Free chapter · Read without an account

Chapter 1

by Rukayya Ibrahim · Duhun da natashi ciki

Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin Ƙai.

Ya Allah, ina roƙonKa Ka sanya albarka a cikin wannan littafi, Ka sa ya zama sanadin alheri, faɗakarwa da tunatarwa ga duk wanda ya karanta shi.

Ya Allah, Ka sanya alƙalamina ya zama mai faɗin gaskiya, Ka ba ni basira da hikimar isar da saƙon da zai amfanar da al'umma.

Ya Allah, Ka sa duk wanda ya karanta wannan labari ya amfana da darussan da ke cikinsa. Ka nisantar da ni daga kwaikwayon aikin wasu, Ka azurta ni da baiwar ƙirƙira da tunani na gari.

Ya Allah, Ka sa wannan aiki ya zama sanadin alheri da nasara a gare ni, Ka kuma kare ni daga duk abin da zai zama sanadin cutarwa.

Amin, Ya Rabbal Alamin. 🤲

*CHAPTER 1:  book one.  

DUHUN DA NATASHI CIKI. 

By✍🏻 Rukayya Ibrahim

Mushiga cikin labarin 


Sunana Ramatu, amma mutane suna kirana da Rammu.

A wani gari mai cike da hayaniya, amma zuciyata tana cikin shiru, na tashi.

Babu wanda ya san abinda ke cikin zuciyata. Mutane suna ganin ina dariya, amma ba su san duhun da ke cikin raina ba.

Rayuwa ta ba ta sauki. 
Rayuwa ta ba ta sauki. Na ga wahala, na ga cin amana, na ga lokacin da nake son in yi kuka amma sai in danne.

A wannan rana, na zauna a gefen katifana, kusa da taga, na kalli waje. Na tambayi kaina...

_"Rammu, har yaushe za ki zauna cikin duhu? Har yaushe za ki boye ciwon ki?"_

Sai wani hawaye ya zubo daga idona. Ba hawayen rauni bane. Na tausayin kaina ne.

Amma a wannan lokacin, na ji wani abu a zuciyata yana cewa - *"Rammu, ki tashi. Duhu ba gidanki

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol