Free chapter · Read without an account

Chapter 17

by Narrnarhh Bukar · BA NI DA MADOGARA

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*








 
*Ba ni da Madogara*
  (Sai Allah...)




 



017

Da matuƙar ƙarfi ƙirjinsa ya bada sautin Dummmmmm! Cike da tashin hankali wanda ke bayyane a fuskarsa ya ɗago da sauri yana duban Hajiya momma, a sanyaye ya ce

"Ammie da mara hankali da kamun kai za ku haɗa ni aure?" 

"Wa ya ce maka Tahseen bata da hankali da kamun kai, yarinya mai natsuwa ga sanin ya kamata ka aibata ta" cewar Hajiya momma fuskarta a ɗaure

Kallon Ammiensa yake baya ko ƙyafta ido, ya yi matuƙar mamakinta a ce wacca ta tsana a baya ko sunan Tahseen bata son jin balle uwa-uba maganar auransa da ita. Ko a da can lokacin da ya dawo bautar ƙasa Nijeriya Abba ya so a haɗasu aure da Tahseen tunda tana masifar sonsa amma Ammie ta yi ruwa ta yi tsaki ta hana auran a cewarta ba za ta haɗa jini da mara hankali da natsuwa ba, me ya shiga ran Ammie da ta canja ra'ayinta lokaci guda. What's going on? Anya babu wata a ƙasa kuwa? Sake kallon Ammiensa ya yi fuskarsa a kwaɓe ya ce

"Ammie please give me time to find the choice of my life" 

Ɗaure fuska ta yi tana kallonsa ta ce

"Ka ga duk wani suki-burutsinka ba zai taɓa saka wa mu canja ra'ayinmu akan auranka da Tahseen ba, ka tashi ina so na yi magana da Abbanka" 

A sanyaye ya juya ya kalli Abba ya ce

"Abba yanzu kaima ka aminta na auri mahaukaciya ta haifamin yara taɓabɓu marasa hankali da natsuwa?" 

Duk maganar da ake yi tun ɗazu Abba yana latsa wayarsa bai tanka musu ba, sai yanzu ya ɗago jin Arqam ya kira shi, ɗan murmushi ya yi sannan ya ce

"Arqam me kake so na ce? You mean I should go against the marriage, Kar ka manta da Ramla da ni ubanmu ɗaya, tana a matsayin ƙanwata ce kamar Nafisa. Tahseen tana a matsayin ɗiyar gareni, taya zan ƙi auranku Arqam, Ammm! Ban hana ka nemo w wacca kake so ba za a iya aura mata biyu a rana ɗaya wannan ba laifi ba ne, kai huɗu ka ce za ka aura bamu da damuwa tunda kana da halin ciyar dasu. Amma maganar wai a fasa auranka da Tahseen bata ma taso ba, daman a baya mahaifiyarka ce taso hana faruwar hakan amma yanzu kuma ta amince, Ni kasan tun farko ina son auran sosai. Arqam! "

Kasalallun idanunsa ya ɗago wanda sun canja kala saboda ɓacin rai ya dubi Alhaji ba tare da ya ce komai ba. Alhaji bai damu da yanayinsa ya ci gaba da cewa

"Ka yi haƙuri da zaɓinmu a yanzu, idan anyi auran za ka iya daga baya ka auri wacca kake so, yanzu ka tashi ka tafi mun sallameka" 

Ba tare da ya ce komai ba yabar ɗakin Melonsa na biye da shi, komai baya masa daɗi ji yake kamar ya kwarma ihu don haushi, shi ba wai baya son bin umarninsu ba ne sai dai wacca suke son haɗa shi da ita baya ƙaunarta saboda babu abin da bai sani akan sharholiyar da ta yi a makaranta ba har ta night clubs ɗin da take zuwa duk ya sani, taya zai zaɓar ma yaransa irin wannan uwar. Sosai lissafinsa ya gama kwancewa ya rasa meke masa daɗi a rai. Kai tsaye ya wuce part ɗinsa saboda kansa yana sara masa, Before, jugging ya so yi amma ya fasa zuwa zai kawai wuce ya kwanta ko kansa zai rage yi masa ciwo. 

A can falon Alhaji Hajiya momma ta dubi Alhaji ta ce

"To yanzu zuwa yaushe kake ganin za a tsaida batun auransu?" 

Ɗan jim ya yi sannan ya ce

"Bari zan yi wa Ramla magana anjima ta yi ma mijinta magana zuwa jibi za mu zo batun auran Tahseen da Arqam, don bana so a ɗauki lokaci mai tsawo, tunda ita ma da kammala karatunta tuntuni, in so samu ne kawai a saka auransu nan da wata ɗaya" 

Murmushi Hajiya momma ta yi tana cewa

"Ai ni wata ɗayan ma ya yi nisa, Allah idan da za a bi ta tawa sati biyu zuwa uku sun isa a yi komai a gama tunda kowa a shirye yake" 

Dariya Allah ya yi yana faɗin

"A gaskiya na yi mamakin saurin canjawarki akan auran Arqam da Tahseen" 

Murmushi kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba, miƙewa ya yi ya shiga bedroom ɗinsa ita kuma ta koma part ɗinta. Wannan ke nan

 🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Ƙarfe 7:59pm na dare*

A daidai wannan lokacin Mas'ud da Mahmoud suka shigo part ɗin Arqam kasancewar yau suka yi akan haɗuwar ta su baki ɗaya don su tattauna akan batun Hujayrah da kuma abin da ya dace su yi. Kai tsaye *secret zone* ɗinsa ya wuce dasu don maganar tana buƙatar sirri sosai. 

A daidai wani bangon da ke a bedroom ɗinsa ya tsaya su ma suka tsaya, akwai wani ɗan ƙaramin abu plain a manne a wurin, yatsansa manuniya ya saka a wurin nan take bangon ya ɓanƙaro waje, sai Arqam ya ya ja gefe suka shiga ciki sai bangon mai shape ɗin ƙofa ya koma yadda yake kamar babu ƙofa a wurin. Suna shiga ya kunna wutar ɗakin lokaci guda haske ya karaɗe lungu da saƙo na ɗakin, babu abin da ɗakin ke ƙunshe da shi sai na'urar computer da wasu na'urorin da ban san sunansu ba, a tsakiyar ɗakin akwai kujeru guda uku, na zaman mutum biyu, sai na zaman mutum ɗaya guda biyu. Kasancewar ya yi shekaru da dama bai yi amafani da ɗakin ba, akwai ƙura sosai a ɗakin. Haka nan kowa ya ɗauki handkey ɗinsa ya goge inda zai zauna. Bayan sun zauna sai Mas'ud ya yi gyara murya ya ce

"To Alhamdulillah kamar yadda na faɗa a ranar da ka dawo daga Germany zamu yi zama mu tattauna akan batun wannan yarinyar Hujayrah da kuma dalilin da yasa na ce ya shafemu , sannan dole mu haɗe kanmu mu yi aiki tuƙuru don ganin mun cetota daga halaka da kuma mutane da dama da suka kasance victims"

"Ok muna sauraronka Mas'ud" cewar Mahmoud don ya ƙagara ya ji meke faruwa 

Juyowa ya yi da kyau yana kallonsu kasancewar a kujera ɗaya Arqam da Mahmoud suke zaune. 

" Hujayrah ita ce first victim ɗin waɗannan mutanan, bara na fara muku bayani dalla-dalla yadda za ku fahimce ni da kyau. Akwai wata ɓoyayyar ƙungiya ta yi shekara da shekera a Nijeriya,ƙungiya ce ta matsafa masu shan jini da kuma cin naman mutane, sunfi amfani da yara wurin tsafinsu. Bayan bincike mai tsawo da na yi Allah ya bani ikon gano sunan ƙungiyar ana kiranta da *Black Pythons Society* a cikin ƙungiyar akwai manya-mayan mutane waɗanda suke faɗa a ji a faɗin Nijeriya sannan ita wannan ƙungiya tana da rassa da dama a ƙasashen Africa, yanzu haka har da wasu ƙasashen fararan fata."

Ɗan tsagaitawa ya yi daga bisani ya ci gaba da cewa

"Sai kuma labarin Hujayrah da kuma alaƙarta da wannan ƙungiyar da kuma mu karan kanmu, kamar yadda ta bani labarin rayuwarta, a yadda ta ce min ita ƴar Kaduna ce, suna zaune a ƙauyen Kwanar Faru ƙwai da ke cikin garin Kaduna, su huɗu ne mahaifiyarsu ta haifa amma babban yayanta ya rasu a sanadiyyar kaisa almajiranci da a ka yi, ita ce ta biyu a familynsu sai ƙannanta maza guda biyu. Mahaifinta makaho ne tun tana ƙara Allah ya jarabceshi da cutar makanta. A cewarta a duk cikin dangin mahaifanta ƙanin mahaifinta kaɗai ne ke taimaka musu amma sauran basu taimaka musu da komai. Wani abun ban mamaki da ke tattare da Hujayrah shi ne tana iya gane idan an yi ma mutum asiri, ko kuma idan wuri da asiri she has that sensibility to perceive it"

Waro idanu Arqam da Mahmoud suka yi waje don mamaki, jinjina musu kai Mas'ud ya yi sannan ya ci gaba da cewa

"Bayan haka tana iya tantance mugun mutum da maye a hanyar bugawan zuciyarta, a haka za ku yi tunanin Hujayrah bata da hankali ko ta cika surutu both she is wonderful at all aspect. Bayan haka ta sanar min Kakarta ta bata laƙanin bada magani saboda makantar da mahaifinta ya samu, before shi ke bada maganin. Idan ka duba idanun Hujayrah za ka ga ba irin na mutane ba ne, in fact ko ƴan ƙasar waje da suke da ire-iran idanu masu launi daban da matuƙar wuya a samu exactly kalar ƙwayar idanunta, so this is what lead us to dalilin da yasa na ce labarinta ya shafemu"

Sauke ajiyar zuwa ya yi yana kallonsu wanda su ma shi suke kallon ba ma Arqam kamar ya cinyesa ɗanye haka yake ji don ya matuƙar zaƙuwa ya ji ƙarshe labarin. Can Mas'ud ya ci gaba da cewa

"Yawwa a yadda ta faɗamin tun tasowarta bata taɓa yin saurayi ba" 

Da mamaki Arqam ya ce

"How kamar Hujayrah ka ce bata taɓa saurayi ba?" 

Ɗan murmushi Mas'ud ya yi yana lanƙwasa hannayansa suna bada sautin ƙas! ƙas! Ya dubi Arqam ya ce

"Mr Man why are you so faster than your shadow, I'm still on the way ok, just have patient with me" 

Kallonsa Arqam kawai ya yi bai ce komai ba sai Mas'ud ya ci gaba da cewa

"A yadda ta ce min babu wanda ya taɓa cewa yana sonta balle kuma zancen aure in fact ƙauyen nasu tsoranta suke suna ce mata mai idon mujiya, duk sa'anninta sun yi aure har ta ƙannanta ma sun yi aure waɗanda suke ƴan uwa gareta. Ta ce min akwai wani yayan mahaifinta yana da son abin duniya sosai, shi ya takura wai sai ta fito da miji ita kuma ta ce musu bata da wani a ƙasa, mahaifin babanta ya yi amfani da wannan damar ya aura mata wani mai suna Alhaji Sambo dala, tsoho ne mutumin"

"What!!! You min tana da aure a haka? " cewar Arqam saboda ya yi matuƙar mamaki 

Jinjina masa kai Mas'ud ya yi sannan ya ci gaba da cewa

"Of course Hujayrah na da aure kuma kasan wa take aure? " 

Girgiza kai Arqam ya yi yana kallo sa, ɗan nisawa Mas'ud ya yi sannan ya ce

"Uncle Ayyub" 

Da sauri Arqam da Mahmood suka miƙe a tare kamar haɗin baki suka ce

"Da gaske?" 

Ko a jikin Mas'ud ya ce

"Tabbas babu ƙarya a zancena friends, shiyasa from initial na ce muku you guys are involve har da Kai Mahmoud" 

"How comes Hujayrah ta auri Uncle Ayyub?"cewar Arqam don kansa ya kulle sosai. 

Gyara zama Mas'ud ya yi sannan ya ce

"ku dai ku ci gaba da saurarena Ok, uhmmmm kamar yadda na ce muku Hujayrah a yanzu haka akwai auran Uncle Ayyub akanta, a yadda ta sanar min bayan yayan babanta ya aura mata Alhaji Sambo Dala wanda yake a matsayin Uncle Ayyub ganin mahaifinta baya gani sai Uncle Ayyub ya taho da ita nan Bauchi duk da ta ce min bata san unguwar da ya kai ta ba, sai dai unguwar masu kuɗi ne sosai. Ya mata ƙarya part biyu ne a gidan, akwai na su Momin Akmal a ciki wai da safe zai kai ta su gaisa, bata damu ba suka shiga ciki har bedroom, wani mai aikinsa ya kawo mata abinci, wanda taƙi ci a sanadiyyar rashin yardar da ta yi wa abinci, wayo ta yi kamar ta ci sai da kwanta, a can dare ta ji kamar ana tattaunawa a ɗayan ɗakin, ba ta yi ƙasa a gwiwa ba ta miki quietly zuwa ƙofar ɗakin wanda a nan ta ji komai har da sunnan dodonsu da suke bauta mawa, da harƙallar da suke na fatucin yara wanda har da saka hannun mahaifin bambanta da mai unguwa garinsu, a yadda ta ce min wai zuciyarta da idanunta dodonsu yake buƙata don ya cika sauran aikin da ya rage musu da zamantowarsu masu kuɗi da kuma ɗaukaka a duniya bama Nijeriya ba. Abin da ya sake saka ni shock shi ne har da Senator Daddyn Tahseen a wannan ƙungiyar, da wai demon King ne ko me ma, Yawwa haka ta ce min da demon king, kunsan wane ne demon king ɗin kuwa? "

Girgiza kai suka yi kamar wasu ƙadangaru, miƙa tare da hamma ya yi sannan ya ci gaba da cewa

" Mahaifin Halima ƴar uwata wacce take Maiduguri wato Sheikh Munnir Haladu"

Wata sabuwar gigita suka shiga saboda har Arqam yasan Sheikh Munnir don babban malami ne sosai kuma ana ji da shi a Nijeriya. Cike da mamaki Mahmoud ya ce

"Wai in tambayeka Mas'ud a ina kasu waɗannan labaran, How did you investigate har haka" 

Wani ƙasaitaccan murmushi Mas'ud ya saki sannan ta ce

"I was very very lucky da na yi nasarar yin binciken nan har na iya gano wasu abubuwa da dama, babban nasarar ita ce akwai wani mutumi da na sanshi sosai a nan Bauchi yana da laundry shop, a can nake kai kayana na wanki,sannan mun yi sabo da shi sosai, yana da ɗan uwa da yake a matsayin yaron Uncle Ayyub wanda yake mishi aiki, mun taɓa wannan zancen da shi a baya sai bayan da Hujayrah ta bani labarinta sai a ranar na komai wurinsa tare da tuntuɓarsa, before bai so contributing amma daga baya dana sakar mishi kuɗi sai kawai ya bada kai bori ya hau, a sannan ne na na ji wasu abubuwa da dama ta hanyar shi, amma fa ba wai naga yaron aikin Uncle Ayyub ba ne sai dai a yadda ya ce min, yaron baya ɓoye masa komai akan aikinsu saboda ɗan uwansa ne na jini"

Sauke ajiyar zuciya kowannasu sai Arqam ya ce

" But ita Hujayrah knows kai ɗan uwan Uncle Ayyub ne"

Girgiza masa kai ya yi tare da cewa

"A'a ban faɗa mata haka ba sai dai na ce zan taimaka mata in shaa Allah wanda naga ta yi farin ciki sosai har fuskarta ta kasa ɓoyewa, domin idan na kuskura na sanar mata Uncle Ayyub kawo na ne to za ta iya guduwa ka ga idan ta gudu ta jefa kanta cikin risk ne don za su iya nemota amma idan tana gidanku nasan Uncle Ayyub will never know tunda basa shiri da mahafinka, bayan haka akwai ZOBE da na bata a matsayin kauta sannan na ce mata duk wuya duk runtsi karta bari zoben nan ya bar hannunta saboda every bit of her move I can figure out by that ring, so Shi yasa na yi mata wannan kashedin, duk inda take zan iya sani ta wannan zoben, so in case wani abu ya faru da ita wanda bama fata i can quickly detect through the ring"

Tafi Mahmood ya yi ma Mas'ud yana faɗin

"Excellent one gaskiya hakan shi ne daidai gaskiya, to yanzu what is the way out" 

Ɗan jimm! Mas'ud ya yi sannan ya ce

"Still ina kan bincike shi yasa na ce you guys have to be involved Don ni kaɗai I can't do it" 

"Haka ne" cewar Arqam yana hamma 

"Yanzu zuwa nan da kwana biyar ko sama da haka bayan na kammala bincike zan zo mu san abun yi"

"Ok Allah ya kai mu rai da lafiya, kasan yau Ammie ta taso da zancen aurena da Tahseen I was surprise because before she is against the marriage" 

Murmushi Mas'ud ya yi yana kallon Arqam don yasan tabbas abin da Hujayrah ta ce shekaran jiya shi ne ya fara aiki, ke nan Hajiya Ramla asiri ta yi ma Hajiya momma. Tab! Akwai ƙura a ƙasa kuwa. Dubansa ya yi da kyau sannan ya ce

"Arqam ke nan ai na daɗe da sanin akwai wata a ƙasa, ba haka nan Ammie za ta yarda ka auri Tahseen ba akwai dai wata shiryayyar a ƙasa" 

"Dole ne sai an aura maka wannan mara hankalin ne" cewar Mahmoud yana mamaki. 

Taɓe baki Arqam ya yi sannan ya ce

"Hmmmm wallahi tunda su Ammie da Abba suka sanar min da batun auranmu, na kasa zaune na kasa tsaye don a gaskiya Tahseen ba ajina bace, tana da so many side effect a tattare da ita" 

"Addu'a kawai ya kamata ka yi Allah ya dawo da hankalin Ammie yasa asirin da aka yi mata ya karye" cewar Mas'ud yana miƙe ƙafa. 

Waro idanunsu suka yi waje suna mamaki, murmushi kawai ya sakar musu sannan ya ci gaba da cewa

"Arqam idan har Hujayrah na gidan nan to tabbas asiri ba zai taɓa daɗewa a gidan nan ba, don sai ta nemo inda aka birne ta cire That's her gift" 

"Really!" cewar Arqam

Jinjina masa kai Mas'ud ya yi sai ya ce

"Nima da farko i thought ƙarya take saboda yanayin rawar kanta ya yi yawa, sai lokacin da ta je gidanmu ita da Razina, ta ce min akwai sihiri da yawa da aka birne a gidanmu, na zaci Kawai ta faɗa ne but daga baya ranar da ka dawo Nijeriya muka tafi da ita gidanmu kasancewar babu kowa a gidan, sai muka yi amfani da wannan damar t nuna duk inda aka birne sihiri ni kuma a cire duk asirin da Mom Zinatu ta yi a gidan, kamar mai aljanu haka take tafiya tana dube-dube mu dai muna biye da ita har muka cire komai a gidan, sannan na kira mom ta samemu waje muka nuna mata komai. Sosai ta ji daɗi har da ƙwalla tana gode ma Hujayrah. So Man just calm down everything will be alright OK! Hujayrah na nan na aikinta, za ta taimaka muku da yardar Allah "

Shiru Arqam ya yi yana kallon Mas'ud sai can ya sauke goran ajiyar zuciya ya ce

" No wonder dole ƙungiyarsu Uncle su so cire idanunta da zuciyarta saboda tana ɗauke da baiwa mai tarin yawa wallahi, kai dare ma ya yi sosai fa"

Yana maganar yana duba agogon hannunsa, ganin kusan 10:58pm na dare. Miƙewa suka yi gabaɗayansu suka fito daga secret zone tare da yin sallama kowa ya yi hanyar gidansu.wannan ke nan... ✍️

 🌎🌎🌎🌎🌎🌎

A ɓangaren Hajiya Ramla bayan sun isa gida ko zama bata yi ba ta kira Hajiya Lubna ta ce mata komai take yi ta bar shi ta zo yanzu don akwai matsala babba. Amsa mata Hajiya Lubna ta yi tana nan zuwa yanzu, sai kai kawo Hajiya Ramla take yi a falon, Tahseen na zaune ta yi tagumi kamar wata marainiya hawaye na gangarowa a bisa kuncinta ba tare da ta gogesu ba. Sun daɗe a haka sai kwatsam! suka ji sallamar Hajiya Lubna ta shigo hankali a tashe, ba tare da sun gaisa ba ta ce

"Hajiya meke faruwa ne, wallahi hankalina ya yi matuƙar tashi sosai" 

Sauke ajiyar zuciya Hajiya Ramla ta yi sannan ta ce

"Mene ne ma bai faru ba Hajiya Lubna, ai komai ma ya faru" tana magana tana zama a bisa kujerar mutum biyu, ita ma Hajiya Lubna zama ta yi kusa da ita tana cewa

"Tooo!!! Wani abu ne ya rafu aminiya ?" 

Sai da Hajiya Ramla ta cije lips ɗinta da ɗan ƙarfi sannan ta dubi Hajiya lubna ta ce

"Wai ni Yaya Imrana da Arqam za su yi ma haka?" 

"Me suka yi miki ne Aminiya kin saka ni a duhu gaskiya" cike da zaƙuwa ta yi maganar

Sauke ajiyar zuciya Hajiya Ramla ta yi sai ta ce

"Wai su rasa wacca za su goyan ma baya sai wata tsinanniyar yarinya mai kama da aljanu, gata baƙa siɗik! Kamar baƙin tukunya, tsintacciyar mage akan Tahseen bayan ita yarinyar ce keda laifi" 

"Hajiya bangane wannan labarin naki ba, kawai ki fito fili ki yi min bayanin abin da ke faruwa, ƙara saka ni cikin duhu kike yi wallahi" cewar Hajiya Lubna tana cire gyalenta saboda zafin da take ji duk da sanyin A.C da ke aiki a falon. 

"Hajiya Lubna bari ki ji na yi miki yadda za ki fahimce ni da kyau. Akwai wata ifriɗiyar yarinya da Hajiya Mubina take riƙo yanzu, basu san daga inda take ba suke zaune da ita. Kinsan jiya ne Arqam ya yi birthday da kuma murnar dawowansa Nijeriya, toni ma naje sai wurin magrib na koma gida. Da yake sun shirya party after isha'i daman Tahseen tana can gidan, wurin ƙarfe tara da wasu mintuna ina chatting a waya sai na ga kiran Salame, da mamaki a fuskana na ɗauki kiran. A nan take sanar min da yarinyar ta zuba ma Tahseen karara a jiki lokacin suna tsakiyar fili suna rawa Tahseen na nan tana soshe-soshe"

"Karara? Me ta yi mata haka da za ta mata wannan muguntar?" 

Taɓe baki Hajiya Ramla ta yi sannan ta ce

"Ni na sanin ma shegiya, Ina katse kiran Salame sai ga kiran Nazima ta sanar min suna asibiti da Tahseen tana ƙaiƙayin jiki, wallahi hankalina ya yi matuƙar tashi, a daren na tafi asibitin tare muka kwana ni da Sakhiyya a asibitin sai da safe aka sallamemu bayan mun dawo mun je part ɗin yaya a yi hukuncin, kowa na zaune har da Arqam da shegiyar matanar nan Hajiya Izzatu ta yi baka-baka tana jiran ta ji ya za ta kaya. Hmmmm! Abin ban takaici wai ni Yaya da Arqam za su watsama ƙasa a ido, su goyi bayan ƴar waje su ƙaryata Tahseen wai ita ce keda laifi, ki ji fa yarinya na shirin illata min ɗiya amma basu ga wannan ba sai goyon bayanta suke yi musamman Arqam wallahi a lokacin ji nake kamar da ɗauke shege da mari ko zuciyata za ta yi sanyi"

Cike da mamaki Hajiya Lubna ta ce 

"To ita Hajiya Mubina fa? Babu abin da ta ce ne" 

Wani wawan tsaki Hajiya Ramla ta ja sannan ta ce

"Cikon benci ce ita ai, me ta iya cewa kin manta halinta ne, tana zaune kamar dutse babu umm! Babu um um" 

Sauke ajiyar zuciya Hajiya Lubna ta yi sannan ta ce

"Lallai yarinyar nan ita har tana da Izzar yi ma Tahseen wannan abu, hala bata san ko ita wace ce ba, dole mu ɗauki mummunan mataki akanta" 

"Hmmmm Hajiya Lubna ba ita kaɗai ba har da su Arqam da Yaya wallahi wallahi sai na ɗauki mataki babba akansu, sun nuna min bare ita ce mai muhimmanci akan ƴar gida. Za su sha mamakina wallahi" 

Ɗan shiru Hajiya Lubna ta yi kamar baza ta ce komai ba sai can ta ce

"Hajiya Ramla dole mu sake sabon aiki, ba Hajiya kaɗai za mu yi aiki akanta ba, har da wannan yarinyar kuwa" 

"Har da Arqam ai, shi ma dole mu yi aiki akansa, Kin san Allah na daɗe ina tunanin meye dalilinsa na goyon bayan yarinyar nan akan Tahseen, bayan Tahseen ƴar uwarsa ce, why?" 

"Mom kawai a kasheta wallahi na tsani yarinya kamar yadda na tsani ranar mutuwata, I hate her with passion Wallahi! Could you imagine a tsakiyar mutane ta jizgani, ga videos mutane sai yi min suke a lokacin, wallahi ban taɓa jin kunya matuƙar kamar jiya ba, ji nake kamar na mutu, Mom i hate her... "

Bata ƙarasa zancen da ta yi niyyar faɗa ba ta fashe da matsanancin kuka tare da faɗawa jikin Hajiya Ramla, sosai take kuka har da shessheƙa, sai faman shafa bayan ta Hajiya Ramla take yi tana lallashinta. Ta yi matuƙar basu tausayi ga fatar jikinta duk ta yi ja duk da an yi mata treatment mai kyau a asibitin. 

"Yanzu goben za ki ta fi can wurin bokan ko?" cewar Hajiya Ramla tana aikin shafa bayan Tahseen 

"Eh zuwa goben za ni" 

"OK yanzu aikin ba na mutum ɗaya ba ne zai yi, bayan Hajiya Mubina, Arqam ma in so ya yi aiki akansa saboda kin ga shi za ta aura, kar a yi auran ya zo yana wulaƙantata, amma yanzu idan muka mallake zuciyarsa shi kenan sai ya koma yana sonta, sai zaman na su ya yi daɗi. Yaya kuma ƙyaleshi kawai za mu yi don ban da wata chapter da shi, sannan na ƙarshe wannan shegiyar yarinyar kamar yadda Tahseen ta ce a kasheta ni ma na goyi bayan haka, Ina so a ɓatar da ita a doron ƙasa, zuwa anjima zan tura miki million ɗaya a fara aikin, daga baya in bokan ya faɗi kuɗin aikin sai na tura miki sauran"

Jinjina kai Hajiya Lubna ta yi sannan ta ce

"To shikenan hakan za a yi, bara na koma gida akwai wasu ayyuka da nake so na kammala don fara shirin tafiya tun yau, Kin san ƙauyen mutumin akwai shegen nisa wallahi don har rafi sai mutum ya tsallake kafin ya je wurinsa " 

Wato ido Hajiya Ramla ta yi sai ta ce

" To ke nan ba a mota kike zuwa ba? "

" Eh akwai inda nake ajiye motar sai na ƙarasa ciki"

Tana maganar tana miƙewa tare da yafa gyalenta sai ta ɗauki jakarta suka yi sallama tabar gidan, Hajiya Ramla ta ci gaba da lallashin Tahseen tana bata baki.wannan ke nan... ✍️


 🌎🌎🌎🌎🌎🌎

A ɓangaren Hajiya Nafisa tun a ranar da Hujayrah ta cire waɗannan asiran da aka birne ta fara ganin canji a gurin Prof. Sosai da shiga mamaki abun sai ka ce almara, wai ita ce da kwana ɗakin Prof har wani abu ya shiga tsakaninsu na auratayya, rabon da Prof ya nemi hakƙinsa daga gareta tun lokacin Mas'ud na ɗan shekera goma a duniya, ranar farin ciki sosai ta shiga tana ƙara godewa Allah da kawo Hujayrah cikin rayuwarsa har ya bata Ikon taimaka mata. Su kansu Mas'ud da Nazima sun ga canji sosai a wurin Prof not like before da gaisuwa kawai take haɗasu amma a yau har da hira da dariya suke yi. Lallai Allah shi ne ma ji roƙon bayinsa, haƙiƙa Hajiya Nafisa ta daɗe tana roƙon Allah ya kawo Mata ɗauki a cikin al'amuranta, sai gashi kwatsam! Allah ya kawo Hujayrah ta taimaketa. 

A washe garin ranar ne Hajiya Zinatu da dawo ita da Nadiya da yake Naila na boarding school a final year ɗinta, shi kuma Rayyan yana can da abokansa suna shaƙatawarsu da kayan maye da ƴan mata, basu wannan hotel ɗin in basu wancan. 

A ɓangaren Hajiya Zinatu ta dawo sai ta kasa zaune ta kasa tsaye don suna shigowa cikin gidan gabanta ya yanke ya faɗi a nan take tasan akwai matsala, ba dai ta ce ma kowa komai ba amma kuma hankalinta ya tashi y haka nan ba tare da sanin dalili ba. Gabanta sai faɗuwa yake ga gumi da yake tsattsago mata a duk ilahirin jikinta. Nadiya ce ta shigo bedroom ɗin da gudu tana faɗin 

"Mom! Mom!" 

Hankali tashe Hajiya Zinatu ta yi saurin juyowa gabanta na bugawa da ƙarfi ta yi ƙarfin halin cewa

"Lafiya Nadiya kika shigo ɗaki da gudu babu ko neman izini, meke faruwa ne" 

Nadiya da ke dafe da ƙirjinta tana haki ta ce

"Mon akwai matsala yanzu friend ɗin Ya Rayyan ya kira ya ce Ya Rayyan yana can ya haukace saboda ƙwayar da ya sha tafi ƙarfinsa, yanzu haka sun ɗauresa saboda hauka tuburan yake" 

"Yana inaaaa!!!" cewar Hajiya Zinatu tana waro idanunta waje, jikinta na rawa saboda kiɗimewa. 

"Yana can hotel shi da friend ɗinsa" 

Hankali tashe ta ce

"Kira abokinsa yanzu ki ce ya kaisa asibitin mahaukata gamu nan zuwa yanzu-yanzu, ban so ki faɗawa kowa wannan batun just zip your mouth" 

Hannun Nadiya na rawa ta kira abokin yayanta ta sanar masa abin da Hajiya Zinatu ta ce. A can ya ce mata yanzu haka suna hanyar asibiti daman yana so idan nun isa asibitin sai ya kirata. Tambayarsa sunan asibiti ta yi, ba tare da ɓata lokaci ba ya sanar mata sai suka yanke kiran. Duban Hajiya Zinatu ta yi tare da faɗa mata sunan asibitin da aka kai Rayyan. Da sauri ta ɗauki gyalenta daman bata daɗe da ajiye shi ba, sai ta yafa suka bar gidan kai tsaye asibitin da aka kai Rayyan suka nufa. 

*Wace ce Hajiya Zinatu*

Hajiya Zinatu babbar ƙawa ce ga Hajiya Izzatu wato Hajiyan sama, aminai ne na ƙut da ƙut, baka taɓa jin sirrinsu, tun suna ƴan mata suke tare da yake ƙauyansu ɗaya. Halinsu kusan ɗaya da Hajiyan sama sai dai ita Hajiyan sama ta fita iya taku, ƙarya ne mutum yasan ainihin wace ce ita, saboda makira ce ta ƙin ƙarawa ga kissa da kisisina duk ta haɗa koma bayan Hajiya Zinatu wacce bata da wannan halin sai dai akwai iya mugunta da bin malamai. Kasancewarsu ƙawaye sai suka aure abokai sai ƙawancen nasu ya ƙara ƙarfi sosai. 

Hajiya Zinatu tana da yara uku, mata biyu da namiji ɗaya wanda ya kasance babba, Rayyan, Nadiya sai Naila autarsu. Sannan ita ce kishiyar Hajiya Nafisa wacca take ƙanwar Alhaji Imrana. Tun auran Hajiya Nafisa da Professor Abdulrahman Hajiya Zinatu take biye biyan malamai don ganin Hajiya Nafisa bata haihu a gidan ba, duk da sau babu a dadi Hajiya Nafisa ta yi ɓari sannan ta haihu amma yaro babu rai, sai Mas'ud da kawai Hajiya Zinatu ta gansu da shi, a cewarsu yaranta ne wanda bata san dashi ba,lokacin Hajiya Nafisa da Hajiya Zinatu basa tare. Sosai Hajiya Zinatu ta yi baƙin ciki da ganin Mas'ud wanda tasha kai masa hari Allah na karesa. Bayan Professor Abdulrahman ya gina gidansa babba mai kyau sai ya haɗasu. Wannan shi ne mafarin komai, don duk wani asiri na hana haihuwa Hajiya Zinatu ta yi, tare da birne layu da tarkacen sihiri a cikin gidan. Tun daga lokacin Professor Abdulrahman ya daina kusantar Hajiya Nafisa a lokacin Mas'ud na ɗan shekara goma a duniya har zuwa yanzu da Uwar gayya Hujayrah ta cire dukkanin asirin da Hajiya Zinatu ta birne a gidan. Ƙarin daɗi yaran Hajiya Zinatu dukkaninsu sai a hankali domin bata tsaya ta basu cikakkiyar tarbiyar da uwa take ba yaranta ba, sai yawon bin malamai don mallake miji. Babu laifi haƙarta ta cimma ruwa don Prof. Abdulrahman ta mai dashi kamar bawanta, sai abin da ta ce zai yi shi yake yi ba tare da ya yi mata musu ba. Kasancewar Hajiya Nafisa akwai haƙuri da juriya duk waɗannan abubuwan da ake mata a gidan bata taɓa sanar ma kowa ba, sai dai ta miƙa dukka lamuranta ga Ubangiji gagara misali ya yi mata maganinsu.

*Cikin labari*

Bayan Hajiya Zinatu da Nadiya sun isa asibitin sai suka tarar har an kai Rayyan emergency room Don duba ƙwalƙwalwarsa. Cike da ɓacin rai ta dubi abokinsa ta ce

"Yanzu miye ribar wannan shaye-shayen da kuke,gashi kun sabauta min ɗa bai ji bai gani ba" 

Mamakin maganar Hajiya Zinatu abokan Rayyan suka yi, ɗaya a cikinsu yana a bugen ya ce

"Kai! Ku ji min wannan tsohuwar kilakin fa! Mun taimaka mun kawo yaronki asibiti shi ne kike da bakin ce mana mu muka saka ɗanki shaye-shaye, kun jita fa!" 

Yana maganar yana rangaji saboda a high yake baya cikin hayyacinsa, su kuma sauran suka tintsire da dariya kamar wasu taɓabɓu ba tare da sun ce mata komai ba suka juya abin su suka tafi. Daɓas Hajiya Zinatu ta zauna a saman kujerar da aka tanadar na recipient, Nadiya ma zaunawa ta yi ba tare da ta ce komai ba. Kowa yana na shi Karatun zucin. Suna a haka na tsawan mintuna 40min sai likita ya fito daga emergency roon ɗin yana dube-duben mutanan da suka kawo Rayyan. Da sauri Hajiya Zinatu ta miƙe tare da cewa

"Doctor gani nan ni ce mahaifiyarsa " 

"Ok follow me to my office" Yana gama Cewa ya wuce office ɗinsa, Nadiya da Hajiya Zinatu na biye da shi har cikin office ɗin, zuciyoyinsu na bugu musamman Hajiya Zinatu tana tsoron mai ya samu Rayyan. Wuri ya nuna musu suka zaune a sanyaye suna kallonsa, ɗan rubuce-rubuce ya yi sannan ya ɗago rai ɓace yana duba Hajiya Zinatu, ita ma shi take kallon tana son ta ji me zai ce. Sauke ajiyar zuciya ya yi sannan ya dubi Hajiya Zinatu da kyau ya ce

"Hajiya your son is in critical condition gaskiya domin hard drugs ɗin da yasha sunfi ƙarfin ƙwaƙwalwarsa, akwai probability ɗinsa na zamantowa mahaukaci for his entire life" 

Waro ido Hajiya Zinatu ta yi waje baki sake, ƙirjinta na lugudan wuta, nan take zufa ta fara yi mata sallama a ko'ina na jikinta. Fashewa ta yi da matsanancin kuka, Nadiya ma hawayen take tana ba Mominta haƙuri, shi ma doctor ɗin haƙuri yake bata yana lallashinsa akan everything will be fine. Sai da ta yi kuka son ranta sannan ta ɗago ya jajayan idanunta ta dubi doctor ta ce

"Sir yanzu baku da wani taimako da za ku yi ya dawo normal, please sir do me that favor ko nawa ne zan iya biya in har zai dawo cikin hankalinsa, ka taimake ni na roƙeka" 

Hannu bibbiyu take roƙonsa tana hawaye, shiru doctor ya yi yana nazari, sai can ya dubi Hajiya Zinatu ya ce

"Kwantar da hankalinki Hajiya ba ina nufin ɗanki zai haukace ba ne a'a ina nufin there is probability ɗin haukacewarsa, amma muna saka ran in shaa Allah maganin da muka ɗora shi akai idan ya yi aiki ƙila ya dawo cikin hankalinsa. Sannan za ku bar shi wurinmu na ƴar wasu kwananki saboda a yanzu he is under medication dole mu kula da maganinsu sannan akwai wasu allurai masu ƙarfi da za mu dinga yi masa a kullum na tsawan sati biyu, kar ki damu zamu kula da yaranki sosai, sai dai za ku iya zuwa ganinsa shi ma Not all time because ba a son ya cika magana. Don haka ga number na da kuma takarda kuje pharmacy ku siya magani, sai wannan kuma accountant office za ku ku biya kuɗin gado" Yana maganar tare da miƙe ma Hajiya Zinatu paper da card ɗinsa wanda akwai address da numban wayarsa a ciki. 

Jiki a sanyaye ta yi ma Doctor Godiya Sai ta ce

"Doctor yanzu ba za mu iya dubasa ba?" 

Girgiza mata kai ya yi yana cewa

"Sai zuwa gobe don yanzu baya buƙatar kowa " 

Miƙewa Hajiya Zinatu ta yi ita da Nadiya suka bar office ɗin, Kai tsaye suka nufi pharmacy da accountant office suka biya komai Sannan suka ɗauki hanya zuwa gida wanda kusan bayan isha'i ne. 

 🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Kwanar Faru ƙwai, Kaduna state Nijeriya*

Ɓangaren Murja da sassafe ta dawo gida saboda ta ɗauki kuɗi sannan ta shirya zuwa Ƙwarin ɗan dodo su haɗu har da Inna suje wurin malam Tani mai allon ƙarfe. Tana shigowa gidan ko ta kan ƴan gidan bata bi ba ta wuce sashenta, ba tare data ɓata lokaci ba ta shirya tsaf! Ta fito ko tunanin mijinta bata yi ba balle tasan ina yake ko yana buƙatar wani abu. Samun mai acaɓa ta yi ta tsaida shi sannan ta hau tare da sanar masa inda za ta je.

Babu ɓata lokaci ya kaita kwarin ɗan dodo daidai gidansu Zaliha ya yi parking ta sauka. Bayan ta sallamesa sai ta shiga ciki, su ma a shirye suke sai suka fito tare, wasu mashinan suka samu, nan da nan suka kaisu ƙarshen garin inda Malam Tani mai allon ƙarfe yake. Suna isa bukkar suka tarar da uban layi maza na layi ɗaya haka mata wani Layin, haka suka haƙura har Layin ya zo kansu sai suka shiga a tare. Zama suka yi a inda aka tanadar ma masu zuwa sai ɗakin ya yi shiru, can Zaliha ta dubi Murja tana mata alamu da ido, sai Murja ta kyafta mata ido, juyowa Zaliha ta yi tana duba Malam Tani ta ce

"Allah ya gafarta malam mu..." 

Bata ƙarasa abin da ta yi niyyar faɗa na ya ɗaga mata hannu, ya ce

"Bai sai kin ƙarasa abin da ke ya kawoki nan ba, ba maganar kina so ki mallake Zakari ba ne, ya zamana kome kika ce mishi hakan zai yi babu musu, ko ba haka ba ne?" 

Da sauri Zaliha ta gyaɗa masa kai tana faɗin 

"Haka ne Malam, haka ne wallahi" 

Ci gaba da jan sharɓeban carbinsa ya yi kamar ba zai sake cewa wani abu ba sai can ya ce Zalihan da kyau ya ce

"Za a iya miki aikin sai dai akwai ƙalubale a zamanki tare da shi akwai wani bala'i da yake shirin tunkarosa gadan-gadan, ita matarsa ta gama tsallake wasu matsalolinsa idan kin ji shawarata ki haƙura da auransa don kina son saka kanki cikin bala'i ne, amma idan kin ji kin gani mu namu aiki ne babu ruwanmu"

Ba tare da ta nemi shawarar Murja ko Inna ba, sai Zaliha ta ce

"Eh na ji na gani zan iya auransa a haka" 

Lokaci guda Inna da Murja suka juyo suna mata wani irin kallo, ita kuwa ko a jikin ta sai ma sake gyara zama ta yi tana duban Malam Tani. Wani munafikin murmushi malam Tani ya saki sannan ya miƙe ya ɗauko wani ƙoƙo, dawowa wurin zamansa ya yi, sai ya ciro wata kwalba ƙamara ya miƙa mata tare da cewa

"Wannan ita ce mallakar kar ki yi wasa da ita, turare ne a ciki da zarar ya zo wurinki kafin ki fita sai ki goga a fuskarki kaɗai. A lokacin da ya yi tozali da fuskarki to shi ke nan kin gama mallakesa sai abin da kika ce zai yi shi zai yi, sannan daga ƙarshe ina miki barka da shiga duniyar tashin hankali da bala'i wanda yake cikin gidan Zakari"

Cike da girmamawa ta amsa kwalbar hannu bibbiyu tare da yi masa godiya sai ta ciro kuɗi ta ajiye masa gefe. Zaliha na ajiye kuɗin sai Murja ta gyara zama ta ce

"Allah ya gafarta malam ni..." 

A nan ma ɗaga ma Murja hannu ya yi tare da cewa

"Ba sai kin ƙarasa abin da kika yi niyyar faɗa ba, kina so yaronki mai suna Jabiru wanda ya komai *JABRITY PRINCESS* Kike so ya dawo yadda yake, ko ba haka ba?" 

Jiki ba rawa ta ce

"Eh malam" 

Shiru ya yi ba tare da ya ce komai ba, sai ya ci gaba da zan carbinsa kamar bai san da wanzuwansu a wurin ba, kusan mintuna goma suna a haka baka jin motsin komai sai can ya dubi Murja fuskarsa a ɗaure ya ce

"Aikinki ba zai taɓa yiwuwa ba" 

"Daram! Dam! Dammm! Haka zuciyar Murja ya bada, notikan kanta sun fara kwancewa, hankalinta ya dugunzuma ya yi ƙololuwan tashi, ƙirjinta sai bugawa yake yana bada sautin Fat! Fat! Fat! Ji take duniyar ta juya mata babu sauran komai, hantar cikin tuni ta fara waƙa da rawar wizkid na *ALL MY LADIES* cikinta ya bada sautin ƙulululuuu! Nan take ta fara jin kashi, kai in taƙaice muku Murja bata taɓa shiga tashin hankali irin wannan ba jin aikinta ba zai yiwu ba, ke nan Jabirunt zai dawwama a ɗan daudu. Nan take Murja ta fashe da matsanancin kuka, cikin kukan ya dubi Malam Tani ta ce

"Yanzu Malam babu abin da za ka iya yi a nan"

Girgiza mata kai ya yi sai ya ce

"Babu abin da zan iya saboda ke ce... ✍️









*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
 ***






Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol