Free chapter · Read without an account

Chapter 14

by Narrnarhh Bukar · BA NI DA MADOGARA

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*











 *Ba ni da Madogara*
  (Sai Allah...)




 




014

Ɗan murmushi wanda bai faɗaɗa ba ya yi yana jinjina mata kai, da yake tasan halinsa  yasa bata damu ba,Alhaji ma rungumesa ya yi yana farin ciki, Mas'ud da Mahmoud suka gaisa. Tahseen da saurinta za ta  rungume Arqam sai ya ja da baya yana faɗin

"Don't even dare try that illetracy here!"

Tahseen ce kaɗai ta ji maganar saboda bada ƙarfi ya yi ba, Allah yasa lokacin da ta zo rungumesa Alhaji da Hajiya Nafisa hankalinsu baya wurin.Gwalo Fauziyya ta yi mata tare da manna mata ido ɗaya har da kwaso *SHOKI* duk don ta ɓata mata rai. Ai kuwa ta yi nasara domin ta ƙulu iya ƙuluwa don bata yi zaton Arqam zai hanata rungumesa ba, ita a tunaninta asirin da aka yi ma Hajiya momma zai shafi Arqam ɗin, shi yasa ta yi haka amma gashi an samu akasi ya jizgata a gabansu Fauziyya. Wani malolon baƙin ciki ne ta haɗiye, a ranta tana faɗin 'Ka gama izzarka da mulki za ka dawo tafin hannuna ne, sai na juyaka kamar waina a cikin tanada Mts!' juyawa ta yi ta bar wurin zuwa wurin motocinsu. Sai daga baya suka shiga motocinsu sai suka ɗauki hanyar gida.

A can gidan bayan Hujayrah ta sha magani, sai ta kwanta wanda ko mintuna talatin basu cika ba ta  ta shi daga kwanciyar ganin marar nata ta ɗan rage mata ciwo.Kai tsaye ta wuce bayi ta yi brush da wanka sannan ta fito. Shiryawa ta yi cikin doguwar rigar abaya mai kalar ruwan madara,ta sha adon stones sai walwali suke. Bayan ta shirya tsaf! Sai ta fito zuwa falon Hajiya momma da sallama a bisa laɓanta ta shiga ciki, babu kowa a falon sai ta samu kujera mai cin mutum ɗaya ta zauna. Ba ta fi mintuna goma da zama ba sai ga sallamar Hajiyan Sama ta ci kwalliya cikin lace mai adon stones, irin ɗaurin A'isha Buhari ta yi. Amsa mata sallamar Hujayrah ta yi ba tare da ta kalleta ba. Wani uban tsaki Hajiyan sama ta ja tana cillama Hujayrah harara kamar idanunta za su fito, Hujayrah ba tare da ta kalleta ba ta saki wani kasalallan murmushi ta ce

"Gani nan bari nan dukiya alawa, wutsiyar raƙumi ta yi nesa da kasa, Ni ɗin dai Hujayrah ɗiyar Audu mai maganin ƴan bana bakwai, hhhhh" tana maganar still idanunta basa kallon Hajiyan Sama amma tana jin yadda take watsa mata mugun kallo. Sosai ran Hajiyan Sama ya yi ƙololuwan ɓaci a ce yarinya ƙarama wacca bata wuce jikarta ba take gaggawa mata magana. Cike da ɓacin rai ta ce

"Ke don kutumar ubanki ni kike gaggasa ma maganganu! E..."

Bata ƙarasa maganar ba Hajiya momma ta fito daga uwar ɗakanta, Waskewa Hajiyan Sama ta yi tana cewa

"Ashe har kun fito!"

Murmushi Hajiyan momma ta yi tana zama ta ce

"Eh Hajiya bismillah"

Wuri ta samu ta zauna tana galla ma Hujayrah harara kamar idanunta za su zubo. Hujayrah ce  ta dubi Hajiya momma ta ce

"Mammi har kin fito" 

Sai a sannan ne ta lura da Hujayrah, murmushi ta yi sannan ta ce

"A'ahhhh Hujayrah kin fito ashe, to ya jikin naki" 

Ɗan murmushi ta saki sannan ta ce

"Eh Mammi Alhamdulillah, jiki ya yi sauƙi sosai"

"To Allah ya ƙara afuwa, nasan su Razina suna a hanya"

"Allah ya kawo su lafiya" 

"Ameen ya Rahman, Hajiya  dasu Fauziyya aka je airport hala" 

Sai a sannan ne Hajiyan Sama ta juyo daga harar da take wurga ma Hujayrah, ɗan sakin murmushi ta yi sannan ta ce

"Eh tare suka tafi har da Zahriyya" 

Gyara zama Hajiya momma ta yi sannan ta ce

"Yaushe Khalil zai dawo daga course ɗin da ya tafi yi ne" 

"Nan da ƴan satittika zai dawo in shaa Allah" 

"To Allah y nuna mana" 

Ɗakin shiru ya yi, Hajiya momma na latsa wayarta , ita kuma Hajiyan Sama na watsa ma Hujayrah harara, kallon ƙasa da sama Hujayrah take aika ma Hajiyan Sama tana murguɗa mata baki. Sosai ran Hajiyan Sama ya sake ɓaci, a ran tana faɗin 'Sai na koya miki hankali yarinya, da Izzatu kike wallahi, bara dai ƙudirina ya gama cika, zan dawo agareki fitsararriyar yarinya kawai'  duk wannan abubuwan da ya ke kai-kawo a tsakanin Hajiyan Sama da Hujayrah, Hajiya momma bata san suna yi ba domin ta yi nisa a latsa wayarta. Sun ɗauki kusan mintuna ashirin suna zaune sai can suka ji hayaniyar mutane na kusanto ɗakin. Ai da sauri Hajiyan momma ta miƙi burinta kawai ta yi tozali da abin alfaharinta Arqam. Ta ci sa'a shi ne a gaba don shi ma ya yi matuƙar ƙosawa yaga Amminsa. Ciki-ciki ya yi sallamar kai tsaye ya nufa wurin mahaifiyarsa fuskarsa a ɗan sake ya rungumeta, ita ma sosai ta rungumesa tana murmushi wanda ke bayyanar da farin cikinta da dawowansa. Sauran mutanan da suke tare suka shigo ciki. Ɗagowa ta yi fuskarta da murmushi ta ce

"Welcome back to your beloved country my lovely son" 

Gyaɗa mata kai ya yi fuskarsa a sake. Hajiya momma ke nan tasan miskilancin ɗanta tun yana yaro baka iya gane farin cikinsa ko baƙin cikinsa, amma ita ce kaɗai idan ta kalli ƙwayar idanunsa take gane hakan.Halinta ne ya biyo sai dai a cewar Hausawa da suka ce *Magaji mafiyi* to hakan take a wurin Arqam domin ya zarce mahaifiyarsa a wurin miskilanci da rashin son magana. Bayan ya gaisa da mahaifiyarsa sai ya koma gun Hajiyan Sama, ita ma rungumeta ya yi, cike da murna ta rungumesa da ta ɗago ta ce

"Oyoyoooooo ɗana! Maa shaa Allah! Wannan girma haka ai sai aure" 

Bai ce da ita komai ya samu wuri ya zauna, kowa ma wuri ya samu ya zauna. Hajiya momma ce ta ce

"Za ka ci abinci ne ko sai anjima idan kayi wanka ka huta" 

Girgiza mata kai ya yi yana miƙewa daga kujerar, kai tsaye ya nufi wasu kujerun da suke a can nesa da tsakiyar falon ya zauna,alamun ya gaji da jin hayaniyar wurin, Mas'ud da Mahmoud binsa can suka yi tare da bodyguard ɗinsa wanda ke riƙe da mage. Sai a sannan Hujayrah wacca tun zuwansu ta tashi daga kujerar ta koma can lungu ta rakuɓe kamar wata marainiya ta kira magen da 

"Mus Mus muss! " 

Abin mamaki da sauri magen ta ƙwace daga riƙon da bodyguard ɗin ya yi mata, ta ruga da gudu wurin Hujayrah, sai a sannan ne kowa yasan da ita a falon. Ɗaukar magen ta yi a jikinta tana murmushi sai shafa jikinta take tana taɓa mata kunnuwa, babu abin da magen take sai lumshe idanu tana sake goga jikinta a jikin Hujayrah alamun tana jin daɗi. Kowa kallon Hujayrah yake tare da mamakinta, ita kuwa gogar ko a jikinta. Da sauri Razina ta matso kusa da ita tana faɗin 

"Hujayrah ya jiki, Ashe kina falon kin wani raƙube a wuri ɗaya" 

Hannunta na shafa jikin magen tana murmushi ta ce

"Naga mutane ba za su samu wurin zama ba ne yasa na tashi daga kujerar na dawo nan" 

Razina za ta kai hannunta jikin magen da sauri magen ta juyo za ta yaƙusheta tana wani irin gurnani irin na faɗa, ai babu shiri Razina ta janye hannunta tana faɗin

"Wayyo Allah! Ka ji min mage za ta yaƙusheni" 

Dariya su kusan kowa ya yi a falon da ya ke tun lokacin da Hujayrah ta kira magen kowa ya bi ta da ido, babu wanda bai yi dariya ba idan ka cire Fauziyya, Zahriyya, Hajiyan Sama da Tahseen. Musamman Tahseen da kishi ya  rufe mata ido, ita a tunaninta babu wanda ya isa ya yi iko da abin hannun Arqam sai ita, don haka ita kaɗai ce ya dace a ce tana wasa da magen Arqam ba wannan ɓaƙar yarinyar mai kama da aljanu ba.Ita kuwa Hajiyan Sama sai watsa mata harara take kamar idanunta za su zubo, haka su Fauziyya da Zahriyya su ma watsa mata harara suke. Duk waɗannan harare-hararan da suke Hujayrah na ankare dasu. 

"Hujayrah da alama magen nan ke kaɗai take so a duk falon nan, tunda har Auta ta so yaƙusa" yana maganar yana dariya 

Buɗar bakin Tahseen ta ce

"Abba har nima magen tana sona bari ka gani" 

Zuwa wurin Hujayrah ta yi za ta ɗauki magen,da sauri ta saketa tana ƙwalla ƙara saboda wasu zafafa yaƙushi magen ta kai mata. Me su Fauziyya za su yi in ba dariya ba har da Hajiyan Sama a cikin masu dariyar.Da sauri Hajiya Nafisa ta matso kusa da ita tana faɗin

"Subhanallahi! Kar dai a ce magen ta yaƙusheki" 

Tana maganar tana duba hannunta, waro idanu Hajiya Nafisa ta yi  ganin har da ɗan jini-jini a yaƙushin da magen ta yi ma Tahseen. Sai matsar ƙwalla Tahseen take tana duba hannunta. Sai sannu Hajiya momma da Alhaji har da Nazima suke ma Tahseen tana Gyaɗa musu kai amma banda Hajiyan sama a ranta daɗi ta ji tana Allah ya ƙara. Su Mas'ud da ke a can side falon suna kallon wainar da ake toyawa a cikin falon, suma dariyan suke, shi kuma Arqam tun lokacin da Hujayrah ta kira magen ya kafeta da mayatattun idanunsa don ya yi matuƙar mamaki a ce Melonsa ta je wurin wani idan ka cireshi ko kuma wanda yake riƙeta. Gashi ya rasa dalilin faɗuwar gabansa a yanzu da ya yi arba da ita, a ranshi yana cewa 'what's happening with me? Wace ce ita? Me yasa nake jin faɗuwar gaba akanta?.

A can falo Tahseen tana nan riƙe da hannu tana raki har da hawaye, kiran Family doctor Alhaji ya yi don a yi mata treatment.Cike da ɓacin rai da zugi Tahseen ta juya za ta koma ɗakinta sai suka haɗa ido da Fauziyya. Uwar tsokana bata yi wata-wata ba ta manna mata ido ɗaya tare da yi mata gwalo. Wani Sabon kuka Tahseen ta saki tare da rugawa da gudu ta bar falon.  Hajiyan sama miƙewa ta yi da yaranta suka yi sallama da su Hajiya momma tare da cewa sai sun zo kwance kaya suka bar ɗakin. Hujayrah dai na nan tare da magen a jiki don har magen ta kwanta a cinyarta. Mas'ud ne ya kira Hujayrah, babu musu ta miƙe tare da magen ta zo wurinsu. Murmushi ya yi sannan ya ce

"Ya jikin naki ɗazu a muka zo aka cemin baki da lafiya" 

Hannunta na shafa kunnan magen ta ce

"Da sauƙi Ya Mas'ud, Ina tunanin ma na fita lafiya don jina nake kamar ingarman doki" 

Murmushi ya yi yana girgiza kai ya ce

"Hmmmm kin faɗa dai ne amma wace ce ke da za ki haɗa kanki da ingarman doki, baki gaishesu Mahmoud da Arqam ba Hujayrah, kuma kina ganin suna zaune" 

Sai a sannan ne ta dubi Mahmoud ta ce

"Barkha da rana, Ina wuni, Ina gajiya, ya aiki, ya yara, ya iyaye, ya matan..." 

Bata ƙarasa abin da ta yi niyyar faɗa ba Mahmoud ya yi saurin cewa

"Koooowaaa yana lafiya!!! Wai!!! Haka kike da surutu" 

Murmushi Hujayrah ta yi sai ta ce

"Allah sarki ai don banda lafiya ne yasa bakina ya rage motsawa" 

Girgiza kai ya yi sannan ya ce

"To Allah ya ƙara sauƙi" 

Za Ta amsa masa Mas'ud ya ce

"Shi kaɗai ne a wurin Hujayrah , ce nake mai magen da kike riƙe da ita yana zaune, kuma yana jin ki" 

Turo baki Hujayrah ta yi sannan ta ce

"To ai KURMA ne baya magana, daman ina so idan na gaishar da wancan sai na gaishe dashi da yaran kurame nasan zai fi fahimtana" 

Waro idanu Mas'ud da Mahmoud suka yi waje kamar haɗin baki lokaci guda suka ce

"KURMAAAA!" 

Ko a jikin Hujayrah ta sake cewa

"Ai ba ƙarya na yi ba, tun da ya zo falon nan ban ji ya faɗin kalma ɗaya ba, sai dai girgiza kai sannan kurame ka ɗai suke wannan, bara ku ga" 

Ajiye magen ta yi  ta juyo wurin Arqam wanda tun lokacin da ta kira shi da kurma ya yi saurin ɗago kansa yana kallonta babu ko ƙyaftawa . Babu tsoro balle firgici a tattare da ita ta fara masa gaisuwar kurame har da duƙawa. Arqam kafeta ya yi da kasalallun idanunsa masu kama da mai jin bacci,ido cikin ido yake kallonta a tunaninsa za ta tsorata amma ina gogar ko a jikinta sai ma ƙara zaƙewa take. Mamaki ne ya cika shi ganinta da koren ƙwayar ido, a ransa yana faɗin 'Anya mutum ce wannan yarinyar' Mas'ud ne ya katse masa tunani da cewa

"Hujayrah! Hujayrah!! Hujayrahhh!!! Ahhhhh! Komai naki daban ne wallahi hhhhhhh, yanzu in banda abin ki Hujayrah waya faɗa miki Arqam kurma ne? 

Turo baki ta yi  cike da shagwaɓa ta ce

" To to ni ai ba ƙarya na yi ba, domin in da yana magana ya kamata a ce ya yi magana a yanzu amma sai bin mutane da ido yake kamar wani..." 

Mas'ud ya yi saurin katseta da cewa

"Hujayrah baki da tsoro ko, idan kuma ya ce zai bugeki fa" 

Dariya Hujayrah ta yi sannan ta ce

"Tsoro! Tsoro tab! Ni ko bindiga na gani zan tsorata ne balle duka, kar ka manta Hujayrah ce fa ɗiyar Audu jikanyar Kamalu Angon Hindatu mai tsoro mutuwa, Ni ɗin ce dai" 

Tintsirewa da dariya Mas'ud da Mahmoud suka yi, Mahmoud har da riƙe ciki shi kuma gogan naku bai motsa ba balle ya yi dariya, sai ma sake kafeta ya yi da kasalallun idanunsa. Su Mas'ud sai da suka yi dariya son ransu sannan ya ce

"Haaaaaaa! Hujayrah yanzu mu bar part ɗin Arqam gidanku ɗaya babu ruwanmu, ni dai ina jiye miki randa za ki kai Arqam maƙura da surutunki, idan ya riƙeki karki kira Sunana, bar ganin bai ce miki komai ba, idanunsa su ne amsarki. Yawwa yau ne fa aikin namu" 

Zama ta yi a saman carpet ɗin wurin tare da cewa

"Ok to zuwa yaushe kenan aikin" ta gane inda ya dosa wato cire asirin da yake a gidansu

"Da kinga fita na kawai ki biyo hanya, zan jiraki a wurin motana, yanzu tashi ki koma cikin ƴan uwanki" 

Babu musu ta miƙe har ta tafi sai ta dawo ta dubi Arqam ta ce

"Ammm! Ya Raqam qam don Allah za ka bani magenka" 

Sake Ɗagowa ya yi tare da kafeta da ido a ransa yana faɗin 'Na shiga uku ni Arqam, wannan wa ce kalar yarinya ce da shegen tsokana, ko Nazima she can't dare talk to me like that' 

Girgiza mata kai ya yi alamun a'a. Nan da nan Hujayrah ta kwaɓe fuska kamar mai shirin kuka ta ce

"Allahu Allahu! Shikenan  Ya Raqam qam ba komai ni ma zan tara kuɗi na siya nawa, kuma idan ka roƙeni na ara maka, bazan bada baaaa!" 

Wannan karon sai da Arqam ya saki murmushin da bai shirya masa ba. Da sauri Hujayrah ta ce

"Laaah! Ya Mas'ud ashe yana murmushi" 

Saurin waigiwa Mas'ud da Mahmoud suka yi don su gasgata, ilai kuwa murmushin yake. Mamaki ne ya cika su, Mahmoud ya ce

"To fa! Arqam yau kai ne da murmushi, Ashe kuwa za a yi ruwan sama har da ƙanƙara" 

Dariya Mas'ud ya yi bai ce komai ba. Duƙawa Hujayrah ta yi tana shafa jikin magen ta ce

"Ƴar kyanwata kar ki damu kin ji, za mu dinga wasa mu kaɗai abunmu, bara na koma anjima zan zo na ɗaukeki mu yi bacci tare" 

Miƙe ta yi sannan ta bar wurin tana ƴan waƙe-waƙenta. Sauke ajiyar zuciya Arqam ya yi bayan ta ɓace ma ganinsa sai ya dubi Mas'ud cikin cold deep voice ɗinsa ya ce 

"Who is she?" 

Sauke ajiyar zuciya shi ma Mas'ud ya yi sannan ya ce

"Labarinta yana da tsowo sosai,daman ina so bayan bikin murnar birthday ɗinka zamu tattauna mu uku,har da kai Mahmoud don labarinta ya shafeka, sannan dole mu miƙe tsaye saboda akwai guguwan da ke shirin tunkaromu baki ɗaya. Abdul ya kirani akan kana son Halima wacca take a Maiduguri ko, kasan sister take gareni domin mahaifiyarta wacca ta rusa da mahaifin Abdul da Daddy na uwa ɗaya uba ɗaya suke"

Jinjina masa kai Mahmoud ya yi, sai Mas'ud ya ci gaba da cewa

"To Mahaifin yarinya wato Sheikh Munnir da Uncle ɗina Uncle Ayyub da kuma daddyn Tahseen Senata abokanai ne masu ra'ayi ɗaya. Labarin yarinyar nan Hujayrah ya shafesu baki ɗaya a dalilin binciken da na yi mai zurfi akansu bayan ta bani labarin arayuwarta, just in two days na yi binciken. Hujayrah na da surutu da ban dariya, a wani gefen Allah ya bata wata ɓoyyayar baiwar wanda sai kana tare da ita za ka gane hakan, yanzu dai zuwa gata That's bayan bikin birthday ɗin Arqam sai mu tattaunawa"

Sauke ajiyar zuciya kowannansu ya yi, Arqam bai ce komai ba bin Mas'ud da ido yake. Shi kuma Mahmoud ya ce

"To shi kenan Allah ya kai mu rai da lafiya, wallahi har na ƙagu na ji what's going on" 

Murmushi Mas'ud ya yi sannan ya ce

"Don't worry we're not in hurry, zan sanar daku komai, don nasan kuma za ku ba da naku gudunmuwan" 

Duba agogonsa Arqam ya yi tare da miƙewa ya ce

"Lokacin sallah" 

Su ma miƙewa suka yi tare da biyosa cikin falon,Hajiya momma ce ta ɗago ta ce

"Son abincin fa" 

Yatsina fuska ya yi yana girgiza kai, sannan ya ce

"Later" 

"To shi kenan, hala za ku tafi masallaci ne don naga Alhaji shi ma ya wuce" 

"Eh Hajiya" cewar Mas'ud 

Fita suka yi daga falon zuwa masallaci wanda yake a cikin gidan. Hajiya momma da Hajiya Nafisa suka miƙe don su yi sallah, Nazima da Razina su ma suka wuce ɗakin Razina yin sallah, Hujayrah kaɗai suka bari a falon  kasancewar bata sallah. 

Bayan an idar da sallah su Arqam sun dawo gida, kai tsaye  ya wuce zuwa part ɗinsa don ya yi wanka ya huta,shi kuma Mahmoud ya ɗauki motar don ana nemansa a gidan. Mas'ud ne ya nufa part ɗin Hajiya momma don ya samu ya kira Hujayrah da dubara saboda baya son kowa yasani sai su tafi can gidansu don ta haƙo sirihin da aka bubburne a gidan. Ya ko ci sa a ita kaɗai ce a falon Hajiya momma, signal ya yi mata sannan ya fita. Tsam! Ta miƙe ta fito, kai tsaye ta wuce ɗakinsu don ta ɗauki hijab ɗinta da glass. Koda ta shiga su Razina na sallah, amfani da wannan damar ta yi,hijab da glass ta ɗauka sannan tabar ɗakin, sauri-sauri ɗan gudu-gudu take don kar su Razina su fito su sameta har su tambayeta ina za ta je. Har ta fito daga part ɗinsu za ta shiga main falo, sai ta ji kamar ana maganganu a ɗan wani lungu da ke kusa da main falon. Dawowa ta yi da baya zuwa lungun,kai tsaye ta matso kusa da lungun, lokaci guda zuciyarta ta buga da mugun ƙarfi ji kake Dummmm! Waro idanunta ta yi waje kasancewar daman bata saka glass ɗin ba, daman ta bari ne sai idan ta shiga mota sai ta saka. Mamaki ne ya cika Hujayrah ganin Salame da wata mata wacca take kyautata zaton mahaifiyar Tahseen ce saboda muguwar kamar da suka yi. A ranta tana faɗin 'Me suke tattaunawa ne a lungu su kaɗai, me wannan matar  take shirin aikatawa a gidan nan ne, tabbas bata da zuciya mai kyau, muguwa ce.juyawa ta yi ba tare da sun ankara da ita ba ta bar wurin zuwa main falo. A nan suka haɗu da Baba Uwale, cike da girmamawa Hujayrah ta gaisheta tana sinne kai, da kulawa baba Uwale ta amsa mata tare da tsokanarta da ta gujeta yanzu. Ɗan murmushi Hujayrah ta yi ba tare da ta ce komai ba tabar falon, kai tsaye ta nufa inda ake ajiye motoci, da yake tasan motar Mas'ud direct can ta nufa. Buɗe murfin motar ta yi ta shiga sai ya tada motar suka bar gidan. 

Bayan sun bar Estate sai ya dubi Hujayrah sannan ya ce

"Yau babu kowa a gidan, Hajiya Zinatu da yaranta tun jiya suka bar gida zuwa Kano biki,yau kuma Mom suna nan shi yasa na ce is better ki yi aikinki a yau tun da mun samu dama" 

"Hakane gaskiya, amma baka tunanin a cikin ma'aikatan a samu munafuka wacca za ta faɗa ma matar" 

Murmushi ya yi sannan ya ce

"Babu damuwa zan ji da wannan fannin " 

Juyowa Hujayrah ta yi tana dubansa ta ce

"Yawwa Ya Mas'ud mahaifiyar Tahseen fara ce kuma suna kama ko" 

Mamakin tambayar ya yi, juyowa ya yi ya ɗan dubeta sannan ta ci gaba da tuƙinsa ya ce

"Hakane suna matuƙar kama sosai, amma mai yasa kika min wannan tambayar " 

Ɗan yatsine fuska Hujayrah ta yi sannan ta ce

"Kawai da ganta yau da wata mai ma Mammi aiki, daman tun lokacin da na haɗu mai aikin zuciyata bata aminta da ita ba, sai kuma ɗazu da zan fito zuwa wurinka na ji  ƙananun maganganu na tashi a wani lungu kusa da babban falo, da har na wuce sai na dawo da baya tare da leƙa lungun, mahaifiyar Tahseen da wannan mai aikin na gani sun ƙus-ƙus, sannan ita kanta mahaifiyar Tahseen ta na kalle ta sai da ƙirjina ya yi matuƙar bugawa. Allah Ya Mas'ud akwai matsaloli da yawa a cikin gidan nan, domin har ta Hajiyan Sama tana da matsala don ita ma ban yarda da ita ba, "

Sauke ajiyar zuciya Mas'ud ya yi sannan ya ce

" Kenan akwai chakwakiya a gidan, zamanki a gidan ba ƙaramin taimako za ki yi ba Hujayrah, Ina so don Allah ki kula da gidan sosai tare da mutanan gidan, na fi tausayin Hajiya momma don duk wani kashi ita ake gogamawa, kusan duk a kanta suke yaƙin da Arqam "

Da sauri Hujayrah ta ce

"Laaah! Ni ba na manta na faɗa ma ba Ya Mas'ud" 

Bai juyowa ya ce 

"Me kenan" 

"Ya Mas'ud akwai sihiri a jikin mammi  kuma mai ƙarfi" 

Ƙuuuuuuuu!!! Ya ja birki da sauri domin ƙiris ya rage ya bigi wata mota, gefe ya yi parking motar hankalinsa tashe ya ce

"Innalillahi wa'inna Ilaihi Raji'un! Hujayrah! Kika ce asiri?" 

"Da gaske nake wallahi Ya Mas'ud kasan bazan maka ƙarya ba balle ba halina ba ne , shi yasa na saka ayar tambaya akan wannan mai yi ma mammi aiki tunda tana shiga ko'ina a ɓangarenta. Sannan yau kuma na gansu a lungu suka ƙus-ƙus da Maman Tahseen" 

Ɗan shiru Mas'ud ya yi yana tunani sai can ya ce

"Hujayrah kinsan me nake so da ke" 

Girgiza kanta ta yi, sai ya ci gaba da cewa

"Ki kula sosai sannan ki saka ido akan wannan mai aikin,sannan ki yi ƙoƙari wurin gano inda aka saka sihirin ki karya don ina da tabbacin Aunty Ramla ce da wannan aikin, tun ba yau ba take son Arqam ya auri Tahseen amma yaƙi saboda shi ba aure ne a gabansa ba, sannan Tahseen bata cikin sahun kalar matar da yake so don bata da kamun kai. Ina ganin ita ce ta yi asirin akan Hajiya don ta sakata ta tirsasa Arqam  ya auri Tahseen tunda tasan baya saɓa umarnin Hajiya. Ke duniya ina za ki damu! Ni dai don Allah Hujayrah ina roƙonki da ki taimaki wannan ahalin da baiwar da Allah ya baki musamman Hajiya momma da Arqam, bar ganinsa shiru-shiru ko ki yi tunanin baya magana, haka halin sa yake na rashin son magana da shiga mutane kamar mahaifiyarsa, amma wallahi yanada sauƙin kai sosai ta yadda bakya tunani, shi ma in so samu ne ina so ki kula da masu kawo masa abinci duk da yafi son girkin Hajiya, amma matsalar masu kai masa part ɗinsa tunda baya cin abinci a dining room, za a iya samun wasu su saka miki wani abu a ciki. Please Hujayrah ki saka ido sosai, sannan a ɓangaren taimakonki da na ce zanyi ina nan Ina yi, har ta Arqam da Mahmoud za mu ci gaba ta bincike akan mutumin da muƙarrabansa "

Wani daɗi ne ya mamaye ilahirin zuciyar Hujayrah sosai ta shiga farin ciki mara misaltuwa jin Ya Mas'ud yana bincike akan Alhaji Sambo Dala. Cike da farin ciki ta ce

" Ina godiya sosai Ya Mas'ud sannan zan ci gaba da saka ido sosai a gidan. Daman ina nan Ina bincike akan Ina aka birne sirihin. Ba sai ka roƙeni ba Ya Mas'ud na ɗaukesu kamar ahalina ne, zan iya komai don farin cikinsu domin sun taimaki rayuwa a lokacin da nake da buƙatar taimako "

Godiya ya yi mata sannan ya tada motar suka bar wurin.Basu daɗe ba suka zo gidan, mai gadi ya buɗe musu gate sai ya shigo da motar ciki kai tsaye zuwa parking space. Bayan sun fito sai ya kira mai gadin da yake mutuminsa ne sosai. Ce masa ya yi

" Lado don Allah zan iya digger wanda ake haƙa rami kuwa" 

Cike da girmamawa Lado ya ce

"Sosai ma Kuwa Yallaɓai bari ɗauko maka a ɗaki yanzu" 

Yana gama maganar ya juya zuwa ɗakinsa da sauri, ya ɗauki ƴan mintuna daga baya ya fito daga ɗakin hannunsa riƙe da digger, miƙa masa diggar ya yi zai koma wurin zamansa sai Mas'ud ya ce 

"Zo muje Lado tare da kai za mu yi aikin" 

Babu musu ya bisu, kai tsaye Hujayrah ta nufi idan ta fara tunanin an binne sirihin wanda yake a tsakiyar gidan wurin da ruwa yake fitowa. Suna zuwa  sai ta nuna ma Mas'ud daidai wurin. Diggar ya ɗauka ya fara haƙa. Da sauri Hujayrah ta ce

"Yawwa Ina zuwa" 

Matsowa ta yi kusa da wurin sai ta ce

"Ya Mas'ud nan ne amma akwai matsala don bazan iya cirowa a yanzu da kaina ba saboda ina al'ada, amma sai ka yi bismillah kafin ka ciro" 

A hankula da ƙarasa zancen saboda wata matsananciyar kunyarsa ce  ta kamata. Murmushi ya yi sannan ya ajiye digger, ya lanƙwasa hannun rigar sai ya saka hannunsa a cikin ramin ya fara lalube, cike da mamaki ya tsaya da aikin jin hannunsa ya taɓo wani abu, a hankali ya jawo abun wanda yake kyautata zaton kwalba ce. Miƙewa ya yi bayan ya ciro kwalbar,fuskarsa ɗauke da mamaki ya ce

"Lado kaga Ikon Allah a nan" 

Miƙa ma Lado kwalbar ya yi, jikin Lado na rawa ya amsa kwalbar yana cewa

"Ikon Rabbi sai Rabbani, ke duniya ina za ki damu! Allah! Allah! ka tsare mana imaninmu! Ko me yake a ciki..." 

Katse shi Hujayrah ta yi da cewa 

"Akwai wasu wuraran ai, ku zo muje" 

Babu musu suka biyota a baya kamar raƙumi da akala, duk inda ta je ta nuna ana haƙa wurin sai a ciro wani ƙullin, a ƙalla sun tara abubuwa da yawa a wurare mabambanta. Bayan sun kammala sai suka taho parking space da karikican a hannun Lado, amsa ya yi daga hannunsa sannan ya ce

"Lado ba wai ka tayani aiki yana nuni da ka faɗawa kowa bane , Ina maka kashedi akan ka kama bakinka babu ruwanka da cewa mun cire wani abu, sannan zan baka kuɗi ka gyara wuraran a yau saboda bana so a gane komai ka ji" 

Cike da girmamawa Lado ya ce

" In shaa Allah ba za ka taɓa samuna da wannan irin halin ba, babu wanda zai sani" 

Miƙo masa kuɗi ya yi bayan ya saka kayan a booth, buɗe masa gate ya yi sai suka bar gidan. Bayan sun ɗauki hanya sai ya dubi Hujayrah  ya ce

"Hujayrah yanzu ya za a yi da waɗannan karikican" 

Ɗan tunani ta yi sannan ta ce

"Abu biyu zuwa uku zamu yi yanzu, na farko dole mamminka tasan da wannan abu domin ta kula da kanta saboda gaba, na biyu tunda kai jami'in sirri ne, mai zai hana ka ɗauki hoton kayan ƙila nan gaba ya yi maka amfani wurin kafa hujja, na ƙarshen sai mu ƙona kayan bayan mun warware abubuwan ciki wanda nasan in shaa Allah asirin zai karye"

Jinjina kansa ya yi yana murmushi ya ce

"A gaskiya Hujayrah kina da tunani mai kyau kamar ba ƴar ƙauye ba, wata ƴar birnin mai ilimi ba za ta nuna miki tunani da hangen nesa ba" 

Murmushi Hujayrah ta yi sannan ta ce

"Ya Mas'ud idan mutum yana so ya zauna lafiya tare da kwanciyar hankali dole yasan mai yake yi, ya zama mai tunanin da kuma hangen nesa. Koda muke a ƙauye mu ma musan da haka" 

Jinjina kansa ya yi yana cewa

"Muna zuwa wurin gidanku zan kira mom ta fito sai mu samu wani wuri a gefe mu yi mata bayani daga bisani mu ƙona kayan"

"To shi kenan haka za a yi" 

Basu ƙara cewa komai ba suka ci gaba da tafiya har suka ida bakin gate ɗin. Kiran Hajiya Nafisa ya yi tare da ce mata ta fito wajen gidan. Da ɗan mamaki ta ce gata nan zuwa.Bayan mintuna kusan goma Hajiya Nafisa ta fito daga gidan, kai tsaye ta nufi motar, bayan ta zo ya ce mata ta shiga mota. Wani sabon mamakin ne ya sake kwanciya a fuskarta, bata ce komai ba ta zauna a sit ɗin baya. Bayan ta zauna ne Hujayrah ta juyo ta gaisheta. Mamaki bai bar fuskar Hajiya Nafisa ta amsa gaisuwar . Tada motar ya yi sannan suka bar wurin, bayan sun fita daga Estate ɗin sai ya samu wani wuri mai kyau wanda ba kowa ya yi parking. Ya fita tare da buɗe bayan motarsa ya ciro tarkacen kayan a Leda ya buɗe murfin bayan ya shiga ciki kusa da Hajiya Nafisa ya zauna. Bai ce mata komai ba ya kwance ƙulli lokaci guda Hajiya Nafisa ta zaro idanunta waje tana faɗin

"Mas'ud ina kuka samo, layoyi haka da kwalban sihiri" 

Ɗan murmushi ya yi sannan ya fara bata labari tun daga farkon da Hujayrah ta sanar mishi da sihirin da aka birne tare da fada mishi Hajiya Zinatu ce ta yi asirin kuma akan Hajiya Nafisa har zuwa yau da yaga babu kowa ya ce ta zo su cire abubuwa.

"Haba biri ya yi kama da mutum domin wasu abubuwan da suke faruwa dani tun daga aurena zuwa yanzu hankali ba zai taɓa ɗauka ba, Hujayrah ƙwaƙwalwata ta gaza tunanin wasu kalamai ya dace na yi amfani dasu wurin gode miki akan wannan taimako da kika min, Na gode Na gode Hujayrah, Tabbas ke alkhairi ce a garemu, ban da bakin..."

Bata ƙarasa abin da ta yi niyyar faɗa ba sai ta saki wani matsanancin kuka. Tana tuno da wasu abubuwa da dama wanda suka yi kama da aikin sihiri a rayuwarta. Hujayrah da Mas'ud sai haƙuri suke bata amma ina kamar ƙara mata ƙarfin kukan suke. Sai da ta yi iya yinta sannan ta share hawayanta ta ce

"Son yanzu ya za a yi da wannan abubuwan" 

"Hotonsu zan ɗauka sai daga baya mu ƙonasu" 

"Yawwa gwara a ƙona shegen sihirin ya karye, kai amma anyi shaiɗaniyar mata, lallai Zinatu ta kai ƙarshe a hatsabibanci, in shaa Allah zan kula sosai yanzu. Mas'ud tunda Arqam ya dawo nasan bai rasa micro cctv cameras, Don Allah Kace ya baka zuwa gobe a sakasu a gidan tunda basa garin "

" Haka za a in shaa Allah, yanzu dai babu ashana ko latter da za mu ƙonasu, bara na sauke ku gida, in ya so sai ya siyo ashana da petrol na ƙona a cikin daji"

"Yawwa haka za a yi , sannan ka kula da kanka sosai" 

Murmushi ya yi sai ya fito daga back sit ɗin ya dawo driver sit ya tada motan. Yana kaisu cikin Estate ɗin daidai gate ɗin gidan ya juya akalan motar ya bar Estate. Kan ka ce me har ya ƙona komai bayan ya ɗauki hotonsu sannan  ya dawo cikin gidan wanda kusan awa ɗaya ya yi yana kai kawo wurin siyan petrol da ashana, sannan ya nufi ɗan wani wuri kamar daji ya ƙona kayan ya dawo cikin Estate ɗin.wannan ke nan... ✍️

       🌎🌎🌎🌎🌎🌎

A ɓangaren Hajiyan Saman bayan  sun koma part ɗinsu,suna zaune a falon sama, sai Hajiyan sama da dubi Fauziyya ta ce

"Fauziyya" 

Juyowa Fauziyya ta yi daga kallon Tv da take ta ce

"Na'am" 

Gyara zama Hajiyan Sama ta yi sai ta ce

"Fauziyya abin da nake so da ke shi ne, duk wuya duk runtsi ki tabbata da kin sace zuciyar Arqam, ya zamana baya kallon kowace mace sai ke. Makirci, kissa, karairaya irin na cikakkun mata nake so kiyi amfani dashi wurin sace zuciyarsa. Naga take-taken Hajiya Ramla da wannan sheɗaniyar ƴarta, saboda zuwa Arqam ne yasa ta kwaso ƙyamusasshan jikinta ta dawo wurin Mubina. To Ina so ki nuna mata kin fita iya kissa da kisisina. Domin akwai wani shiri na musamman da nake a kansu Mubina da yaranta. Jira nake Khalil ya dawo daga course ɗinsa, shi ma nemi auran Nazima, tuwona mai na nake so ayi. Hakan kaɗai ne zai sa shiri na ya tafi yadda ya kamata"

Murmushin jin daɗi Fauziyya ta ta yi don tun tana yarinya take mutuwar son Arqam sai dai Hajiyan Sama ta hana ta nunawa, a cewarta ba yanzu ba. Tunda akuyar ɗaure ta samu sake to me ya rage, ai dole Arqam ya so ta ya kuma ƙaunaceta, domin ta hanyoyi mabambanta za ta kai masa farmaki wanda tasan dole ya faɗa a ɗaya daga cikinsu. Cike da farin ciki Fauziyya ta ce

"Mom baki da matsala akan wannan, just ki saka a ranki Arqam ya gama zama mallakina, don Tahseen bata isheni kallo ba, a cikin mata ko darajar yatsana bata kai ba. Duk kai kawon da za ta yi akan Arqam ba za yi nasara ba, domin  kissar da kika koyamin zan fito da ita. Ina alfahari da ke Mom"

Sosai Hajiyan Sama ta ji daɗin kalaman Fauziyya, babu laifi ta yi dacen ƴaƴan riƙonta, dukkaninsu suna mata biyayya tare da bin umarninta kowani iri ne, shi yasa bata kukan rashin haihuwa saboda tanada masu share mata hawaye. Ci gaba da magana ta yi 

"Sannan na gaba shi ne wannan iblishiyar yarinyar da Mubina take riƙo yanzu Hujayrah ko, yarinyar da ko sati ɗaya yarinya bata yi duk da addabi mutane. Yau na tsinke da lamarin yarinyar nan wallahi ni Izzatu Hujayrah wacca bata wuce jika a wurina ba take cemin  *_Gani nan bari nan dukiya alawa, wutsiyar raƙumi ta yi nesa da kasa, Ni ɗin dai Hujayrah ɗiyar Audu mai maganin ƴan bana bakwai_* kai!!! Wallahi sai na yi maganin yarinyar nan, da Izzatu take, idan ba ta yi wasa ba zan iya ɓatar da ita a doron duniya hankali kwance"

Taɓe baki Fauziyya ta yi sannan ta ce

"Ai mom kawai ki yi hakan mu yada ƙwallon mangwaro mu huta da ƙuda, shegiya sai ƙarfi kamar namiji, anya ma tana da hankali kuwa" 

Dariya maganar Fauziyya taba Zahriyya da Hajiyan Sama. Sai a yanzu ne Zahriyya ta ce

"Mahaukaciya ce wallahi, baki ga idanunta ba kamar na aljanu, mom nifa a ranar da naganta sai ta nayi mafarkinta wallahi, kawai mom ki ɓatar mana da ita" 

Wani ƙasaitaccan murmushi Hajiyan sama ta saki sannan ta ce

"Mai kuke ci na baka da zuba ɗiyan albarka, bara na gama da Mubina da yaranta, zan dawo gareta wanda lokaci guda zan ɓatar da shegiya" 

Dariya suka yi sannan suka ci gaba da hirarsu suna raha hankalinsu kwance, wanda kusan hirar akansu Hajiya momma ne da uwar gayya Hujayrah...✍️

       🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Kwanar Kwara ƙwai, Kaduna state. Nijeriya*

A ɓangarensu Murja tun bayan amincewar Alhaji Zakari suka fara shirye-shiryensu. Da yake a ranar Alhaji Zakari ya turo mai unguwa da wani abokinsa suka zo wurin neman auran Zaliha. Kasancewar mahaifin Zaliha na raye sai suka je wurinsa, lokaci guda aka  yi komai aka gama, sannan aka saka ranar auran zuwa nan da kwana uku wanda ya kama ranar Asabar. Cike da farin ciki Zaliha ta kira Murja da yake lokacin har Murja ta koma gida. Bayan ta sanar mata da saka ranar bikin sai Murja ta ce zuwa gobe ta shirya su haɗu a hanya, don tun yanzu ya dace su fara shiri saboda da zafi-zafi ake bugun ƙarfe. Dole su kai Hannatu ƙasa, ya zamana su suke juya Alhaji Zakari a tafin hannunsu.

Washe gari da safe Murja ta shirya tsaf! Ta ci kwalliya kamar za ta gidan biki. Bayan ta fito daga gidan ta samu ɗan acaɓa ta hau, daman tun fitowarta ta kira Zaliha akan ta fito sannan ta sanar mata inda za su haɗu. Bayan sun je wurin da mai mashin ɗin sai suka yi sa a Zaliha ita ma mai mashin ɗinta ya karyo kwana. Signal kawai ta yi mata alamun su biyosu, sanar ma mai mashin ɗin Zaliha ta yi akan yabi mai wancan mashin ɗin, babu musu ya bishi. Sun daɗe suna tafiya daga bisani suka isa daidai Layin gidan boka mai zamani. Bayan sun sallami masu mashina sai suka taka zuwa cikin Layin har gidan bokan. Koda suka iso gidan sun tarar da mata suna bin layi,haka suka bi layi a cikin gidan har layin ya zo kansu. Zaliha ce a gaba Murja na biye da ita suka shiga cikin ɗakin, kamar yadda kuka san ɗakin to haka yake babu wani canji. Boka mai zamani yana zaune yana shafe-shafansa irin na mata. Bayan sun zauna sai Murja idanunta a ƙasa ta ce

"Sarkin ƴan daudun duniya! boka mai zamani boka namu! Mai Share kukanmu yau gamu munzo gareka don ka sake Share mana kukanmu" 

Cak! Ya tsaya da abin da yake ya ɗago jajayan idanunsa ya saukesu akan Murja lokaci guda rauhanan kansa suka tashi. Ajiye kayan kwalliyar ya yi tare da gyara zamansa. Sosai yake mata mugun kallo idanunsa na ƙara ja. Hankalin Zaliha ne ya yi matuƙar tashi saboda suffarsa ta fara canjawa daga na asalinta zuwa wani halittar na daban. Hanyar cikinta har ta fara kaɗawa saboda tsoro, ba wai yau ne farkon zuwanta wurin boka ba sai dai wannan bokan ya bambanta da sauran bokayan saboda yanayin. Cike da tsoro Zaliha ta ɗan ta taɓa Murja tana mata nuni da bokan, Murja da bata san wace waina bokan ke toyawa ta juyo wurin Zaliha tana mata nuni da lafiya, yi mata alaman ta dubi bokan Zaliha ta yi, bata kawo komai a ranta ba Murja ta juya wurin bokan, ai nan take gabanta ya yanke ya faɗi, da matuƙar ƙarfi ƙirjin ya buga ji kake Dammm! Darammm!! Damdammm!!! Sosai hankilinta ya dugunzuma ya yi ƙololuwan tashi ganin wata halitta ta daban ba boka mai zamani ba. Idanunsa sun kaɗa sun yi jajur kamar jan gauta, gashin kansa duk ya miƙe tsaitaye kamar tsintsiya,fuskarsa ta canja zuwa wani kalan launin daban. Mafi ƙololuwan tashin hankalin a wurin Murja ita kaɗai yake kallo yana huci kamar wani kurmucin maciji wanda yake jira ya ji ance *kule* ya. ce *cas* 

Da wata kalar murya mai amon sauti da ƙaraji ya fara magana 

"Ke maciyiya amana!!! Mu za ku sa ka a ƙonamu da zafafa ayoyi masu illata jikkunanmuuu!!! Mu muku aiki ku koma wulaƙantamuuuu!!! Muuuu!!!" 

Lokaci guda jikin Murja ya fara rawa, wani irin gumi wanda bata san da zuwansa ba ya fara kwaranyo mata a duk ilahirin jikinta. Cike da tsoro muryarta na rawa ta fara magana 

" Ammmm Boka mai zamani bani bace mai aikin Hannatu ceee... "

Wata uwar tsawa ya daka mata lokaci guda suka razana, Zaliha tuni ta saki fitsarin da take riƙewa tana ƙanƙame Murja saboda tsoro. Cin amon muryarsa mai cike da ƙaraji ya ci gaba da cewa

"Ƙarya zamu yi miki!!! Kece farkon wacca ta fara rusa mana shiriii!!! A sanadiyyarki wasunmu sun zama guragu saboda azabaaaa!!! Tafi ƙarfinmuuuu!!! Tafi ƙarfinmuuuu!!! Ita da ahalinta sunfi ƙarfinmuuuu!!! Dole ne mu ɗauki fansarmu akan babban ɗanki wanda...✍️









*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
 ***











Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol