Free chapter · Read without an account
Chapter 5
Ƙazafi
Page 5
By
D BUGAJE
> Take ta ji ba ta kyauta ba, ta shiga ba shi hakuri, har suka isa bakin babban titi. Inda suna isa suka hau keke-napep sai gida, bayan sun sallami mai ƴar kurkira sun yi masa godiya.
> Da misalin ƙarfe goma muka isa ƙofar gidan mu muka shiga tare da Yaya Najeeb, inda kuma na sake samun wani abin tausayi. Yaya Salima ce kwance a ƙasa, ga abin shimfiɗa amma ta gaza shimfiɗawa, sai sauro ke binta, babu hannun korewa, ga zafi don lokacin zafi ne, sai hawaye kawai ke bin fuskarta har ma ya bushe don bnaccī take. Take Sireenah ta tayar da ita ta yi mata...Shinfiɗa ta ɗaura mata gidan sauro ta ce ta shiga ta kwanta, sai da ta kwanta lafiya lau kafin Sireenah ta shiga cikin ɗakin da sauri ganin hayaki yana tashi. Yaya Na'ima ce kwance akan kattifa, itama baccin take, an kunna maganin sauro shafto har ya fara kama kattifar bata saniba.
Yaya Najeeb ne ya yi saurin jika kattifar suka yi masu komai kafin suka fito a tare don neman Yaya Saratu saboda bata gidan. Hanyar Asibiti suka nufa don ganin halin da Mama take ciki, da kuma ganin ko can Yaya Saratu ta je.
Suna isa bakin babban titi inda za su hau keke-napep, suna tsayawa wayar Yaya Najeeb ta hau ruri, wacce (Itel) ce ƙarama mai malatsai, take ya ɗauka ya ƙara a kunnansa.
"Subhanallah to gani nan yanzu zan zo."
Sune kalaman da suka shiga kunnuwan Sireenah inda kuma ta hau kallon sa da mamaki a fuskarta.
Yana sauke wayar ya kalleta cikin rikicewa ya ce, "Sireenah jikin Baba ne ya motsa wai yana aman jini, zan je mu kaisa Asibiti."
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Subhanallah yau mun ga rayuwa, Allah Ubangiji Ya ba shi lafiya, ka hanzarta kaje, na gode sosai."
Sai da ya ba ma Sireenah kuɗin keke-napep kafin ya bar wajan.
Tana juyawa da nufin tsayar da keke-napep ta ji _keeeyyy_ ƙarar jan birki, da sauri ta juyo tana kallon motar, aiko ta yi mummunan gani da motar da ta tsani ganinta a duniya, da ma mai motar baki ɗaya wato Faisal.
Zuge glass ɗin motar ya yi na gidan baya, take fuskar Yaya Saratu ta bayyana, fuskarta tayi jage-jage da hawaye da majina da alama ta sha kuka har ta gaji. Cikin tashin hankali da firgici Sireenah ta kalli Faisal.
Ya ko sakar mata wani shu'umin murmushi wanda ya sa gabanta ya yi wata irin mummunar faɗuwa. Kafin ta mai da kallon ta ga Yaya Saratu, kuka take tana mata magana cikin yaren ɓebanci, gwanin ban tausayi, duk irin yadda ta iya maganar sai ta kasa gane abin da take son ta faɗa mata, kawai sai ta mai da kallon ta ga Faisal tana cewa,
"Faisal me ya haɗa ka da 'yar uwata? Me taimaka? Me za ka yi mata? Ka ji tsoron Allah beebiya ce fa?"
_tsuuut_ ya ja tsaki kafin ya ce, "Ke wannan abin ya shafa ni, ke kaɗai nake da buƙata. Ke ce ki ka ja mata tun da kin ƙi ba ni dama sai yawo ki ke yi mini da hankali. Ba zan mata komai ba miɗɗin ki ka kawo min kanki, ga katina yana ɗau ke da address ɗin da zaki Same ni .”
Ya tullo mata wani ƙaramin kati ƙasa kafin ya ɗaura da faɗin, "Cikin daren nan za ki zo, inko ba haka ba to rayuwar 'yar uwarki tana cikin haɗari kuma ke ma ba zan bar ki ba don ina buƙatar ganin ki."
Yana kaiwa ƙarshen maganar ya zuge glass ɗin motar ya ja ta a guje ya bar wajan, bayan ya baɗe ta da ƙura. Sunkuyawa ta yi ta ɗau katin sai ta ji hawaye na bin fuskarta, kanta ya kulle ta nemi natsuwa ta rasa. So take ta yi tunani amma hakan ya gaza samuwa, sai ta rasa inda za ta nufa tsakanin bin bayansa da kuma zuwa Asibiti don ganin halin da ake ciki. Sai kawai ta fashe da kuka mai sauti, a zuciyarta take faɗin, shin kasantuwata mai kyau laifine da kowa zai dinga bibiyata ana son ɓatamin rayuwa? Ko talauci ne ya ja man? Miyasa ƙaddara za ta mini haka ba ta duba na yi karanta da za ta dinga zoman da manyan abubuwa masu taɗa hankali, to me a jikina da za su dinga burin kusantata, meyasa ba za su aure ni ba sai nemana da sharri, ƙayya ƙayya wacce bata cikin yabo lallai yau ina cikin tsaka mai wuya.
> Ƙiƙiyy taji an ja ta da sauri, tana ɗagowa ta ga mai mashin ne ya tafi da ita saboda yadda ta matse ma titi har abayarta ta maƙale ga kan mashin ɗin ba tare da ta ankaraba, da sauri mai mashin ɗin ya taka burki yana bata hakuri bayan ya cire mata abayar daga kan mashin ɗin wacce har ta fara kecewa.
> Sai a sannan ta dawo hayyacinta, ta ce da mai mashin ɗin “Allah Ya tsare Ya kare gaba, babu komai tunda ni ce da laifi”.
> “To na gode Allah Ya kare gaba” ya kai ƙarshen maganar yana ƙoƙarin tayar da mashin ɗin ya yi gaba.
> Dole ta sa Sireenah komawa gida don abayar ta kece sosai kuma har takalminta ma ya tsinke dama ya kusa saboda ya dafe da saye duk ya tsufa.
> Tana shawowa kwana ta sami cakurindon jama'a a ƙofar gidan su, Dam! Gaban ta ya yi wani irin mummunar faɗuwa, a fili ta ce me kuma yake shirin faruwa ne da ni a yau nina ga haza yau na ga takaina. Ta kai ƙarshen maganar tana taraɗɗaɗin abin da zai faru.
> Tana isa ta sami samari ukku suna ƙoƙarin saka Yaya Na'ima a cikin motar, ita ko sai ihu take tana kiran sunan Sireenah da na Baba, gefe guda ga Yaya Salima tana ta kuka tana ba su haƙuri da roƙon su akan su bar Yaya Na'ima, maganar kawai take iya yi amma babu hannun da zata saka wajen ceton ƴar uwarta, sai faɗi take “Don Allah ku rabu da ita makauniya ce bata ganin komai kiyama Allah ku bar ta”.
> Wasu irin hawaye ne masu zafi suka shiga gangarowa a cikin zuciyar Sireenah na tausayin yayyen nata, wajen cike yake da jama'a amma an rasa me yi masu magana bare kuma a sami wanda zai yi ƙoƙarin hana su.
> Sai da ta kutsa cikin mutane sosai kafin ta gane ko su waye Sauban ne da Khamis da Fahat da wani irin ƙuzari ta kai hannunta akan na Yaya Na'ima da nufin ƙwatar ta, sai dai suna yin ido biyu da Fahat ya saki hannun Yaya Na'ima yana faɗin “Ashe kina kusa kin zo a dai dai lokacin da ya dace”.
> “Me yasa kuke bibiyata? Ita kuma wannan me ta yi maku? Wai ta yaya kuka gano inda nake rayuwa”.
“Kin manta an ce garin masoyi baya nisa, ai mu sai dai idon ba mu so aikata abu ba amma ko menene sai mun yi don ba mu taɓa neman wani abu mun rasa ba kuma ba za'a fara akan ki ba”.
> “Ai ko za'a fara a kaina yau na ga ikon Allah kun zamemin mașifa daga haɗuwa yau sai ku biyoni har gida, na gaya maku ni ba irin matan da kuke nema ba ce ku rabu da ni ku bar ni tun kafin na zame maku mașifa don wallahi kuka kai ni bango sai kun yi dana sani, kuma babu wanda ya isa ya saka ni aikata sabo, idon kuka sake zuwa nan to wallahi hukuma ce zata raba mu da ku”. Ta kai ƙarshen maganar cikin ɗaga murya da nuna alamar barazana don sun fara kaita