Free chapter · Read without an account

THE CONFESSION

by Jiddaah Barkum · KADDARAR ZUCIYA

KADDARAR ZUCIYA

CHAPTER THIRTY: 30

THE CONFESSION

JIDDAAH BARKUM

————


Gidan Alhaji Kabeeru ya karɓi zuwansu da wani irin sabon sanyi da nutsuwa da ba a ji a cikin gidan ba tsawon kwanaki, motoci suka tsaya ɗaya bayan ɗaya a cikin farfajiyar gidan, tayoyinsu suna yin ƙara a kan interlock din, yayin da aka buɗe ƙofofin motocin aka fara sauke kayayyakin da aka dawo da su daga asibiti, ma’aikatan gidan, babba da ƙarami, duk suka kewaye harabar, suna ta yi wa Alhaji Kabeeru sannu-sannu tun kafin ma ya fito daga motar, shi kuwa dattijon yana ta ɗaga musu hannu tare da yalwataccen murmushi a fuskarsa, a hankali aka fito da Alhaji Kabeeru daga motar cikin kulawa ta musamman, fuskarsa ta fara dawowa da ainihin haskenta, ko da yake har yanzu akwai alamun gajiya a idanunsa, amma zuciyarsa cike take da wani irin sanyi da nutsuwa mai daɗi, nutsuwar dawowa gida cikin iyalansa bayan ya sha wahala, ya kuma sake samun damar rayuwa cikin farin ciki.

“In Sha Allah, Daddy, ka dawo kenan, ba za ka sake tafiya asibiti ba!” Khalil ya faɗa cikin muryar jin daɗi, yana ɗaga hannayensa biyu sama kamar wanda ya tsere daga wani babban nauyi, Adam ya yi murmushi kawai, yana buɗe musu ƙofar gidan, “Alhamdulillah…” Abubakar ya furta a hankali, idanunsa na bin kowane taku na mahaifinsu da tsantsar kulawa, Inteesar kuwa tana manne a gefen Daddy, hannunta yana cikin nasa da ƙarfi, kamar ba za ta sake shi ba har abada, a hankali take ɗaga ƙafafunta tana tafiya, kamar wadda zuciyarta ke tsoron ko gidan zai ɓace idan ta saki hannunsa, “Daddy, ka shiga a hankali…” ta faɗa cikin murya mai laushi, wadda ke ɗauke da tsantsar soyayyar da take yi wa mahaifinta, Alhaji Kabeeru ya kalle ta da idanunsa masu cike da ƙaunar uba, “Princess ɗina… kin gaji sosai,” ta girgiza kanta da sauri, “A’a, Daddy, ban gaji ba,” ta ƙarasa maganar tana murmushi, amma kowa da yake wurin ya san cewa faɗa kawai ta yi, she looked so exhausted, fuskarta ta rame, idanunta sun nuna tsananin gajiya, zuciyarta kuma ta yi mata wani irin nauyi da ke neman kwace mata nutsuwa.

Da suka tura ƙofar suka shiga ciki, babban falon gidan ya tarbe su da daɗaɗɗen ƙamshin turaren wuta na alfarma da aka saba ƙona wa, Mommy Haleema ta duba ko’ina a cikin falon, tana jin wani irin relief mai daɗi a tsakiyar zuciyarta, “Alhamdulillah…” ta sake maimaitawa a hankali, cikin sanyin jiki, a hankali aka shigar da Daddy har cikin ɗakinsa na musamman, aka kwantar da shi a kan gado don ya samu damar sake hutawa, Inteesar ta zauna a gefen gadonsa, tana gyara masa pillow kamar yadda ta saba yi a asibiti, “Ki huta mana, Princess…” ya ce mata a hankali, yana kallon yadda take ta zirga-zirga a kansa, “Ban gaji ba fa, Daddy, bari na gama gyara maka nan,” ya yi murmushi kawai cikin dattako, “A’a, ke ma kina buƙatar hutawa,” ta yi murmushi kawai, sannan ta kunna masa AC, duk da cewa sun dawo gida, gidan ya cika da sabon yanayi na farin ciki, hidimar ma’aikata da kuma dukan family energy, amma zuciyar Inteesar ba ta samu cikakkiyar nutsuwa ba, akwai wani abu da ke yawo a ranta tun rabuwarta da Aliyu, wani tunani da duk ƙoƙarinta na kawar da shi bai yi nasara ba.

Da dare ya yi, gidan gaba ɗaya ya yi tsit bayan kowa ya wuce ɗakinsa don ya huta, Inteesar tana zaune ita kaɗai a saman gadonta, sanye da kayan bacci, shiru ya mamaye ɗakin, wanda hakan ya ba ta damar fuskantar ainihin tunaninta, hoton fuskarsa ya fara dawo mata a hankali: kalaman Aliyu na ƙarshe, yadda ya tsare ta da idanunsa yana lallashinta, da kuma daɗaɗɗiyar muryar matar nan da ta ji ta cikin wayarsa tana kiransa da “Sweetheart,” ta turo baki kamar yana kallonta, sannan a hankali ta furta: “Ashe ma yana da mata,” wani irin yanayi mai cike da ruɗani da ba ta taɓa ji ba ya mamaye ta, “Me ya sa nake jin haka a raina?” ta tambayi kanta cikin sanyin gwiwa, a daidai wannan lokacin, wayarta da ke ajiye a gefenta ta fara ringing, ta duba screen ɗin da sauri, Aliyu, sunan da ta yi saving ranar da ya zo duba Daddy ya bayyana a screen ɗinta, ta ci gaba da kallon wayar har kiran ya katse, ba ta ɗauka ba, a karo na biyu, wayar ta sake ringing, sai da kiran ya kusa katsewa sannan ta ɗaga ta kara a kunnenta, muryarta a ɗan raunane, “Assalamu alaikum,” “Wa alaikumus salam,” muryarsa ta fito cikin daɗaɗɗen sauti mai cike da nutsuwa, “Na zata ba za ki ɗauka ba,” ya faɗa yana sauke numfashi, ta yi shiru, sai can ta ce: “Ina yini?” “Lafiya lau, kin tashi lafiya? Kun koma gida lafiya? Na kira ne don in ji yadda kuke, kuma in sake tambayar jikin Daddy,” “Alhamdulillah, jikin Daddy ya yi sauƙi sosai, mun dawo gida lafiya,” ta amsa masa a taƙaice, cikin sanyin jiki, “Alhamdulillah, Allah ya ƙara masa lafiya da tsawon rai mai albarka,” “Amin,” shiru ya biyo baya na kusan mintina biyu, sai can ta ƙara da cewa: “Idan babu komai… sai anjima, zan kwanta.”

Aliyu da ke can ɓangaren ya ɗan tsaya, cike da ruɗani, kafin ya ce cikin sanyin murya: “Korata kike yi ko?” Inteesar ta turo baki, kamar yana gabanta, “A’a… ba haka ba ne,” ta amsa, sai kuma kamar an janyo maganar daga bakinta tace: “Saboda kar matarka ta gan ka kana waya ne a daidai wannan lokacin,” shiru ya ratsa tsakaninsu na wasu daƙiƙu kaɗan, Aliyu ya daskare a wurin, sannan ya ja dogon numfashi a hankali yayin da ya fahimci abin da ke faruwa a zuciyar yarinyar, wani irin daɗi ya mamaye shi, ya fahimci cewa Intee kishi take yi, kuma wataƙila ta fara kamuwa da sonsa a fakaice, “Na ce miki tana nan ne?” Aliyu ya tambaya cikin wata murya mai ɗauke da ma’ana, tare da murmushin gefen baki, “Uhmm…” ta faɗa kawai, sannan ta yi shiru, ta kasa cewa uffan, Aliyu zai yi magana kenan, sai Inteesar ta ga wani kira yana shigowa a wayarta, Bloodline, ta ɗan firgita, sannan ta ce wa Aliyu: “Yaya Abubakar yana kirana, zan kashe,” ba tare da jiran amsarsa ba, ta yanke kiran Aliyu da sauri, sannan ta ɗaga na yayanta cikin girmamawa, “Yaya…” Muryar Yaya Abubakar ta fito da wani irin tsauri da ke ɗauke da nutsuwa, “Intee… kina ina ne?” “Ina ɗakina, Yaya,” “Ki fito yanzu zuwa corridor ɗin sama, ina son yin magana da ke,” zuciyarta ta yi wani irin tsalle! Ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta amsa: “To, Yaya, gani nan fitowa.”

A dogon corridor ɗin saman gidan da ke da ɗan haske, Yaya Abubakar yana tsaye, ya haɗe hannayensa biyu a bayansa, fuskarsa babu alamar wasa ko kaɗan, Inteesar ta fito ta matso kusa da shi a hankali, kanta a ƙasa, “Na’am, Yaya, gani,” Abubakar ya juyo ya zuba mata idanunsa, yana kallonta sosai na tsawon lokaci kafin ya buɗe baki ya yi mata tambayar da ta firgita ta, “Intee… who is the man that came to the hospital? Wane ne wannan mutumin da ya zo duba Daddy?” Ta firgita kaɗan, ta fara in-inaaa: “Wanne… wanne kenan, Yaya?” “Aliyu,” Abubakar ya faɗa kai tsaye cikin tsauri, “A ina kika san shi? Kuma mene ne alaƙarku da zai sa ya bar duk abin da yake yi ya zo asibiti, yana nuna miki irin wannan tsantsar kulawar?” Tambayoyin sun sauka a kanta tamkar wani babban nauyi, ta sadda kanta ƙasa gaba ɗaya, tana murɗe yatsun hannunta cikin fargaba, “Yaya… kawai fa ya zo duba Daddy ne,” Abubakar ya ƙura mata ido, yana nazarin fuskarta, “Intee, ba haka nake tambaya ba, ina son sanin gaskiyar abin da ke tsakaninki da Aliyu gaba ɗaya, and don’t lie to me,” ya faɗa yana zuba mata idanunsa cikin tsanaki, shiru mai nauyi ya ratsa wurin, yayin da Inteesar ta kasa buɗe baki ta ba shi amsa gamsasshiya.

Ta ji numfashinta ya tsaya na wasu daƙiƙu kaɗan lokacin da tambayoyin Yaya Abubakar suka sauka a kanta tamkar gungun dalma, ta tsinci kanta cikin tsananin rashin shiri da fargabar kada yayanta ya gano ainihin abin da ke faruwa a zuciyarta, ta shiga yin kame-kame, yatsun hannunta suna rawa yayin da take murɗe su da juna, ta buɗe baki da ƙyar, muryarta tana ɗan ɓari, “Yaya… wallahi… wallahi babu komai a tsakaninmu, kamar yadda na faɗa maka, kawai na san shi ne a flight lokacin da zan dawo gida, shi ya dage sai ya karɓi number ɗina… amma bayan nan babu wani abu daban a tsakaninmu, Allah,” Yaya Abubakar bai ce uffan ba, ya tsare ta da idanunsa masu kaifi, yana binciken kowace motsin idonta da kuma fuskarta da ta canza launi saboda tsananin fargaba, wannan kallon tuhumar ya tsawaita ƙwarai, har sai da Inteesar ta ji kamar ƙasa ta tsage ta shige ciki saboda tsananin kwarjinin yayanta, daga ƙarshe, ganin yadda jikinta yake ta faman rawa, Abubakar ya ja numfashi mai nauyi sannan ya ɗan juya kansa, “Shikenan, wuce ki tafi ki kwanta,” ya faɗa cikin murya mai sanyi, amma tana ɗauke da gargaɗi, “To, Yaya, sai da safe,” ta amsa da sauri, tamkar an ce ta gudu daga gidan yari, kallon tuhuma da Abubakar ya yi mata shi ne na ƙarshe kafin ta juya, amma a cikin ransa, ya riga ya ƙuduri aniyar gano kowane sirri da ke tattare da Aliyu, bai gamsu da bayaninta ba sam, domin a idon kowa a asibiti, an ga yadda Aliyu yake kallon ƙanwarsa da tsantsar ƙauna da kariya, ya sha alwashin bincikarsa tun kafin ƙanwarsa ta afka cikin soyayyar da zai yi wuya ta iya fita daga cikinta.

Tana shiga ɗakinta, ta tura ƙofar sannan ta dafe bayanta a jikin ƙofar, kafin ta sulale ƙasa ta zauna a wurin, ta saki wani nannauyan numfashi mai ɗauke da tsananin fargaba, hannunta ɗaya yana kan ƙirjinta, wanda yake bugawa da sauri tamkar zai fito waje, “Na tsallake rijiya da baya,” ta furta ƙasa-ƙasa, tana goge gumin da ya tsatstago mata a goshinta, zuciyarta ba ta gama daidaitawa ba, kwatsam sai ga kiran Aliyu ya sake shigowa a karo na biyu, ta kalli screen ɗin wayar, ta haɗiye miyau sannan ta mika hannu ta dauko ta ɗaga ta kara a kunnenta ba tare da ta ce uffan ba, “Intee…” muryarsa ta fito cikin daɗaɗɗen sauti mai ɗauke da wani salon da ke tsakanin soyayya da tsantsar kulawa ta musamman, “Yayan naki ya kusa miki duka ne? Na ga kin kashe wayar da sauri,” ya faɗa cikin sigar tsokana da ke sanyaya rai, Inteesar ta gyara zamanta cikin sanyin jiki, tana jin yadda muryarsa ke ratsa ƙofofin zuciyarta, sai dai wani ɓangare na zuciyarta ya tuna da muryar matar nan ta cikin asibiti, wanda hakan ya sa wani ɗaci ya sake dawowa mata, ta daure ta murguɗa baki, kamar yana ganinta, sannan ta ce: “Akwai abin da nake son tambayarka…” “Haba? To, ina jinki, na ba ki dama gaba ɗaya,” ya amsa cikin wata murya da ke nuna cewa dukan hankalinsa yana kanta.

Inteesar ta ja dogon numfashi, ta daure sannan ta jefa masa tambayar da ke ƙona mata zuciya tun ɗazu, “Kana da mata… har da yara ko?” Shiru ya ratsa can ɓangaren na tsawon daƙiƙu biyu, sannan Aliyu ya saki wani ɗan gajeren murmushi mai nuna kwanciyar hankali, ya gyara zamansa sannan ya amsa mata cikin sautin da ke nuna gaskiya tsaf, “Eh, Inteesar, ina da mata biyu… da kuma yara huɗu,” amsar Aliyu ta sauka a kunnen Inteesar tamkar an watsa mata ruwan ƙanƙara, dukan jikinta ya daskare a wurin!

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol