Free chapter · Read without an account
002
_ NI DA YAYA NABEEL _
_YOUNG WRITER✍️
* 002 *
Haka kwanaki suka cigaba da garawa har satin zuwan su Nabil ya shigo, inda ake sa ran saukar su a yau. Ilahirin familyn nan sai shirye shirye suke, in banda kamshin girke girke dana turarukan wuta babu abinda ke tashi, compound ɗin gidan kuwa ko ganyen bishiya ɗaya babu, an kalkale shi fess.
"Wai Hamma shafik duk zuwa dauko su ya Nabeel dinne irin wanna daukan wankan haka?".
"Wato baza ki gane irin yadda mukayi kewar Bro bane a gidan nan Hamdah. Har so nake muyi mu tafi ma whl".
Naseem tayi karaf tace, "Ai ni duk na fiku matsuwa whl, dan ji nake kamar na kifta ido na ganni a airport ɗin". Duk juyawa sukayi suna kallon ta har saida ta tsargu ta shiga kame kame.
Taɓe baki Hamdah tayi tace, " In dai ya Nabeel ne murnarku zata koma ciki, dan whl kowa saiya nadi kanbunsa aka cox naga alama yan shekarun da yayi acan yasa kuka manta halin sa har kuke mararin zuwansa irin haka".
"Wait wai ita wanna yau mutanan nata ne motsa ne. Naga tun ɗazu ana ta magana amma kamar bata falon". Hamma Safwan ya fada yana nuna Asum dake ta dacin rai tunda aka sanar da zuwan su Nabil ɗin. Tana zaune ta ɗaura kafa ɗaya Kan daya hankalin ta na Kan wayar ta da take chatting da ita ba kuma dan bata jin Maganganun nasu ba sai dan baza ta bata yawun bakinta akansa ba ne kawai.
"Assuma". Hamma Safwan ya kira sunanta. Ɗagowa tayi ta kalle shi ba tare da tayi magana ba. "Wai meke damunki ne yau? Mun saba da hayaniyarki in mukaji ki shuru duk sai mu damu Whl"
"Uhmm". Shi ne iyakar abinda tace kawai ta maida kanta Kan wayarta. Hamma Abid yace, "Ka dai na bata bakinka akan Yarinyar nan, dan ni inajin bata rasa bishiyar kuka a kanta ba, cox yanzu mutum anjima jinnu²". Shigowar wani matashin saurayi ya katse shi. "To, masu tafiya su fito, kun dai san halinsa baya san jira, akan 1 minutes in muka ƙara yanzu sai ya tada hankalin kowa". Duk miqewa sukayi banda Hamdah data koma gefen Asum ta zauna.
************
AIRPORT
Wani hadadden matashin saurayi ne mai ji da kansa ya sako kafar sa dake sanye cikin wani hadadden farin loafers, kan staircase ɗin jirgin. Kyakyawa ne ajin karshe, dan kallo ɗaya zaka masa ka fahimci ya gina jikinsa da gym. Tako ina bashi da makusa, daɗin dadawa ga kwarjini da haiba. Duk macen data masa kallo ɗaya dole ne taji ya birgeta har taji sha'awar sake kallonsa a karo na biyu. Yana sanye da white suit sai shirt ɗin ciki data kasance black, idon sa manne da polarized sunglasses, a qalla zai Kai shekaru 36 amma in ka kalle shi zakayi tunanin baifi 22 years ba, gefen sa wata matashiyar budurwa ce da zata kai shekaru 25, taci kwalliya cikin wando da riga sai dan ƙaramin mayafin data yafa wanda ko gashin kanta bai gama rufewa ba. Ƙarasawa su Hamma safwan sukayi suna musu barka da zuwa, matar ce kawai ta tsaya suka gaisa daya bayan daya, amma shi saida ya jira suka gama aiko gaisuwar tasu kafin ya hada ya basu amsa ɗaya ya wuce mota ko kula sojojin dake ta aikin sara masa baiyi ba, da sauri ta bi bayan sa su ma su Hamma safwan da Abid suka yi saurin shiga motar, Awwab shafik da Naseem kuma suka shiga mota ɗaya sai motocin sojoji da suka rufa musu baya dan yi masa rakiya.
Hamma Shafik ne yace, "Wai su kuma wa'annan sojojin daga ina haka?". Hararar sa Awwab yayi Kafin yace, "Bangane daga ina ba? Ka manta waye muka taryo ne?".
"To Amma ni dai nasan ya Nabeel in zaizo baya san ma kowa yaji zaizo sai dai idan bayan yazo ɗin, shiyasa nayi mamakin wanda ya sanar dasu".
"Malam ka sani ko ya canja ra'ayi haan". Haka dai suka cigaba da hirarsu su biyu, Naseem dai tana jinsu amma bata ce musu komai ba har suka isa gida.
Suna shiga gidan ya basu Umarnin tsayawa a ƙofar part ɗin sa, Naseem data fito tana kallonsu tace, "Aunty Jumayma ke baza kizo mu shiga wurin su Mommy ba ku gaisa". Saida ta shaqa ta fitar tana bin gidan da kallo kafin tace, "Sai mun huta zuwa anjima". Daga haka tabi bayan mijin ta. Haka Naseem taja malaman ƙafafunta ta koma mota suka wuce bangaren su.
***************
Daga masallaci ya dawo, yana shigowa ya sameta kwance kunnenta maqale da earpiece, wayarta a hannunta tana latse², tsayawa yayi daga kofar dakin tare da harde hannuwan sa a kirji yana kallonta, jin sharp eyes ɗin sa a kanta yasa ta ɗagowa ta kalle shi sai kuma ta cire earpiece ɗin ta ajje gefe, tana wani narkewa kamar candle tace, "Babe lpy?".
Karasowa yayi cikin dakin ya zauna bakin gadon, sai kuwa ta tashi ta shige jikin sa tana wani marmar da idanu tace, "Wai babe me sa kwana biyun nan duk kabi ka sauya ne, tun muna russia nake faman tambayar Ka meke damun Ka kaki fada min".
Numfashi ya furzar kafin ya furta, "Gyara muyi magana". Noqe kafada tayi tana sake shigewa jikinsa tace, "Ni gsky kayi maganar a haka". Ta karashe tana da ɗan turo baki.
Kallo ɗaya ya mata, ba shiri ta tashi tana gyara zamanta a gefensa. "Kinyi sallah ?".
" Au an kira sallah ne?". Da ido ya nuna mata agogon dake manne a bangon dakin. Da sauri ta tashi tana fadin, "Laa ai banji ba whl". Tsaki yaja a zuciyar sa yana faɗin ina zakiji bayan kin maqala gangar shaidan a kunne.
Yana nan zaune ta ɗauro alwalar ta fito ta tayar da sallar, ta idar, ta sake dawowa kusa dashi ta zauna tana kallon sa cikin Ido. Dauke kansa yayi cikin jimamin abinda zai fada, kamar ya fasa amma kuma ya san ya zama dole ta sani tunda lokacin daya kamata dole ta sani ɗin yayi, rasa ta Inda zai fara yayi daƙyar ya aro jarumta yace, "Jumayma".
Zuba masa Ido tayi cikin fargabar abinda zai biyo baya dan tunda ya Kira sunanta haka tasan akwai wani abu marar daɗi da zai biyo baya.
" Jumayma kin san ina sanki ko?". Saurin tarar sa tayi da faɗin, "Wait wait Babe, wanna sentence ɗin daga ina?".
Shuru ya sakeyi can kuma yace, "Inada wani auren tun kafin na aure ki". Kallon rashin fahimta ta shiga yi masa, ya sake cewa, "Yes ina da wata matar kafin ke amma bata tare ba saidai....". Shuru ya sakeyi dan ji yayi Maganar ta fara bashi haushi cox ya tsani irin wanna dogon bayanan. Tsaki yaja kafin ya cigaba, "Nayi aure almost a year kafin na aureki, cousin ɗi na ce, zabin mahaifina, a cikin gidan nan take. Kasancewar ita ɗin zabinsa ce yasa lokacin dana kawo ki a matsayin zabina ya amince min na aure ki saboda shi ma nayi masa biyayya wurin amincewa da zabinsa. Sannan shi da kansa yasa lokacin da yake so ta tare yanzu kuma lokacin nasa yayi, wannan shine dalilin dawowar mu".
Wani irin ihu Jumayma tayi ta shiga sambatu, "Whl baka isaba Nabeel, ni zaka nunawa halinku na maza? Ai dama tunda naji Ka fara cewa kinsan ina sanki na zargi abinda zai biyo baya kenan, whl ba zabin mahaifin Ka ba ko zabin uban waye sai Ka rab.....". Bata samu damar ƙarasawa ba saboda ɗauketa da yayi da wani shiryayyen mari me spices, da ya sa ta hantsila tsabar gigicewa, yoo taji hannun maza.
"Mind ur tongue". Ya faɗa yana nunata da yatsa alamar gargadi. Kuka ta fashe dashi, da sauri kuma ta dawo gaban sa tayi kneel down, da rawar murya ta shiga fadin, "Dan Allah karka min haka Nabeel, dan Allah Ka fadamin duk abinda nakeyi wanda baka so ko ma miye zan daina, amma whl bazan iya sharing dinka da kowacce jaka ba, wayyoo Allah na shiga uku Nabeel Ka taimaki rayuwata dan ALLAH ". Ta karashe tana sakin wani marayan kuka.
Dagota yayi ya rungume yana dan bubbuga bayanta cox yasan dama za'a yi haka shiyasa yaji tsoron sanar da ita, duk wanna tada hankalin nata da tayi dan tana son sa ne kuma tana kishin sa shiyasa ya mata uzuri dan shima zuciyar sa zafi take, ba wai son auren yake ba kawai dai yanawa Mahaifinsa biyayya ne, amma babu tsarin zama da mata biyu a rayuwarsa.
Fisge² ta shiga yi kamar mahaukaciya tana ihun kuka, duk kokarin sa na ganin ya lallabata sun fahimci juna ya gagara, in ya tarota ta nan sai ta bulla ta can. Gajiya yayi ya sake ta ya koma yayi kwanciyarsa. Buge² ta fara duk abinda ta dauka saita fasa gabaɗaya ta hargitsa ɗakin.
Wata irin tsawa ya daka mata wadda ta dira har qoqon kanta amma dake kishi ya riga ya rufe mata Ido sai cewa tayi, "Kai ɗin wa? Whl na daina sauraranka da duk wani hayagaga taka Nabeel, duk abinda zai faru ya dade bai faru ba".
Tashi yayi ya bar mata ɗakin dan kansa ya fara ciwo ga kiran mommy dake ta shiga da fita a wayar tasa. "Whl duk wasu masu bita da kulli akan Auran nan, sai sun haƙura sun warware dan bazan taba zama da wata yar iska can ba".
Bai kula ta ba ya koma falo ya yi zamansa tare da amsa Kiran mommy "Wani sabon iskancin ne kuma tun dazu nake kiranka kana gani kaqi ɗagawa".
Kwantar da murya yayi yace, "Kiyi hakuri mommy wayar na silent ne".
"To mahaifin Ka ne ya buqaci kuzo ayi dinner daku, in ma baza ku shigo ku zauna damu ba".
"Ya hakuri Mommy dama yanzu muke shirin shigowar ma ai".
"Ya rage naka kuma". Ta faɗa tana kashewa. Tashi yayi ya shiga kai kawo a falon, saboda yana so ya taushi kansa ne ta yadda zai iya kauda Kai daga haukan Jumayma harya lallabeta ta fito su tafi.
Dakin ya nufa ya sameta a kasa tayi zaman yan bori tana kuka karasawa yayi ya dagota tare da nufar toilet da ita, fuskarta da hannuwan ta ya wanke mata sannan ya jata suka koma dakin a kunne ya rada mata wani abu, kadan² ta fara share hawayen dake zirga² Kan kumatun ta kafin ta sake shi ta dauko hularta tasa. Yanaso yayi magana kan kayan jikinta amma kuma bayason wata rigimar, ga mommy kuma Kar taga sun dade itama ta sake bude sabon shafin nata fadan .
***************
A tare suka shiga falon tana kankame da hannun sa kamar wadda za'a kwace mata shi, doguwar riga ce a jikinta irin rubber din nan marar hannu, duk mutanan dake zaune a dining din dagowa sukayi suna kallon su banda Asum da kanta ke Kan wayarta. Wani takaici ne ya kama mommy ganin yanayin shigar dake jikin Jumaymah, ko ba komai ai ta suturta jikin ta tunda wurin surukai zatazo, shi kuwa baffah laifin Nabeel ya gani dan ji yayi kamar yaje ya rufe shi da duka, ganin yadda ya zama wani sha³ tunda gashi ya kasa control din matar sa, tunani ya shiga yi anya ma kuwa Nabeel zai iya riqe mata biyu? Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya ji Nabeel din na gaisheshi, amsawa yayi ba yabo ba fallasa, Jumayma ma ta gaisheshi amma ko kallon ta baiyi ba, dan wata irin gaisuwa ta ɗaga masa kamar wani sa'anta, kujeru sukaja suka zauna .
Mommy ce tace, "To Assuma a tashi ayi serving ɗin mu ko?". Da sauri Naseemah ta tashi tana rawar jiki tace, "Mommy barin yi serving ɗin ku, yau dai ɗaya abar Asum ta huta, naga kamar batajin daɗi ma".
Ajje wayar hannun nata tayi ta miqe tana faɗin, "Ki dai zubawa wanda zaki zubawa amma Mommy da Baffah kam ni zan zuba musu". Murmushi Mommy tayi, Baffah kuwa cewa yayi, "Ni kam dama in ba Assuma bace ta zubamin abinci ai ji nake dandanon abincin ya silale min".
Awwab yace, "To mu dai yanzu burin mu a zuba mana abinci mu bawa cikin mu hakkin sa".
Haka dai sukayi Asum ta zubawa Mommy da Baffah sannan ta zubawa kanta ta koma ta zauna tana ci tana danna wayarta. Naseemah kuma ta zubawa sauran, lokacin da tazo Kan Nabeel hannunta har rawa yake ta shiga zuba masa garin ajjewa chokalin miyar dake hannunta ya gogi dantsen hannun jumayma wani wawan mari ta sauke mata da yasa tayi tsalle ta tsallake staircase din dining area ɗin, sai kuwa karar saukan wani bahangon mari ya biyo baya wanda ya karade gabadaya dining din ya kuma janyo hankalin mutanen dake wurin ciki harda Nabeel da ya rufe wayar sa ya dago yana kallon abinda ke faruwa.
Assuma ce tsaye ta wanke Jumayma da marin da yafi wanda ita Jumayman ta yiwa Naseem, ta nunata da yatsa tare da faɗin, "Whl kika kuskura kikace zaki taba min lafiyar yar uwa kema saina bar miki tabo. Uwar mai ta miki? Da saninta zata goga miki ko akwai wani abu tsakanin ki da ita da zaisa ta aikata hakan a gareki da dagangan? Amma saboda rashin sanin darajar dan adam zaki dauki wanna kafatarin hannun naki ki mareta, Ko an gaya miki gidan mu gidan dabbobine da zaki fara dukan mu daga zuwanki". Naseem ce ta riqo hannunta cikin kuka take faɗin, "Haba Asum ya isa haka dan Allah, ki koma ki zauna, ni nayi mata laifi na amsa, kuma ni ta mara ki bar abin nan haka". A fusace ta kwace hannun ta tana faɗin, "Kika ƙara magana whl ina iya haɗawa dake, wawiya kawai marar sanin ciwon kanta". Ta fada tana wucewa. Jumayma da tunda taji mari ta rasa bakin magana sai lokacin ta juya wajen Nabeel dake kallon su kamar ya samu TV ya ma rasa mai zaiyi.
"Babe Kana kallo a gabanka wata tasa hannu ta mareni". Kafin ta rufe bakinta, ya furta, "Keee". Da kakkausar murya.
Asum data dauki hanyar barin dinning ɗin kuwa ko juyowa batayi ba bare tasan da ita yakeyi. Wata tsawa ya daka mata wadda har su mommy sai da suka firgita. "Ke ba dake nake ba kike kokarin fita".
"Kai bansan rashin hankali kuma? Miye hakan? Zaka firgita mutane". Mommy ta fada tana hararar Nabeel din.
Dukda taji tsawar amma taurin kanta bazai barta ta nuna ba, juyowa tayi tana kallon su ba alamar taji tsawar ma bare taji wani shakkarsa, ta riqe kugu tana kallonsa cikin ido. Tashi yayi ya nuna Naseem da Jumaymah yace, "Ku biyoni". Saida ya karasa kusa da Asum zai wuce yace, "Harda ke". Sannan yayi ficewar sa.
Tashi Naseem tayi daga tsugunnewar da tayi saboda tsawar da Nabeel yayi, ta karasa wajen Asum Jikinta na rawa ta riqo hannun ta da karfi ta jata suka fice dan tasan zata iya qin zuwa. Bayan su Jumaymah ta biyo itama a fusace kafin ta shige gaba suka rufa mata baya har part ɗin nasa. A falonsa suka sameshi zaune fuskar nan a hade kamar hadarin farkon damuna, tana zuwa ta fada jikin sa tana sake fashewa da wani kukan kissa.
Ƙarasa shigowa su Asum sukayi murya ba alamun wasa yace, "Kneel down". Kafin ma ya rufe bakinsa Naseem tayi ita kuwa Asum cogewa tayi tare da faɗin, "Ai ba mu kadai mukayi laifin ba, ita yar gwal ɗin ba'a hukunta ta ne?".
Tsawa ya sake daka mata, "I said kneel down". Kauda kanta tayi daga kallon sa tanajin kamar zuciyar ta zata fito dan whl in dai Jumaymah ba tayi ba itama baza tayi ba. Cikin mamaki yake kallon ta yarinyar da in tayi gudu tayi 17yrs, shi da manyan² sojoji ma tsawa ɗaya yake musu su shiga hankalin su amma ita ko a jikin ta, to wanna wace irin yarinya ce haka? Tashi yayi yana ƙoƙarin yakice Jumaymah daga jikinsa amma sai ta sake lafewa kamar wata mage. A fusace yace, "Dalla sakeni malama". Ba shiri ta sake shi a tsorace.
Gaban Asum ya tsaya tare da harde hannuwansa yace, "Turancin ne bakyaji ko me? Durkusawa nace kiyi kamar yadda yar uwarki tayi". Ya fada yana ƙare mata kallo, wata yar firit da ita.
Harara ta galla masa ba ko digon tsoronsa a cikin idanunta, dan bakin tsiwarta ta motsa ta shiga fadin, "Ai billahillazi, in kaga nayi to sai waccan matar ma tayi dan b......". Wasu kyawawan maruka biyu ya sauke mata.
Dafe kuncinta tayi yayinda Naseem ta fashe da wani irin kuka me sauti kamar ita aka mara, da gudu ta dawo gaban sa tana bashi hakuri ita kuwa Asum tsabar yadda ranta ya baci bata san lokacin data isa gaban Jumaymah ba, a fusace ta fincike hular kanta ta riqo gashin kanta, ta shiga zabga mata maruka. Kokawa ce ta balle a tsakaninsu, Naseem na son raba su amma tana tsoro, gabaɗaya ta rasa inda zata sa kanta kuka kawai take baiwar Allah duk tayi wujiga wujiga da ita, dan ita ba abinda ta tsana irin tashin hankali a rayuwar ta.
Belt Nabeel ya kunce ya shiga zabga musu su duka, ko gezau Asum batayi ba sai Jumaymah ce ta fasa ihu ta ture Asum ɗin tare da yin tsalle ta koma gefe, lokaci guda jikinsu yayi rudu² da shatin belt ɗin. Da sauri Asum ta fice saboda wani kuka daya taho mata.