Free chapter · Read without an account

BACK HOME

by Jiddaah Barkum · KADDARAR ZUCIYA



KADDARAR ZUCIYA

CHAPTER TWENTY-NINE: 29

BACK HOME

JIDDAAH BARKUM

—————

Bayan jin muryar matar ta cikin wayar Aliyu, Inteesar ta ji wani irin abu mai matuƙar nauyi da zafi ya sauka dafifi a tsakiyar ƙirjinta, wani sashe na zuciyarta ya cika da wani irin ɗaci da ba ta san ko na meye ba, ba ta san dalilin da ya sa kalaman macen suka daki zuciyarta da irin wannan ƙarfin ba, ba ta san dalilin da ya sa daddadan murmushin da ke shimfiɗe a fuskarta ya ɓace tsaf cikin ƙiftawar ido ɗaya ba, amma abu ɗaya ta sani da yakini… wani sabon yanayi mai cike da sarƙaƙiya da sanyin gwiwa ya mamaye ilahirin ranta, a hankali ta sauke idanunta ƙasa, tana kallon wajen, yatsun hannunta suka shiga murɗe juna cikin wani yanayi na rashin sanin madafa da rashin kwanciyar hankali.

Aliyu kuwa, a matsayinsa na gogaggen mutum, tun kafin matar da ke can ɓangaren ta ƙarasa maganarta, idanunsa tass suka sauka a kan kyakkyawar fuskar Inteesar, kuma nan take ya fahimci komai, ya lura da yadda murmushinta ya ɓace a daidai lokacin da sautin muryar matar ya fito, ya lura da yadda fuskarta ta canza, ta nuna wani irin yanayi na damuwa, ya lura da yadda ta sadda kanta ƙasa da sauri, da kuma yadda wata irin nutsuwa mai cike da ɓoyayyen abu ta lulluɓe ta tamkar mayafi.

Aliyu bai cire wayar a kunnensa ba, amma sautin muryarsa ya ɗan sauya yayin da yake amsa kiran, “Ehh… na fito ne, ina wani wuri yanzu haka,” ya faɗa cikin daddadar muryarsa mai cike da dattako, “In Sha Allah zan ƙaraso,” daga can ɓangaren kiran, matar ta saki wata ’yar gajeruwar dariya mai cike da shagwaɓa da nuna tsohon sabo, “Toh, sweetheart, amma dai kada ka manta fa, tun ɗazu nake zaune a shirye ina jiran ka,” Aliyu ya ɗan yi wani gajeren murmushi da ya bayyana a leɓɓansa, ya ce: “Ba zan manta ba,” “Allah Ya kiyaye hanya, drive safe, I love youuuuu!” Muryar macen ta fito sarai kafin kiran ya yanke, “Ameen,” ya kashe wayar cikin nutsuwa, sannan ya mayar da ita cikin aljihun farar shaddarsa.

Daga nan ya zuba wa Inteesar kyawawan idanuwansa, yana kallon yadda take ƙoƙarin danne abin da ke damunta, ita kuwa har lokacin kanta yana ƙasa, ta ƙi ɗago kai don kada ya hango abin da ke yawo a idanunta, wanda ko ita kanta ba ta san mene ne ba, Aliyu ya ɗan lumshe idanunsa kaɗan, kamar wanda ya fahimci wani sirri da ke ɓoye a ranta, sai ya kira sunanta cikin daddadan sauti mai cike da lallashi da kwantar da hankali, “Inteesar,” ta ɗago kai da ƙyar ta kalle shi, idanunta sun canza launi, “Ya kamata ki koma ciki yanzu, za mu yi magana anjima, kin ji?” ya faɗa yana karewa fuskarta kallo da kyau, “Toh,” ta amsa masa a taƙaice, sai dai muryarta ta kasa ɓoye wani irin rauni da yanayi na daban, wanda ita kanta ba ta san ainihin mene ne shi ko daga ina ya fito ba.

Aliyu ya tsare ta da idanunsa na tsawon daƙiƙu da dama, wani irin kallo ne mai cike da ma’anoni da yawa, kallon da ya sanya jinin jikin Inteesar gudu da sauri, zuciyarta kuma ta fara dukan uku-uku, da sauri ta sake sunkuyar da kanta ƙasa don guje wa kwarjinin idanunsa, Aliyu ya yi wani tattausan murmushi na gefen baki, ya ce: “Ki rage yawan tunani, ba shi da kyau ga lafiyarki,” Inteesar ta yi saurin girgiza kanta alamar ƙaryatawa, “Ba tunani nake yi ba,” sai dai muryarta ba ta da wani tasiri ko ƙarfin da zai tabbatar da abin da ta faɗa, Aliyu ya ɗan karkatar da kansa yana kallonta, “Hmmm,” shi kaɗai ya furta, sannan ya saka hannayensa cikin aljihun shaddarsa ya ɗan matso kusa da ita cikin natsuwa, ba tare da ya keta hurumin tazarar da ke tsakaninsu ba.

“Kada ki wahalar da zuciyarki da abubuwa da yawa lokaci guda,” ya faɗa cikin wata murya mai sanyaya jiki tamkar ruwan sanyi, “A irin wannan lokacin, gaba ɗaya hankalinki ya kamata ya kasance wajen Daddy kawai,” Inteesar ta jinjina kanta a hankali, tana jin ɗumi a ranta, “Na sani,” Aliyu ya yi murmushi, “Good,” sai ya matsa ya buɗe ƙofar baƙar motarsa mai ɗaukar ido, kafin ya shiga ciki, sai ya sake juyowa gaba ɗaya ya kalleta, idanunsa suka sake sauka a kan kumburin idanunta na kuka, ya ɗan girgiza kansa cikin wani irin yanayi na rashin jin daɗin ganinta a haka, “Kuma ki tuna ainihin abin da na ce miki,” ta ɗago idanunta ta dube shi, “Me?” “Ki daina kuka,” ya amsa mata cikin muryar lallashi, “Idan kika ci gaba da kuka haka…” Ya ɗan dakata, sannan ya ƙarasa cikin murmushi, “ba zan ji daɗi ba.”

Inteesar ta ji wani daddadan sanyi ya sake ratsa ƙofofin zuciyarta, ta yi wani ɗan gajeren murmushi, “In Sha Allah,” Aliyu ya gyada kai yana mata wani tattausan murmushi, sannan ya shiga cikin motar ya zauna a mazaunin matuƙi, amma kafin ya ja ƙofar motar ya rufe gaba ɗaya, sai ya sake kiran sunanta a karo na ƙarshe, “Inteesar,” ta ɗago cikin sauri, “Na’am?” Aliyu ya ɗan yi shiru na wasu daƙiƙu kaɗan yana kallonta, sannan ya ce cikin muryar dattako: “Ki kula da Mommy, ki kula da yayyenki, kuma fiye da komai…” Ya ɗan dakata, sai ya ƙarasa maganar cikin daddadan sauti, “…ki kula da kanki, nutsuwarki za ta taimaka wajen kwantar musu da hankali duka, har da ni, duk da cewa ba na wajen,” Inteesar ta ji zuciyarta ta ƙara yin wani irin bugawa na daban, ta gyada kai a hankali, “In Sha Allah,” ya yi mata wani tattausan murmushi mai cike da ƙarfafa gwiwa, ita kuma ta ce: “Allah Ya tsare,” ta faɗa tana ɗan ja da ƙafafunta baya a hankali don ba shi filin fita, “Ameen,” daga nan ya ja ƙofar motar ya rufe, cikin daƙiƙa kaɗan, engine ɗin motar ya tashi cikin wani sanyayan sauti mai daɗi.

Inteesar tana tsaye a wajen tamkar an dasa ta, idanunta na bin bayan motar da kallo tun tana juyawa har sai da ta fita daga babban gate ɗin parking lot ɗin asibitin gaba ɗaya, sai a lokacin ta sauke wani uban dogon numfashi mai nauyi, ta ɗaga hannunta ta dafa daidai saitin ƙirjinta, saboda dukan da zuciyarta take yi ya yi mata yawa da gaske, amma kafin ta juya da nufin komawa ciki, wata murya mai cike da tsantsar tsokana ta daki kunnenta daga bayanta, “Princess,” Inteesar ta firgita ta ɗan zabura, ta juyo da sauri, sai ta tarar da Yaya Khalil ne tsaye jikin bishiya, ya haɗe hannayensa biyu a ƙirjinsa, wani ƙasaitaccen murmushi na muguwar tsokana shimfiɗe a fuskarsa, idanunsa kuwa… kai tsaye daga kanta suke kallon hanyar da motar Aliyu ta bi, sannan ya dawo da kallonsa kanta gaba ɗaya, ya kafe ta da idanunsa masu cike da muguwar tsokana.

“Hmmm…” ya furta a hankali cikin zolaya, “Da alama rakiyar nan ta yi tsawo sosai fa, Princess, ko har an kulla wani abu ne?” Nan take idanun Inteesar suka zaro waje cikin tsantsar kunya, “Yaya Khalil!” Khalil kuwa ya ƙara faɗaɗa murmushinsa, “Haba, Princess… ai ni ban ce komai ba fa,” sai ya ɗaga hannayensa biyu sama cikin sigar miƙa wuya, “Amma gaskiya, wannan abin ya burge ni, finally! Gimbiyar ta samu gwarzo,” Inteesar ta turo baki gaba cikin shagwaɓa, “Wallahi, ba abin da kake tunani ba ne,” Khalil ya fashe da dariya, “Toh, na ji,” ta sake tura baki gaba tana ɗan gunguni, ya yi murmushi, “Did I say anything?” Ya faɗa yana ɗan mata alama da idanunsa.

Nan take Inteesar ta ji idanunta sun cika da hawaye, ta fara kuka a hankali, tamkar dama wani abu ne ke cin ranta tun ɗazu, kuma take jiran ta samu damar zubar da shi, ganin haka, sai Khalil ya canza salon maganarsa, ya yi saurin ɗaga yatsansa guda, “Eh, eh! No more tears, wallahi, idan kika sake yin kuka a nan, zan nemo number Aliyu yanzu na kira shi, na gaya masa cewa kin karya alƙawarin da kika yi masa na rashin yin kuka,” Inteesar ta zaro ido cikin sauri, “Yaya!” Khalil ya sake yin dariya mai daɗi, sai ya janyo hannunta cikin kulawa ya ce: “Muje ciki, Mommy tana jiranmu,” a tare suka juya, suka nufi cikin dogon corridor ɗin asibitin domin komawa ciki, a daidai wannan lokacin, daga saman bene na biyu na asibitin… Yaya Umar yana tsaye kusa da wani babban window da ke kallon parking lot ɗin, idanunsa suna kallon ƙanwarsa da Khalil da ke tafiya a ƙasa, suna hira cikin dariya, sai ya sauke idanunsa ƙasa a hankali, ya ja wani dogon numfashi mai cike da sanyin jiki da ɓoyayyen juyayi, sannan ya furta wata kalma cikin muryar da shi kaɗai ya san ma’anarta, “Ya Allah… Kai kaɗai ka san halin da nake ciki a yanzu,” sannan ya juyo da jikinsa da ƙyar, ya koma cikin corridor ɗin asibitin cikin sanyin jiki da tarin abubuwan da ke yawo a ransa.

—————
BAYAN KWANA UKU

Safiya ce… tun kafin fitowar rana ta haskaka sararin samaniya gaba ɗaya, corridor ɗin asibitin ya fara ɗaukar wani sabon yanayi na daban, yanayi mai cike da sauƙi, ni’ima da kwanciyar hankali, ba kamar kwanakin baya da suka kasance cike da duhu ba, babu sautin kukan tashin hankali, babu fuskokin firgici ko zullumi, ko da yake alamun gajiya da rashin barcin kwanaki suna nan shimfiɗe a kan fuskokin kowa, amma akwai wani irin haske na farin ciki da fatan alheri da ya fara bayyana a zukatan iyalin gaba ɗaya, saboda… jikin Daddy ya yi sauƙi sosai, Alhamdulillah.

Tun bayan kammala sallar Asuba, Alhaji Kabeeru ya sami damar zama da kansa, ya sha tea kaɗan da bread mai laushi, har ma ya yi wata daddadan hira da Mommy Haleema cikin tsantsar natsuwa, abin da ya sanya Mommy Haleema zubar da hawaye na farin ciki da godiya ga Allah a ɓoye, domin tun kwanakin baya, ko ɗan ruwa sai da ƙyar yake iya sha ya tsallake makogwaronsa, yanzu kuma… har ya fara yi musu korafin irin na mara lafiya, “Haleema, gaba ɗaya kin hana ni sukari, wannan shayin babu sugar ko kaɗan a ciki, yana da ɗaci,” ya faɗa cikin wata muryar da ta fara dawowa da daɗinta kamar yadda suka saba ji a da, Mommy Haleema ta fashe da dariya mai daɗi, ta ce: “Dole mana, Alhaji, ai umarnin likita ne ya ce ka rage sukari gaba ɗaya,” Alhaji Kabeeru ya ɗan kalle ta ta gefen ido cikin sigar shagwaɓa, “Haba, Haleema, wai ni yanzu shikenan ma ba ni da wani iko kenan da zan zaɓi abin da zan sha?” Mommy Haleema ta yi murmushi, “Ba ka da shi kuwa a yanzu, duk wani umarni na likita, shi za mu bi daki-daki,” Alhaji Kabeeru ya girgiza kansa, “Ni dai na ji daɗina da ku,” dukansu da ke cikin ɗakin suka fashe da dariya mai daɗi, har Inteesar da ke zaune a gefensa tana gyara masa pillow ɗin da ke bayansa, ta saki wata dariya mai daɗi a karon farko cikin kwanakin nan na baƙin ciki.

Jin dariyar Princess ɗinsa ya sanya Alhaji Kabeeru juyowa da kansa ya kalleta da kyau, sai ya tsaya yana nazarin fuskarta, ya ga yadda ta rame sosai, idanunta sun canza launi, amma duk da haka… a gare shi, ita ce ainihin Princess ɗinsa har abada, ya miƙa hannunsa a hankali gare ta, “Intee,” ta matsa kusa da shi sosai, “Na’am, Daddy?” Ya shafa kumatunta cikin tsantsar tausayi da ƙaunar uba ga ’yarsa, “Kuka ya isa haka, kin ji?” Ta yi murmushi tana jin sabbin hawaye na farin ciki suna taruwa a ƙwayar idanunta, “Daddy…” “Kada!” Ya katse ta da sauri, cikin nuna cewa ba ya son kukan nata, “Ba na son sake ganin hawaye a fuskarki,” nan take ta goge idanunta ta ce: “To, Daddy,” a gefe guda kuma, Khalil ya ce da sauri cikin tsokana: “Good! Saboda ni ma na gaji da kallon kukan nan, gaskiya, idan ba a daina ba, idanuwanta za su koma ja tsaf tamkar tumatur,” dariya ta ƙara kaurewa a cikin ɗakin asibitin, har shi kansa Alhaji Kabeeru ya kasa daurewa sai da ya yi dariya mai daɗi, “Khalil! Ka daina tsokanar ƙanwarka haka,” Khalil ya yi murmushi, “Daddy, I just wanna cheer her up,” ya faɗa yana kashe wa Inteesar ido ɗaya ta gefe, Yaya Abubakar ya girgiza kansa yana murmushin jin daɗi, “Allah Ya shirye ka, Khalil,” sai Yaya Adam ya sauke wani nannauyan ajiyar zuciya mai daɗi gaba ɗaya, Alhamdulillah, wannan kalmar ita kaɗai yake ta faman maimaitawa a cikin ransa, domin tun ranar farko da aka kwantar da Daddy a asibitin nan, yau ne karo na farko da ya ga annuri, dariya da farin ciki sun sake bayyana a fuskokin iyalinsu.

Da misalin ƙarfe goma na safe, likitan da ke duba Daddy tare da wasu nurses guda biyu suka tura ƙofar ɗakin suka shigo ciki, kowa ya yi shiru gaba ɗaya, domin duk suna jiran jin ainihin hukuncin da likitan zai yanke game da lafiyarsa, likitan ya duba sakamakon gwaje-gwajen da ke riƙe a hannunsa, sannan ya yi wani kyakkyawan murmushi na gamsuwa, “Masha Allah, jikin Alhaji ya yi sauƙi sosai fiye da yadda muke tsammani,” Mommy Haleema ta dafe ƙirjinta cikin tsantsar daɗi, “Alhamdulillah!” Likitan ya sake gyara tsayuwarsa ya ce: “In Sha Allah, idan komai ya ci gaba da tafiya a haka, za mu sallame shi yau ya koma gida ya ci gaba da hutawa,” wallahi, ba wanda bai furta kalmar Alhamdulillah da ƙarfi ba a cikin ɗakin saboda tsananin daɗi, Khalil har da miƙewa tsaye da sauri, “Da gaske, Doctor?” Likitan ya yi dariya, “Eh mana, amma a ci gaba da kula da magungunansa sosai a gida,” Mommy Haleema ta ɗaga hannayenta biyu sama, “Ya Rabbi, mun gode Maka da wannan ni’imar!”

Inteesar kuwa, nan take hawayen tsantsar farin ciki suka cika idanunta, ta kama hannun Daddy ta matse shi tana murmushi mai daɗi, “Daddy,” ya kalleta cikin ƙauna, “Princess,” “Za mu koma gida yau!” ta faɗa cikin muryar jin daɗi, Alhaji Kabeeru ya yi wani tattausan murmushi, “In Sha Allah, Princess ɗina,” kasa da awa biyu bayan haka, ainihin corridor ɗin asibitin ya cika da motsi da zirga-zirgar iyalin, Yaya Abubakar da Adam suna can wajen counter suna kammala shirin biyan kuɗaɗen asibitin gaba ɗaya (hospital bills), Yaya Umar da Faisal kuma suna ɓangaren pharmacy suna karɓar magungunan da za a tafi da su gida, Salim kuwa yana tattara takardun sallama gaba ɗaya (discharge papers).

Khalil kuwa… tun da aka ce za a sallami Daddy, tsananin farin cikinsa ya hana shi zama wuri guda, sai faman zirga-zirga yake yi a corridor ɗin yana rera waƙa ƙasa-ƙasa, har wata nurse ɗaya ta yi dariya ta ce da shi: “Please, ka zauna mana wuri guda, saurayi,” Khalil ya yi murmushi, “Wallahi, farin ciki ne ya yi yawa, ma’am, na yi kewar ganin Daddy a cikin gidanmu sosai,” daga can gefen kujerar ɗakin kuwa, Inteesar ce ke ta faman kwashe kayayyakinsu da ke cikin ɗakin tana shirya su tsaf, bayan ta gama, sai ta matso kusa da Daddy da ke zaune a gefen gadon, tana gyara masa hularsa, tana sa masa links ɗin hannun rigarsa cikin tsantsar kulawa, Alhaji Kabeeru yana zaune yana kallon kowane motsi na ’yarsa cikin murmushin ƙauna, sai ya ce mata: “Princess,” ta ɗago idanunta da sauri, “Na’am, Daddy?” Ya yi murmushi na dattako, “Kamar ni ne yaron, ke kuma kamar ke ce uwata yanzu,” Mommy Haleema ta fashe da dariya a gefe guda, ta ce: “Wallahi, haka ne kam, Alhaji, kwana biyu kacal da rashin lafiyarka, gaba ɗaya yarinyar nan ta rame ta canza launi saboda kai,” Alhaji Kabeeru ya girgiza kansa cikin jin tsantsar tausayin ’yarsa a ransa, Allah Ya sani… yana son yarinyar nan fiye da yadda kowace kalma a duniya za ta iya bayyanawa da baki.

Bayan komai ya kammala tsaf, a hankali aka fito da Alhaji Kabeeru daga cikin ɗakin asibitin mai ɗauke da lamba ta musamman, kowa na kewaye da shi cikin nuna kariya da soyayya, Yaya Abubakar da Adam suna takawa a gefensa, Mommy Haleema na biye a bayansu, yayin da Inteesar kuma… hannunta yana cikin nasa, kamar yadda ta saba yi tun tana yarinya ƙarama da ke tafiya tare da mahaifinta, har yanzu ba ta sake hannunsa ba, kuma ita kanta ba ta son sake shi ko da na daƙiƙa guda, saboda a ainihin zuciyarta, ta riga ta rasa Ahmad, ba za ta iya jure tunanin sake rasa Daddy ba a rayuwarta gaba ɗaya, sai ta ƙara matse hannunsa a hankali cikin nata, kuma cikin ikon Allah da jinƙansa mai yawa, a karon farko cikin kwanaki masu cike da duhu da zubar da hawayen fitar rai, babban asibitin ya ga iyalin Alhaji Kabeeru suna fita daga cikinsa… ba cikin tashin hankali ko kuka ba, sai dai cikin tsantsar godiya da jinjina ga Ubangijin talikai.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol