Free chapter · Read without an account
THE WARMTH OF A FATHER!
by saddiqa.writes · NURI
Akan idonsa ta tsugunna a wajen ta fara kukan. Kukan da ko daga nesa mutum yake yana iya jiyowa bare shi da ba'a nesa yake ba. Bama shi ba, ya tabbatar duk wanda suke tare dashi suna jin kukan nata har ma da maganganun da take. Hannu ya dagawa babban aminin masa alamar ya dakata sannan ya juya kai tsaye ya nufi inda take a tsugunne.
"Assalamu alaikum... baiwar Allah..." Da sauri Nuri ta dago fuskarta tana share hawayenta don idan akwai abinda ta tsana yanzu bai wuce wani ya ganta tana kuka ba.
Akan magidancin mutumin ta sauke fuskarta, fuskar da take hango wasu kamanni na wani mutum data sani acikinta. "Tashi daga nan kinji akan yashi fa kika zauna.. Sannu kiyi haquri kinji..." Dan shiru yayi for some moments kamin ya sake cewa "dukkan tsanani yana tare da Allah.. kuma Allah yana jarabtar bayinsa da yake so ne kawai, so please enough of the crying. Kinyi ya isa... "
Maganganunsa kamar Maminta! Sak shigen kalaman da take amfani dasu wajen kwantar musu da hankli. Kallonsa ta sake yi, babba ne sosai don harda furfura akansa aqalla zai kai shekaru 62 a duniya, farin bafulatani usul da kallo daya zaka yi masa ka shaida hakan.
"Aliyyu ya dai ka santa ne?" Juyowa Abbie yayi ya kalli abokinsa Ibrahim kamin ya girgiza masa kai kawai ya maida kallonsa kanta. Miqewa Nuri tayi ahankali bata damu data karkade jikinta ba zata wuce Abbie yace "waye baya da lafiya?" Ba zata iya masa shiru yadda ta saba ba, saboda Mami ba tayi mata wannan goyon ba kuma ko ba haka ba ya cika mata ido akwai kwarjini atare dashi. Zata iya cewa shine mutum na biyu daya taba mata kwarjini duk duniya.
"Kakata ce."
Kai Abbie ya gyada yana cewa "kiyi haquri da tambyar da nake mki kinji..." Kai tayi saurin girgiza masa tana jin wani sabon kukan, kawai yadda yake binta a sannu kamar mahaifinta..the way he was speaking to her so softly reminded her of her father who was no longer with them. That made her burst into tears all over again. Ta tsugunna gaban Abbie ta fara wani sabon kukan.
Kallon Alhj Ibrahim Abbie yayi kamin yace dashi "I think you guys should take over from here. Ku je zan biyoku.. I need to comfort this little girl here." Kai kawai Alhaji Ibrahim ya daga masa yana juyawa baya shi kuma Abbie ya tsugunna nan gaban Nuri yana sake sassauta muryarsa fiye da da yace "I'm sorry. I shouldn't have asked you that. Taso muje naga Grandma din naki.. mene yake damunta?"
Tana kukan ta bashi amsa da "kidney stone, wai surgery zasu mata.." The way she ended her sentence told him everything he needed to know. Maybe they couldn't afford the cost, which was why he said "Let's go kinji? Za'a mata aikin lafiya. She will be okay In Sha Allah."
Da kukan ta kalli Abbie da tunda take bayan mahaifinta babu wanda ya kalleta da irin idon da Abbie ya kalleta babu, wanda taji kalmominsa kawai suna mata kama da na Abbanta sai Abbie (that feeling is so emotional... tunda suka taso family dinta kawai ta sani, Abba Mami sai Afif. Hatta Inna bata dubesu da idon rahama lokacin da suke da buqata ba. Sun rasa Abba sannan banda Fu'ad babu wanda ya taba looking after them bare ma aje ga wani ya jiqansu ko da kalma mai dadi ne kuwa).
Wannan muryar nata, wannan muryar shagwabar nata data dauka ta mutu ne yau taji ya dawo don for the past two years bata taba magana da irin wannan muryar ba. Ammn yau an samu wani daya farfado da wannan habit din "bamu da kudi Kuma she's seriously ill."
"Za taji sauqi. The bills are on me now. Muje na biya inasu Abbanki?"
"Ya Ilaahil Aalameen!" This man was bringing back memories she had tried so hard to bury deep in her heart. Kai kawai ta girgiza masa ba wani dogon bayani tace "she's all I have. Banda Abba da Mama....."
"Ya Salam!" Abbie ya furta yana cire hularsa dake kansa. Ba wai bai taba ganin mutane irin Nuri bane, no. Kawai dai haka kawai yaji wani iri kamar he's attached to the girl, kamar irin jininsa ce haka yake ji.
"I'm sorry, very sorry. Taso muje na biya ayi mata aikin kinji..."
Wani kallo more like na yara tayi masa tana goge hawayen dake fuskarta tana yiwa Abbie wani kallo irin na wanda ya sare dinnan tace "kudin da yawa.." murmushi yayi mata kawai don ya kwantar mata da hankali ya furta "All is well and will be In Sha Allah. Taso muje..."
Kai ta gyada masa ta miqe tana jin wani iri. Tun bayan qaddarar rasa Abba yau ne rana ta farko da wani babba magidanci yayi mata kalar abinda tasan Abbanta ne kawai zaiyi though this man was even older than her father. Itace agaba shi a baya har suka qarasa ward din da Inna take zuwa dakin da aka kwantar da ita. Suna shiga Nabeela ta miqe ta nufo Inda take "Ina kika shiga?" Girgiza mata kai kawai tayi tana yin gaba Nabeela ta gaisar da Abbie data lura kamar tare suke da Nuri. Da murmushi Abbie ya amsa mata suna qarasawa wajen Inna dake bacci. Ganin bacci take yi ya sashi cewa "zo ki kaini wajen likitan dake dubata kinji.." Kai ta gyada masa tana sake yin gaba suka wuce har office din likitan.
Bata wani zauna ba ta fito ta basu waje amman ta kasa barin bakin qofar dakin ta tsaya har zuwa sanda Abbie ya leqo da kansa ya kirata yana sake tambyarta dagske bata da kowa ne za'a yi signing takardar biyan kudin aikin ne ta tabbatar masa sai kawai shi yayi. A take awajen akayi fixing date din da za'ayi ma Inna aiki washegari da yamma.
Kasa godewa Abbie tayi ta sashi agaba tana kuka. It was as though her habit of crying had returned today as well. Shine ya rinqa bata haquri yana kwantar mata da hankali kamin ya miqe yace zai tafi bayan ya tabbatar mata zai dawo gobe idan za'ayi aikin ya dubata. Shi fa yarinyar tafi tsaya masa arai, especially because he could see a striking resemblance in her features. He left thinking about the girl. Pity was the strongest emotion he felt for her.
Nuri ma kusan hakan ne awajenta. At that moment, there was no one she wanted to talk to more than Afif. Kawai ta fada masa yau wani ya dubata irin yadda Abba yake dubasu. Fuskarta alokaci. yanda kasan anyi wiping damuwar da take ciki. Hatta Nabeela tayi noticing hakan don is hard kaga Nuri a irin wannan yanayin. Sai dai ta kalli Inna kawai tayi dan murmushi. Duk wani resentment da take having wa Inna taji babu shi. Taji kawai ta yafe mata dukkan abinda tayi mata don Inna has learned the hard way.
Hannun Inna ta kamo ta hade a nata tana yin magana qasa-qasa tace "Allahumma Yashfiki Inna..." Haka kawai Nabeela tayi murmushi tana kallonta kamin ta miqe ta dafata tana cewa "zan koma gida na shirya night duty ne dani kuma already lokacin shift din ya wuce..." Kai ta gyada mata tana cewa "Jazakillahu Khairan Nabeela ngd..."
"Haba babu komai Nuri Allah ya bata lafiya yasa kaffara ne."
Da "Aameen" Nuri ta amsa Nabeela ta fice. It now remained only Nuri and Inna along with the other patients sharing the room with them.
ABBIE'S POV
Yana fita wajen motarsa ya wuce ya shiga back seat. His driver was already inside, waiting for him because he had seen Alhaji Ibrahim leave. Babu bata lokaci ya tada motar ya kaishi hotel din daya sauka. Sai dai zuciyarsa was full of thoughts, thoughts about that poor girl, that girl da kallo daya yayi mata yaga she's desperate, that girl who had no one, and finally, that girl who had found a place in his heart, earning a position even higher than that of his youngest daughter, Suhana!
Alwala kawai yayi ya sauya kayansa zuwa jallabia ya fita masallaci don lokacin sallar magariba ya gabato. Yana masallacin akayi kiran sallah bai kuma bar masallacin ba sai bayan daya idar da shafa'i da wutiri sannan ya koma masaukinsa. Yana komawa ya tarar da kiran Ammi. Calling her back, he sat down on the sofa in his room and relaxed.
Da sallama ta amsa tana cewa "Yallabai na jika shiru yau ko nemana baka yi ba.."
"I'm sorry Fulani am. Na fada miki zamu je duba Isyaku ne ai, to acan dai something came up da yasa bana jin zan dawo zuwa gobe."
Qasa Ammi tayi da muryarta tana cewa "haba Yallabai kwana nawa baka nan ka dubamu fa.. me ya faru ammn ba matsala bane ba ko?"
"It's not a problem Fulani. Sannan nasan even you abnd nayi shi zakyi Fulani. Wato akwai mutane da suke cikin wani hali aqasar nan"
Shiru Ammi tayi jikinta yana yin sanyi Abbie ya dora da "Na rasa gane me shugabannin mu suke akan mulkin da talakawanmu ne suka basu wannan damar. Yau naga abubuwa da yawa a asibitin nan wanda idan baka da dakakkiyar zuciya you must cry... An bar mutane suna yawo helter skelter ba abinci, babu karatu, babu kwanciyar hankali, Fulani lafiya ma babu wata ingantacciya.. Ina zasu kai wannan haqqin?" Shiru yayi har cikin ransa yana jin ciwon abinda yake faruwa a qasar da bashi da ikon gyarawa.
"Well that's not the point Fulani. I met a girl today who broke my heart into pieces. Mun fito daga duba Isyaku muna maida magana da Alhj Ibrahim sai gata ta taho ta zauna akan yashi kina gani kinsan bata cikin hayyacinta ta fara kuka. I don't know what drew me to her, but I bet it was pity. Yarinyar nan is in need.. 100% Fulani, just one look into her eyes would tell you how desperate she is. I asked her lafiya tace kakarta ne babu lafiya, and there's no need for me to tell you that they don't have money. You already know that. I then asked her about her parents. Kinsan me tace min?"
Ammi da Abbie ya gama kashe mata jiki da maganarsa ta girgiza kai kamar yana gabanta tana cewa "a'a Yallabai."
"She has no one!! Wannan kakar nata kawai take dashi ita ma tana kwance rai ahannun Allah! Billah I feel her pain Fulani. I put myself in her shoes naji ban san idan nine ya zanyi ba amman yarinyar nan banda kukan nan tana nan calm and well-reserved.."
"Yallabai pay the bills for her.."
Murmushi yayi kawai kamin ya dora da "Done with that part. Abu na biyun shine Fulani I'm feeling myself connected with that girl. Yau na fara ganinta ban santa ba amman I'm feeling her like my Suhana..."
"Yallabai Wallahi your words are getting to me... Kasa naji Ina son ganin yarinyar nan, Yallabai I want to see her please 🥺..." Shiru yayi na dan sakan kadan kamin yace "Ok Fulani am,, zaki zo I will check the available flights for you idan an samu fa amman kenan. Za'ayi ma Grandma dinta surgery ne gobe gwara ma kizo din bansan ya za taji ba idan aka shiga da ita ta ganta ita kadai though I will also be there In Sha Allah.."
To Nuri fam... I know y'all have something to tell me... I'm waiting for your comments, guys.
To be continued....
like, comment and share