Free chapter · Read without an account
11
by Asmy b Aliyu · OMRI HAYATII
OMRI HAYATII
by....
Asmy b Aliyu
11
bugun xuciyana da fitar numfashina duka na kane my mu'azzam..."ta fada wearing a big smile ,juya ido yayi Yana furta
oh really??"yadda yayi din da ido ya bata kunya dan shagwabe fuska tayi
tana jin yadda ya motsa bakinsa
lebensa na kasa da na saman na motsawa kusan lokaci daya ya furta kalmar sorryyyyyy my malaak!!!"yadda yaja sunan nata batareda sauti ya fita ba ko kadan
ya Kara buga zuciyarta da wani mugun soyayyarsa dake bin duka jininta,
a hankali suke fallasawa junansu sirrin dake kwance acikin zuciyarsu.
kankame filo malaak tayi tana fitar da wani numfashi mai dumi haka yanayinta na canjawa lokaci daya,ga wata irin kewarsa da takeji tana danneta.idanunta da yanayin ta kawai da ya kalla ya fahimci mugun kewarsa take ba kadan ba
da haka ya samu ya lallabata da kalamansa
masu zauta kwakwalwarta yayi mata sallama,dan har Abba ya fara Kiransa ta dayan Wayan da alamar shi kawai ake jira. tamkar Kar suyi sallama.wani irin kiss
ya sako mata ta cikin vidcall din da ta jisa har tsakiyyar zuciyarta babu shiri ta fara hade kafafu tana jin mu'azzam marafa na kasheta da soyayyarsa.....
#####
tana kwance a kan bed dinta tana kallon pics din mu'azzam har lokacin nishadin dake kwance akan fuskarta a bayyane yake da haka mum ta turo kofar.daga Kai tayi ta kalli kofar haka tasan duk duniya babu mai shigo mata daki babu neman izini Sai mum ko maleeka
hatta da dad dinta idan zai shiga dakinta Sai ya nemi izininta,da gudu ta sauko daga kan bed
ta kama hannun mum din tata tana zagaye dakin daita,wani irin farin ciki mum din ke hangowa cikin fuskar malaak din
Kuma tana fatar farin cikin ya cigaba da wanzuwa cikin rayuwarta na har Abada.........
"mum Ina son mu'azzam
mum ina tsananin kaunarsa, murmushi mum
tayi tana Jan hannunta Suna zama gefen bed.anan ta shiga baiwa mum din labarin yadda mu'azzam yayi mata magana ta Whatsapp da Kiran da yayi mata,komai da komai Sai da ta fadawa mum dinta.saboda mum tayi masu wani irin horon da komai nasu basa boye mata hatta maleeka da tayi aure babu sirrin aurenta wanda take boyewa mum,ba Karamin murna mum tayi ba da jin wannan labarin na malaak
ya faranta zuciyarta sosai.murmushin jin dadi mum tayi tana shafa kan malaak
din cike da tsantsan so take fadin"
farin ciki na har abada my baby girl."
rungume mum din malaak ta karayi
tana jin wani sanyi na rasta duka zuciyarta da gangar jikinta...
######
wuraren qarfe 3 na rana suka shigo garin kaduna,kai tsaye gida suka wuce
cikin farin ciki mami ta tarbesu tana masu sannu da zuwa rungume Mami yayi
Yana sauke ajiyar zuciya.cike da kulawa Mami ke dan shafa kansa,anan Abba
yabarsu dan kaunar Mamin da mu'azzam
maigirma ce.mami ta dago mu'azzam
tana fadin yaje yayi wanka abincin na jiransa,dagaawa mami Kai yayi
tareda kama fuskarta ya sauke mata kiss akan goshinta.da haka ya nufi bangarensa,
itakuma mamin ta nufi bangaren Mijinta
a cikin bedroom ta samu Abba Yana rage kayan jikinsa,da murmushi cikin fuskarta
ta karaso wurin abba tana tayasa rage
kayan jikinsa.jawota yayi ajikinsa Yana binta da kallon so.hannunsa duka biyu ya saka ya hade filin dake tsakaninsu,cike da tsananin kewa ya zagaye kugunta.
"kina manta mijinki a yaronki kawai kike sani."Abba ya fada murya kasa kasa,
murmushi mami tayi tana dora hannunsa akan kirjinsa cike da soyayyarsa
take jefawa abban wani irin kallon da ya Kara narkasa Yana jin wata irin tsananin bukatar matar tasa na bijiro masa,
daukarta yayi dukanta ya nufi kan bed daita wara idonta tayi tana kallonsa,
"Abba da tsakiyyar rana ka manta yara na nan , mu'azzam na gida."Yaranmu duka Sun girma Ayshaa babu Wanda xai shigo bangaren nan batareda izininmu ba,
da haka Abba ya fara shinshinar wayanta cikin tsananin kewarta da kaunarta.........sosai Mami ta basa hadin Kai bayan wani lokaci suka samu natsuwa wani wankan suka sakeyi suka fita dinning area,Sai dai babu motsin kowa har lokacin
Mami tayi serving Abba, murmushi yayi
Yana furta thank you.""
"Abba!!!"fareeda ta karaso wurin cike da murna tazo ta rungumesa ta baya a zaune da yake."I really miss you Abbanmu.""
nima nayi kewarki my fareeda."murmushin jin dadi ta saki daidai nan Ayusherh ta karaso cikin dinning din da sallama a bakinta daga Mami har Abba suka daga Kai Suna kallonta kusan atare suka amsa,
ta karaso tana gaisheda abba cike da girmamawa tana masa sannu da zuwa
ya amsa a natse da Kuma kulawa Yana tambayrta ya karatunta da Kuma kaka
ta amsa da Alhmdullahi Kuma kakan na masa sannu da zuwa kafin ta shigo
gaishesa,ya amsa gaisuwar kaka
kafin ya cigaba da cin abincinsa,
Mami yayanmu fa??"
Yana bangarensa jeki ki dubasa
yazo yaci abincisa,fareeda ta juya itada Ayusherh Suka nufi bangaren
mu'azzam, har cikin bedroom dinsa suka shiga baya ciki.har bathroom fareeda ta leka baya ciki,haka ya saka suka nufi
balcony dinsa dake bayan part dinsa
mai dauke da swimming pool aciki,
Banda iska babu abunda ke kadawa acikin wurin,
yana tsaye ya bada baya Yana waya cikin natsuwar da ko tashin muryarsa bakaji
cikin ihu fareeda taje ta rungumesa ta baya.juyowa yayi daita ta gabansa batareda ya cire wayar ba.
"yayanmu munyi kewarka."fareeda ta fada sounding so very happy.ya lakaci hancinta kafin ya daga Kai ya kalli Ayusherh da take tsaye tana kallonsa murmushi dauke a fuskarta ,hannu ya bata alamar ta karaso
Sai ta karaso tana sakin fili a tsakaninsu
da ido yake fadamata ta karaso mana
Banda murmushi babu abunda takeyi
tasan me yake nufi ta qaraso itama ta rumgumesa kamar yadda fareeda tayi
fareeda ta kalleta tana sakin dariya
take fadin"Yayanmu Ka kyale Queen
bakauyace ,girgiza Kai mu'azzam yayi
Sai ya ware mata hannunsa alamar to su gaisa babu musu ta basa hannun sukayi shaking hands,a tsakaninsu bai cire hannunsa cikin nata hannun ba Sai ma kara matse hannun nasa da yayi
da sauri ta kallesa zuciyarta na bugawa.
Kuma lokaci daya tana tuna khudubar kaaka wacce take yawan yimata.....
"karki ga Yan gidan nan Suna rayuwarsu ta boko kice kema Zaki saba daita karki ga yadda fareeda ke rungume yayanta kice kema Zaki gwada haka Ayusherh,keda farida akwai banbanci ita fareeda jininisa CE kanwarsa ce jininsa ke aiki ajikinta.
ke Kuma baku hada komai dashiba baku da wata dangantaka ta jini bayaga dangantakar musulunci.
karki kuskura shaidan ya ribanceki ko hannunki mu'azzam ya rike dan Zaki iya daukar ciki a haka."kalaman da ke Kara nisanta da mu'azzam din kenan duk da Akwai shakuwa a tsakaninsu Amman
bata yadda ta wuce iyakarta,
runtse ido tayi zuciyarta na mugun bugawa da sauri ta zare hannunta cikin nasa tana dan Jada baya.murmushinsa mai kyau da tsada ya sauke mata
tareda furta thank you my queen
be happy, fareeda ta tsaya gefensa
tana fadin"Yaaya har yanxu baka sauka akan wayar ba fa."sai lokacin ya tuna waya yake da malaak.
a natse ya kira sunan malaak din da take jin zuciyarta na mugun tafarafasa dan duk kalaman da ya fadawa Ayusherh din acikin kunnenta,ta tsani wannan Queen din da Yan gidansu mu'azzam din ke Kiran Ayusherh dashi.lokaci daya ta katse Kiran,
bin wayar yayi da kallo da mamaki,
"Yayanmu muje kayi lunch Mami na jiranka,da haka suka sakasa a gaban Suna komawa bangaren mamin.duk cikin cimar da Mami ta cika table dashi snacks kawai
ya iyaci Sai milk drinks dan ba yunwa yakeji sosai ba ,yaci abinci a jirgi.
basuma tashi akan dinning din ba sukaji
sallamar Fadeela itada da kyawawan yaranta ,da mai sunan mami Aisha wacce suke kira imaan Sai babban Wanda yaci sunan surikin Fadeela din Almustapha
suna Kiransa Habeeby,da gudu yaran sukaje suka shige jikin mu'azzam Shima Duka ya daukesu daya bayan daya Yana manna masu kiss Yana dorasu akan cinyoyinsa cike da kulawa da soyayyar yaran.
da sauri Fadeela taje ta rungume Abba tana masa sannu da zuwa Yana shafa kanta yake fadin"mun sameku lafia??"
lafia lau Abba ,amman munyi kewarka sosai. ta fada tana Kara kwantar da jikinta cikin na Abba , murmushi Abba ya sauke
Yana kallon Mami dake kallon Fadeela
tana harararta.rufe baki Fadeela tayi tana sakin dariya a hankali take fadin"AI banyi Karya ba mami kin manta kina kirana a waya cikin kwanakkin nan kina fadin
gidan babu kowa babu dadi,kema kinyi kewar Abba nasani ,wata hararar Mamin
ta Kara jefa mata batareda tace komai ba.
Fadeela dai Sai daria take a hankali
ta karasa wurin mu'azzam da har yanxu
yake dauke da yaran Yana sauraren shirmensu na yara.zagayowa tayi
ta bayan kujerar da yake akai tasa hannunta duka biyo ta sakalosu ta cikin wuyan mu'azzam din a hankali da muryar natsuwa take fadin"I miss you so badly Yayanmu."juya ido yayi Yana da karkatowa
Yana kallon cikin fuskarta ya kalla sama da kasa,zaro ido tayi tana fadin"dan Allah baka yadda ba."ganin ya dauke kansa akanta ta zagayo ta gabansa ta jawo kujera ta zauna tana fuskantarsa take
fadin"Allah nayi kewarka yaaya doctor."
kedai yaaa Fadeela kawai ki fito fili kice Ina tsaraba?"ta kalli fareeda da sauri da take daria daga Mami har Abba kallon yaran nasu suke cike da kauna da soyayya.ni babu tsarabar da nayi
Fadeela marafa."da sauri fareeda ta karaso gabansa tana fadin"Kai Yayanmu."
su habeebi kawai na zowa da chaculate
banda lokacin zuwa shopping."
fareeda ta kwabe fuska tana kallonsa
ko kadan bataji dadi ba ,har list din abubuwan da sukeso ta tura masa itada Ayusherh.
ya kalli fareeda ganin tayi shiru,
zan tura maku kudi a account dinku kowa Sai ya siya abunda yakeso."dan sakin fuska fareeda tayi tana fadin"mungode yayanmu Allah ya Kara arziki da wadata."A natse ya amsa da ameen,Fadeela ta juya tana kallon Abba take fadin"Abba sauran naka,
nasan Kaima empty hand ka dawo."nima zan tura godiya sukayiwa Abba cike da farin ciki.
#OMRI HAYATII
#LOVE/FATE
#BESTLOVE
#ASMY B ALIYU
#***