Free chapter · Read without an account
THE RULES AND THE PROMISES
KADDARAR ZUCIYA
CHAPTER THIRTY-TWO: 32
THE RULES AND THE PROMISES
JIDDAAH BARKUM
———-
Wannan tambayar ta sauka a kunnen Inteesar tamkar karar fashewar abu, ta rintse idanunta da ƙarfi, wani irin sanyi yana ratsa dukan gabobinta, ba ta taɓa zama ta yi wa kanta wannan tambayar ba, ko da yaushe tana fakewa ne da cewa “mutumin kirki ne,” amma yanzu da Humaira ta tunkare ta da gaskiyar lamari, ta tsinci kanta cikin rashin amsar da za ta ba ta, ganin Inteesar ta yi shiru ta kasa magana, Humaira ta sake gyara zamanta, muryarta ta fito cikin sigar rarrashi da nusarwa, “Forget about his wives for a second, manta da matansa na ɗan lokaci, Intee, manta da maganar yaransa huɗu, kauda duk wani shamaki da ke tsakaninku gaba ɗaya, idan Aliyu ba shi da mata ko guda ɗaya a rayuwarsa, kuma ya zo ya nemi aurenki a yau… da za ki amince da shi?”
Wannan furucin ya buɗe wa Inteesar wata sabuwar ƙofa a cikin tunaninta, nan take, hotunan abubuwan da suka faru a baya suka shiga gilmawa a idanunta tamkar guguwa, ta tuna ranar farko a cikin flight, yadda ya nuna mata tsantsar kulawa da kariya ba tare da ya san ko ita wacece ba, ta tuna kwanakin wahala da fargaba a asibiti lokacin da Daddy ba shi da lafiya; yadda Aliyu ya zama tamkar garkuwarta, yana goge mata hawaye tare da hana ta kuka a duk lokacin da ta karaya, ta tuna irin juriya da haƙurin da ya nuna a kanta tun lokacin da ya san ta, duk da irin wulakanci da kuma yadda take yi masa watsi a wasu lokuta, bai taɓa fushi ko daina nuna damuwa da lamuranta ba, mafi muhimmanci, ta ji yadda zuciyarta ke yin wani mahaukacin tsalle mai cike da daɗi a duk lokacin da sunansa ya bayyana a kan screen ɗin wayarta.
Dukan waɗannan abubuwan suka haɗu suka yi mata nauyi a ƙirji, ta kasa daurewa, ta fashe da wani irin nannauyan kuka mai ban tausayi, muryarta tana rawa gaba ɗaya, “Ina jin… ina jin ina sonsa, Humaira! Ina matuƙar sonsa a cikin zuciyata!” Ta fashe da kuka, ta kasa ɓoye abin da ke zuciyarta, Humaira ta saki wani tattausan murmushi mai cike da tausayi da fahimta, “To, wannan shi ake kira falling in love, Intee, zuciyarki ta riga ta tafi,” amma ba tare da ta tsawaita wannan farin cikin ba, Humaira ta ja numfashi don dawo da ita cikin ainihin zahirin rayuwa, “Amma soyayya kaɗai ba ta isa ba, Intee, dole ne ki fuskanci gaskiya guda ɗaya, ki tambayi kanki… kina iya rayuwar kishiyoyi? Kina iya zama mace ta uku, wife number three, a gidan aure? Kina da juriyar raba miji da wasu mata biyu daban?”
Waɗannan kalaman sun soki zuciyar Inteesar tamkar kibiya, suka sake jefa ta cikin wani sabon ruɗani mai duhu, “Intee… kina jina?” Humaira ta sake tambaya daga ɗayan ɓangaren wayar, Inteesar ta ji zuciyarta ta cika da wani irin nauyi, ta kasa daurewa ta ce cikin sauri: “Humaira… zan kiraki anjima, don Allah, jikina duk ba daɗi,” ba ta jira amsar Humaira ba, ta yanke kiran, ta jefa wayar a gefenta, ta tura kanta cikin pillow sannan ta fashe da wani irin nannauyan kuka mai ban tausayi, ta tabbatar wa kanta cewa ta riga ta kamu da son Aliyu, amma fargabar zama mace ta uku tana neman raba ta da nutsuwarta.
Dare ya yi, kusan ƙarfe goma sha ɗaya na dare, Inteesar tana kwance a kan gado, idanunta a buɗe suna kallon rufin ɗakin, yayin da kalaman Humaira ke ta faman amsa-kuwwa a ranta, kwatsam, wayarta ta fara ruri, ta duba screen ɗin, Aliyu, zuciyarta ta yi wani irin mugun bugu, ta lumshe idanunta, ta haɗiye miyau sannan ta ɗaga wayar ta kara a kunnenta, “Assalamu alaikum,” muryarsa ta fito cikin daɗaɗɗen sauti mai cike da nutsuwa, “Wa alaikumus salam,” ta amsa, muryarta gaba ɗaya a mace, “Kaddarar zuciyata ta hana ni bacci, ban ji yadda kuka kwana ba, ya jikin Daddy? Da fatan ya sami isasshen bacci da hutu yau?” Aliyu ya tambaya cikin tsantsar kulawa, “Alhamdulillah, jikin Daddy ya samu sauƙi sosai, yana ta samun sauƙi, Alhamdulillah,” “Ma sha Allah, Allah ya ƙara masa lafiya mai ɗorewa, su Mommy fa da su Yaya Abubakar? Da fatan kowa yana lafiya, kuma gajiyar asibitin ta ɗan ragu?”
Inteesar ta ji wani ɗumi a ranta saboda yadda yake damuwa da iyalanta, “Dukansu suna lafiya, kowa ya huta sosai yau, na gode sosai,” bayan sun gaisa a taƙaice cikin muryoyi masu cike da shauƙi da ɗan fargaba, Aliyu ya ja dogon numfashi, sai ya sauke muryarsa ƙasa sosai har ta koma mai zurfi da taushi, cike da fargabar amsar da yake dakon ji, “Intee…” “Na’am,” ta amsa cikin raunin murya, “Kin yi tunani a kan maganar da na yi miki daddaren jiya? Kin yi mini alƙawarin za ki ba ni amsa, zuciyata tana jiran sanin matsayina a wurinki,” Inteesar ta ji dukan jikinta yana rawa, ta tuna duk abubuwan da suka faru, da kuma tsoron da ke ɗarɗar a ranta, ta ja dogon numfashi mai zafi, ta kira sunansa cikin raunin murya, “Aliyu…” “Na’am, ina jinki,” “Ina tsoron sonka… Ina tsoron abin da zai faru a gaba idan na miƙa maka zuciyata.”
Aliyu ya firgita daga can ɓangaren, hankalinsa ya tashi, ya gyara zamansa cikin sauri, “Me ya sa, Intee? Me ya sa kike tsoron sona? Ina sauraronki…” Ta numfasa sannan ta share hawayen da ke neman zubo mata, ta tattaro dukan jarumtarta, “Zan amince…” Aliyu ya yi shiru na ɗan lokaci, kamar bai tabbatar da abin da kunnuwansa suka ji ba, sai ya sauke wani numfashi mai zurfi wanda ya fito tun daga ƙasan zuciyarsa, “Intee…” ya kira sunanta cikin farin ciki da ba zai iya ɓoyewa ba, “Amma ina da sharadi,” ta katse shi, cike da zumuɗi ya amsa: “Faɗi sharadinki, babygirl, and consider it done, ina jinki,” ta ja numfashi sannan ta fara magana cikin nutsuwa, “Ba na son ka yi mini ƙarya, saboda ba na son a yi mini ƙarya ko kaɗan a rayuwa, no lies, no secrets, ko da gaskiyar za ta cutar da ni, ina son ka buɗe mini zuciyarka ka faɗa mini ita duk da ɗacinta, na riga na sha raɗaɗin rasa Ahmad a baya, ba zan iya jure wa wani cin amana ko yaudara a halin yanzu ba,” Aliyu ya katse ta cikin gaggawa, muryarsa cike da gaskiya, “Na amince, Inteesar, indai wannan ne, kada ki damu, In Sha Allah, za ki same ni mai gaskiya, na yi miki alƙawari,” ta gyada kanta kamar yana ganinta, “Shi ne sharadi na farko, sai na gaba…”
Ta ɗan dakata, tana tara ƙarfin hali kafin ta ci gaba, “Kuma ba zan taɓa shiga wata alaƙa da kai a ɓoye ba, idan har da gaske kake sona, to ka zo gidanmu ka nemi izini a wurin magabatana, idan kuma wata rana na ga ba zan iya jure wa irin wannan rayuwar gidan auren naka ba… zan so ka yi mini abu guda, ka sallame ni cikin mutunci,” Aliyu ya sake katse ta, “Haka ba zai faru ba, babygirl, In Sha Allah, mutuwa ce kawai za ta raba mu, kuma ko yau kika ce in aika magabatana gidanku, a shirye nake!” Ya ƙarasa maganar cike da tsantsar zumuɗi da farin cikin da muryarsa ta kasa ɓoyewa.
Waɗannan kalaman sun taɓa zuciyar Inteesar ƙwarai, amma sharadin da ya fi kowane firgita shi kuma ya girgiza Aliyu shi ne na ƙarshe da ta jefa masa cikin kuka, “Aliyu…” ta kira sunansa cikin raunin murya, “Ba na son na zama mace ta uku kawai a lissafi, ina son ka ba ni irin soyayyar da za ta sa, ko da wasa, ban taɓa jin kamar ina rabonka da wasu mata ba a rayuwata!” Shiru ya ratsa tsakaninsu, yayin da Aliyu ya daskare da wayar a kunnensa, yana jin girman nauyin da wannan yarinyar ta ɗora masa, bayan ɗan lokaci, ya fara magana cikin sanyin murya, “Kamar yadda na amince da sharadunki na farko, wannan ma na amince da shi,” ya ja numfashi kafin ya ci gaba, muryarsa cike da taushin da ya fito daga zurfin zuciyarsa, “Inteesar, ba zan yi miki alƙawarin cewa rayuwa ba za ta taɓa jefa mu cikin ƙalubale ba, amma ina miki alƙawarin cewa ba za ki taɓa fuskantar su ke kaɗai ba, na rantse da Allah, zan yi iya ƙoƙarina wajen ganin kina murmushi fiye da yadda kika yi kuka, ba zan taɓa ɗaukar soyayyarki da wasa ba, mutuncinki, farin cikinki da kwanciyar hankalinki za su zama amanar da zan tsaya tsayin daka wajen karewa, ba na alƙawarin zama cikakken namiji, amma ina miki alƙawarin zama namijin da kullum zai zaɓe ki, ya saurare ki, kuma ya girmama ki, idan kika ba ni zuciyarki, zan ba ki soyayyar da za ta taimaka miki ki warke daga duk wani ciwo da ya taɓa ratsa zuciyarki, ina miki alƙawari, ba zan bari ki ji kamar ba ki da matsayi a rayuwata ba, za ki kasance ni’ima ce da zan yi godiya da ita a kowace rana, zan yi iya ƙoƙarina wajen ba ki daɗin duniya, ba da dukiya kaɗai ba, amma da kulawa, tausayi, mutuntawa da soyayyar da mace take mafarki da ita, a duk ranar da hawaye suka cika idanunki, zan so in zama dalilin murmushinki, ba dalilin kukanki ba, ko bayan shekaru masu yawa, ina son in ci gaba da kallonki da irin kallon da na fara yi miki tun ranar da Allah ya haɗa ni da ke.”
Inteesar ta runtse idanunta, hawaye suna zuba a fuskarta, kamar yadda hawayen suke zuba, haka kalaman Aliyu da soyayyarsa suke ratsa kowace gaba da jijiya ta jikinta, a wannan lokacin, zuciyarta ta yi mata nauyi fiye da kowane lokaci, ba don ba ta son shi ba, sai don tana jin irin girman soyayyar da yake yi mata, tare da fargabar abin da makomar wannan soyayyar za ta kasance.