Free chapter · Read without an account
Chapter
Ina nan zaune cikin tunani, ban san tsawon lokacin da ya ja ba. Sai da na ji kiran Mama, na dawo hayyacina.
"Rammu! Zo ki ɗauki abinci ki ci."
Na tashi na nufi inda take, ta miƙo min abinci wanda ya yi sanyi ƙalau. Na karɓa, ina jin kamar tunanin da nake yi bai bar ni ba.
Na kalli abincin, sai na tuna cewa ko ban ci ba Banda wani da yafishi Na amsa ne kawai ba dun Raina naso ba sai dun Banda yanda xanyi
Na zauna na fara ci, domin ko a haka ma, na gode wa Allah.
Domin a wurin Gwaggo, wani lokacin yunwa ce kawai za ta kashe ni. Amma Mama, ko da yake ba kullum take ba,ni ba sau da yawa ta fimin Gwaggo.
Na ci gaba da cin abincin a hankali, ina tunanin rayuwata. Ashe rayuwa haka take? Wani ya samu kulawa ba tare da ya nema ba, wani kuma sai ya gode da ɗan abin da aka ba shi, ko da kuwa ba yadda yake so ba.
Na gama cin abincin, na ajiye kwanukan a gefe, sannan na share hannuwana. Har yanzu zuciyata cike take da tunane-tunane, amma na san babu amfanin ci gaba da damuwa a kan abin da ba ni da ikon sauyawa.
Na miƙe zan koma inda nake zaune, sai na ji sallamar Babanmu. Yana shiga gidan, na ɗago kai na kalle shi.
Gashi dai, in ka gan shi, za ka ga cewa Babanmu mutum ne wanda ba ya cika kula da iyalinsa yadda ya kamata. Ba ya yawan tambayar abin da muke buƙata, balle ya damu da halin da muke ciki. Ko abinci kuwa, sai ya ga dama yake kawowa.
Wani lokaci nakan yi mamakin irin rayuwar da muke yi a ƙarƙashinsa. Shi ne ubanmu, amma ba kasafai muke samun kulawar da ya kamata mu samu daga gare shi ba.
Na sunkuyar da kaina, na yi shiru ina jiran ya wuce. Amma sai ya tsaya a tsakiyar tsakar gidan, ya kalle ni.
"Ke Rammu! Me kike yi a nan? Kin gama ayyukan da aka ba ki kuwa?"
Na amsa a hankali.
"Na gama, Baba."
Ya gyada kai, sannan ya wuce ciki ba tare da ya ƙara cewa komai ba.
Na koma na zauna a gefe, ina tunanin yadda wasu 'yan matan suke rayuwa cikin kulawa daga iyayensu, yayin da ni kuma kullum nake ƙoƙarin ganin na yi abin da aka buƙata daga gare ni.
Amma duk da haka, ban taɓa daina fatan cewa wata rana abubuwa za su canza ba. Na san ba zan iya sauya halin kowa ba, amma ina roƙon Allah Ya ba ni ƙarfin zuciyar da zan iya jure duk abin da rayuwa ta tanadar min.
Na ɗan lumshe idanuna, ina cikin tunani, sai na ji muryar Babanmu daga cikin ɗaki:
Ke rammu zo nan
Nan take zuciyata ta ɗan buga, na gyara tsayuwata, sannan na ƙarasa zuwa bakin ƙofar ɗakin Baba.
"Ina zuwa, Baba," na amsa a hankali.
Ina shiga ɗakin, na tarar da Baba zaune. Na durƙusa a gabansa, sai ya ɗago kai ya kalle ni.
"Rammu, zo ki zauna."
Na zauna a hankali, ina jiran jin abin da zai faɗa min.
Baba ya ɗan yi shiru kafin ya ce, "Yaya kike? Komai lafiya?"
Na ɗago kaina na kalle shi. Ban yi tsammanin wannan ce zai fara tambayata ba, domin ba kasafai yake tambayata irin haka ba.
"Lafiya lau, Baba," na amsa.
Ya gyada kai, sannan ya kai hannunsa cikin aljihunsa, ya fito da wani abu ya miƙo min.
"Ga wannan."
Na karɓa cikin mamaki, ina kallon abin da ya ba ni. Ban san abin da zan ce ba, sai na sunkuyar da kaina.
"Na gode, Baba," na faɗa a hankali.
Gaskiya, duk da yadda rayuwata take a gidanmu, akwai wasu lokutan da Baba yake nuna min kamar ya damu da ni. Sau da yawa idan zai dawo gida, yakan dawo min da rogo ko wani abu da zan ci. Waɗannan ƙananan abubuwa ne, amma a wajena suna da muhimmanci sosai.
Abin da ya fi ba ni mamaki shi ne, ni ba na yawan roƙon Baba wani abu. Amma idan ya ga dama, yakan tuna da ni ya kawo min abin da zai sa ni farin ciki.
Sai dai abin takaici, ba kowa ne yake jin daɗin hakan ba. Su kuwa, ba sa son su ba ni daga cikin abin da suka samu suka ci tare da 'ya'yansu, duk da cewa ni ma ɗiya ce a gidan. A wasu lokutan, Baba ne yake tuna da ni ya kawo min abin da zan ci.
Wani lokaci nakan yi mamakin dalilin da ya sa duk abin da ya shafe ni yake zama abin magana. Ni dai ba na neman abin da ba nawa ba, kuma ban taɓa tilasta wa Baba ya ba ni wani abu ba.
Amma duk da haka, idan Baba ya yi min wani abu na alheri, nakan ji daɗi a raina. Ba don abin da ya ba ni yana da yawa ba, sai don a waɗannan lokutan nakan ji kamar ni ma ina da wani matsayi a wurinsa.
Na kalli Baba, ina jin wani irin taushi a zuciyata. Wani ɓangare na raina yana farin ciki da wannan kulawar tasa, yayin da wani ɓangaren kuma yake tunanin dalilin da ya sa irin wannan kulawar ba ta zama abu na yau da kullum a rayuwata ba.
Na sake sunkuyar da kaina, ina riƙe da abin da ya ba ni. A raina na yi addu'ar Allah Ya sa wata rana in samu kulawar da ba sai na jira wani lokaci na musamman ba kafin in ji ana tuna da ni.
Na tashi kenan zan fita daga ɗakin Baba, sai ga Gwaggo ta shigo. Na lura fuskar Baba ta sauya, ya ɗan daure fuska.
Kafin ma in samu damar fita, Gwaggo ta fara ruwan bala'i.
"Malam, kana nuna bambanci!" ta faɗa, tana kallon Baba.
Na tsaya cak a wurin, na kasa fita. Na san maganar ba ta zo a banza ba. Daga yadda Gwaggo Tapito ta fara magana, na fahimci cewa abin da ya sa ta shiga ɗakin shi ne kiran da Baba ya yi min da kuma abin da ya ba ni.
"Malam, kana da yara a gidan nan, amma sai ka zaɓi wadda za ka riƙa nuna wa kulawa. Sauran yaran fa? Su ba 'ya'yanka ba ne?"
Na sunkuyar da kaina, ina jin nauyin kalamanta. Gaskiya, ban san abin da zan ce ba, domin ni ban nemi Baba ya ba ni ko yabani Kuma Ina da haqqi Akan shi
Baba ya kalleta, bai yi saurin amsa mata ba. Ni kuwa ina tsaye a gefe, ina jiran samun damar fita daga ɗakin, amma maganar Gwaggo Tapito ta ƙara tsananta.