Free chapter · Read without an account

10

by Asmy b Aliyu · OMRI HAYATII

OMRI HAYATII 
by
Asmy b Aliyu

10...
washegari Karfe 9 driver ya jasu cikin lafiyayyar frado new model 2025 zuwa garin abuja.....
mum ce zaune a gaban malaak ta sakata a gaba da tagumi rana daya duk ta firgice ta fitini kanta da soyayyar balai. soyayyar yaron Aisha da take neman ta zautar da yarta ta saka ta fita daga hankalinta.
banda karkada kafa babu abunda mum keyi.maleeka ce taja numfashi tana fadin"toke mum a bita karkashin kasa 
mana meyasa Zaa zauna ana bata lokaci 
a banza a wofi ae wannan ba lokacin jira bane ga hanyar da Zaa bi ta cikin ruwan sanyi  a saka shegiyar uwarsa ta dawo 
hankalinta."maleeka ta fada tana jin zuciyarta na wani irin tafasa dukansu a jiyan ba wani baccin kirki suka samu ba
duka saboda malaak din da ta dorawa kanta shegiyar soyayya.!!!"

"ni bata hanyar magani ko boka nakeso ya aureni ba cikin hayacinsa nakeso ya aureni."malaak ta fada da wani irin daci a muryarta .daga mum har maleeka bude baki sukayi Suna kallonta.wata dariya maleeka ta fashe daita kafin ta dora da fadin"ae kuwa indai ta hankalinsa kikeso ya aureki to wallahi tallahi ba baki nayi maki ba baxai taba aurekiba."Yaaa maleeka stop it!!!!! malaak din ta fada tana dakawa maleekan tsawa tamkar wata sa'anta
cikin zafin zuciya malaak din ke fadin"so kike nima nayi irin gantalallen aurenki 
da babu komai aciki Sai tarin nadama da bakin ciki."meye amfanin zuwa wurin boka
mijin da kika aura wanda baisan ciwon kansa ba baisan darajarki ba tunda Yana neman matan bisa titi har yanzu tsofai tsofai dashi."malaak !!!"
maleeka ta fada tana daka mata mugun tsawar da sai da dakin duka ya dauka.
cikin zare ido malaak din ke fadin"Karya na fada kin San ni dake dinma akwai mugun banbanci wallahi."mu'azzam baya neman mata haka Shima Yana sona kamar yadda nake sonsa.matsalarmu dayace uwarsa 
kinga ko akwai banbanci tsakanin nidake
ma da kika auri ragin wata macce!!!"

a fusace maleeka ta daga hannu Zata saukewa malaak din cikin fuska
mum tayi saurin rike hannun nata tana wani irin hucin da sukaji har zafi ke bugawa cikin numfashinta.....akan maza kuke kokarin aibanta Ya'n uwanku?
duka Ina wanannan soyayyar da kaunar da kuke yiwa Yan uwanku Wanda na raineku dashi.jikin maleeka banda girgiza babu abunda yakeyi saboda bacin rai 
da maganganun da malaak din ta yarfa mata,juyawa kawai maleekar tayi
ta fice daga dakin. dakinta ta koma tana hada kayanta Kara ta nemi flight tun wuri 
tabar kaduna kafin  ta kona malaak din da ranta .jin take kamar ta dauki waya ta kira Mami ta fadamata meya faru tsakanin malaak din da Mu'azzam ko Zaa samu wani labarin a wurin Mamin,Sai dai Sam 
girman kanta baxai bari ta kira Mami ba,
Zata cigaba da zuba ido taga iya gudun ruwan mu'azzam din kafin tayi wani motsi
dan jin malaak din kawai take da tace Kar abi ta karkashin kasa lokacin da taje tabi ta karkashin kasar ai ba sani zatayi ba....

kusan kwana biyar shiru malaak keji babu labarin mu'azzam babu waya babu text duk wata hanya da tasan xata samesa 
yabi ya tosheta jin tayi tamkar zata zare a lokacin,har dan fadawa tayi saboda kwata kwata bata da natsuwar tsiyawa taci abincin kirki.da taje gidan Fadeela kuwa 
Sai da tasan yadda tayi ta bugi cikin besty dinta ,da mamaki Fadeela ke fadin''"Auhhh
bai gayamaki Sun tafi kasar Italy ba shida Abba,yau Inajin kusan kwana ukku ma,
nima a bakin mami nakeji dan kwana biyu 
mun daina waya Sai dai idan na kira abba
ta vidcall ya hadamu.a lokacin wani irin mugun sanyi jikin malaak din yayi....

tun kafin tabar gidan Fadeela ta shiga online ta duba idan ana samun jirgin zuwa Italy a yau ko zuwa gobe,Sai dai yadda ake nuna mata nan da kwana ukku,
a lokacin jin tayi tamkar zatayi hauka haka ta dawo gida tana yiwa mum din bayani,
da mamaki mum ke fadin"Auhhh daman shi da Abban nasa suka tafi meeting din
ai tareda dad dinku aka tafi daga Us xai wuce Italy ,mum ina ganin zanbi mu'azzam ,
can ayita ta qare mum baxan iya jira ba,
zuciyata tana gafda bugawa akan rashin mu'azzam .da sauri mum tace bazaki bisa ba gaskiyya wane bayani zakiyiwa dad 
din idan yaganki."Sai me idan ya ganni 
mum kin San dad baxai yi magana ba
ya bamu dukkan freedom dinmu."
kiyi hakuri ki jirasu su dawo dai."
mum baxan iya ba malaak ta fada Kai tsaye tana barin wurin,dakinta ta koma ta fara Shiri ta siya ticket na zuwa abuja gobe da safe Kara taje a abuja ta jira
da mum ta dagula mata Lissafi.....

######
tayi shirin bacci cikin riga da wando designer ta haye gadonta kusan Karfe 10 
daidai lokacin mai aiki tayi knocking kofar dakinta ,Sai da ta bada umurni sannan mai aikin ta shigo da madaidaicin tray a hannunta taja center table karami 
a gefen bed din ta dora tray din akai.
cup din tea ne da yake famar tiriri
Sai Kuma cincin ,mai aikin na tsaye ta saukar da kanta tana jiran umurnin tafia
Banda danna wayarta babu abunda take
hannu daya ta mika mata akan ta bata cup din ,cike da taka tsantsan maiaikin
ta dauki cup tea din ta saka a hannunta.

"Zaki iya tafia."
ta fada mata batareda ta kalleta ba
tamkar ance ta duba Whatsapp dinta a daidai wannan lokacin taga kamar mu'azzam din ya tura mata sako,
zare ido tayi tana saurin maida cup din akan tray.

"how are you??"
jin tayi zuciyarta tana saki sakin da tamkar an saka wani abu an daureta...sakon kawai take karantawa tana kirga kalmomin cikin kanta,tafi minti goma sha biyar a haka batareda tayi masa replay ba Kuma har lokacin Yana online.
kasa daurewa tayi ta rubuta masa
"meyasa???"
kife wayar tayi tana jin zuciyarta na mugun zafi.kenan lafiarsa kalau ya shareta na kusan lokaci,,
tana ganin ya kirata vid call taki dauka 
kusan kira ukku yana jera mata Sai a na hudun ta daga a mugun fusace 
tana kallon cikin fuskarsa,Shima kwance yake akan bed Yana kallon cikin fuskarta 
"ni kike yiwa yanga?
ya fada da wani yanayi a muryarsa 
da yasa ta Kasa daurewa kawai ta sakar masa wani irin kukan da take ta riqewa tun dazu Kar yazo.lumshe idonsa
yayi Yana jin kukan nata na mugun taba zuciyarta,
"da ganga kake ganamun azaba saboda kasan baxan iya jure rashinka ba koda na kwana daya,meyasa?? meyasa kake wasa da zuciyata mu'azzam dan kaga Ina sonka shiyasa kake wulakantani duk yadda kaga dama."
"kiyi hakuri dan Allah kiyi mun uzuri.
kalmar hakuri kawai da taji Yana fada
zuciyarta ta Kara tunxura jin take tamkar ta jawosa ta cikin wayar ta rufesa da duka,
duk yadda zan maki bayani bazaki fahimta ba idan na dawo zamuyi magana dan Allah karki daga hankalinki."uzurin gaggawa ya taso mun tafiya ce ta kamani zuwa Italy nida Abba,ko anan din banada cikakken lokaci malaak kullum busy nake
koma menene na maki alkawarin idan na dawo komai zai zama daidai,haka taji kalaman nasa Sun fara saukar daita
shi Kuma baigaji ba ya cigaba da lallaba har ta sauko Sai kusan asuba suka katse Kiran,Sai lokacin malaak ta samu tayi bacci mai cike da natsuwa da kwanciyyar hankali ,daman ba maganar sallah akeyi ba dan badamuwar ta tayi ba Sai tayi sati bata Kai goshinta kasa ba.

mum wuraren Karfe 8 na safe ta shiga dakin malaak din ga mamakinta baccinta take cikin natsuwa,juyawa mum din tayi
tabar dakin Cike da jin dadi kila malaak din ta hakura ta yadda makamanta Zata dauki shawararta .nan kuwa batasani ba mu'azzam ne ya samu ya rarrasheta da kalamai masu tausasa zuciya da taji ta fasa binsa kasan Italy din tunda yace Suma nan da kwana hudu Zasu baro su dawo Nigeria,

ko bayan tashinta daga bacci wuraren qarfe 12 na rana ta fito daga dakin baccinta tayi wanka taci gayu Banda kamshi babu abunda ke tashi ajikinta.
Kai tsaye dakin mum dinta ta nufa 
ta samu mum din da bakuwarta,
cikeda fara'a malaak din ta karasa wurin mum ta rungume mum tareda fadin."good morning mum"good morning to my baby.".irin wannan fara'a haka,mum kinada bakuwa idan ta tafi Sai muyi magana bara naje nayi breakfast.da haka ta juya ta wuce daga dakin batareda ta gaisheda bakuwar mum dinba.dan duka ya'yan mum ba kasafai suka cika daraja mutane ba musamman malaak da tafi maleeka wani irin zafin Kai.....

"yanzu zainab kina ganin Yarinyyar nan 
malaak ta shigo ta ganni bazata iya gaisheni ba ni kawarki ma bani da daraja gareta."murmushi mum tayi tana fadin"Haba Jamila kin San halin kurciya 
Kuma kin San malaak din ba wani son mutane da hayaniya takeyi ba,
wacce aka kira da Jamila cike da takaici 
ta yagi bread din dake gabanta ta debi soyayyen kwai ta hade ta saka a bakinta
tareda daga cup din tea,
"Ai shikenan Allah ya shirya mana."
murmushi mum din tayi tana fadin ameen
kafin su canja wata hirar.....



#ASMY B ALIYU 
#LOVE/FATE
#BEST LOVE
#MU'ZZAM MARAFA 
#MALAAK FAROOK RANO 
#OMRI HAYATII 
#***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol