Free chapter · Read without an account

Chapter 10

by Rukayya Ibrahim · Duhun da natashi ciki

Kuluwa ta shigo ɗakin, tana taɓe baki, sannan ta ƙaraso inda nake zaune.


“Rammu, lafiya kuwa? Me ya sa kika yi shiru haka? Tun daga waje nake kallonki, kamar kina cikin wani tunani.”


Na yi ƙoƙarin murmushi, na girgiza kai.


“Ba komai, Kuluwa. Ina lafiya.”


Ta zauna kusa da ni a kan katifa, sannan ta zuba min ido.


“Rammu, don Allah ki daina ce min kina lafiya alhali na san akwai abin da ke damunki. Na san halinki tun muna ƙanana. Idan wani abu ya faru da ke, ba kya son ki faɗa wa kowa.”


Na yi shiru, ina kallon hannuna. Ban san yadda zan bayyana mata abin da ke zuciyata ba. Ba na son ta shiga cikin matsalar da ke tsakanina da Gwaggo, musamman saboda na san Mama ba ta son ta kusance ni sosai.


Ta taɓa hannuna a hankali.


“Rammu, Baba ne ya kira ki ɗakinsa ko?”


Na ɗago kai da sauri, ina kallonta cikin mamaki.


“Ta yaya kika sani?”


Ta ɗan yi murmushi.


“Na gan ki lokacin da kike fita daga ɗakin Baba. Na kuma ga fuskar Gwaggo lokacin da kika wuce. Na san ba za a rasa wata magana ba.”


Na sauke ajiyar zuciya, sannan na ce, “Gwaggo ta yi fushi ne saboda abin da Baba ya ba ni. Har ta fara yi masa magana a kaina.”


Fuskar Kuluwa ta sauya.


“To, me ya sa take haka? Ashe ke ba ɗiyarsa ba ce? Me ya sa duk lokacin da Baba ya yi miki wani abu mai kyau, sai ta ɗauki abin kamar kin yi mata laifi?”


Na yi saurin riƙe hannunta.


“Kuluwa, ki yi shiru. Kada Mama ta ji kina magana haka. Kin san ba ta son ki tsaya a gefena.”


Ta ja dogon numfashi, sannan ta kawar da kai.


“Ni dai ba zan daina kula da ke ba, Rammu. Ko Mama ba ta so, ba zan iya kallonki kina shan wahala ba tare da na taimaka miki ba.”


Kalaman nata suka taɓa zuciyata. Na kasa riƙe hawayen da suka cika idanuna.


Ta lura, sai ta matso kusa da ni.


“Rammu, me ya sa kike kuka?”


Na girgiza kai, ina share hawayena.


“Ba komai. Na gode, Kuluwa. Allah Ya saka miki da alheri. Wani lokacin nakan ji kamar babu wanda yake fahimtar halin da nake ciki, amma idan kina tare da ni, sai in ji kamar har yanzu ina da wanda zai saurare ni.”


Ta matse hannuna.


“Ki daina tunanin ke kaɗai ce a duniya, Rammu. Ina tare da ke.”


Na jingina kaina a kafaɗarta, ina jin wani irin sauƙi da ban daɗe da ji ba.


Amma a raina na san cewa wannan ɗan kwanciyar hankalin ba zai daɗe ba. Domin a gidanmu, ko farin cikin da na samu na ɗan lokaci ne, ba kasafai ake barina in more shi ba.


Muna cikin hira da Kuluwa, sai ga Aisha da ƙannenta sun dawo daga tallah. Duk sun gaji, suna ta ƙura-ƙura da goge zufa a fuskokinsu.

Ba su tsaya a ɗakinmu ba. Suna shigowa ne kawai suka wuce kai tsaye zuwa ɗakin Gwaggo, inda suka ajiye kayan tallarsu.

Ni da Kuluwa muka ci gaba da zama a kan katifarmu.

Kuluwa ta kalle ni, ta ce, “Rammu, kina ganin yau ma Gwaggo za ta yi wa Aisha faɗa ne saboda ta dawo a makare?”

Na ɗan girgiza kai.

“Ban sani ba, Kuluwa. Ai ni ban san abin da ke faruwa a tsakaninsu ba.”

Muna cikin wannan maganar ne muka ji muryar Gwaggo daga ɗakinta.

“Aisha! Ina kuka tsaya har yanzu? Me ya sa kuka ɗauki tsawon lokaci haka kafin ku dawo?”

Sai muka yi shiru, muna sauraron abin da zai biyo baya.


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol