasan tana dakin ta, wanka nai ma shirya cikin simple riga na dauki breakfast dina ina cikin ci naji wayata tana ringing, banza nai da ita ganin sabuwar number sai dai kirin da aka sake yi ne yasa ni daga wayar.




Ciki ciki na yi sallama muryar data amsa nice tasa gabana faduwa, daure wa nai nace "waye yake magana"




Daga dayan bangaren aka ce "Yusuf ne........"














Wai shin waye wannan Yusuf din ne馃馃




Mai yasa Batul bata son ta aure sa shin amanar waye zata ci da take cewa in ta aure sa taci amana馃馃馃









***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol