Free chapter · Read without an account
Chapter 18
*_The Amazing Pen_ ✍️..........*
*Ba ni da Madogara*
(Sai Allah...)
018
Daram! Dam! Dammm! Haka zuciyar Murja ta bada, notikan kanta sun fara kwancewa, hankalinta ya dugunzuma ya yi ƙololuwan tashi, ƙirjinta sai bugawa yake yana bada sautin Fat! Fat! Fat! Ji take duniyar ta juya mata babu sauran komai, hantar cikin tuni ta fara waƙa da rawar wizkid na *ALL MY LADIES* cikinta ya bada sautin ƙulululuuu! Nan take ta fara jin kashi, kai in taƙaice muku Murja bata taɓa shiga tashin hankali irin wannan ba jin aikinta ba zai yiwu ba, ke nan Jabirunta zai dawwama a ɗan daudu. Nan take Murja ta fashe da matsanancin kuka, cikin kukan ta dubi Malam Tani ta ce
"Yanzu Malam babu abin da za ka iya yi a nan"
Girgiza mata kai ya yi sai ya ce
"Babu abin da zan iya saboda ke ce silar komai, banda makarin wannan asirin, ki tashi ki bani wuri, annamimiyaaa!"
A zafafe ya ƙarashe maganar yana cilla mata wata uwar harara. Jiki na rawa su Murja suka bar ɗakin hankali tashe musamman ita Murja. Koda suka fito kuka Murja take yi sosai su Inna da Zaliha na bata haƙuri. Suna tafiya kafin su samu mashin Murja ta dubi Inna cikin muryar kuka ta ce
"Yanzu Inna shikenan Jabiruna ya koma ɗan daudu gabaɗaya?"
"A'a Murja kin manta Kawunki ya ce yana da wani malamin mai aiki kamar yankan wuƙa,sai muje Maraba daga nan muji ta bakinsa, idan dama taƙi ai sai mu koma hagu. A tunanina za mu samu biyan buƙata a nan shi yasa naga dacewar mu zo nan tunda ba yau ya saba yi mana aiki ba har da Innarki kafin ta rasu, kuma aikinsa na yi sai dai yau na yi mamakinsa wallahi " cewar Inna tana taɓe baki.
Cikin kuka Murja ta ce
"Inna! wallahi ji nake yi kamar duniyar na juyani irin juyin wainar Bauchi, yanzu idan Kawu ya kaimu wurin malamin shi ma ya ce aikin ba zai..."
"A kul ɗinki Murja! Karki ma fara yi ma kanki wannan fatar" Faɗin Inna gyara riƙon ƴar Jakarta.
"Inna zuciyata cike take da tsoro da taraddudi akan wannan aikin" tana maganar hawaye na zuba a bisa kuncinta.
"Ni dai na faɗa miki Murja, ki daina ma kanki mugun fata, atoh!"
Duk wannan hirar tsakanin Inna ne da Murja domin Zaliha ta lula kogin tunanin sahibinta Alhaji Zakari, sai ayyana abubuwa kala-kala take yi a ranta na yadda zamantakewarsu za ta kasance. Ɗan bubbugata Murja ta yi tana faɗin
" Wai ke Zaliha lafiya kike kuwa?"
Kamar wacca aka tsikara firgigit ta dawo cikin hankalinta tana cewa
"Ciwon kai ne ya tasoni gaba daga fitowanmu wurin malam Tani mai allon ƙarfe" zunzurutun ƙarya ta yi ma Murja don ta kare kanta. Murja bata ce komai ba har suka samu masu mashina. Kai tsaye masu mashina suka wuce dasu Maraba bayan sun yi jingar nawa za su biya.
A lokacin da suka isa gidan sai ya yi daidai da fitowan Kawun Murja,turus! Ya tsaya yana kallonsu cike da mamaki. Bayan sun iso wurin da yake sai Murja ta fashe da kuka tana cewa
"Kawu na shiga uku na lalace, malam Tani ya ce Jabrina zai dawwama a..."
"Haba Murja! Wani rashin lissafi ne haka! Kina yi ma kanki mummunar fata, Mts!" Faɗin Inna tana hararar Murja.
"Mu shiga ciki" cewar Kawu yana komawa cikin gidan, binsa suka yi a baya zuwa ƙofar turakarsa, suna isa daidai tsakiyar gidan suka tsaya cak! Cike da mamaki suke kallon Jabiru. Wasu zafafan hawaye suka sake zubo mata a bisa kuncinta, ganin ɗanta mafi soyuwa a gareta a irin wannan yanayi, kwata-kwata an canja masa kamanninsa kamar ba namiji ba, a ranta tana ayyana sai ta ɗauki fansa akansu Hannatu da Zaytuna. Sai dai ayi mutuwar kasko amma sai ta illata rayuwar yaran su gabaɗaya.
"To to! Na ji sai yaushe za mu je bikin gimbiya Yalisar... OK zuwa goben? Haba ai ni ce gaba saboda ni ce babbar ƙawarta, he he heeee! Chases! Ki ce akwai rawar basada da juya kwankwaso" faɗin Jabiru shi kaɗai yana sururunsa yana dariya kamar wani zautacce.
Ƙarasawa cikin ɗakin Kawu suka yi, bayan sun zauna sai Kawu ya dubi Inna ya ce
" To ya wurin wancan malamin? "
" Ai yaya bamu dace ba, ya ce aikin ba zai taɓa warwarewa ba" Faɗin Inna fuskarta shimfiɗe da damuwa.
"Tooooo! Haka abun yake! Tunda shi ya kasa bari na haɗaku da malamina nasan za a dace wurinsa. Sai dai kuma ba yanzu ba gaskiya don ya yi tafiya sai nan da kwana bakwai zai dawo"
Da sauri Murja ta ɗago kanta tana duba Kawu jin yana faɗin ba yanzu za a je wurin malamin ba, cike da damuwa Murja ta ce
"Kawu yanzu babu wani malamin sai shi kaɗai, tunda ba yanzu zai dawo ba mai zai hana muje wurin wani malamin ko za a dace"
"Daɗina da ke Murja gaggawa, in banda abinki nan da kwana bakwai shi ne wani abu, Ni nafi yarda da aikinsa ne gaskiya. Idan kuma kina da inda kike tunanin aikinsa yana yi sai ki je ni ba hanaki na yi ba" a ɗan zafafe ta ƙarashe maganar.
"To Kawu za mu jira ɗin ka yi haƙuri" faɗin Murja ranta a jagule. Bai ce da ita komai ba sai ya dubi Zaliha ya ce
"Ke ya batun auranki"
"Kawu na samu miji Alhaji Zakari zan aura" tana maganar fuskarta da murmushi.
"a'aahhh Alhaji Zakari dai wanda na sani yayan mijin Murja? "
"Eh Kawu"
"Tooo, Ikon Allah ashe ƴar gida za a yi, Allah ya sanya alkhairi"
A ɗan kunya ce ta ce
"Ameen Kawu"
Gyara zama Inna ta yi don magana take so ta yi ma Kawu a game da abin da Malam Tani ya faɗa akan auran Zaliha da Alhaji Zakari.
"Kawu nifa wannan auran da Zaliha take son yi da Alhaji Zakari ban wani amince ba"
Da sauri Zaliha da juyo tana duban Inna, sake ɗaure fuska ta yi sannan ta ci gaba da cewa
"A wurin malam Tani ɗazu da muka je, ya ce akwai bala'in da yake tunkarosa sannan idan Zaliha ta aureshi ita bala'in zai shafa ba uwar gidansa ba, na yi ma Zaliha alamun karta yarda amma ta amince akan Malam Tani ya bata asirin mallaka wanda za ta mallakesa".
Mamaki fal! Ransa ya ya juyo da idanunsa gun Zaliha wacca ta yi ƙasa da kanta tana wasa da ƴan yatsunta. Murya ya gyara sannan ya ce
"Yanzu Zaliha in banda abinki me zai sa ki kai kanki ga halaka bayan kin ji da kunnuwanki abin da boka ya ce, sai ka ce shi ne autan maza da za ki ƙwallafa ranki a kansa, meke damunki ne Zaliha?"
Shiru Zaliha ta yi ba tare da ta ce komai ba Still idanunta na kallon ƙasa, a ranta tana faɗin 'nifa duk abin da za ku ce sai dai ku ce don ina nan kan bakana, aure ne babu fashi sai na auresa na ji daɗi irin na ƴan gayu'
" Ba da ke nake ba Zaliha" da ɗan faɗa-faɗa ya yi maganar.
"Kawu ina sonsa a haka ni dai"
Mamaki ne ya cika su suna kallonta.
"Zaliha bazan so ki shiga walaha ba a matsayinki na ƴar uwata, a da bansan Zakari na cikin bala'i ba na so haɗaku aure tunda naga kina mutuwar sonsa amma yanzu a gaskiya Zaliha ki haƙura da wannan auran don ba alkhairi ba ne tunda Malam Tani ya ce haka" faɗin Murja wanda sai yanzu ta saka musu baki.Tana son ƴar uwarta sannan bazata so wani abu mummuna ya shafeta ba domin kamar ita ce ya shafa.
"Innar Balki ni dai ina sonsa a haka gaskiya, abin da ma aikin Malam Tani baya yi tun da ya kasa taimaka miki, ƙila ma ƙarya yake saboda baya so na dangwali arziƙi " faɗin Zaliha tana zunɓuro baki don ita bazata fasa auransa ba komai zai faru sai dai ya faru.
"To shi kenan ai tunda ke za ki zauna da mijin mu miye namu, Allah ya baku zaman lafiya, an ɗaura auran ne?" cewar Kawu
"A'a Kawu ya dai kawo komai, nan bada jimawa ba za a yi bikin" faɗin Zaliha fuskarta ɗauke da farin ciki.
"Allah ya nuna ma, Ni zan fita kasuwa daman ganinku ya sa na dawo, zuwa nan da kwana bakwai zan turaku wurin malamina lokacin nasan ya dawo sai mu ji ta bakinsa, nasan za a dace" yana maganar lokaci guda yana miƙewa.
Suma miƙewa suka yi suna masa godiya sai suka fito tsakar gidan don su gaisa da matan gidan daga bisani kowa ya koma garin su. Murja cike da damuwa ta dawo gidansu tana tunanin neman wani malamin ko za ta yi dace a warware asirin don ita gaskiya kwana bakwai ya yi mata nisa a yadda take ganin Jabirunta,zama bai ganta ba a yanzu ba, da zarar Jabiru ya komai daidai, za ta maido hankalinta kacokar akan yaran Hannatu, Zaytuna har da Fatsima duk sai ta lalata musu rayuwa kamar yadda suka so illata yaronta. Wannan ke nan... ✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
A ɓangaren iyayen Hujayrah suna cikin kwanciyar hankali basu da matsalar komai sai tunanin halin da ƴarsu Hujayrah take ciki, shin tana cikin farin ciki ne? Ko kuwa akasinsa? A kusan kullum Abbu sai ya yi maganar Hujayrah a gidan, wani lokacin har kuka yake yi yana tunanin a wani hali take ciki yanzu. Tun bayan auranta basu ƙara jin ɗuriyarta ba ko wani ya ce ya ji labarinta. Shi sai a yanzu yake da na sanin wakilta Alhaji Zakari bada auranta,saboda ko sau ɗaya bai ji Alhaji Zakari na zancenta ba. Kamar kullum yau ma yana zaune a bisa tabarmar kaba yana lazumi, Mammi ta kawo masa abincinsa sai ta samu wuri kusa dashi ta zauna. Bayan ya kammala lazumin ya ci abinci sai ta tattare kwanunkan ta fita dasu sannan ta dawo wurin da take da zaune. A sanyaye Abbu ya juyo da kansa inda ya ji motsin Mammi, cike da karayar zuciya ya ce
"Zaytuna har yanzu babu wanda ya ji labarin Hujayrah ko?"
Damuwar da ta daɗe tana ɓoyewa ya bayyana a fuskarta, ita ma kamar shi da tunanin Hujayrah take kwana kuma take tashi, don dai bata da magana sannan bata buɗe cikinta koda kuwa Fatsima ce, ta dai bar ma Ubangiji ya yi ikonsa a kai. Cikin sanyin murya mai nuni da damuwa ta ce
"Babu har yanzu Audu, Ni wannan lamarin na matuƙar damuna, a ce ko wani wanda ya taɓa jin labarinta babu. Sai dai babu yadda za mu yi ne Audu" tana ƙarashe maganar tare da goge hawayan da suka zubo mata da tsumman zaninta.
Sauke ajiyar zuciya ya yi sannan ya ce
"Allah Zaytuna ban taɓa damuwa da rashin ganin nan nawa ba sai yanzu, ban taɓa damuwa da wannan jarabtar da Ubangiji ya saukar min ba sai lokacin auran Hujayrah, ban san waye mijin ba, daga ina yake, waye shi, danginsa, iyayensa, ɗan wani gari ne, wani irin aiki yake duk ban sani ba, na bar ma Zakari wuƙa da nama ya yi komai sai gashi tashi manufar daban take, Ni tsorona Allah yasa ba saida min da yarinya ya yi ba" kuka ne ya suɓuci masa,yana tunanin inda Alhaji Zakari ya kai yarinyarsa don jininsa bai bashi Alhaji Zakari aurar da ita ya yi ba, yana tunanin saidata ya yi, don yasan waye Zakari wurin shege son ƙudi da abin duniya tun suna yara balle yanzu.
"Haƙuri ne ya dace mu yi a yanzu domin mun daɗe da barin gini tun ranar zane, da a ce mun hana auran da yanzu Hujayrah na tare damu hankali kwance, to amma me addu'a ce mafita a gare mu a yanzu,Ni ma ina jin raɗaɗin rashinta a kusa damu. Haushina wai har yanzu Zakari bai buɗi bakinsa ya yi mana maganar Hujayrah ba, alhalin shi ka ɗai ne yasa inda take "
" Ai Ina tunanin gobe zan yi mishi maganar ko kuma bari na faɗama Inna ta yi masa magana da kanta " faɗin Abbu yana ɗaukar carbinsa.
" Allah ya kaimu goben lafiya, Yawwa Fatsima ta ce Musa da Salim zuwa gobe za su dawo gida"
"Allah ya kawo su lafiya, wallahi ina alfahari da Musa domin idan da Allah bai ƙaddara Musa na taimaka mana ba da ban san wani irin mugun hali za mu shiga ba"
"Hakane, Allah ya ci gaba da dafa mana a duk al'amuranu gaba ɗaya, shi kuma ya yi masa jagora"
Amsa mata ya yi da amin sannan suka ci gaba da hirarsu. Wanda suna tsaka da hirar Haroun ya dawo daga wasansa.
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
A ɓangaren Alhaji Zakari komai ya tsaya masa cak! Har wata ƴar rama ya yi,babu abin da ke damunsa irin matsalar da ke tsakaninsa da Alhaji Sambo Dalana ɓatan Hujayrah. Bai ji bai gani ba an samu wani ammanini ya ƙulla masa sharri a wurin Uban gidansa. A ta wani ɓangaren kuwa tunanin yadda Hannatu za ta ɗauki auransa da Zaliha ƙanwar Murja yake yi. Bai san ta inda zai saka ransa ya ji daɗi ba. A yau ya shirya gyara inda za a saka Zaliha, ɗakuna biyu ne zai haɗe wanda a da ƴan matan gidan kafin su yi aure a nan suke kwana, ya kira masu aiki sun yi ciniki sannan ya biyasu don ya faɗa musu ba sai ya duba aikin ba, su dai kawai su yi yadda ya kamata. Bayan ya koma ɗakinsa sai ga Haroun ya shigo sashensu da sallah, Hannatu ta amsa masa fuskarta ɗauke da fara'a ta ce
"Ba dai ka biyo ma Faisal wasa ba?"
"Eh Inna wasa za mu yi, sannan Kakulle ta ce baba Zakari ya zo tana nemansa"
Haka nan ƙirjin Alhaji Zakari ya buga ba tare da yasan dalili ba, ba yau ta saba kiransa zuwa ɗakinta don su tattauna ba amma me yasa a yau daya ji kiran zuciyarsa take bugawa. Miƙewa ya yi ba tare da ya ce komai ya bar ɗakin zuwa ɗakin Kakulle. Shiga ya yi ya samu wuri ya zauna. Sai a sannan ya lura da Abbu wanda yake zaune a gefe. Wata uwar harara ya cilla masa haka nan basu gaira dalili.
"Yau babu gaisuwa ne ɗan Inna"
Da sauri ya juyo daga hararar da yake aika ma Abbu wanda bai ma san yana yi ba ya ce
"Ina wuni inna"
Murmushin dattawa Kakulle ta yi tare da girgiza kai ta ce
"Lafiya lau ɗan Inna, magana ce mai muhimmanci za mu tattauna da kai"
Ɗan shiru ya yi sai can ya dubi Inna ya ce
"Har da Audu za a yi tattaunar batun?" yana maganar yana hararar Abbu ta wutsiyar ido.
"Eh, to ai shi ne maƙasudin tattaunar ta mu"
"Toooo! Ina sauraranki Inna"
Gyara zama ta yi sannan ya fara magana
"Ba komai ya taramu a nan ba sai maganar Hujayrah"
Da sauri Alhaji Zakari ya ɗago yana duba Kakulle, gabansa sai faɗuwa yake, zuciyarsa na bada sautin Fat! Fat! Fat! Bai san akan me za a yi maganar Hujayrah ba amma yasan akwai matsala don shi ko yankasa za a yi bai san inda Hujayrah take ba. Sannan ko wurin Uban gidan nasa Alhaji Sambo Dala babu labarinta, hasalima shi ake tuguma da guduwa da ita. Ai nan take gumi ya fara tsattsago masa a duk ilahirin jikinsa, ya rasa wannan dalilin bala'i kala-kala sai taso masa suke, daga wannan sai wancan, bai gama da matsalar Murja da Alhaji Sambo Dala ba yanzu ga wani sabon tashin hankali da ɗumi-duminsa. Shiru ya yi bai ce komai ba sai ya sake sadda kansa. Yanayinsa kawai Kakulle ta kalla sai kawai ta ci gaba da cewa
"Kaga anfi wata ɗaya zuwa biyu da auran Hujayrah, ba mu ji labarinta ko Wurinka ba, kai ne wakilinta kuma kai kasan wanda ta aura, don haka ka shirya rana ɗaya za mu je Katsina ni da su Fatsima har da matarka da ƙanwar Zaytuna muga gida don shirun ya yi yawa haka"
Alhaji Zakari bai taɓa shiga tashin hankali irin wannan ba, ɗan sauran lissafinsa da ya rage ya ɓace ɓat! Wata sabuwa in ji ƴan caca, shi da yanzu Alhaji Sambo Dala yake neman ya fito masa da Hujayrah, Ina shi ina tambayarsa inda Hujayrah take. Bai san wace amsa ya dace ya bata ba,ko kuwa ya shirga mata ƙarya ne wanda yasan zai kuɓuta ko kuwa ya sake komawa wurin Malam Tani mai allon ƙarfe a rufe bakinsu kamar yadda aka rufe na Musa. Wai wai wai! Duniya juyi-juyi...
"Ka yi mana shiru ɗan Inna"
Kamar wanda aka tsikara ya yi saurin dawowa cikin hankalinsa, magana ya fara da cewa
"To Inna ai sun yi tafiya amma nan da kwana bakwai za su dawo, jiya muka yi waya da mijinta shi ma ya ce yana so ya kawota don ta damesa tana son ganin ahalinta " Addu'a kawai yake su yarda da maganarsa don idan ba haka ba bai san wace ƙarya zai yi mata ba, yasan kafin nan da kwana bakwai zai san abin yi.
" Ka ce nan da kwana bakwai ɗan Inna? "faɗin Kakulle tana kallonsa da kyau don ta gaskata abin da yake faɗa ko gaskiya ne, ilai yaƙi yarda su haɗa ido saboda yasan Inna tun suna yara tana da saurin gane mutum idan ya yi ƙarya ta hanyar kallon idanunsa ta karanci yanayinsa. Kansa a sunkuye ya ce
"Eh Inna har da Audu ma sai muje dashi"
"Allah ya nuna mana ranar, za ka iya tafiya"
Kamar jira yake ya ji umarnin Kakulle da sauri ya miƙe yabar ɗakin ba tare da ya dubesu ba.
Juyowa Kakulle ta yi wurin Abbu ta ce
"Ka ji dai abin da ya ce ko Audu, mu jira nan da kwana bakwai muga iya gudun ruwansa, nima na gaji da wannan shirun haka, a ce tun bayan auranta ko labarin ta babu Haba don Allah, Ni ban ma yarda da auran da ɗan inna ya yi mata da wannan mutumin ba, ko daginta ya hana a je dasu lokacin da za su tafi, in ba akwai wata manufa ba taya za a yi ya hana ƴan uwanta zuwa inda yake "
Murmushin takaici Abbu ya yi sannan ya ce
" Allah ya nuna mana lokacin, Ni dai fatana Allah yasa Hujayrah tana cikin ƙoshin lafiya"
"Allah ya amsa"
Daga haka sai suka ci gaba hirarsu wanda yawanci akan abin da ya shafi Hujayrah ne da kuma matsalar Zakari na rashin nuna kulawarsa a kai ko dan ba yarinyarsa bace.
A can ɓangaren Alhaji Zakari bayan ya fito daga ɗakin bai koma sashensa ba sai kawai ya fita daga gidan zuwa inda yake zama a can wata gindin bishiya fruit mai yalwataccan iska. Kasancewar akwai wani ɗan ice babba a wurin wanda bishiya ce aka sare sai yake zama a saman icen. Yanzu ma haka a saman icen ya zauna ya zabga uban tagumi ya rasa meke masa daɗi a rai. Inda ya ɗauki wannan ɓangaren ya ƙulla sai can ya koma ɗayan ɓangaren. Abubuwan da ke masa yawo akai sun yi nesa da gaban kwatance, shin matsalar Alhaji Sambo Dala ne zai fara warwarewa? Ko kuwa matsalar da Murja take niyyar saka shi ciki na auran ƙanwanta ko kuma matsalar da a yau ɗin nan ta taso masa? 'Wayyo ni Zakari naga ta kaina' haka ya ci gaba da karanta wasiƙar jaki wanda ya kasa tantance wace matsala ce ya dace ya fara warware sai daga baya ya koma gun ɗayar. (Hmmmm matsala ai baka ga komai ba Alhaji Zakari, Allah baya bacci 🤔🤔🤔)
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
*Legacy Housing Estate, Bulunkutu, Maiduguri, Borno State. Nijeriya*
A yau ne yaran Sheikhu Munnir mata suka zo ziyara kasancewar sun daɗe rabonsu da gidan, daman sun shirya lokaci guda za su zo gidan. Suna zaune tare da mahaifiyarsu suna hira sai ɗaya daga cikin ta dubi mahaifiyarta ta ce
"Mom wai ina Halima ne, naga tun da muka zo ban ganta ba?"
Taɓe baki Mom ta yi sannan ta ce
"Tana can tana mugun halin da ta saba na kuka, taƙi bin zabin da Papynku ya yi mata"
"Ai mom mu ma kamar yadda Papy bai bari mu mun zaɓi wanda muke so, ita ma karku bari ta auri wanda take so, ku ji min shegiya mai suffar mayu" faɗin Maryam tana shayar ya yarinyarta.
Su biyu ne yaran wanda kana ganinsu kaga Mom saboda kaman da suka yi ta ɓaci, bambancinsu kawai shi ne launin fata, don basu ɗauko farin mahaifiyarsu ba sai dai kaminta amma kyawawa ne sosai ga hanci har baka da manyan idanu. Kowaccansu ta yi aura, sannan ta auri mai kuɗi sosai wanda hakan daga tsarin Sheikh Munnir ne, a ƙa'idarsa yaransa basa auran talaka sai mai kuɗin gaske ko kuma sanannan ɗan kasuwa wanda Nijeriya tasan da zamansa, ko kuma ɗan siyasa mai babban matsayi. Yaran Sheikh Munnir shida ne, biyar mata sai namiji ɗaya, babban ɗansa namiji baya ƙasar, yana Misra karatun addini, tun yana ɗan shekara 20 Sheikh Munnir ya tafi dashi Mirsa karatu wanda har yanzu bai dawo ba, sai dai ana saka ran nan da ƴan wasu watanni zai dawo Nijeriya gabaɗaya. Haladu shi ne sunansa amma ana kiransa da Babagana, sai Zaynab wacca take binsa tana da yara biyu, Maryam wacca take bin Zaynab tana da yarinya ɗaya sannan Halima wacca ta kasance ba mahaifiyarsu ɗaya ba, sai ƴan biyu masu ƙusumbi Hassana da Hussaina.
"Keda kika san kome Maryam, da ta haƙura kamar yadda muka haƙura da mazajen da Papy ya zaɓa mana, gashi har Allah ya azurtamu ya haihuwa" faɗin Zaynab.
"Baƙin ciki ta kai yi akan duk mazajenku sunfi nata" cewar Mom tana gyara ɗan kwalin kanta. Wari idanu su Maryam suka yi waje sai Zaynab ta ce
"Tab! Ashe kuwa tana da aiki ja wai sarar dawa da haƙori, who is she to compare herself with us, Mts!"
"Barta kawai daman ni na ce Papynku ya aura mata shi don bazan bari ta auri namijin da ya kai naku mazajen kuɗi ba" cewar Mom tana yamutsa fuska.
"Woooow Mom hakan shi ne daidai wallahi" faɗin Zaynab tana murmushi. Ci gaba da hirarsu suka yi wanda yawanci akan Halima ne.
A can ɗakin Halima zaune take a saman gadonta tana chat da Mahmoud kasancewa yau bai da aiki, amfani da wannan damar ya yi wurin nuna ma masoyiyarsa tsantsan so da ƙaunar da yake mata ta hanyar kiranta, har da video call suka yi. Sosai yake ƙara ƙarfafa mata zuciya akan komai zai dede, shi dai kawai ta riƙe alƙwari, duk wuya duk runtsi karta kujesa.Bata san su Zaynab sun zo ba da yake wunin ranar a ɗakinta ta yi, tun bayan saukarta ƙasa zuwa kitchen ta girka abin da take so sannan da hauro sama abinta. Su Zaynab sun so ganin Papynsu kafin su wuce gida amma har yanzu bai dawo gida ba gashi har drivers sun zo ɗaukarsu. Haka Kowaccansu ta wuce gida rai babu daɗi. Wannan ke nan... ✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
*Gidan Abdulrahman Saminu Kwankiyal. Bauchi State Nijeriya*
A ɓangaren Hajiya Zinatu damuwa fal! cikin ranta, cikin dare ma ta kasa bacci saboda tunani yaƙi barinta. Rayyan na kwance gadon asibiti bai san inda kansa yake ba, gashi gabanta sai faɗuwa yake ta kasa tantance abinda ke damunta tun bayan dawowanta gidan daga biki. Idan ta juya nan gefan sai ta juya can gefan. Washe gari da safe bayan ta shirya za ta fita zuwa asibiti wurin Rayyan ita da Nadiya sai taci karo da abin da kusa gigita lissafinta, nan da nan hantar cikinta ta fara kaɗawa a ranta tana faɗin 'Prof da Nafisa a inuwa ɗaya?' murza idanunta ta yi don ta tabbatar da ba mafarki take ba, ilai kuwa Prof ne da Hajiya Nafisa sun fito daga part ɗin Prof suna hira har da raha. Ta gabansu Hajiya Nafisa da Prof suka wuce ba tare da sun ankara dasu ba, kasancewar su Hajiya Zinatu basu riga da sun fito main falon ba. Mutuwar tsaye Hajiya Zinatu ta yi wanda hakan yasa Nadiya girgizata. Firgigit kamar wacca aka tsikara ta dawo cikin hankalinta tare da sauke wata ajiyar zuciya. Wani malolan baƙin ciki ta haɗiye sannan ta juya zuwa sashenta. Nadiya ma bin ta ta yi a baya zuwa part ɗinsu. Koda ta isa falonta kasa zama ta yi sai kai kawo take yi a falon tana cije lips ɗinta da matuƙar ƙarfi kamar za ta cire. Cike da damuwa Nadiya ta dubi Hajiya Zinatu ta ce
"Mom meya faru kika fasa tafiya? Ƙila Ya Rayyan ya farka yana buƙatar ganinki a tare dashi" cewar Nadiya fuskarta ɗauke da damuwa.
Dunƙule hannunta Hajiya Zinatu ta yi tare da bugawa a ɗayan hannun tana cewa
"Dammmn it! Wallahi akwai matsala, dole akwai matsala amma hakan ba zai taɓa faruwa ba in har ba ansamu wani ya cire sihirin da na birne a gidan nan ba, Nadiya?" da ƙarfi ta kira sunanta fuskarta a ɗaure. Cike da sanyi murya Nadiya ta amsa da
"Na'am Mom"
"Tashi ki kiramin Lado mai gadi yanzun nan"
Babu musu Nadiya ta miƙe ta fita, ba a jima ba sai gata da mai gadi sun shigo cikin falon Hajiya Zinatu. A ɗan tsorace Lado yake ganin yanayin Hajiya Zinatu kamar tana cikin ɓarin rai. Hajiya Zinatu na ganinsu ta samu wuri da zauna, bayan Lado ya zauna a bisa centre carpet sai Hajiya Zinatu ta dubeshi ta ce
"Lado!"
A ɗan zafafe ta kira sunansa wanda ya tayar masa da hankali, cikin raunin murya ya ce
"Na'am Hajiya"
"Su waye suka cire abubuwan da na birne a cikin gidan nan"
Nan take hantar cikinsa ta kaɗa,cikinsa ya bada sautin ƙulululuuu! Gumi tuni ya fara keto masa a duk ilahirin jikinsa. Cike da jarumta wanda yake so ya bayyana kar Hajiya Zinatu ta gane tsoransa ya ce
"Abubuwa kuma a gidan nan? A gaskiya bansan komai akan haka ba"
Wani mugun kallo ya jefa masa tare da cewa
"Karka raina min hankali Lado, su waye suka cire abin da na birne a cikin gidan nan?"
A nan ma dake ya ce
"Hajiya nifa bansan komai akan waɗannan abubuwa ba, hasalima ban gabaƙon da ya shigo gi
gidan nan ba tun bayan tafiyanku, su Hajiya Nafisa basa wuni gidan ba saboda dawowan abokin Mas'ud, amma ni bansan komai ba gaskiya"
Kallonsa ta yi na ɗan wasu sakanni sannan a ta ce zai iya tafiya, ba dob ta yarda dashi ba ne sai dai dole ta yi saurin ɗaukar mataki tun kafin wankin hula ya kai ta dare. Zumbur ta miƙe kamar wacca aka tsikara ta suri jakarta Nadiya na biye da ita suka bar gidan. Kai tsaye suka nufi sashen da aka kwantar da Rayyan. Suna isa daƙin wani sabon tashin hankali ya ziyarci zuciyar Hajiya Zinatu ganin Rayyan na hauka tuburan, nurses da wasu maza a ɗakin sun ƙulle shi da kaca a jikin gadon, babu abin da yake sai bibbige-bibbige yana dukan sa a ƙarfan gadon yana ihu. Da sauri Hajiya Zinatu ta ƙarasa inda yake tana rumgumesa tare da fashewa da kuka, babu shiri da sakesa lokaci guda tana duba hannunta wanda haƙoran Rayyan ne jere sunyi round kamar circle, ga jini na fita daga wurin cizon. Sosai ta tsayar da kukanta da take tana kallonsa cike da mamaki ta ce
"Rayyan cizo? Ni Mom ɗinka ka ciza?"
Bai san ma tana yi ba, sai jijjiga gadon yake yana ihu, nan da nan likitoci da wasu nurses suka shigo ɗakin. Mazaje ne suka riƙe shi don ayi masa allura, sun sha daga kafin ya yarda aka yi masa allura da ƙarfin tuwo. Cikin mintunan da basu Gaza goma ba bacci ya ɗauke Rayyan. Sai a sannan ne likitocin suka sauke ajiyar zuciya. Likitan da su Hajiya Zinatu suka je wurin ya ya ce
"Hajiya kibi nurses ɗin nan su wanke miki ciwon sannan su yi miki allurar tetanus sai ki zo office ɗina Ina son ganinki"
Babu musu tabi nurses ɗin, Nadiya na riƙe da jakarta har ɓangaren nurses ɗin, bayan sun wanke mata ciwon sai ta wuce office ɗin Likitan. Suna Zama ya ce
"Hajiya akwai matsala babba a tattare da ɗanki"
Wato idanu waje Hajiya Zinatu ta yi tana duban Likitan. Bai jira me za ta ce ba ya ci gaba da cewa
"Yanzu za ku ɗan ja baya da zuwa asibitin nan, don akwai wasu manyan allurai da za mu bashi, idan Allah ya ƙaddara sai dawo normal fine don 50-50 ne chance ɗin"
"Likiti za ka iya bamu referral zuwa ƙasar India kuwa? don a gaskiya hankali yafi kwanciya idan a can ne, tunda sun fi Nijeriya kayan aiki"
Murmushi Likita ya yi sannan ya ce
"Hajiya ke nan, karki manta wannan asibitin is one of the best hospital Wanda ake ji da ita a faɗin Nijeriya, muna da kayan aikin da a can ƙasar ba lalle a samu ba, in fact mai asibitin nan ba ɗan Nijeriya ba ne idan har akwai yiyuwar kawo wani likita daga ƙasar waje, mu a nan za mu iya samun ƙwararran likitan da zai iya taimakawa. Don haka ki kwantar ta hankalinta kisa a ranki kamar kina Indiya ne"
Yana ƙarashe maganar da murmushi a fuskarsa. Ɗan shiru ta yi sannan ta ce
"Yanzu nawa ne bills ɗinku"
Rubuta mata abubuwan da ake buƙata ya yi sannan kuma ya miƙa mata takardar ya ce ta wuce accountant office ta yi payment Sai daga bisani ya wuce Pharmacy section ta siye abubuwan da ake ji dasu buƙata. Tashi ta yi ta amshi takardar Nadiya na biye da ita suka biya komai sannan ta dawo office ɗinsa ta miƙa masa, sai suka wuce inda ɗakin da aka kwantar da Rayyan, ta window ya kallesa, baccinsa yake kashirɓin, wasu zafafan hawaye ne suka gangaro mata sai kawai ta juyo suka nufi hanyar gida bayan sun hau motarsu. A cikin motar ma tunani kawai take yi tana neman ma kanta mafita, abu biyu ne suke damunta;Na farko ɗanta wanda take addu'ar dawowansa cikin hankalinsa, na ƙarshen kuma abin da idanunwanta suka gane mata a yau, wato Prof da Hajiya Nafisa suna cikin inuwa ɗaya. Dole da tarwatsa zamansu, Prof nata ne ita kaɗai da yaranta, bazata lamunci wata ta kusanceshi bayan ita da yaranta , wannan alƙwari ne dole ta yi wani abu koda kuwa sake komawa wurin hatsabibin bokanta ne mai aiki da sheɗanun aljanu. Haka ta yi ta saƙa da warwara a cikin ranta har suka iso gidan, kai tsaye ta wuce bedroom ɗinta ta haye gado ta kwanta... ✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
*Gida dubu, gubi Housing Estate,Bauchi State. Nijeriya*
A ɓangaren Hajiyan Sama su uku suna zaune a falon sama, fruits salad ne a tsakiyarsu, kowa na ɗiba da spoon ɗinsa Yana kaiwa bakinsa, suna cikin sha ne Fauziyya ta dubi Hajiyan Sama ta ce
"Mom yaushe za k yi ma Alhaji batun aurana da Ya Arqam ne, naga kamar Hajiya Ramla na son Tahseen ta aure Ya Arqam, kar su rigamu Mom". A shagwaɓe ta ƙarasa zancen.
Hajiyan Sama da ke shan fruit ta kai dubanta gareta fuskarta ɗauke da murmushi ta ce
"Daɗina da ke Fauziyya wutar ciki, ki jira ki ga abin da zan yi mana, Ina sane da kitumurmurar da take haɗawa duk don ayi auran Tahseen da Arqam. Da zarar Khalil ya dawo, a daran ranar zan bijiro ma Alhaji da zancen auranki da Arqam, sai Khalil da Nazima, kinga shikenan mun yi tuwona mai na"
Wani daɗi Fauziyya ta ji a ranta, cike da farin ciki ta ce
"Woooow Mom ina godiya sosai, nasan kina magana babu musu Alhaji zai amince da batunƙi"
"Sosai ma Kuwa, don idan bai amince ba ma sai dai kowa ya rasa, bana ƙwallafa rai akan abu ba tare da na sameshi ba, idan har ban san samu abun ba to lalata shi nakeyi ta yadda kowa zai rasa, don haka Khalil na dawo maganar auranku za ta tsaya, kede na ki ido ne"
"Mom to ya za ki yi da shegiyar yarinyar nan Hujayrah mai idon aljannu?" cewar Zahriyya wanda sai yanzu ta saka musu baki.
Wani ƙasaitaccen murmushi Hajiyan sama da saki sannan ta ce
"Banda damuwa da ita don a rana ɗaya zan gama da babinta, kallon ta kawai nake yi don idan naso a yau tabar duniya sai ta barshi ko kuma na saka a ɓatar da ita" (A'uzubillahi ni Narrnarhh🤔🤔🤔 ke! Hajiyan Sama fara istigirafari fari don kuwa kin goce hanyar musulunci, babu mai rayawa da kashewa sai Allah🤔🤔🤔😏😏😏).
"Mom da ita kika fara ɓatarwa daga baya sai ki koma kansu Hajiya Ramla" cewar Fauziyya tana tuno ciwon da ta ji a ranar da Hujayrah ta tunkuɗeta.
Wani murmushi Hajiyan sama ta sake saki sannan ta ce
"Wai meyasa kuke tada hankalinku akan wannan ƙwaron yarinyar da kiyashi yafi min wahalar kisa akanta, nifa ban ɗauketa komai a gidan nan ba, kamar tsoronta ma kuke yi Fauziyya"
"Laah Mom a'a wallahi kawai dai munfi son a fara kawar da ita ne tukunna" cewar Fauziyya a ranta tana faɗin 'Tsoron Hujayrah dole ne kodan waɗannan idanunta'
"Kwadai ji dashi"
Tana maganar takai fruit salad a bakinta. Daga haka suka ci gaba ba hirarsu suna shan fruits salad ɗinsu hankali kwance... ✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
A ɓangaren Hujayrah bayan Lesson teacher ɗin da yake koyar da ita ya tafi sai kawai ta ji sha'awar zuwa garden kallon furanni da shan kayan marmari. Bayan ta yafa ɗan kwalin abayarta sai fito tana ƴan waƙe-waƙenta zuwa garden ɗin. Arqam na zaune a wani ɓangare na garden ɗin yaga shigowanta ciki, kallon kawai yake da mamaki, a ranta yana cewa kome ya kawota ciki oho. Bata kawo komai a ranta ba ta shiga cikin garden ɗin ta zauna inda aka tanadar wurin zama. Kamar wacca aka tsikara ta yi wuff! Ta miƙe ta shiga cikin garden ɗin kasancewa babba ne sosai ga kayan marmari da dama an shukasu a ciki, tafiya take yi tana tsinkan duk kayan marmarin ya yi mata ba tare da ta wanke ba take sha. Kamar ance ta juyo gefen hagunta, waro Dara-daran idanunta ta yi waje ganin Salame tana haƙon rami a gefanta kuma wata ɓaƙar Leda ne a ƙulle. Nan da nan Hujayrah ta ɗaure fuska ta nufi inda Salamen take gadan-gadan. Tana zuwa wurin ta tsaya cak! Hannunta riƙe a ƙugu ta ce... ✍️
*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
***