Free chapter · Read without an account

Chapter 4

by Abdulhakim Umar · HANGEN DALA

HANGEN DALA 

Page 4


 Daga haka ta hau tunani akan yadda zata raba kanta da wannan talaucin da suke ciki, bata da burin da ya huce ta yi irin rayuwar gidan su sholy, nan take ma ta fara hango kanta a duniyar Masu kuɗi da irin yadda zataci karenta babu babbaka don haka ko ana ha maza ana ha mata sai ta auri mai kuɗi ko ɗan mai kuɗin, haka dai tai bacci ranta da ruhinta cike da tarin burika masu yawa da wahalar cikawa. 
Kamar a mafarki taji ana dukan cinyarta ana faɗin “ ke Namsiyya ki tashi lokacin sallar asuba yayi ”. 

Raɗau taji maganar mahaifiyar tata akunnuwanta amma sai ta ƙara gyara kwanciya ta kalli gabas batare da tace komai ba 
Ganin haka sai mamar ta ta tace “ au gyara ma kwanciya zakiyi ko to bara na sanar da Baban ku tunda ni kun rai nani, sai yazo ya tasheki.”
mama na kaiwa ƙarshen maganar ta fice tabar ɗakin don tasan idon zata shekara anan to Namsiyya bazata tashiba. 
Mamar na fita ta miƙe da sauri zaune don tasan middin ta bari Baban yaji to daa bulala zai shigo don bai shakkun ya zaneta duk da cewa ko ta zama budurwa , tana miƙewa tsaye yana shigowa hannunsa ɗauke da tsimingiyar iccen bedi, ganin ta miƙe yasa baice komai ba ya koma waje ya fice ya bar gidan baki ɗaya ya nufi masallaci don gudanar da sallar asuba. 
Sai da tai Alwallah kafin ta koma ɗakin tanata guni ta yi sallar tana gamawa ta koma bacci batare da ta zauna yin azkarba. 
 ƙarfe bakwai dai dai na safe mama ta sake komawa ɗakin ta tafkama Namsiyya duka acinya tana faɗin “ maza ki tashi kiyi shirin makarantar boko, "

A firgice Namsiyya ta tashi zaune tana mitsittsike ido saboda yadda dukan ya shige ta, sai da tai hamma kafin ta hau faɗin “ inna lillahi wa inna ilaihir raju'un ni Namsiyya naga ta kaina wannan bokon asara Allah kai mani tsari da ita kullum boko mutum na bacci awani tasheshi wai yatafi boko, ni wallahi mama da zakuji shawarata da kun ƙyaleni nabar zuwa boko nan don babu komai acikin ta sai wahala da asara gani ni bama gane komai nakeba, natsani boko nan wallahi. "
“ Duk tsanar da kikai mata sai kinjeta don karatu abin sone, ba abin wofinnrarwaba, kuma dole zakiyi karatu middin ina lumfashi don karatu dole ne arayuwar duniya, don haka ki gaggauta shiryawa tun kafin Babanku ya shigo. ”
Haka dai ta miƙe ta hau shiri ta fito sanye da kayan makaranta tayi tsaye akan mamar tana kallon yadda ƙannanta suka duƙufa shan kwakkon da ko suga babu. 
“ Ina kalacina? ”. 
“Gashi ”. Cewar mama tana miƙoma ta ƙaramin kofin kwakko 
Kallon kofin take tana ya tsuna fuska kafin ta fara faɗin “ wai wa zai sha kwakkon ko suga babu, Allah ya tsareni wallahi, tashi zakiyi kizo ki ɗaukoman ko ɗari biyu ce naje nasawo shayi da bready wajan ILah mai shayi, ”
“ lallai Namsiyya kina cikin rayuwar wahala, ni ina naga wata ɗari biyu idon ina da ita ma nabama su Aisha su sawo ƙosai ”. 
“ kai inna lillahi wa inna ilaihir raju'un Allah kai mana tsari da Talauci sai kace babu kanku ta ƙare, to ni dai wallahi na gaji da wannan rayuwar wahalar don haka zan samama kaina mafita, don middin naci gaba da wannan rayuwar to nankusa zan mutu kwanana bai ƙare ba wuyar duniya ta kasheni, da ace gidan su sholy nake abinci sai na zaɓa kuma ko nama nace zanci to a wadace zancisa naƙoshi nai hani'an”. 
“ ke Namsiyya yaushe kika zama haka to wallahi ina maki gargaɗi da babbar murya ki natsu kisan abinda kike don HANGEN DALA ba shiga birni ba ne kuma wannan rayuwar ƙaryar da kika ɗauka ba rayuwa bace ina tsoron ki hau makauniyar hanya wacce zata kai ki ga sikata aikin assha don kwaɗayi dai ƙarshen sa wahala yake zama ”. 

“ mama kiman addu'a kawai Allah ya sa nasamu ɗan manya na aura don har ku sai na rabaku da wannan rayuwar da kuke marar tushe”. 

“ To Allah ya sa mudace ”. 

“ Amin mama, shine kawai, na tafi makarantar ".
 
“Anya kuwa zanbarki haka bakici komai ba”. 

“Ai gara nafita haka don wannan ruwan kwakkon bai da maraba da babu, dana sha da ban shaba duk ɗaya ne don bai mani maganin yunwa don haka sai na dawo.” tana kai ƙarshen maganar ta fice abinta tana jiyo muryar mama tana mata addu'ar Allah yasa ta gane gaskiya. 

Namsiyya a madadin ta nufi hanyar makarantar su sai ta nufi hanyar da suke mahaɗa da sholy don ta jira sholyn tazo ta ɗauketa, don yau tsawon wata guda kenan da ta fara rayuwar ƙarya da gudun makaranta, kullum zata fito da shirin makaranta daga gida amma bata zuwa sai dai sholy tazo ta ɗauketa a mota sushiga gari, don ita dai a duniya bata da abin tsana da ƙiyayya kamar boko. 

Yau ma kamar kullum tana fitowa gidan ta shiga lungun da zai kaita bakin hanya inda zata shiga Badarawa don anan take jiran sholy kullum. 

Bata jima da tsayawaba sai ga motar sholy ta tsaya a gabanta, motar ƙatuwace baƙa ta kanfanin GLK sai walƙiya take da ɗaukar ido. 
Washe baki Namsiyya tai kafin tace “ kai ƙawa yau kinzo a dai dai, ina kuma kika samo wannan haɗaɗɗiyar motar haka kamar ta shirin kaima shugaban ƙasa ziyara ?, ”

“ wallahi ta yaya Samir ce na ɗauko don yau wani sabon waje zamuje ance cikin satin nan akai lancing ɗin wajan don yau so nake mu yaƙi samari. ”

Buɗe motar Namsiyya tai ta shiga gidan gaba tana mai jin farin ciki marar musultuwa duk ya mamayeta da zuciyar ta. 
Namsiyya na rufe marfin motar sholy tai mata key suka lula akan hanya, sai da ta fita Badarawa kafin ta shiga unguwar sarki ta ɗau hanyar sabon kawo inda aketa rusa gidaje da alama dai za'a ƙara faɗi da girman titi Anan cikin sabon kawo suka tsaya gidan kakarsu sholy suka shiga suka sauya kayan jikinsu zuwa wasu ƙananan kaya na Componyi , masu kyau da ƙyale -ƙyalen duniya, sai da suka feshe kayansu da jikinsu da Turare kafin suka fito, kai tsaye unguwar Dosa suka nufa a sulta road inda aka buɗe sabuwar Rastorente ɗin suka tsaya. 

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol