Free chapter · Read without an account
Chapter 3
HANGEN DALA
Free book
Page 3
“ ke tsohuwar guzuma ba maraba da marhabun suka kawoni ba, gargaɗi da jankunne ne suka kawoni nazo na gayamaki ɗanki Abbas ya rabu da ƴata ya gaggauta bata takardar saki tun kafin na makasa kotu, ki kirashi ki gaya masa ya saki Ahanah tunda ba tare aka haifosuba inko ba haka ba to kotuce zata rabamu da shi wallahi. ”
“ inna lillahi wa inna ilaihir raju'un Subhanalla hajiya shamsiyya kinsan abinda kike faɗa taya zakizoman da wannan baƙin albushir, me yay zafi haka, komai Abbas yayi ai baikamata kice ya saki Ahanah ba sulhu ya kamata ayi tunda dama ai zaman aure ya gaji haka aiyi tsiya ayi daɗi kuma ba ashiga tsakanin ma aurata, komai yay zafi maganinsa Allah shigo daga ciki muzauna mu fuskanci matsalar, dama lamarin aure ai ya gaji haka. ”
“ sulhu ko sasanci kalmomine na gyara ni kuma sam bana da wannan ra'ayi, burina ɗaya aduniya naga ƴata gabana tare warware wance ƙasƙantaccen auren mai kama da na ƙaddara, yo in baccin ƙaddara ina Abbas ɗan jagaliya ina Ahanah kyakyyawa kalar ƴan gayu, kaddara ce kawai ta haɗa kuma ina mai tabbatar maki yau zata raba, don haka ina maki magana da babbar murya idon har kece kika haifi Abbas kuma da aure ba akan titi ba to ki gaggauta sakashi ya sakarman ƴa, idon kuma ba ɗan sinna bane ɗan titine wanda baki isa da shiba to ni zan gwadamasa dai dai nake dashi don ni wandon robace dai dai da ƙugun kowane shege a garin nan . "
“ Tou la'ilaha illalahu wannan rayuwa yau naga ƙarshen duniya " faɗin Hajiya Larai mahaifiyar Abbas tana mai ɗauke da mamaki a fuskar ta
" idon kunne yaji to jiki ya tsira idon kunne baijiba to jiki magayi”.
Tana kaiwa ƙarshen maganar ta fuce fuuu! Kamar anfura balan balan
Hajiya Larai mahaifiyar Abbas tuni ta gama ruɗewa kira take yau naga ikon Allah wai nakwance ya faɗi kodai Shamsiyya ta fara shaye - shaye kai wannan gaskiya bata acikin hayyacinta, amma bari na kira Abbas naji meke faruwa,.
Ɗakinta ta koma ta ɗauko wayarta keypad mai malatsai (itel) ta kira layin Abbas.
Bugu ɗaya ya ɗauka zuciyarsa na dukan ukku ukku don yasan dalilin kiran bai wuce akan aurensa bane.
“ Duk abinda kake ina son ka barshi kazo gida Gobarau yanzu yanzu ”.
Batare da taji amsar da zai bata ba ta ƙashe wayar ta mai da ita mazaunin ta.
Abbas
Kansa ya dafe da ƙarfi sakamakon wani irin mayen ciwon da yake masa kamar zai ɓalle gida biyu, idon akace ya saki Ahanah don dole to ya zaiyi da rayuwar sa, yana ƙaunar matar sa ƙauna ba ta wasaba, yana sonta son da ya zarce masifar so tabbas zai shiga mawuyacin hali middin ya rabu da matarsa, amma bari ya koma gidan nasa yaji ko wani mummunan laifi akace ya aikata da har ake ƙoƙarin rabasa da farin cikin sa, miƙewa yayi ya shiga lungun da zai maidashi ƙofar gidan sa domin yana kusa da gidan baiyi nisaba.
Shamsiyya mahaifiyar Ahanah tana fitowa daga gidan su Abbas ta nufi titin bakin kasuwa, tana tafe tana sababi har ta isa ƙofar sauro don dama babu nisa kai tsaye police sitasion ta nufa ido rufe don yau sai anyita ta ƙare.
KADUNA STATE
Rafin guza, unguwa ce ta masu ƙaramin ƙarfi wato geto Aria, bayan maƙabarta akwai wani lungu mai ɗauke da kwazazzabo na tudu da kwari ga ledoji da manyan kwatoci duk sun ɓata lungun saboda cushewar da wajan yayi kamar bola wani gida mai ɗauke da shukar giginya ginin ƙasa da langa langa da misalin ƙarfe Tara na dare.
Namsiyya ce kwance acikin wani ɗanƙaramin daki na ƙasa, abisa tabarmar da ta shinfiɗa zani akai sai juyi take ta kasa bacci, saboda cunkushewar da sukai ita da ƙannanta ga zafi da sauron da suka hayyaceta kasantuwar ana tsakiyar watan mayu ne
“ kai Allah kai man tsari da Talauci ”
ta furra cikin kaicon irin rayuwar da suke yi agidan su, kafin ta ɗaura da cewa “ ya zama dole na samama kaina mafita dole na raba rayuwa ta da wannan baƙin Talaucin, dole na samarma kaina mafita wallahi haba abin yayi yawa, "
Take gidansu ƙawarta sholy ya faɗo mata arai wanda yake a unguwar sarki yadda suke rayuwar su kamar yaƴan wani Gamna....
Ɗin Ɗin sugowar messagge aciki ƴar ƙaramar wayarta shine ya dawo da ita hayyacinta ta zaro wayar dake ƙarƙashin fulonta A33. Camon
Ta duba saitin App ɗin WhatsApp sai taga ɗigon ja alamar sakon ta whatsapp ya shigo.
Dama ta manta bata kashe databa tana duba sakon sai taga sholy ce ta turo mata vidio, duka zuri'arsu ce suke dinar abincin dare.
Ido buɗe take kallon ƙaton teburun dake cike da kayan abinci kala-kala suna ta ci gwanin birgewa, bidio ɗin gaba kuma sholy ɗin ce kwance bisa ƙaton gadonta na ƴaƴan hutu, ɗakin fayau da haske ga fanka ga Ac. Na aikinta hankalinta kwance.
Wani irin so da ƙaunar irin rayuwar sholy ya mamaye zuciyar Namsiyya, afili kuma abayyane ta furta “ kai arziƙi yayi Allah ka bamu kuɗi masu albarka ”.