Free chapter · Read without an account
Chapter 7
Na shiga
gida ina juye ruwa a randar, sai ga Aisha, wadda muke kira Indo, 'yar wajen Gwaggo Tapito.
Ni da Indo ba ma shiri da juna saboda halinta na raini. Ita tana ganin kamar ta fi kowa a gidan, musamman idan tana tare da wasu 'yan mata. Ba ta cika magana da ni cikin mutunci ba, domin a ganinta, ni ba ni da wani matsayi a gidan.
Ina cikin juye ruwan ne ta shigo gidan, fuskarta ɗauke da murmushi.
Da ta hango ni, sai ta tsaya ta kalle ni daga sama har ƙasa.
"Ke, Rammu! Har yanzu baki gama aikin da Gwaggo ta sa ki ba?" ta tambaye ni cikin wani irin yanayin raini.
Ban ɗago kaina ba, na ci gaba da abin da nake yi. Na san Indo da halinta, don haka ba na son na ba ta damar samun abin da za ta yi faɗa da ni a kai.
Amma ita ba ta tsaya nan ba.
"Yar wahala kawai! Sai kyau babu masunci!" ta faɗa tana kallona da murmushin raini.
Maganarta ta soki zuciyata, amma na danne abin da nake ji. Na san ba ni da wanda zan kai wa ƙara a gidan, don haka na gwammace in yi shiru.
Domin na san gaskiya ta faɗa. Ina da shekara goma sha shida a duniya, amma babu wanda yake zuwa wajena don hira ko zumunci.
Ba kamar su ba, waɗanda kullum sai sun dawo gida da ledoji, su shige ɗakinsu tare da uwayensu suna ta hira da dariya. Ni kuwa, ko da ina cikin gidan, sau da yawa nakan ji kamar ba na cikinsa.
Wani lokaci nakan tsaya ina kallonsu daga nesa, ina tunanin dalilin da ya sa rayuwata ta bambanta da tasu. Me na yi da ya sa nake rayuwa cikin irin wannan kaɗaicin, alhali ni ma mutum ce kamar su?
Na ɗan ɗago kaina na kalli Indo, sannan na ce cikin sanyin murya, "Indo, don Allah ki bar ni in ƙarasa aikina."
Ta yi dariya, ta girgiza kai, kamar abin da na faɗa ya ba ta mamaki.
Ba tare da ta ƙara cewa komai ba, ta juya tana dariya, ta wuce cikin gida, ta bar ni tsaye a wurin.
Na ci gaba da juye ruwan, amma zuciyata ta yi nauyi. Na ji hawaye suna neman zubo min, sai na sunkuyar da kaina don kada wani ya ga halin da nake ciki.
A raina na tambayi kaina, Shin, har yaushe zan ci gaba da rayuwa cikin wannan wulaƙancin? Shin, ni ma wata rana zan samu wanda zai damu da ni, ya saurare ni, kuma ya ɗauke ni a matsayin ɗan Adam kamar kowa?