Free chapter · Read without an account
THE PROPOSAL
KADDARAR ZUCIYA
CHAPTER THIRTY-ONE: 31
THE PROPOSAL
JIDDAAH BARKUM
———-
Wannan amsar Aliyu ta sauka a kunnen Inteesar tamkar an watsa mata ruwan ƙanƙara, zuciyarta ta yi wani irin mugun tsalle, ilahirin jikinta ya saki, ta ji wani irin jiri na neman kwashe ta duk da cewa a zaune take, sai da ta dake da ƙyar, ta haɗiye wani ɗaci da ke neman tasowa daga maƙogwaronta, ta daure ta fito da wani ƙasaitaccen murmushin yaƙe, muryarta tana rawa amma tana ƙoƙarin nuna kamar ko a jikinta, “Ma sha Allah… na gane.”
Daga can ɓangaren, Aliyu ya ji canjin sautin muryarta, kuma ya fahimci yadda amsar ta daki zuciyarta, ya gyara zamansa sosai, ya sauke muryarsa ƙasa gaba ɗaya har ta koma mai zurfi, cike da tsantsar seriousness, “Intee…” ya kira sunanta cikin wani irin sauti mai ratsa jiki, “Ina so mu yi wata magana mai matuƙar muhimmanci da ke, don Allah ki tausaya mini…” Inteesar ta ji wani iri, ta haɗe fuska kamar yana gabanta, “Na tausaya maka kuma? Me na yi maka?” “Kin san abin da nake nufi, Intee,” Aliyu ya faɗa, muryarsa cike da tsantsar rauni da nuna soyayyar da ta daɗe tana tunkudo shi, “Ina matuƙar sonki, tun ranar farko da idanuna suka sauka a kanki, zuciyata ba ta sake samun hutu ko gurbin nutsuwa ba, don Allah ki amshi soyayyata… Na yi haƙuri na tsawon lokacin nan da muka kwashe, don Allah ki taimaka mini ki ce kin amince.”
Inteesar ta yi shiru na wani lokaci mai tsawo, tana sauraron yadda ƙirjinta ke faman bugawa da ƙarfi, kalaman nasa sun taɓa wani ɓangare mai zurfi na zuciyarta, amma hoton matansa biyu da yaransa huɗu ya tsaya mata a idanu, cikin rawar murya da sanyin gwiwa, ta ce: “Ba na jin zuciyata ta shirya don shiga maganar soyayya a halin yanzu… Don Allah ka yi haƙuri,” ba ta gama ƙarasa maganar ba, Aliyu ya katse ta da sauri cikin wata murya mai cike da roƙo da fargabar rashin samun karɓuwa, “A’a, Inteesar! Don Allah kada ki ce haka… Ki ba ni dama ko da kaɗan ce, just a little chance, na yi miki alƙawari zan canza dukan tunaninki da kike da shi a kan soyayya, I promise to change your world, ina matuƙar ƙaunarki, kin ji?”
Inteesar ta sake lulawa cikin wani uban shiru, ta kasa cewa komai, tamkar ma ba ta kan layin wayar gaba ɗaya, hankalin Aliyu ya tashi, ya shiga kiran sunanta cikin sauri, “Hello… Intee? Hello?” “Uhmm…” ta furta cikin rawar murya da ƙyar, bayan ta dawo da numfashinta, “Kina jina?” Daga ɗayan ɓangaren ta amsa da raunin murya: “Uhmm…” Ya sauke numfashi, “To, ki yi magana,” ta sake yin shiru, sai can ta buɗe baki a hankali, “Ni yanzu…” Sai kuma ta sake yin shiru, ta kasa ƙarasa maganar saboda yadda maƙogwaronta ya bushe, Aliyu ya gyara zamansa cikin shauƙi da matsuwa, “Ki faɗa mana, ina jinki, ke me…?” Ta daure, ta haɗiye ragowar jarumtarta, ta tara dukan courage ɗinta sannan ta buɗe baki ta ce: “Ni yanzu ta ina zan fara, bayan ka ce kana da mata biyu kuma da yara huɗu? Ƙila ma a cikin yaranka akwai wanda yake sa’a na, ko ma ya girme ni…”
Bayan jin kalaman Inteesar da ke cike da kishi wanda ita kanta ba ta san dalilinsa ba, Aliyu ya saki wani tattausan murmushi mai sauti ta cikin wayar, ya gyara zamansa sosai, muryarsa ta ƙara yin ƙasa da laushi, cike da tsantsar lallashi, “Intee…” ya kira sunanta cikin wani sauti mai ratsa jiki, “Kada ki fassara ni yadda kike tunani, ki saurare ni da kyau kafin ki yanke mini hukunci,” ya ɗan dakata, sannan ya ci gaba da ba ta taƙaitaccen tarihin rayuwarsa cikin nutsuwa, “Ni Bafulatani ne daga Yola, aiki ne ya kawo ni nan jihar Katsina har na zauna, matata ta farko, ɗiyar baffana ce, wato cousin ɗina ta jini, tana can Yola, kuma ina zuwa duba ta duk bayan mako biyu, every two weeks, ita kuma matata ta biyu, a nan Katsina na aure ta, kuma muna tare da ita a nan.”
Inteesar ta gyara zamanta a kan darduma, tana sauraronsa da dukan hankalinta, yayin da zuciyarta ke faman bugawa da sauri, Aliyu ya ci gaba da bayanin yaransa ɗaya bayan ɗaya don ya kwantar mata da hankali gaba ɗaya, “Kuma game da yarana da kike tunanin za su iya zama sa’o’inki… hakan ba zai taɓa kasancewa ba, babban ɗana na fari, Arham, shekarunsa goma kacal, 10 years old, ta biyu, Nihal, shekarunta bakwai, 7 years old, na uku, Mahfouz, shekarunsa biyar, 5 years old, sai auta gaba ɗaya, Ayaan, jariri ne ɗan watanni takwas kacal, 8 months old,” ya ja numfashi mai ɗumi, sannan ya ƙarasa maganar cikin muryar roƙo da tsantsar ƙauna, “Kina gani, a cikin waɗannan akwai wanda zai zama sa’anki? Na yi miki alƙawarin zan kare mutuncinki da darajarki idan kika amince da ni, don Allah ki ba ni wannan damar, Intee…”
Inteesar ta tsinci kanta cikin wani sabon sanyin gwiwa da ruɗani na daban, duk da cewa bayanan da Aliyu ya yi mata sun rage mata fargaba, amma matsayinta na mace ta uku a rayuwarsa ya tsaya mata a rai, ta sauke wani nannauyan numfashi a hankali, sannan ta ce masa cikin murya mai rauni: “Ka ba ni lokaci… zan yi tunani a kai,” Aliyu ya ji maganar ta daki zuciyarsa, ya canza salon muryarsa, yana nuna rashin son jinkiri da fargabar rasa ta, “Haba, Inteesar… wane tunani kuma ya rage bayan na faɗa miki dukan gaskiyar da ke raina? Please…” Ta sake yin shiru na wasu daƙiƙu, tana sauraron bugun zuciyarta, can ta daure, muryarta cike da shagwaɓa da roƙo ta ce: “Ina buƙatar lokaci mai yawa don in yi tunani… don Allah,” Aliyu ya tsure da jin yadda take marairaice masa, sai ya sauke numfashi a hankali, ya amince cikin sanyaya rai, “Alright… take your time, babygirl.”
Shiru ya sake ratsawa tsakaninsu na ɗan lokaci, inda kowa ke jin sautin numfashin ɗan uwansa ta cikin wayar, can Inteesar ta ce da ƙyar: “Zan kwanta yanzu… it’s getting late,” Aliyu ya sake sauke muryarsa sosai har sautin ya koma mai zurfi, cike da taushin da zai iya narkar da kowace zuciya, “Okay… good night, and sleep like a baby… I love you,” jin kalmar “I love you” ta fito sarai daga bakinsa ya sa dukan jikin Inteesar yin tsit, tamkar an dasa ta a wurin, wani irin ɗumi da shauƙi ya ziyarci ilahirin ranta, cikin hanzari da firgicin da ita kanta ba ta san dalilinsa ba, ta yi saurin yanke kiran, click! Ta tura wayar gefe, sannan ta rungumi matashin gadonta ta matse shi a ƙirjinta, ta rintse idanunta da ƙarfi tana sauke numfashi akai-akai, yayin da zuciyarta ke wani irin mahaukacin duka mai cike da daɗi da fargaba a lokaci guda.
Washegari da safe, hasken rana ya riga ya ratsa ta cikin babban window na kitchen ɗin gidan, inda Mommy Haleema da wata daga cikin ma’aikatan gidan suke tsaye suna ƙoƙarin haɗa abincin karin kumallo, Inteesar tana gefenta, tana ƙoƙarin zuba kunun gyada a babban flask ɗin da ke gabanta, amma gaba ɗaya hankalinta ba ya wurin, a wani ɓangare na zuciyarta, tana jin daɗi da shauƙin kalaman Aliyu na daren jiya, amma a ɗayan ɓangaren kuma, duk lokacin da ta tuna cewa yana da mata biyu da yara huɗu, sai jikinta gaba ɗaya ya yi sanyi, numfashinta ya fara yin nauyi, Mommy Haleema, wadda take lura da kowane motsi na ’yarta tun da suka shigo kitchen ɗin, ta tsayar da aikin da take yi, ta juyo gaba ɗaya tana fuskantarta, ta lura da yadda Inteesar ke kallon gefe guda, alamar ta yi nisa a tunaninta, “Intee…” Mommy ta kira sunanta cikin muryar uwa mai cike da kulawa, “Me ke damunki ne? Tun ɗazu nake kallonki, gaba ɗaya ba kya cikin nutsuwarki.”
Inteesar ta ɗan firgita, ta ɗago da sauri sannan ta tilasta wa fuskarta fitar da wani ƙasaitaccen murmushin yaƙe, “Wallahi babu komai, Mommy, gajiyar zaman asibiti ne kawai ke damuna… Ina buƙatar in huta sosai, jikina duk babu daɗi,” Mommy Haleema ta sauke ajiyar zuciya, ta karɓi flask ɗin daga hannunta, “To, ya kamata ki huta sosai, daughter, dama tun farko ban san me ya sauko da ke ba, alhali ba ki sami isasshen bacci ba,” Inteesar ta ɗan karkatar da kanta gefe guda cikin shagwaɓa, sannan ta ce: “To, Mommy… ai sai na ji ba daɗi na bar ki kina aiki ke kaɗai a kitchen ɗin,” Mommy ta yi murmushi ta shafa kanta, “Babu komai, ba ga Saleema tare da ni ba? Wuce ki tafi ɗaki ki huta,” Inteesar ta juya a sanyaye, ta wanke hannunta a cikin sink kafin ta fita daga kitchen ɗin gaba ɗaya.
Tana komawa ɗakinta, ta tura ƙofar sannan ta nufi gadonta kai tsaye ta faɗa a kai, ta ɗauki wayarta tana ta jujjuya ta a hannunta, tana kallon screen ɗin cikin rashin natsuwa, zuciyarta tana buƙatar wanda za ta faɗa wa abin da ke damunta don ta sami sauƙi, ba tare da ta tsawaita tunani ba, ta danna lambar Humaira, kiran bai yi nisa ba, Humaira ta ɗaga a ɗayan ɓangaren, muryarta ta fito cike da kuzari da murna, “Hey, Intee! How far? Ya jikin Daddy fa?” Inteesar ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce: “Alhamdulillah, Daddy ya ji sauƙi sosai, yanzu haka yana can ɗakinsa yana barci,” “Alhamdulillah! Allah ya ƙara masa lafiya da sauƙi mai ɗorewa,” Humaira ta amsa cikin farin ciki, can kuma ta ɗan dakata lokacin da ta ji yadda muryar Inteesar take a sanyaye, sai ta tambaya cikin mamaki: “Amma ke kuma, me ya sa nake jin muryarki so cool haka? Ba dai har yanzu jikin Daddy ba ne?” “Uhmm… jikin Daddy dai na faɗa miki ya yi sauƙi sosai,” Inteesar ta turo baki tana gyara kwanciyarta, “Kawai dai ina cikin wata gagarumar damuwa ne… tunani ya yi mini yawa a kai.”
Jin haka ya sa Humaira ta tashi ta zauna da sauri a kan gadonta, dukan hankalinta ya dawo kan wayar, “Lafiya kuwa? Me kuma ya faru, Intee?” Inteesar ta runtse idanunta ta ce cikin ƙaramar murya, kamar mai rada: “Aliyu ne…” Nan take Humaira ta saki wani murmushi mai cike da tsokana, ta fashe da ’yar dariya sannan ta ce: “Tab! Lallai ma… ashe ya riga ya cika miki zuciya gaba ɗaya! Shi ne kike ta faman yin ƙasa da muryar nan,” Inteesar ta turo bakinta gaba sosai, tamkar Humaira tana gabanta, ta damƙi matashin gadonta da hannu, “Uhmm! Humaira, gaskiya kina da matsala, ki tsaya ki saurare ni da kyau mana kafin ki fara mini dariya!” Look ɗinta ya canza gaba ɗaya, damuwa ta bayyana a fuskarta, Humaira ta tsagaita da dariyar da take yi, ta gyara zamanta lokacin da ta ji sauyin muryar ƙawarta, “Okay, sorry dear, I’m all ears now, faɗa mini, me ya faru da Aliyun?”
Inteesar ta tura kanta cikin pillow, ta rage saurin muryarta zuwa ƙasa-ƙasa, tamkar ana sauraron su a ɗakin, “Humaira… he has a family, yana da mata… kuma ba guda ɗaya ba, guda biyu fa! Plus four kids!” Ta ɗan ja numfashi cikin rawar murya, idanunta suka ciko da hawaye, “Imagine, Humaira! Ni yanzu ta ina zan fara? Ta yaya zan je na zauna a matsayin mace ta uku a gidansa? Oh my God, na rasa yadda zan yi gaba ɗaya, zuciyata is so heavy right now, I’m so confused!” Ta ƙarasa maganar cikin tsantsar damuwa, muryarta ta yi ƙasa yayin da take ƙoƙarin hana hawayenta zubowa, shiru mai nauyi ya ratsa ta ɗayan ɓangaren wayar, Humaira ta daskare na wasu daƙiƙu, tana nazarin girman maganar da kuma yadda abin ya daki ƙawarta, can ta numfasa, muryarta ta fito daban, babu alamar wasa ko kaɗan, “Intee…” Inteesar ta ɗago kanta da sauri, ta share hawayen fuskarta, “Na’am…” “Tsakaninki da Allah… do you really love him? Kina son Aliyu da gaske?”