Free chapter · Read without an account

003

by SultyWrites · NI DA YA NABIL

_ NI DA YAYA NABEEL _




  _YOUNG WRITER✍️




* 003 *



Sai da ta shiga ɗakin su sannan ta zube ta fashe da kuka mai cin zuciya, tana cikin kukan ne Naseem ta shigo, rungume ta tayi suka cigaba da kukan tare. Saida sukayi me isar su kafin Asum ta janye jikinta ta tashi ta shige toilet, ruwa me dumi ta hada tayi wanka ta gasa jikinta ta fito, sama sama ta shafa mai ta zira kayan bacci ta haye gadon ta shige bargo, dan ita kam Naseem har tayi baccinta a nan Kan carpet ɗin.

Washe gari kuwa da zazzabi Asum ta tashi. Naseem ce ta garzaya da gudu taje ta sanar da Umma, suka taho tare. Sosai ran umma ya bace da ganin yadda jikin asum ɗin ya tasa yayi ja ga fuskarta da shatin yatsu guda biyar sunyi radau². "Naseem wanene ya mata irin haka?". 

Murya na rawa Naseem tace, "Ya Nabeel ne Umma, jiya ne da....... ". Ta kwashe duk abinda ya faru ta faɗa mata.

"Ohk akan ita matar so ɗin tasa ya mata haka?". Umma ta faɗa da ɓacin rai, ba kuma wai dukan bane yafi bata mata rai a yanzu, dalilin dukan ne yafi ƙona mata rai.

"Umma dan Allah kiyi hakuri duk ni naja".

"Hmmm, jeki waje ki jira mu, muna zuwa". Sake kallon Asum ɗin Naseem tayi tana share kwalla kafin ta juya ta fita.

Umma ta dawo da kallon ta kan Asum, ta kamo hannunta ta taimaka mata ta zauna, sannan ta kalleta tace, "Kinga dai abinda nake fada miki ko? Ke zabin mahaifin sa ce Jumaymah kuma zabin sa, dole zaki fuskanci haka dan ke dolen sa ce ba wai ra'ayin sa ba, nasanki nasan halin ki Asum shiyasa mahaifin ki ya dage kan cewa ke za'a bashi ba Naseem ba, saboda ke zaki iya amma Naseem cutuwa kawai zatayi. Dan haka karki bamu Kunya s...".

Katse ta tayi ta hanyar faɗin, "Umma ni ma bazan iya ba whl, a wancan lokacin ma dana amince kuruciya ce kawai da rashin sanin ciwon kai, kuma bugu da qari ma a wancan lokacin ai bashi da mata. Amma yanzu whl na hakura, ba zan taɓa iya zaman aure dashi a haka ba". Jawota Umma tayi jikinta tana bubbuga bayanta kafin ta shiga lallashin ta tana kwantar mata da hankali, saida ta tabbatar da ta samu nutsuwa taja hannun ta ta kaita toilet, ta haɗa mata ruwa me dumi ta fito ta barta dan tayi wankan.

Barin ɗakin tayi ta nufi waje, tana fitowa kuma mahaifin su Asum ɗin na shigowa falon shi ma. "Yanzun nake neman ki a ciki ashe kin zo duba yaran naki". Naseem ce ta katseshi da fadin, "Abbah ina kwana".

"Lpy kalau Baby Naseem kin tashi lpy?".

"Lpy kalau Alhamdulillah". Juyawa yayi wurin Umma da faɗin, "Farida ina Asum?".

Ɗan ɓata fuska tayi kafin tace, "Danku ne ya mata dukan tsaraba jiya da daddare gata can tana fama da kanta".

"Duka kuma? Wani irin duka?".

Cikin ƙosawa tace, "Dan Allah Alhaji Ka barni da tambayoyin nan haka, duka duka dai mana daka sani. Sai ma kaga yadda shatin yatsunsa ya zauna akan fuskarta kuma duk akan wancan matar tasa, yanzu haka da zazzabi ta tashi".

"Subahanallahi, Me ya haɗa su?". Nan Umma ta bashi labari. Ya ɗan yi shuru kafin yace, "Yanzu me take yi?".

"Na dan haɗa mata ruwan dumi dai tayi wanka wai ko jikin nata zai warware".

"Ohk ina zuwa, ki kula da ita". Ya fada yana ficewa ita kuma ta wuce kitchen.


*************


Tashi Naseem tayi a sanyaye ta koma dakin, ta zauna bakin gado ta buga uban tagumi, tayi zurfi cikin tunani har bata san fitowar Asum ba saida ta yarfa mata ruwan hannunta a fuska. Firgigit ta dawo nutsuwarta tana tashi ta isa gaban Asum ɗin ta shiga shafa kumatunta inda shatin yake har lokacin. "I'm so sorry Assuma duk ni naja miki k...".

"Dan Allah kiyi shuru Naseem, ni ba abinda kika ja min dama can halinsa ne bakin hali da mugunta, kuma whl Allah sai ya saka min". Ta faɗa idanunta na kawo ruwa.

"Amma Asum ni sai nake ganin kamar baki fahimci ya Nabeel bane, cox baiyi niyyar dukan ku ba, faɗan da kuka shiga yi ne yasa ya dake ku dan ku rabu". Tsayawa kawai Asum tayi tana kallonta baki buɗe, kafin tayi magana wayarta tayi ƙara, matsawa tayi ta dauka tare da yin sallama, bansan me akace daga ɗaya bangaren ba naji tace tho baffah gani nan zuwa.

Wucewa tayi ta shirya a gurguje ta ɗauki dogon hijabi ta ɗora akan dogon wando da vest ɗin data sanya sannan ta fita.

Part din Nabeel ta nufa tana tafiya kanta a kasa taji ance, "Naseem yau ba magana? Ɗagowa tayi tare da faɗin, "Ina kwana uncle".

"lpy kalau. A'a ai na dauka Naseem ce ma, ba dan kinyi magana ba ai bazan gane ke bace. Ina zaki ne da sassafen nan?".

"Part din Hamma". Ta faɗa kamar an mata dole.

"Hamman ai da yawa, wanne daga ciki". Bata sake bashi amsa ba ta wucewarta. Da kallo ya bita kafin yace, "Shegiyar yarinya me ido a tsakar ka. To indai wanna baudadden yaron ne zakiyi ki bari".

Tana shiga ta samu Baffah da Abbah zaune a Kan 2 seater ga Nabeel da Jumayma zaune a gabansu. Ita Jumaymah wayarta take dannawa shi kuma uban gayyar ya sunkuyar da kansa kasa yana sauraren su Abban. Da sallama ta shiga, Baffah ya amsa mata. Ƙarasawa tayi kusa da kafarsa ta zauna tana gaisheshi .

Amsawa baffah yayi cike da kulawa yana ƙarewa fuskarta kallo kafin yace, "Kai Nabeel". Ɗagowa yayi yana kallon Baffahn. "Abun da kazo dama Kayi Kenan?". Shuru yayi tare da maida kansa ƙasa. Nan Baffah ya shiga fada ta Inda yake shiga bata nan yake fita ba dan dama yana cike dashi, saida ya wanke shi tas sannan ya daura da fadin, "So nake inji dalilin da yasa ka daura hannunka a jikinta?".

Ɗagowa Jumayma tayi tace, "Baffah ba fa ita kaɗai ya daka ba har dani da nake matar sa". A tsawace Baffah yace, "Ke na tambaya ko shi? Ko kuwa kece bakin sa? Sannan itama ai matar sa ce ko bai gaya miki ba ne. Kai baka gaya mata ba ne?". 

Nabeel da idanun sa suka kaɗa sukayi ja yace, "Baffah dan Allah kayi hakuri".

"Ai bani zaka bawa hakuri ba, wanda Ka yiwa laifi ita zaka bawa hakuri. In banda abun ka ina maka kallon Babba har ka tsaya dukan mata, matan ma iyalinka".

Kamar wata aljana haka Jumayma ta buga tsalle ta cafki wuyan Asum tana faɗin, "Kece shegiyar data auremin miji ko? To dan ubanki sai na kasheki, na kuma kashe banza". Ko gezau Asum bata yi ba ballantana tayi yunqurin cire Jumayma daga Jikinta, sai ma wani Murmushin cusa haushi da take.

Baffah ne ya daka mata tsawa wadda tasa ta sakin Asum ba shiri tana me rushewa da kuka, ta koma gaban Nabeel ta riqo kafadunsa tana girgiza shi, dan ita tasan ta gama in dai wanna aljanar aka aurawa Nabeel. Sai a lokacin Abbah yace, "Kayi hakuri yaya a bi komai a sannu".

"Baza a bi a sannun ba Mus'af, rainin wayon Nabeel yayi yawa dole yasan shi ma ɗa ne, kuma yana da na gaba dashi. Wannan halin banzan ba zan ɗauke shi ba, ni ina masa kallon mai hankali Ashe kallon kitse nake ma rogo. In ba haka ba ina ka taɓa ganin wani namijin kwarai na dukan matan sa, wanda ya kamata yafi kowa tausaya musu ?". Abbah ya sunkuyar da kai kawai.

Jumayma ce tace, "Whl babe sai Ka saki wanna aljanar in har kanaso Kaci gaba da zama dani, dan ni bazan zauna da kishiya ba".

Baffah ya sake hasala yace, "Gwara ma ki shirya zama da ita domin a duk ranar da Nabeel ya saki Asum a ranar ya shirya neman wasu iyayen. Sannan ke ba'a zama da kishiyar uwarki ta zauna da ita, ko ba su biyu bane a wurin mahaifin naki. Kai Nabeel, Ka shirya domin nan da kwana hudu Asum zata tare a nan part ɗin in Ka tashi tafiya Ka haɗa da ita Ku tafi dan baza mu cigaba da dauka ma nauyin da yake naka ba".

A razane ya dago zaiyi magana ya tare shi da faɗin, "Ba abinda zaka gayamin Nabeel. Abinda kawai zance ma shi ne in kaga dama in ka tafi da Asum dan Allah Ka dawo min da gawar ta kaji ko". Yana gama fadin haka ya tashi ya fice.

Rarrafowa yayi gaban Abbah tare da riqo kafafun sa, murya a raunane yace, "Abbah dan Allah Ka bawa Baffah hakuri, ka bashi haƙuri ya yafemin na sauwake mata, whl ina zaune lpy da matata. Ga sauran nan su Awwab da basu taɓa aure ba ma, ba sai ya aurawa wani a ciki ba". Magana yake amma sam ya manta waye a gabansa, ya manta cewa mahaifin Asum ɗin ne yake roqo kan ya taimaka a yafe masa ya saki yar sa.

Murmushin takaici Abbah yayi tare da dafa kan Nabeel ɗin yace, "In dai hakan kake so za'ayi Nabeel. Ka kwantar da hankalin ka, ni zan tsaya ma". Yana faɗin hakan ya tashi ya bi bayan Baffah. Cikin hayagaga Jumayma tace, "Tashi ki fitar mun a falo munafuka algunguma, whl in baki fita ba sai na nakasa ki". Ko kallon ta Asum bata yi ba, hankalinta yana kan Nabil tana tunanin abinda yayi a yanzun.

"Zaki bar wurin nan ko yaya?". Ta sake faɗa muryarta na rawa. Sai a lokacin Asum ta ɗago ta kalleta a wulakance tace, "Mahaukaci dai baiji dadi ba whl". Mug ɗin dake kan center table Jumayma ta dauka ta wurga mata, saurin kaucewa tayi ya samu bango, karar sa ne yasa Nabeel dagowa ya zuba masu Ido. Tashi tayi tare da nuna Jumayma ta kalli Nabeel da har lokacin kallon su yake, a fusace tace, "Whl ka yiwa wannan mahaukaciyar matar taka magana ta fita harka ta tun kafin na nuna mata salon nawa haukan ya take nata ya wuce".

Kwarai ya daina mamakin Asum tun jiya ya lura ba karamar marar kunya bace gata da taurin kai, shi kam an aura masa zaune tsaye duk abun Jumayma in ya zare mata Ido tana tsoron sa amma wannan yarinyar ko gunduwa² zaiyi da ita bai ga alamar zata saduda ba. Da gudu Jumayma ta wuce kitchen sai gata da zungureriyar wuka sai kyalli take da sauri Nabeel ya miqe yana mata magana. Asum kuwa tana ganin haka tuni ta koma bayansa ta rirriqe shi. Ai Jumayma na ganin yadda Asum ta cukuikuiye mata miji sai kuwa ta ƙara tunzira ta nufe su gadan gadan. Da sauri Nabil ya riqe wukar gam yaqi saki duk kokarin kwacewar da take, dan yasan in ya saki za'ayi barna babba dan itama Jumayman wani lokacin ba hankali ta cika ba especially akan kishi ba abinda baza ta iya ba. Wuqar duk ta yayyankesu jinin su da ya haɗu dana juna sai ɗiga yake a ƙasa, ganin haka yasa Asum fita daga bayansa ta nufi ƙofa tana kokarin ficewa daga falon. 

Jumayma na ganin haka ta sakar masa wuqar ta warci parlour palm ta jefeta dashi, wani irin U-turn tayi suka shiga zagaye falon, duk yadda yake magana ba mai jin sa dan kamar da gini yake.
A zuciyarsa faɗi yake Baffah kazo Ka ga bala'in da ka haddasa min, kazo ka gani ko Allah zai sa ka yarje min in sauwakewa yarinyar nan. Tsallen da Asum tayi ta dira a bayan sa kamar wata zomo ne ya katse shi daga zancen zucin da yake. Wurinsa Jumayma ta nufo da yankakken glass ɗin mug ɗin data ɗauka tana faɗin, "Barin in kashe ki in gani in zai zauna da gawa" 

"Whl whl in baki ajje wanna abun dake hannun ki ba zakiyi dana sani Jumayma". Cak ta tsaya tana kallon yadda yayi maganar, sai kuma ta wurgar da glass ɗin ta wuce daki da gudu tana kuka.

Ajiyar zuciya ya sauke yana goge goshin sa jin yadda yake zufa dukda wadataccen sanyin dake falon, gsky masu tara mata hudu a gida suna kokari wai kowa haka yake fama ko kuwa ni kadai ne?

Asum da har lokacin take maqale a bayansa tace, "Kai kadai ne mana, saboda kai kadai ne ka auro marar hankali, matarka tana da matsalar ƙwaƙwalwa ya kamata ka kaita a duba kanta tun wuri". A fusace yace, "Kee sauka daga bayana dan.... ".

" Whl Kana Ƙarasawa zanje in kirasu Ka maimaita a gaban su". Lips dinsa na kasa ya Kamo ya ciza da karfi kafin ya fisgota daga bayan sa ya dire ta ƙasa. "Tashi ki fita a falon nan ko na kakkarya miki kafafu shegiyar yarinya kawai" .

"Yi maza to karka bata lokaci, ai kaji abinda yace ka karyamin kafafu whl Ka fita cikin ahalin mu, sai zuciya kamar kuturu, kuma ni ba shegiya bace da uba na tunda har kasan ka kama kafarsa ka roqi ya nema ma alfarma a yafe maka Ka saki yarsa, ai kaji kunya whl". Tana gama fadar haka ta kadai hijabinta ta fice .

Da kallo ya bi ta kafin ya zauna yana tunanin maganarta ta karshe, sosai ya fahimci irin shirmen da ya tafka, sai yaji kunyar Abbah ta kamashi duk da baya gabansa amma kuma in dai Baffahn zai amince masa ai shikenan, zai fake da cewa shi matsayin mahaifi Abban yake a wurinsa. Dan shi Jumayma ta isheshi rayuwa, me ma ya kaishi tara mata biyu da qananun shekarun sa, mtweeee yaja tsaki tare da tashi ya bi Jumayma daki.


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol