Free chapter · Read without an account

9

by Asmy b Aliyu · OMRI HAYATII

OMRI HAYATII

by
Asmy b Aliyu 

9.....
malaak duk hankalinta yaki kwanciyya,
ta dubi mum din dake famar danna waya tana fadin"mum ko dai anan zan barki 
na samesa a clinic kawai.nasan zan ma samesa acan din."kafin mum tayi magana daidai nan Mamin ta karaso wurinsu da murmushi a fuskarta.kasa daurewa malaak din tayi ta kalli Mamin tana fadin"Mami yayanmu fa?"ta fada kamar yadda su Fadeela ke Kiran sunansa.anya Yana gidan nan kuwa tun safe da ya fita bai dawo ba."
Mami ta Karasa xance tana kallon yanayin malaak din,bakuyi waya ba??"dan girgizawa mamin Kai tayi tana fadin"bamuyi waya ba."
mum tayi murmushi tana fadin"ae wannan soyayya ta malaak da mu'azzam Sai Allah,
iyayema suzo a shiga maganar nan musha biki Aisha tunda Sun daidaita kansu."

"Ae wannan hadin zainab kamar da wuya."
Mami ta fada tana kallon cikin idon mum
da wani irin shock malaak ta dago tana kallon mamin,jin tayi jinin dake aiki ajikinta Yana daskarewa wani abu mai nauyi
yazo yayi mata tsaye a wuya kallon mamin take ko kiftawa batayi.dariya mum tayi tana fadin"me zai hana ya faru tunda Suna son junansu Aisha."ai zainab ba anan matsalar take ba ,ke kina masifar son ya'ya nima haka Kar watarana a samu matsala yara suzo su bata mana zumunci....."dan shiru mum tayi tana kallon mamin da mamaki.kasa daurewa malaak din tayi ta miqe tsaye ta juya tabar cikin falon tamkar Zata tashi sama
Banda tafasa babu abunda zuciyarta keyi,
da wani irin kallo Mami ta bita,itama mum
bata tsayarda malaak din ba.

"mudai bisu da addu'a kawai Aisha tunda Suna son junansu Kar mu wani takura masu,babu abunda zai faru.'"Mami ta gyada Kai tana fadin"Allah ya tabbatar da abunda yafi zama Alkhairi."cike da farin ciki mum ke fadin Amin dai........hira sosai sukayi irinta abokai tamkar babu abunda 
ya faru.......malaak na fita motar ta nufa 
batajin ko uwar data haifi mu'azzam din batajin Zata iya hanata aurensa,a nan take 
taji wata irin tsanar mami na lullubeta
kenan duk yadda take tattalinta bata dauketa a matsayin surukarta ba."
wani murmushin takaici malaak din ta saki tana jin kwallar takaici na cika mata 
ido ,shigewa tayi motarta tayi gamida saka  key ta tada motar wani irin horn na fitan hankali ta rika dannawa.a gigice maigadi ya fito ya nufi get ya bude da wani mugun gudu ta fisgi motar sauran 
kadan ta taka masa kafa wani irin tsalle
yayi ya koma gefe yabi motar da kallo da mugun mamaki a Kuma tsorace,
wannan yarinyya ba kanta daya ba anya bata sha kwaya ba."bayan ya maida get din ya rufe gefe ya koma Yana maida numfashin wahala......

######
wani irin gudu take shararawa akan titin da zai kaita clinic bude ido kawai takeso 
tayi ta ganta gaban mu'azzam marafa 
tasan imagination kawai mami keyi 
to idan ba ita malaak din ba daman akwai maccen da mu'azzam din zaiso har ya aureta bayan ita,acan bayan kasan zuciyarta ta adana kalaman mami a wannan lokacin dan kalaman basuda wani muhimmanci a tare daita,da wani irin gudu ta shiga cikin clinic din mutanen dake 
harabar wajen tsayawa sukayi Suna kallon ikon allah,dan sauran kadan ta bugi wata motar da Zata fice cikin clinic din,
da sauri security ya karaso wurin motar tata daidai lokacin ta fito daga motar,
ganin malaak yasa ya dan jada baya
Dan ba motar da tasa ba zuwa daita bace
motar mum ce suka fito daita.
kallon lafia take masa da yazo ya tsaya agabanta,saurin saukar da kansa kasa 
yayi cikin rawar baki yake mata sannu 
da zuwa dan babu Wanda bai Santa tare da dc.mu'azzam ba ko kara kallon security din batayi ba ta nufi entrance din shiga clinic din,babu Wanda ya tsiyar daita
har ta qarasa bakin office din doc.mu'azzam,hannu ta saka ta tura kofar
batareda ta jira tayi knocking ba 
taji kofar a rufe hannu tasa tana dan buga kofar Sai dai shiru kakeji tsaye tayi a bakin kofar tana jin zuciyarta na mugun tafasa,
wata nurse da tazo wucewa ta kofar
ganin malaak din na buga kofar 
ta saukar da kanta tana gaisheta ,ko kallonta malaak din batayi ba.

"madam Ina jinfa doctor bayanan."wani irin kallon balai da masifa malaak din ke aikawa nurse din da yasa tayi saurin wucewa batareda ta Kara furta kalma ko daya ba.tafi minti biyar tsaye a bakin kofar
kafin ta juya ta fice daga clinic din bakidaya,tun a hanya ta daga waya ta kira mum dinta.
a fusace mum din ta daga tana kunduma mata mugun zagi akan me Zata tafi da mota tabarta tamkar wata ya'r iska.
shiru malaak din tayi tana jin notin kanta na Kara kuncewa,shirun da mum din 
taji yasa gabanta yayi mummunan faduwa
da Karfi take Kiran sunan malaak din.
sai yanxu ma ta tuna malaak din cikin mugun fushi take ,Wanda malaak din tun 
tana yarinyya idan tana fushi kowa 
kasa controlling dinta yake saboda
tamkar mai jinnu haka take komawa,
tabi ta jima kanta ciwo.sai su mum din sun kamata Sun danneta,
"malaak kina Ina ???"mum ta fada da wani irin ihu,lokaci daya hankalin mum din
yayi mummunan tashi.
Ina hanya."
malaak ta fada da wata irin murya
cikin rawar baki mum ke fadin koma a Ina take ta tsayarda motar tayi parking gatanan zuwa yanzu nan,
dan bayan wucewar malaak din mum da ta gaji da zama tacewa Mami zata wuce
cike da kulawa Mami ke fadin"bazata jira malaak din ba.mum tace itadai Zata tafi 
gashi Kuma driver bayanan daya saukeki
bari na dauko maki car key Sai kiyi amfani da motar,
godiya mum din tayiwa mami dan har bakin mota mami ta raka mum Sai da taga 
fitar motar mum ta koma cikin gida......

######
mum agigice ta karaso wurin da malaak din ta Kwatanta mata,koda ta samu malaak din ta kifa kanta akan sitiyarin motar,a gigice mum din ta bude kofar 
tana tallabo fuskar malaak din tana Kiran sunanta da idon da suka sauya sukayi wani irin ja malaak din ke kallon Mum ko kiftawa batayi,rungumeta mum tayi
tana jin yadda zuciyar mum din ke wani irin bugawa.....dan allah ki dawo hankalinki malaak karki yiwa kanki illah."!na maki alkawarin xaki sami mu'azzam marafa 
zaya zama naki ke kadai."ajiyar zuciya malaak din ke saukewa har lokacin Kuma batayi magana ba,mami ta kalli Mai baiwa flowers ruwa da ta taho dashi tace yayi maza yaje gidansu
mu'azzam din yakai masu tsinannen motarsu,ta fito da malaak din bangaren driver ta bude front seat ta sakata
ta rufe kofar ta zagayo bangaren driver 
ta shiga taja motar,
kurawa titi ido malaak din tayi har lokacin batacewa mum komai ba abubuwan da suka faru tun ranar take tunanowa
da Kuma abubuwan da suka faru a yau.

#######
Anan cikin clinic yayi sallar magrib
bayan ya fito daga massalaci office ya koma ya tattara kayansa ya rufo office din,
a reception ya hadu da nurse din da ta hadu da malaak daxun,ta gaishesa da respect ya amsa a natse Yana kallonta 
Wanda ya fahimci akwai magana a bakinta 
doc.dazu da yamma madam tazo nemanka."cak ya tsaya Yana saurareta,
dukansu Sun sa Mami,itama madam suke kiranta haka malaak tsakanin malaak da Mamin baisan wacce take nufi aciki ba,
kamar tasan me yake tunanin da sauri tace madam malaak!""cak ya tsaya Yana jin iskar da yake shaka tana kokarin tsayawa.nurse din ta cigaba da fadin"ta dade kafin  ta tafi."ta fada batareda ta lura da yanayin da mu'azzam din ya shiga ba,
ok nagode."Ya fadamata Yana wucewa.

bai samu shiga wurin Mamin ba Sai bayan sallar ishaai dan tareda Abba suka dawo daga massalaci anan yake fadawa Abba jirgin 12 Zasubi zuwa Italy daman ta abuja Zasu tashi gobe zuwa 9 Zasu bar kaduna zuwa abuja,shi dai Abba banda kallon yaron nasa babu abunda yakeyi gaba daya yabi ya canja ya wani firgice,bayan ya shiga wurin mami ta daga Kai tanata kallon yanayinsa batareda tace komai ba,
shiru ne ya ratsa a tsakaninsu kafin mamin tace muje can bangaren abba ka dibi abincin kaci."dagawa mamin Kai yayi 
ya nufi bangaren abba,lokaci daya mami ta bisa da kallo tana jin zuciyarta na karyewa.

tare sukaci abincin dare da Abbansa
bai jimaba yayiwa iyayen nasa Sai da safe ya nufi bangarensa.zama yayi a bakin bed Yana shawarar kunna wayarsa ya kira malaak wata irin kewarta ke danne dashi 
dauriya kawai yakeyi saboda bin umurnin maminsa Yana ta kokari Yana ta danne zuciyarsa ,daga malaak din har Mami 
sunada muhimmanci acikin rayuwarsa
baya son hurting din kowa acikinsu 
haka Yana son malaak din su rabu cikin salama da mutuntawa bayason wani tashin hankali ko hargitsi.gaba daya jin yayi nigeria ta fice masa arai musamman hukuncin mami na watanni shidda da ta kayayyade masa ko a mafarki bayajin zai Kara son wata macce anan kusa.

nan da wata biyu zaiyi magana da Abba
companynsa dake Italy zaije ya cigaba da kula dashi hakan kawai zaiyi ya tsira da hukuncin Mami....zai mayar da kansa busyn da zai shafe malaak farook Rano acikin rayuwarsa duka........


#OMRI HAYATII 
#LOVE/FATE
#CRAZY LOVE
#MALAAK FAROOK RANO 
#MU'AZZAM MARAFA 
#ASMY B ALIYU 
#***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol